KE CE RAYUWA TA

Three

by @103005574259332015665

🌹KE CE RAYUWA TA 🌹



WOMEN WRITERS ASSOCIA......🖊️🖊️



Mallakar jamila (maman amir)


Wattpad @jami1020


Free page



Three


......... To haka dai rayuwa ta kasance, Samhat tana girma fitinar ta na Kara habaka,ga daurin gindin da take samu daga wajen kakus da iyayen ta maza,saboda wani irin so suke yiwa yarinyar,domin akwaita da shiga rai,Alhaji Karami ne kawai yake tsawatar mata da Mamma, saboda fadan da suke mata sai tace,ita ta dai na kwana a wajen su bangaren kakus za ta koma,saboda haka kakus da kan ta ta zo ta tattara kayan Samhat sannan tasa aka dauka aka Kai bangaren ta.duk Wanda ya tambaye ta,sai tace"ai su Mamma ne da ya Samir suke takura ma ta(dama shi already ya dawo part din su Mamma da zama dakin sa Yana cikin bangaren) sun tsane ta, kakus kuwa ta daure mata gindi. ita ma Hajiya Babba riritata take yi sosai kamar kwai , Mommy kuwa tsanar yarinyar ne ke Kara girma acikin zuciyar ta ,ita tafi son ace Mannira ce ake yiwa haka ba wata ba da ta zo ta takashin baya(hmmm sai dai mu ce Allah ya kyauta yarinya batayi Miki komai ba ki dauki Karan tsana ki daura ma) ta bangaren guda Kuma idan ya Samir ya zo hutu to fa ta shiga uku a gidan, don hana ta sakat ya ke yi, ba Kuma wai magana yake yi ma ta ba ko Kuma duka,idan tana cikin rigirma ta ta idan ya zo wajen to kallon ta kawai zai yi ta shiga taitayin ta domin ita tasan ma'anar kallon,na ka da ki bari na kamaki fa ,ko Kuma za ki sani ne,ko Kuma ya daka mata wata tsawa da sai Yan hanjin cikin ta sun kad'a.to su kan su Yan gidan basa samun salama sai idan ya Samir ya zo hutu,idan kuwa wani laifi tayi, to zai ba ta punishment ne na musamman da sai ta wahala ta jigata sannan ya kyale ta,duk da dai har cikin zuciyar sa ba ya son yadda yake yi mata din,to ya zai yi,ita .... ce sai da wuta to.idan yayi mata wannan punishment din to ana Dan samun hutu na kwana biyu kafin ta cigaba.


     Akwai wani zuwa hutu da yayi ya bar sauran yayyin sa a can suna karatun su,lokacin ne ya gama secondary school,Yana jiran result ya fito ,alokacin kuwa shekarar Samhat goma, Samhat ba ta San da cewa ya dawo gidan ba, ta na zaune a kofar da zaka shiga part din kakus, sai ta hango Mannira ta na tahowa ta Kuma tabbatar nan za ta taho. kawai don mugun ta sai ta dauki oil din da yake hannun ta da take shafawa a kan ta don wai kawai ta bawa kakus haushi ta ce yau ita za ta yi oiling da kanta ba kakus ba, Kakus ta hana ta amman taki.sai ta fito waje tana shafawa ga ta da gashi tubarkalla.


   Samir da yake a tsaye wajen parkin motoci, Yana kallon ta yadda take ta kiciniyar kwance kitson na ta kwaya biyu. sai ya bar duk abinda ya ke yi ya tsaya kallon ta,


  shi haka kawai sai ya ji ba ya gajiya da kallon ta, ko ya ji yana son duk in da yake to ta kasance tana wajen,(Amma shi ya ta'allaka Hakan a matsayin don ya hana ta duk wata fitinar da ta ke yi ne,shi yasa yake jin haka).


  sai ya ga tabar abinda take yi ta tsaya tana murmushin nan na ta shi Kuma yasan menene ma'anar hakan,

  ya tabbata wata muguntar za tayi,sai ta tashi tsaye,oil din da yake hannun ta ta kama yar yadashi a kan tiles din nan in da zaka shiga part din kakus,tana gamawa ko ta daga kan ta ta hango Mannira ta ki ta Kara so sai wani tafiyar yauki takeyi(ita Kuma tana hakan ne gannin ya Samir a wajen ta ga Kuma nan shashin yake kallo ba ta San shi ko kallon ta ma bai yi ba hankalin sa na kan samhat)

    ganin za ta bata mata lokaci sai kawai ta fara kwalla ma ta kira da sauri da Kuma karfi tana cewa"ya Mannira ki zo da sauri,ke in ma za ki iya ki zo da gudu,ya Samir ya turo da wani abu a baki" jin haka ita Kuma sai ta Kara sauri har da dan sassarfa,cikin yanga take Karasowa tana zuwa kuwa ta taka oil din nan sai kuwa ta zame suuuu sai ji kake kwal goshin ta ya bugu,hannun ta da kafar ta ma sun bugu da kasa,ta saki razanan nan ihu, Samhat kuwa me za tayi in ban da dariya har da kwanciyar da rike ciki saboda tsabar ta ga kyeta.


