ABIN CIKIN ƘWAI

25&26

by @rabiattu0444

*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚* 


📃Littafi na 1





By🪶

*®️Ummu maher(Miss green)🍏🍀*

 

 


_*TEAM GAWURTATTU BIYAR 5🔥*_


*Wattpad user name*

  Rabiatu333


*Arewabooks*

rabiattu0444



Ya ku ƴan uwana mu yawaita addu'ar fita daga gida don neman kariya daga sharrin shaiɗanu.

---------------


 25🟩26



. .. . ...Kai tsaye ya wuce gidansu captain,yana isa kai tsaye ya shiga gidan,da kansa yazo ya taresa,Halisa matarsa ta fito suka gaisa harda ɗansa ɗaya wanda sunan Bilal ɗin yaci,Bilal kusan shine hope ɗiin captain ya tsaya masa a komai,shi ne ya nemo masa aiki har yau gashi yana a matsayin captain shiyasa ya ke matuƙar girmama Bilal ɗin,don shi a sahon masu arziƙi masu taimako da gudu zai saka Bilal don mutum ne mai tausayi sosai da kuma son talakawa.


 Abinci Halisa ta kawo musu,ruwan shayin dai ya kurɓa wanda yasha coffie sosai don shi arayuwarsa yana bala'in son shayi da coffie suna ɗan taɓa hira captain ya ce"ah mutumina ni fa tunda na ke da kai ban taɓa ganin ranar da naga kana magana kana dariya ba,sai dai inga ka yi murmushi,to meye sirrin A.D? Ko dai ka kamu ne kaga wata ƴar geton namu".?


 murmushi ya yi sannan ya kurɓi coffie ɗin sannan ya ce"Captain tabbas ka yi gaskiya,don wallahi na ga wata yarinya wacce ta ƙwantamin sosai a zuciyata".



 Dariya sosai captain ya yi sannan ya ce"lallai mutumina wannan wata yarinya ce mai sa'a haka?".


"Hmm captain ni ne dai mai sa'ar don Wallahi yarinyar nan cikin mintina ƙalilan naji ina azabar sonta wanda ban ma san lokacin da ya kamani ba".sosau captain ya ke dariya sannan ya ce"ina ma zan haɗa baki da ita da na ce wallahi kada ta yadda".


 dariya sosai Bilal ya yi sannan ya ce"hmm kaga oga maganar ma da na ke maka yanzu ai har na kai maganar wajen mahaifinta,kuma yarinya ta yaba don haka sai ka nemi wata hanyar".


 har dukan dining table ɗin captain ya yi sannan ya ce"shege mutumina sharp shooter kenan,ka ce har ka kai magana daga haɗuwa yau"?.


 "To zan tsaya ne abuga min ball?ai kai ma kasan ni winner ne akan komai".dariya dukansu sukayi Halisa na ɗaku tana mamakin jin dariyar Bilal haka,duk tsahon tarayyarsu da mijinta bata taɓa ji ya yi dariya ba koda kuwa awaya ne,don mijinta captain yana da ban dariya sosai.



Suna cikin dariyarsu captain ya ce"yauwa A.D ni kuwa ya maganar case ɗinka da Alhaji Damas"?.


 ɓata rai sosai Bilal ya yi sannan ya ce"captain mutumin nan ya zarce duk inda ba ka tunani,mutum ne mai mummunan hatsari,yanzu fa wai so ya ke adole gidanmu ya zama mallakinsa,kuma duk akan case ɗinmu dashi ne ya janyo hakan,amman ni nasan ta inda zan ɓullo masa idan ya san wata bai san wata ba".



 Yana faɗar hakan ya tashi tsaye ya saka hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya ce"ni zan wuce captain Allah ya ƙara sauƙi".


 "Haba mutumina har tafiya?ah to tunda dai ka samu ƴar geto ai dole ka koma gida da wuri"?.dariya sosai Admiral B ya yi sannan ya sanya kyakkyawan glass ɗinsa ba tare da ya ce komai ba ya fita.


