Binto

Binto 1

by @fadimafayau

Da sunan Allah me rahma mejin qai.


************

Tunkinta take cikin kwanciyar hankali dan har sakin murmushi take lokaci zuwa lokaci kai kace ba'abinda ke damunta cikin duniya,motar kanta abar kalo ce.


Kamar wadda aka ce tai unguwar kawai ta murda sitiyarin motar zuwa unguwar dorayi, nima dai yau bara inga ya dorayin take ta fada aranta.


Titin qonannen gidan mai tai wanda yai har yan babura ahankula take jan motar gurin ya sauya mata sosai dan ta taba zuwa tun da jimawa, gurin ya sauya sosai ya cika ga jama'a ko ina.


Matasa ne da sauran mutane keta hada-hada a dan qaramin titin wasun su hira suke zazzaune gaban kantunan da ke gefen titin wasu kuwa harkar sa'ar su kawai suke.


Sosai ta qara rage saurin motar koma ta mance a titi take oho hakan sosai yaja hankalun matasan dake ta hada hadarsu, wadanda bamasu da niyar kallonta se sun kalleta.


Kashi tamanin na masu kallon nata zaginta suke wai su za'ama qaryar mota kadan ne kawai ke kalla suyi shiru, yayin da wasu ke fatan dama sune da motar.


Dai dai layin da zata keta taga wata matashiya gaban kasko na suya mutane sun bai bayeta yara ko ina na harkarsu, duda batasan me ake soya wa ba jitai kamar taje ta siya sosai taji sun burgeta ita unguwarsu seka gama yawonka ma baka kowa ba balle yara.


Idanta ne yakai kanwata yar matashi goye da yaro wani tana jansa sosai taji ta burgeta dudu yarinyar batafi sa'ar su taslim ba ina ita ce abinda take fada aranta kenan.


Tazo dedai mararrabar da ke yan kifi tadan kalla gani tai ba wadda tai mata kawai ta miqe zuwa unguwar bello, tama mance da yanma tayi tamance da fadan momy tafiya kawai take hankali kwance.


Unguwar bata kuma birgeta ba seda tashigo unguwar kuka sai take ganin kamar a kauye komai yai mata dai dai da tsarinta, arayuwarta tanasan jama'a kazalika tanasan qauye.


Mai kifin da tagani gabanta kadan yasanya tadan faka motar gaba kadan dashi dan tanasan karfashe sosai balle wannan da kamshinsa ya cika mata hanci, gabaki daya idan yan matansan dake gun kifin yayo kan motar danma basu kula da wadda ke ciki ba.


Bashir ne tadan bugi tsalha da ke zaune baiko kalli inda motar take ba yace kaga wata shegiyar mota ya dan juya ya kalleta gami da dan jan qaramin tsaki, Bashir ka cucen wallahi kasa na baima Uzairu mashin dina jibi yanzu yaqi dawowa kai kuma kana nan kallon motoci.


Rufe bakin tsalha da sun kuyar da kansa ga tunanin mashin dinsa yai dedai da futowarta daga mota, tijjani ya saki wani ashar kut....kai kaga wata halitta tsalha ya dago yadan kalleta gami da sakin dariya kai da kake wannan ashar haka in ance ka kulata zaka iya.


Tijjani yace banga fuska bane anman mazaje ai basa tsoron mace duk kudinta ah lallai aiseka zage kwanji suka saka dariya me kifi da ke ta faman debewa da juyewa yace basshi dai tsalha.


Assalamu Alaikum ta fada cikin muryarta me sanyaya zuciya cikin zumudi su Tijjano suka amsa, kifi nake so dan Allah mai kifi yai saurin baro kaskon yana fadin na nawa ake so hajiya.


Na dubu biyu da dari biyar tace to to ya fada gami da qarawa da manya ko qanana ahadamin duka dan inji wanne yafi dadi dan gaba.


Yawwa gashi hajiya anzuba harda gyara tai dariya aiko ba gyara haka zaka ce da gyara yai dariya hajiya kenan ta zaro dubu uku ta miqa masa gami da daukan kifinta ta juya Habu yai saurin miqa hannu zai amsa kawo akai miki yace tai dariya a'a basshi nagode.


