NA ƊAYA
by @babanimam
Pam, na zaune a ƙarƙashin babbar bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gonar sa. Ya harɗe ƙafafunsa, ya ɗauki ƙoƙon burkutun da ke gaban sa ya kafa kai yana kurɓa.
Jim kaɗan ya ɗago kansa ya yi wata gyatsa tare da yamutsa fuska, ya ajiye sauran burkutun da ya rage a gefe, yayin da ya ji wata zufa ta keto masa. Wani sanyi ya ratsa gadon bayansa saboda wata iska da ta kaɗa, sakamakon wani hadari da yake shirin haɗuwa.
Lokaci ne na tsakiyar damina, don haka ana samun ruwan sama sosai yanzu. Pam ya yi tunani a ransa, lallai lokaci ya yi da zai tashi haka ya tafi gida, mai yiwuwa matarsa Kaneng ta dawo daga kasuwar da ta ce za ta je cefane, domin kuwa yamma ta fara yi, kuma ga garin yana rufewa.
Ya miƙe tsaye ya fara karkaɗe ƙasar da ke jikin sa.
Pam, matashi ne da ba zai wuce shekaru talatin da biyar ba. Baƙi ne kakkaura, ba shi da tsayi sosai. Magidanci ne da yake da iyali, matarsa Kaneng da yaransa biyu mace da namiji, Noro da Dung. Su ýan ƙabilar Birom ne da ke zaune a wani ƙauye kusa da birnin Jos. Manomi ne sosai, daga damina zuwa rani, yayin da matarsa da wasu ýan uwanta ke taimaka mata wajen sayar da amfanin gonar da aka samu a kasuwanni da kuma gefen titi, inda masu mota ke wucewa suna tafiye tafiye zuwa wasu garuruwa.
Mutum ne mai sauƙin kai da da haƙuri, kuma ba shi da son faɗa ko ƙyamar wani addini ko ƙabila. Duk da kasancewar sa Kirista, amma yana zaman lafiya da makwaftansa Musulmi a gida ko a kasuwa, musamman ma dai Fulani, waɗanda su ne suka fi kusa da ƙabilar Birom wajen zamantakewa, kasancewar suna zama cikin dazukan da ke kusa da su, su da dabbobinsu. Suna haɗuwa a yi zumunci da mazan waɗanda ke fita kiwo ko kasuwa, ko kuma matansu da ke sayar musu da nono da kindirmo.
Tsawon shekaru a haka suka taso suka ga iyayen su da kankaninsu suna zumunci da juna. Har ma an fara samun auratayya a tsakanin su, inda mazan Birom ke auren yaran Fulani mata, su ma haka daga nasu ɓangaren, kodayake ba kasafai ake barin matan Fulani suna auren samari daga ƙabilar Birom ba, saboda bambancin addini. Domin kuwa su Fulani waɗanda akasarin su Musulmi ne, ba sa yarda su aurar da ýar su ga wanda ba ya Sallah, sai dai idan soyayyar ta yi ƙarfi sosai, kuma an kasa raba saurayi da budurwar.
Lokacin da Pam ya miƙe yana goge jikin sa da tsumman rigar da ya rataye a jikin bishiyar mangwaron da yake zama, ya ji alamun wani motsi, amma sai bai kula ba, saboda yana tunanin ko daga can nesa ne, amma da ya ji alamun motsin na matsowa kusa da shi, sai nan da nan ya razana, ya fara dube dube.
Kamar yadda yake zato ashe kuwa hakan ne, ta tsakanin ganyayen masarar da suka lulluɓe gonar ya hango wasu matasan shanu sun shigo gonar suna cinye masa amfanin gona. Cikin zafin nama ya sungumi fatanyarsa ya nufe su da gudu, yana ƙoƙarin korar su. Kafin ya ƙarasa inda suke sun juya suna fita, sai dai kuma bai yi sa'a ba har sun fara cinye masa masarar da ta fara fitar da kai, da tattake masa shukar gyaɗar da ta fara baza ganye.
"Kai...! Kai...!! Wanne wawan bafulatanin ne ya sako min shanunsa cikin gona ta? Wannan ai rashin hankali ne."
Sai da ya kusa fita daga gonar yana bin shanun da jifa yana mita, sannan ya hango yaron da yake kiwon shanun shi ma yana kora su da sandar sa.