 Har mota captain ya rakosa sannan ya koma gida.


       Har yaje gida tunanin jidda kawai ya ke,yana godewa Allah yau ya samu wacce ya ke so muradin ransa.




 Sanda ya sako hancin motarsa muma lokacin muka fito daga cikin gidan,ya wani kallemu ya watsar ya wuce abinsa,na haɗiye wani irin yawu mai zafi.da zanyi da tuni na cire son yaya Bilal araina amman na kasa,kallonsa na ke har ya fito ya wuce sashensa.



 Rashida ta dungureni ta ce"to ya wuce sai ki taho mu tafi?".ta faɗi hakan tana hararata,kunya ta kamani muka wuce gaba.



Muna dawowa daga islamiyya kai tsaye na wuce sashen hajiya kaka,ina shiga na tarar da mutane sosai,muna cikin gaisawa sai kuwa hajiya kaka ta ce"inno kin gane wannan kuwa?".


 "A'ah gaskiya ban gane taba?kinsan rabona da birni na daɗe tun su khairat suna ƙanana".sai kuwa kaka ta ce"ahaf ai wannan i'ta ce khairat ɗin?".gwalalo idanuwa inno ta yi sannan ta ce"ikon Allah girman ɗan mutum babu wahala yau shekara 17 kenan rabona da garin nan tun sunansu,amman kinga yara sunyi wayo".


 ɗan murmushi na yi kawai sai kuwa kaka ta ce"khairat sunzo saukarku ne fa?ga mairo cen don Allah ta zauna a sashenku,tunda ita dai ta dawo nan da zama yanzu,kunga idan tana cikunku za ta ƙara gogewa".kallon wadda aka kira da mero na yi sai kuwa ta ce"hannunki dafatan kina lafiya".nima murmushin na maida mata muka cigaba da hirarmu,na fuskanci mairo aƙwai ƙauyanci sosai akanta.ga ƙiriniya sosai ni kuwa dariya kawai na ke azuciyata don tun yanzu har sun fara faɗa da Hajiya kaka.





****

Su Rashida suna zaune a farlonsu harda mahaifiyarsu sai ga yaya Bilal nan ya shigo,da sauri Su Rashida suka tashi don sunsan karon nasu bai musu ƙyau dashi.


Suna fita hajiya Ruƙayya ta kallesa ta ce lafiya kuwa Bilal".?



 Babu abinda ya ɓoye na dangantakarsa da Jidda,har unguwarsu babu abinda ya ɓoye mata.sosai ta yi murna da jin hakan sannan ta ce"to insha Allah kuwa xan gayawa Babanku idan ya dawo,sai ayi bincike sosai don daga jin labarinta mutuniyar kirki ce sai dai yana da ƙyau binciken.

*****


"wallahi khairat atsorace na ke sosai,don gaskiya ni tsoron rikici ne dani ko yaya ya ke?,ni fa har yanzu ban amsawa yaya Aliyu ina sonsa ba?".



 kallonta na yi sosai sannan na ce"ke dai kawai ki fito kice min bakya son yaya Aliyu?amman ina ruwanki da anty khadija wanine ya ce kada ta riƙe mijinta da ƙyau".?


 Murmushi maryam ta yi sannan ta ce"hmm khairat ko dai ma yaya ne?ai macece ƴar uwata nima kuma bazan so hakan ya faru dani ba".ta faɗi hakan kamar za ta yi kuka.


 "Maryam ni dai don Allah ki taimakeni kiso yaya Aliyu,don wallahi ina jin tausayinsa wannan auren da zaiyu shine zai kawo solution ga dukkanin matsalolin da suke faruwa tsakanin yaya Aliyu da anty khadija".


"Khairat bari in fito miki a mutum sosai kinga nan na daɗe inason yaya Aliyu amman ban taɓa nunawa kowa ba,sai dai in shiga ɗaki inyi kuka idan abin ya dameni,amman duk da haka ina jin tsoron abinda zai faru khairat?kin san ku ƴan uwane ni kuma bare ce acikinku to kinga aure na da yaya Aliyu zai iya kawo matsala tsakanina dashi."