Hajiya canjinki inji mai kifi ta juyo No basshi kawai nagide ai zan dinga zuwa naga guri kodan adinga samin gyara ta fada cikin yanayin barkwanci mai kifi ya hau godiya,Tsalha da tun dazu bai dago ba yai saurin dagowa danjin anbar har dari biyar kodai kunnensa ne beji dedai ba.


Dagowarsa tai dedai da juyowarta wanda hakan yabasu damar kallon juna nadan sakanni taja qafarta tabar wajen.


Kai tsaye gida ta nufa se yanzu hankalinta ya koma gida tasan tabbas zata sha fada gurin Mommy yayin da gefe daya kuma zuciyarta ta cika taf da tunanin matashin saurayin da ta gani gurin me kifi wanda batasan komi kansa ba ko sunansa bataji wani ya kiraba.


Tai sa'a mumy bata nan taslim qanwarta ke fada mata tun rana momy ta tafi unguwa dadi ya cikata kashedi tai ma qannen nata sannan tai daki.


Saida tai wanka tai sallah ta hau kan dinning zata fara cin abinci sannan tama tuna da kifinta.


Kadija qanwarta ta kira dje kinga na sayo kifi na mance shi a mota pls jeki ki dauko mun ki dumamamin shi a oven.


Kai yaya dan Allah waike baki da aiki sai wahalar da mutane ina ba akwai kifin agida ba shine zaki sayo wani wataqil ma kwantai ne, naji ni maza jeki ki dumama min shi ki raba biyu kashi daya kibaima taslim tamin miya dayan ki dansa yai zafi ki kawon kidan yanka masa albasa.


Ta turo baki ni wallahi na gaji gashi kuma an bamu aiki a sch kuma da yawa Binto tai dariya indan aiki ne ki kawao in miki, bata kuma cewa komi ba ta dau makullun motar tai waje rai duk abace.


Abincin ta hau budewa sakwara ce miyar ajuji dadi ya cika ta best food dinta kenan bata jira komi ba tahau ci.


Jin shiru kadija bata kawo kifin ba yasa Binto miqewa tai waje wataqil ma bata je ta dauko ba, baya motar da alamu tama barshi ya gama qonewa tana can tana kallon indian da ta saba ta fada cikin ranta da sauri tai kitchen din.


Ga mamakinta su ta gani sunyi rashe rashe a qas suna cin kifin salame na gefensu suna miqa mata kai da qaya se yar tsoka insun ga dama.


Haushi ne ya cika ta tace oh kwantan kenan kike ci ko inda yai dedai da lunkuma wata qatuwar tsoka da kadija tai abaki cikin irin murya ta wanda yake cin abinci tace kai yaya wannan wane irin kifi ne kwai dadi wallahi.


Taslim tace kema ai fade kike dadinsa ba'a magana salame dake gefe itama cikin muryarta ta yan qauye tace danma ba kansa kuke ci ba sauri binto tai ta dauke farantin da kifin ke kai tai waje.


Biyota sukai suna roqon ta temaka ta basu hakan yai dedai da shigowar momy mene hakan kike gudu kamar wata yarinya ta fada haba momy na siyo abu dan inci anman yarannan sun zauna suna cinye min shine na dauko abuna.


Eyye banda shirme duk kifin dake gidannan sekin sayo wani momy dan baki ci wannan bane na daban ne inji taslim.


Dady(qaramin qanunsu me sunan kakansu) yace nima zanci wallahi Binto taja tsaki Allah yan gidan nan kwadayayyu ne, momy tace eyye karki qara cemusu kwadayayyu kya siyo abu kice bazasu ci ba inkinsan bakyasan bawa kowa ki dinga cinyewa a waje.


Muji irin kifin inji momy din ta dauki guda ta fara ci momy da ke faman mitar akwai kifi agida se gashi ta cinye ta kuma dauka ta cinye ta kuma dauka ganin zata cinye yasa Binto dauke abinta tai daki dady yabi bayanta kan ta dada masa.


Zonan dady inji Momy kyaleta in ta ajiyema Abbanku sai ya baka kasan halinta duk girman nan naka bataqi ta dakeka ba yai dariya maza jeka ka daukon abinci na bazan iya zuwa dinning ba to yace ya miqe.