Yaro ne ƙarami da bai wuce shekaru goma sha biyu ba. Tun daga nesa ya gano wanene Bello ne yaron wajen Buba na Rugar Shehu.
Ganin yaron yana kora su, kuma shi ma alamun ya tsorata da yadda ya ga Pam ya nufo shi a fusace sai shi ma ya ruga da gudu yana ƙoƙarin barin bakin gonar.
Pam ya tsaya a bakin gonarsa yana ta haki da ƙwafa saboda ɓacin ran ɓarnar da waɗannan shanu suka yi masa. A ransa ya tuna wata shekara da irin haka ta faru, a gonar makwafcinsa Mancha, wanda abin sai da ya so haifar da rikici a tsakanin ɓangarorin Birom da Fulani, da ƙyar suka shawo kan lamarin, amma dole sai da Fulanin nan suka biya diyyar asarar da dabbobin su suka yi.
Suna samun labarin irin yadda ake samun mummunan rikici, da yake haifar da asarar rayuka da dukiyoyi, saboda ganganci irin wannan da kuma rashin hankalin wasu yaran Birom da ke yi wa Fulani sace sacen dabbobi. Sai dai su a nan Dwal ba a taba samun ta kai ga haka ba, amma fa akwai abin fargaba nan gaba, idan hakan ta cigaba.
Ya yi ajiyar zuciya, har yanzu yana jin ƙuncin ɓarnar da aka yi masa a ransa. A fusace ya je ya canza kayana ya ɗauko tsohon babur ɗin sa da ke ajiye a gefe, ya haura zuwa Rugar Shehu, don ya kai ƙara wajen Arɗo Manu, domin gaskiya ba zai lamunci irin wannan ɗanyen kan ba. Alhalin fiye da rabin kuɗin da ya zuba a wannan noman bashin su ya karɓa daga bankin manoman Fadama da gwamnati ta kafa, don ya riƙa tallafawa manoma da basussuka, saboda su samu bunƙasa noman su na rani da na damina.
Ya isa Rugar Arɗo Manu dab da lokacin sallar Magrib, ya tarar da shi da wasu yaran sa matasa su biyu suna alwala za su yi sallah, don haka gaisuwa kawai suka yi sama sama, ya kafe babur ɗin sa a gefe yana jiran su idar da Sallah kafin su yi magana.
Ba da jimawa ba kuwa suka kammala, bayan sun yi addu'a Arɗo Manu, ya ƙarasa har kusa da inda Pam yake zaune a kan babur ɗin sa, suka gaisa. Sannan suka samu wani kututturen ita ce da ake zama a ƙarƙashin wata bishiya suka zauna. Pam ya kwashe labarin duk abin da ya faru ya gayawa Arɗo, ya kuma sanar da shi yaron da yake zargin shi ya kora shanun suka shiga masa har cikin gona suka yi masa ɓarna.
Pam ya lura da yadda fuskar Arɗo ta sauya, kasancewarsa farin bafulatani ya sa nan da nan fuskarsa ta yi ja, duk da yake duhu ya fara shiga, amma za ka fahimci bai ji daɗin labarin da Pam ya je masa da shi ba.
Sai dai a daidai lokacin da ya fara nuna damuwar sa kan ɓarnar da aka yi wa Pam, sai kwatsam suka ji sallama, suna waigawa sai ga Malam Buba nan ya nufo su, hannun sa riƙe da sanda, kansa kuma da hular malafa ta kaba, dogo ne marar jiki, sai dai shi ba fari ba ne kamar Arɗo Manu. Ya ƙaraso kusa da su suka gaisa, yayin da ya samu waje a ƙasa ya zauna.
"Yanzu nake shirin aikawa a kira min kai," Arɗo ya ce masa.
Buba ya ce, "Ai nima yanzu dawowa ta kenan ko zama ban yi ba, ake sanar da ni rashin hankalin da yaro ya yi. Shi ya sa na hanzarta na zo in sanar da kai."
"Yanzu wannan bawan Allah mai gona ya zo yake sanar da ni abin da ya faru," ya yi ajiyar zuciya. "Kun san ina gargaɗin ku kan wannan al'amarin, musamman a wannan lokaci na damina. Ita dabba ba hankali ne da ita ba, haka shi ma yaron da ba shi da cikakken hankali bai dace ana haɗa shi da garken shanu a cikin wannan yanayin ba."