 "Babu wata matsala da zai kawo?".da sauri muka ɗaga idanuwanmu Rashida ce tsaye akanmu tana murmushi ta samu waje ta zauna ta ce"Maryam haƙiƙa na jima ina jiran wannan ranar tazo da wani ɗan gidanmu zai aure ki maryam,kina da tarbiyya sosai da kuma nasaba mai ƙyau babu namijin da zaiso ya auri macen da take da hali irin na anty khadija.tunda har ya buɗe bakinsa ya ce yana sonki don Allah kada ki bawa maraɗa kunya ki yadda musha biki".ta faɗi hakan tana dariya.


 Maryam dai ta kasa ce wa komai,a wani ɓangaren na zuciyarta son yaya Aliyu ne tsan-tsa acikinsa,tsoronta ɗaya anty khadija don ita sam a atsarinta ba zata so ta auri namiji mai mata ba.


 Nan dai mukaci gaba da hirarmu akan saukarmu da kuma bikinsu Rashida,anan ne Rashida ke yi mana albishir da Babansu ya nemo mana admission a makaranta,ni ɓangaren law sai kuma Rashida, nadiya,Iman, khalisat,Bara'atu sai kuma maryam aminiyarmu duk harkar lafiya ne amman kowa da nasa ɓangaren.



 Ni daman tunda na taso ina masifar son karatun lawyer don ina tausayawa talakawa musamman idan suka shigar da ƙara aka yi biris da abin ko kuma a cuce su,ko kuma fyaɗe da akewa ƙananan yara wanda ayanzu ya zama ruwan dare sai dai Allah ya kawo mana mafita.


Soyayyar A.D da jidda sai daɗa haɓaka take,wani mugun son Bilal ne ya ke damun jidda ko bacci zata yi idan ta rufe idanuwanta shi take gani,ta rasa wani irin love take masa.uwa uba ga irin taimakon da ya ke mata ba kaɗan bane,yanzu haka ya bada kuɗi a ruguje gidansu a sake musu wani,daga haɗuwarta dashi zuwa yanzu ya kashe mata kuɗi yafi a ƙirga,ko a mafarki ita jidda bata taɓa tunanin za ta auri miji irin Bilal ba,haƙiƙa tafi kowacce mace sa'a.ga wani irin mugun kishinsa da ke cin zuciyarsa sai take ji kamar duk ranar da ta ganshi da wata mace za ta iya yin komai akanshi.




****



Ina shiga sashen Hajiya kaka na tarar Mero ta tsaya tana wani muzurai,Hajiya kaka na tsaye da ɗan madoki hannunta,tana bin mero ita kuwa mero sai gwaliya take wa hajiya kaka tana dariya tana mata gwalo tana rufe ido.


 Sosai abin ya bani dariya,sai kuwa hajiya kaka ta ƙara biyo mero ji ka ke timm,kaka ta faɗi a tsugunne ta kasance a ƙasa hajiya kaka ta saki kuka ta ce"shegiyar yarinya aljana wallahi na ɗauki masifa tun ba'aje ko ina ba".


 ta faɗi hakan tana fashewa da kuka,sosai na tausayawa hajiya kaka na matso na ɗagata sai kuwa mero ta ce"ai wallahi don baki san yadda na taɓa kada megari bane shiyasa,har rawar banjo na sakasu da na saka musu karara ajikinsu,ni fa wallahi ba'a taɓani in ƙyale".ta faɗi hakan tana yi wa hajiya kaka dariya.


 Abin takaici abin baƙin ciki yarinya ƙarama na caskare hajiya kaka amman ta kasa magana,ina ƴar dariya ta na ce"to wai kaka me ma ya haɗaki da wannan basa mudiyar yarinyar?ai sai taji miki ciwo wallahi".