Sai da hajiya ta cika cikinta da abinci ta dubi taslim tace taslim wai yaushe yayarku ta dawo, Taslim tadan muskuta gami da cewa ai mum baki dade da fita ba momy tadan kalleta kamin tace ok duda ta gano qarya take.


Jin tsaiwar motar Abbansu(me gidan) yasa duk sukai waje har ita momy din kamar koyaushe binto ce ta amso kayansa tana manne jikin baban nata dan sunfi shaquwa dashi kan kowa a agidan suka rankayo sukai ciki cikin farin ciki kamar koyaushe.


Tunda Abban ya gama cin abinci ake labarin kifi kaini na banu ya fada wannan wani irin kifi ne Kadija ta miqe tai kitchen ta dauko wanda binto ta ajiye masa a oven tana tafe tanaci.


Wata uwar harara Binto ta aika mata tai saurin dauke ido gami da maida kifin ganin binton ta dauke ido yasata saurin dauke abinta gami da hadawa da wani dan qarami.


Abba kaji irinsa inji kadijan kai nifa bansan harkar qarni kun sani Binto ta dan bata fuska irin na shagwaba Allah Abba da dadi ya amsa yafara ci.


Binto wai a ina kika sayo kifinnan tai saurin cewa lah Abba a dorayi ne Momy ta saka salati yanzu Binto bakyajin kunyar qarya dazufa a gadon qaya kika ce hanyarki ta dawowa daman nasan baki dawo da wuri ba duk kinbi kin koyawa yara qarya.


Kunya ce duk ta rufe Binto sin sin ta miqe tai dakinta momy da dady suka kalli juna sukai murmushi tabbas yaransu sun shaqu dasu sosai ta yadda ko yaya sukai abin rashin gaskiya basa buqatar su taresu se sun fada musu suna zaune zasu fada in hira tai dadi.


Tun bayan da ta hada kayan lecture dinta na gobe tai nafilfulunta ta fada gado danyin bacci sai daime tafi awa biyu a kwance baccin yaqi zuwa ranta zuciyarta da idanunta cike yake da tunanin matashin saurayinnan da tagani gurin me kifi a dorayi idanunta sun bushe babuma alamar bacci a tattare da su.


Ta dade akwance qannenta su taslim suka zo basu fi minti goma ba ta fara jin saukar numfashinsu alamar sunyi bacci.


Duk yadda taso cireshi aranta ta kasa adazun tayi zaton kamar da ne in taga mutun me kyau taji tana sansa saidai bata ta6a kasa bacci kan tunanin wani ba sai yau.


Wayarta ta dauka ta kunna data tuni messages suka fara shigowa ta WhatsApp yawanci na Isma'il ne duk na neman soyayyarta tsaki taja gami da fita daga WhatsApp din tai Facebook nan dinma shine aranta tai tsaki ta koma Instagram tahau duba hotunan mutane da gajerun videos.


Batafi minti biyar da shiga insta dinba saqon Isma'il ya shigo taja tsaki gami da kashe datar can kuma hawaye ya biyo kuncinta itakanta ta rasa meke damunta tarasa me yasa indai namiji zaice yanasanta sai ta dinga jin haushinsa anman zuciyarta se ta dinga hango mata wasu daban itaman zuciyarta bata mata adalci ba ko kadan....... 


Pls vote,

Comment and

Share.

Binyo


F.A.Ya'u


**********


Batasan sa'adda bacci ya d'auketa ba tana can tana ta saqe-saqen shirme, sai kiran asuba taji koda ta idar da sallah bacci ta koma da yake yau bata da aji da safe, Sai wajen goma ta farka.


Agaggauce tai breakfast sannan ta shirya tsaf ta fito cikin shigarta ta hausawa atamfa ce green super wax ba wata kwalliya tai ba sedai tayi kyau sosai salma taima mum ta fice.


Tana fitowa ta ci karo da yaya Isma'il yana shirin shigowa tana ganinsa ta had'e fuska yayin da shi kuwa bawan Allah gabaki d'aya ya tattaro fara'arsa guri guda adan qagare irin na wadda aka takurawa tace yah "Barka da safiya" dadi ya cika shi ya amsa lafiya qalau qanwarmu.