"Gaskiya ne, an yi kuskure. A yi haƙuri." Buba ya faɗa yana kallon fuskar Pam, yana ƙara nuna damuwar sa kan abin da ya faru.
"An san cewa al'adar mu ce bai wa yara kiwon shanu," in ji Arɗo. "Amma lokaci ya canza dole kuma mu yi tafiya da zamani. Don Allah shi ne ya kawo haka. Kuma lallai ne mu riƙa gargaɗi yaran mu, a daina yin nesa da dabbobi, gudun kada su jawo damuwa."
"Wannan babu shakka haka ne," in ji Pam, wanda tun ɗazu yana sauraron su ne kawai ba tare da ya ce komai ba.
Aka yi shiru jim na wasu daƙiƙoƙi, babu wanda ya ce uffan, kafin Buba ya ɗan yi gyaran murya ya ce, "Wato dama ni fa ina da wani abu da ya daɗe yana damun zuciyata, wato matsalar rashin burtalolin kiwo na daga cikin dalilan samun irin waɗannan damuwoyin da muke ciki. Ko'ina ya zama gona ko ya zama gari, dabbobi ba sa sakewa su yi kiwo, mu ma hankalin mu ba ya natsuwa idan an fita da su, saboda fargabar abin da zai je ya zo."
Arɗo ya ce, "Haka ne kam, wannan na daga cikin dalilan da suka sa kullum muke sanar da gwamnati, matuƙar ana son kawo ƙarshen fitintinun da suke faruwa a wasu wurare tsakanin makiyaya da manoma tilas a mayar da hankali wajen duba batun inganta rayuwar makiyaya, kamar yadda ake yi wa sauran ýan ƙasa."
"Kowanne ɗan Nijeriya yana da ýanci daidai da kowa, kamar yadda mu ma muke kukan ba a cika bai wa tsirarun ƙabilu ýancin da hakkin da ya kamata su samu ba." A cewar Pam, wanda yanzu fuskar sa ta fara sakewa da fushin da ya zo da shi.
"Malam Pam," Arɗo Manu ya kira shi da girmamawa. "Ina mai ƙara baka haƙuri, a madadin Malam Buba, wanda ka ga da kansa ya zo ya kawo rahoton abin da ya faru. Dukkan mu ba mu ji daɗin abin da ya faru ba, kuma da yardar Allah ba za mu bari haka ta sake faruwa daga ɓangaren mu ba.
Malam Buba ya ƙara risinawa yana duban Pam. "A yi haƙuri, rashin hankali ne na yara. Za mu ɗauki matakin hana cigaba da faruwar haka."
Arɗo Manu ya ce, "Za mu zo wajen gonar taka gobe da safe, don mu ga ɓarnar da aka yi, sai mu san abin da za a yi na diyya ko?"
"Haka ne. To, ba komai. Allah ya kai mu."
Pam ya tashi, suka yi sallama da Arɗo da Malam Buba, yayin da ya buga babur ɗin sa ya nufi gida.
Arɗo da Buba sun ci gaba da tattaunawa game da ƙalubalen da rayuwar Fulani ke ciki a wannan zamani, fiye da kowanne lokaci a baya, yayin da suke jiran lokacin sallar Isha'i ya yi don su yi jam'i kafin su shiga gida baki ɗaya.
Ba su ankara ba sai suka ji, wata hayaniya na fito wa daga gefen gidan su Giɗaɗo, wanda tsakanin su da gidan Arɗo ba nisa, duk cikin ruga ɗaya ne.
Nan da nan suka miƙe tsaye suka nufi inda suke jin hayaniyar na fitowa.
Kafin su ƙarasa sai ga Malam Giɗaɗo a fusace ya nufo gidan Arɗo.
Arɗo ya tari numfashinsa kafin ya yi magana. "Malam, lafiya kuwa? Mai yake faruwa ne?"
"Arɗo, gaskiya abin da mutanen nan ke yi mana fa ya isa haka. Ba zan iya haƙuri da wannan cin mutuncin ba." Giɗaɗo ya faɗa a fusace.
Arɗo ya dafa kafaɗarsa. "Ka yi haƙuri, dattijo. Komai ya yi zafi maganin sa Allah. Ka yi bayanin mai ya faru."