 Da sauri kaka ta ce"ai wannan shaiɗaniyar yarinya ce ta ƙarshe,wai fa daga na ce ta ɓatamin tap ɗina shikkenan take wannan rashin mutuncin".muna cikin maganar yaya Salim ya shigo fuskarnan a murtuke yasha ɗanyar shaddarsa skye blue ya yi ƙyau sosai don shi daman da Babanmu ya ke kama sosai kamar an tsaga kara.


 Sai kuwa ya ce"a'a Hajiya kaka waye kuma ya taɓa mana ke?".kukan ta cigaba da yi ta faɗa masa duk abinda mero ta yi mata.cikin ɓacin rai ya ce"ke ma kaka ai kinga matsalarki ko wace shara sai ki kama ki ɗakko mana i'ta,ai gashinan yanzu kin ɗebo ruwan dafa kanki".


 Sai kuwa yaji mero ta ce"caɓɓi ai wallahi ko yanzu idan ta yi min wallahi sai na rama,tsohuwa masifaffiya kawai. . .tun kafin ta ƙarasa maganar yaya salim ya ƙwarfeta ta faɗi ƙasa ta hau kuka wai ya bugeta a cikinta,ƙara haurinta ya yi sai kuwa ta tashi zumbur za ta arta ana kare ya cafkota sai kuwa ta rungumesa taba ce wa"don Allah kaji ƙaina ka ƙyaleni wallahi ƙafafunka da guduma aka yi su".



 wani irin shork yaji tunda ga kansa har ƴan yatsunsa da sauri ya saketa yana nuna ta da yatsansa ya ce"to oya! ɗauki bocket kije ki ɗabo ruwa a tap ɗinmu ki cika mata komai ko kuma inyi miki tsinannan duka wawiya ƴar ƙauye kawai.


Sosai ta zabura ta ɗauki bocket ɗin ta fita tana mita,inno da ke cikin ɗaki tana yi wa ƴar ta addu'ar Allah ya shirya mata mero.tunda mero ta taso bata huta da magana ba ita ce ta shiga gonar wane,ta tsokani wane.





Ni na nuna mata yadda ake ɗiban ruwan a tap sannan na wuce sashen maman arman.


Tare da maman arman muka fito sashen Hajiya kaka,sai dai fa muna zuwa naga mero tana kallon kaka tana murguɗa baki,kaka kuwa tana tsaye idanuwanta sun cika,na ce"a'ah hajiya kaka bata gama ɗiban ruwan bane?".


 Kaka ta ce"hmm taya ni baƙin ciki khairat yarinyar nan hawan jini take so ta sakani,yanzu fa tunda ki ka fita babh abinda na gani na alamar an zuba ruwa."


 sai kuwa mero ta ce"anty khairat don Allah zo muje in nuna miki inda na zuba ruwan"binta na yi kamar raƙumi da akala sai me a masai ta zama take ta zuba ruwan".


 sai kuwa mero ta fashe da kuka ta ce"wallahi anty tun ɗazu na ke ta zubawa ya ƙi cika"?sai kuwa ta fashe da kuka.


 Dariya ce ta kamani har da riƙe ciki,lallai na yadda da abinda kaka ta faɗa ƙauyanci da gidadanci sun cika ƙwaƙwalwar mero.




*hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba*







*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*



1, *MU GANI A ƘASA...*🔥

   _Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

   _Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥

   _Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

  _Mrs Bukhari_


 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

   _Miss Hajo_



Guda biyar 1k

Guda huɗu N700

Guda uku N600

Guda biyu N500

Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728

Fatima Rabiu Sunusi

StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


***


Masu tura katin MTN👇


***


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


***


Guda biyar 1000f

Guda huɗu 700f

Guda uku 600f

Guda biyu 500f

Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨



*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


 *Enter your name:* (Cikakken sunanki)


 *Enter your mail:* (Email ɗinki)


 *Enter an username* (Sunanki)


 *Enter your password:* ( misali 12341234)


 *Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


 *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.



*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3



Masu iPhone 


Zaku iya bibiyar shafinmu

 https://arewabooks.com



*miss green ce👉🏿*.