Yadda yaketa wani washe baki ya qara bata haushi ta rasa me yasa shi baya fishi ko kadan duk abin take masa se kace ba jiya ne ba taga saqunansa sunfi aqirga ba taqi amsa masa ko daya anman duda haka ko ya nuna yaji haushi.


Katse mata tunani yai da fadin "qanwar anfito ne" tad'an ta6e baki gami da turoshi tace "eh" to ko inzo inkaiki" ya fad'a tai saurin cewa a'a basshi kawai ai kaima kana da abinyi yai dariya ganin yadda tai din "to aini bani da wani aiki da ya wuce naki Allah."


Wayyo ni na shi na take fad'e cikin ranta ni wallahi da yah ba d'an uwana bane da se ince maye ne duk cikin ranta take magana bama tasan ta fito fili ba yasa dariya to ai sani ne bakiyi ba tuni na zama mayen saurin toshe bakinta tai tayi waje kunya duk ta rufeta shi kuma yai ciki yana dariya.


Tana tafiya a mota tana dariya wato maganar zuci kan iya fitowa fili kenan.


Yau lecture uku take da ta kammala biyu ta ukun sai yanma wajen uku hakan yasa ta garzaya matattararsu ta yan bautar qasa da yawa suna wajen maza da mata yadda ake firar ne yad'an d'ebe mata kewar matashin da ta gani jiya ad'orayi wanda ta kasa cirema ranta tunaninsa mintina kadan kamanninsa kan fado mata rai.


Ba ita ta fito daga F.C.E ba sai wajen biyar saura hakan yasa take ta sauri dan ta je gida domin tanasan ta had'a questions d'in exam da aka ce ta kawo na students din da take dauka ta yunwa da take mugun ji.


Batai aune ba ta hange su daf da ita suna qoqarin tsallaka titi duk yadda taso kauce musu ina dan gudu take sosai da gudu sauran suka tsallake yayin da dayar ta tsaya diri diri yayin da akai rashin sa'a sai da ta bugeta.


Hankali tashe ta fito daga mota ganin yadda jini ya malale gurin yasata fashewa da kuka kasantuwar yanma ce yasa tuni gurin ya cika da jama'a cikin police d'in da ke zaune nan zone one d'aya ciki ta taso ya d'auki yarinyar yasata cikin motar tata.


Yaran da suke tafe tare biyu ciki suma yace su shiga dan suje suga inda za'a kwantar da ita yayin da sauran yace su je gida su fad'a.


Kasa tuqa motar tayi kuka kawai take dan ita ko kad'an batasan taga jini irin mutanen nance da suke da blood phobia police dinne ya amshi key din yau driving seda ya hau titi yace wani asibiti zamu tace Nasarawa.


Suna zuwa aka amshe ta sabida sunzo da police sa'annan da dama cikin ma'aikatan sun saba da binto sosai, temakon gaggawa aka baima yarinyar seda binto ta tabbatar ta fita daga danger hankalunta yad'an kwanta, se asannan ta kira mum ta fad'a mata.


Bada jimawa ba mum ta iso ita da yah isma'il da abinci se asannan Binto tama tuna wai d'azun yunwa takeji sosai taci sannan tai sallah ta zauna tana kallon yarinyar.


Yarinya ce qarama batafi shekara goma ba anman sabida tsabar rashin kula ace an turota tallah ta dubi sauran yan mayan da suka tawo tare daga ina kuke zuwa nan?


Bilki tace daga garu Binto tadan zaro ido inane garu kuma sukai dariya qauye ne can tace yakai fanshekara sukai dariya ai gaban nan ne sosai towo to me kuke siyarwa nidai Gyad'a ce inji Bilki.


Au ba abu daya kuke saidawa ba eh kowa da abinda yake saidawa ta6 kunqi cin abincin fa suka kalli juna alamar tsoro.


Daqar tasha kansu suka ci, sai bayan isha ta kira Toli qawar service dinta ta roqeta kan gobe ba zata iya shigowa da wurwuri ba zata turo mata questions din ta WhatsApp ta temaka ta mata submitting.