"Ba za mu yarda ba! Haƙurin mu ya ƙare!! Ba za mu yafe ba!!!"
Hayaniyar matasa kenan da ke fitowa daga lunguna riƙe da sanduna, suna magana cikin fushi da nuna ɓacin rai.
Da ƙyar Malam Buba da Arɗo Manu suka shawo kan yaran nan suka yi shiru, kasancewar akasari yaran su ne kuma ko kuma jikoki, don haka suna jin maganar su sosai.
Bayan hayaniya ta lafa, sai ýan koke koke da ake jiyowa daga nesa ta sashin gidan Malam Giɗaɗo, sai Arɗo ya tambaye shi. "Mai yake faruwa?"
"Yaya," da sunan da yake kiransa kenan, domin kuwa yayansa ne uwa ɗaya uba ɗaya. "Hawwa ce ta je cikin gari tallen nono, wasu yaran Birom daga wajen loton kuza suka biyo ta hanya suka yi mata fyaɗe!" Ya ƙarasa maganar cikin hawaye.
"Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un!!!"
Gaba ɗayansu Buba da Arɗo suka shiga jimamin abin da ya faru.
"Lallai babu shakka akwai damuwa."
"Ƙaramar yarinyar da ba ta wuce shekaru goma sha biyu ba, ita ce don rashin imani za a yi wa wannan ɗanyen aiki!"
***** ****** *****
Tun da sanyin safiya, Da Gwom, shugaban al'ummar ƙauyen Dwol, Babban Limamin Rugar Shehu, Malam Jatau da Arɗo Manu, da sauran dattijan yankin suka hallara a farfajiyar gidan basaraken yankin wato shi Da Gwom Dalyop, sakamakon kiran gaggawa da Babban Jami'in Ýan Sanda na yankin DPO Azi Yakubu ya yi wa duk wasu masu faɗa a ji na yankin, kamar yadda ya saba idan irin haka ta faru, domin tattaunawa da samo maslaha cikin gaggawa, gudun kada abin da ke faruwa a wasu yankunan Jihar Filato Ya faru a nan wajen su.
DPO Azi ya ce, "Jiya na kwana cikin fargaba da damuwa game da abubuwan da suka faru a wannan ƙauyen, duk da zaman lafiya da muke samu wasu yara marasa hankali da tunani na son ganin sai sun haɗa mu rikici da junan mu. Suna son su ga abin da muke ji yana faruwa a wasu wuraren mu ma nan ya same mu."
Wani daga gefe ya yi caraf ya ce,"Ba za mu yarda ba, shaiɗan sai ya ji kunya."
"Na samu rahoton wasu shanu sun yi ɓarna a gonar Pam da ke kan tudu, wasu yara kuma sun je sun yi wa yarinyar Fulani, ýar wajen Malam Giɗaɗo Maikaba fyaɗe, duk a jiya. Nima na aika da saƙo gaggawa zuwa Dibishon kuma sun min alƙawarin kawo ƙarin ýan sanda, don kwantar da hankalin kowa. Na kuma sa a yi bincike kan abin da ya faru wajen aikin loto, da yaran da suka aikata laifin da ake zargi an yi na fyaɗe, don a hukunta su.
"Na ji daɗin shiga tsakanin da Arɗo ya yi na kwantar da hankalin Pam da aka lalatawa amfanin gona da kuma matasan da suka nemi ɗaukar fansa cikin dare. Muna jinjina masa, muna kuma son mu ga kowanne shugaba shhi ma ya misalta irin haka a bangaren sa don kwantar da hankalin kowa, a lokacin da aka samu saɓani, da sanar da hukuma cikin gaggawa, don a magance matsalar.
"Ina son kowa ya je gida ya ja wa yaransa kunne, don su sani babu abin da ya fi zaman lafiya, kuma duk wanda ya nemi tayar mana da hankali, za mu nuna masa fushin hukuma, ba sani ba sabo. Ba Za mu naɗe hannu wasu suna ƙoƙarin kawo mana damuwa a tsakanin mu ba."
"Zaman lafiya muka sani, kuma a kansa za mu rayu."
Da Gwom ya ce, "DPO, ka yi magana mai kyau. Kuma za mu ƙara sa ido mu kiyaye."