  A guje Samir ya Karaso wajen Yana kokarin ya daga Mannira,samhat tana ganin shi sai ta tsaya cak da dariyar da take yi,sai take mamakin anya kuwa shi ne?don dai a iya sanin ta tasan Yana can America, ba zai yuwu ace daga faruwar wannan abun har ya biyo jirgi ya zo don ceton Mannira ba,sai tasa wa ran ta ai ba shi ba ne kawai imagination ne da wani lokacin in za tayi wata barnar sai ta ga kamar yana nan,sai ta tuno lokacin da Mannira tayi wani tsalle da ta ka man nan ta Fadi sai ta Kara fashewa da wata mahaukaciyar dariya kyalkyalkyal da tayi niyyar yin shuru sai ta Kara tuno sai tasa wata dariya tana yi tana nuna Mannira.

  

  kawai tsayawa yayi Yana kallon yarinyar nan har da su rawa da tsalle tana cewa I am the winner (ko da wa tayi gasar oh 😀)maimakon ya cigaba da taimakon Mannira, sai ya tsaya kallon ta Yana rayawa aran shi an ya kuwa yarinyar nan ba ta da aljanu?.

  Wata tsawa ya daka mata ta tsaya cak tare da zaro ido tana kallon shi sai ta Kara so wajen in da yake a hankali ta kurawa fuskar sa ido sai Kuma ta dan sa dan ya tsanta ta cokali fuskar sa ta ji da gaske shi ne,jin shine sai ta saki uban Kara ta juya aguje ta zo kofar shiga ciki ta Kara juyowa ta ganshi still a tsaya ta sake Sakin Kara ta rugawa a guje tana cewa na shiga ga mala'ikan mutuwa ya zo wayyo Allah zai zo ya dauki Raina kakus kina Ina? Kukus da take lazimi ta ke juyo ihun ta kafin tayi wani abu ta ji an fado jikin ta an kankame ta yadda jikin ta yake rawa ne yasa kakus fara yi mata addua tana tofa mata don ita har ga Allah tunanin ta Gamo tayi,ta Dan dauki miti daya tana yi mata addu'a sannan ta ce "Me ya faru ne samahatu"duk da tana cikin tsoron nan sai da ta Harare ta oh mai hali baya fasa halin sa to naji gayamin menene?kakus mala'ikan mutuwa na gani,kakus tasa dariya tace waye zai iya ganin mala'ikan mutuwa ai sai Wanda lokacin sa yayi,to ni Ina jin lokacin nawa yayi don shi nagani,ke banason hauka wallahi kakus shi na gani,sai abun ya fara bawa kakus tsoro don tasan dai duk shirmen samhat ba ta rantsewa akan karya idan har kaga ta rantse to akan gaskiya ta rantse sai kakus ta fara cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un mun shigo shi je nan lokacin ki ya zo tun da dai ke kadai kika gan shi jin motsi bude kofa samhat tace wallahi gashi nan ya shigo ai kuwa kakus ta rufe idanun ta samhat na cewa ki bude ki gani gashi nan ita Kuma ta na cewa wallahi bazan bude ba ki cuce ni ki sa a dauki rai na yanzu ke dai sa lokacin ki yayi kiyi ta kallon sa ki rinka kalma shahada kad'a ya dauki ranki kina fada... 😂


A can Kuma bayan shigewar ta cikin gida sai da tayi murmushi don abun dariya ya bashi da yake Bai fiye dariya sai sai yayi murmushi,to murmushin kawai yayi,ya taimakawa mannira ta Mike tsaye da kyar sai Kara lanjarewa takeyi tana mitar ya Samir hannuna goshi na zafi wayyo Allah sannu kawai tayi mata Sau biyu Bai Kara ce mata komai ba har ya Kai ta cikin falon dai dai lokacin samhat Ra sake Sakin Kara ta ce shikean ya shigo kakus ki bude ido ki Hana shi daukar raina ,ita ma kakus tana wallahi ba zan bude idona ba na gan shi na ga mutuwa don gidan ku ba zaki rinka Kalmar shahada ba "la ila ha illallahu muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam".........


To fa kujimin iKon Allah ga dai samhat ta rikitar da kukus....sannan ba musan Kuma wani irin hukunci ya Samir zai dauka ba....

Ko me yasa kakus ta bar cikin family house ta koma wani gida can...


     Ku biyo ni don jin wannna labari ka da a barku a baya fa.


In Sha Allah Free pages zai tsaya ne a page 10 sai ku hanzar ta ku biya naku 200 kacal jamila ibrahim zenith bank 2008237969 ki karanta cikin kwanciyar hankali da nishadi da ilmantarwa😘😘😘😘


Love yo all 😘😘😘🌹🌹