Washe gari da safe bayan kadija ta kawo musu abinci dan Binto qin tafiya gida tai anan ta kwan shima isma'il qeme-me yace ina yana nan bayan sun karya tace kadija ta zauna da kubra ita kuma zata sauke Bilki ahanya seta je gida ta fadi inda suke dan tasan yanxu hankali duk ya tashi.


Haka kuwa akai a malan qato ta sauke Bilkin ita kuma tai gida dan shiryawa ta tafi sch dan tasan yanzu an kusa shiga exam din tata.


Bata wani jima a gida ba tai makaranta dan tanasan taje taga komi yana tafiya dedai.


Ko da Bilki ta isa gida tun abakin titi ta hangi jama'u tsububu ana jiran ganin ta ina zasu bullo yayin da iyaye mata hankalinsu ya tashi sosai dan zatonsu ko an sace su duka ukun mahaifiyar bilki na hangota ta share hawaye gami da yo wajenta haka ma mahaifiyar sahura tambaya take ina sahun take.


Nan ta zayyene musu komi harda qarin bayani kan lefin tsahare ne sunyi sunyi su jata ta maqale kunsan ita wani irin hali gareta.


Iya aikin san asibitin nasarawa ko Tsalha ya tambaya eh ba inda Salamatu ta kwanta ba eh nanfa to ku tawo keda umma Bilki inyaso se in d'auki Bilki a mahin d'ina muje.


Anman ai ka bari ta ci abinci ko inji ummanta Bilki tai saurin cewa wa ni Yau dai kam na qoshi da abincin daza abinci mukaci me rai da lafiya ni binsa zanyi ko nasamu na dare tana fad'e tana d'ane mashin d'in baice komi ba yaja zasu tafi.


Kasan asibitin da girma ina zamu ganku iya tai saurin tambaya yace kinji tace emergency to inda aka fara kai Salamatu kafin asauya mata guri oh oh naji seka bamu kud'in mota yazaro dubu uku ya miqa mata gami da jan mashin d'in dan yanzu se tace bai isa ba shi kuma dubu biyu suka rage masa kar yaje ko se yasai magani.


Binto bata jima a sch ba ta tawo ana gama papers din yan NCE one ta kamo hanya kai tsaye asibitin ta wuce.


Ko da ta dawo cewa kadija tai suje gida ita da sahura tayi wanka kafin Bilki din ta dawo.


Ganin mara lpy tata na bacci yasa itama ta d'an kishin gid'a bakin gadon tuni bacci ya d'auketa.


Tunda Sahura ta shiga motar take zuba qauyanci ta kalli can ta ta6a can dan ba irin motar da suka saba shiga bace.


Bata qara sakin baki ba saida suka shiga gidan tamfatsetsen gida ne na qin qarawa nan dai kasa shiru tai seda tai magana ca6d'i tace kadija tace mene gani nan mu ahe gidajen da muke zuwa talla mugansu na gayu ahe ba komi bane.


Kadija tai dariya kawai sahura ta kuma qarawa mu kan ahe a dajin Allah muke kadija ta sheqe da dariya kai sahura baki da dama kam.


A hankula Bilki ke ta6a Binto da ke bacci ta bud'e idanunta alamun me bacci da sauri ta ware su sosai gani fuskar da tun da ta ganta ta kasa sukuni arayuwarta sai take zaton mafarki take hakan yasa ta maida idanunta ta rufe da zummar ci gaba da baccin ta.


Bilki takai hannu zata kuma tashinta Tsalha yace kyaleta bacci ne a idanta tabbas muryar namiji taji hakan yasa tai saurin tashi gami da gyara zama tad'an saki fuska gami da fadin sannu ko ga guri ta nuna masa daya kujerar da ke gefen gadon tsahare.


Shuru suka zauna na tsawon lokaci ba wanda yace da kowa komi yayin da Binto take da abubuwan fad'e da yawa kwarjininsa ya hanata fade.


Ahankula tsahare ke bud'e idanunta da saure ta bud'esu ganin ta d'orasu kan tsalha dake zaume gefenta cikin qaraji ta fada Baba da sauri shima ya qarasa Tsahare kin farka sannu yarinyar ta fara kuka Baba qafata.


Hankalin binto tuni ya tashi wato ma yanada aure harda yarinya Nikam nashi na.....