Binto 2
by @fadimafayau
Binto
2
************
Ta farka abinda ya ce da ita kenan tai qoqarin danne damuwarta kamin tace bari in kira likita ta miqe gami da yin waje jiki ba kwari.
Sun dawo ita da doctor ya dubata yace ba wata matsala asannu a hankali zata warke ok doctor zata iya cin abinci binto ta tambaya eh why not ya bata amsa binto tai waje ina zuwa tace musu.
Yau ba kowa gurin tsahare umma bilki dake gunta ta fita alwala sai binto tana bata abinci nan cikin dabara take tambayarta alaqarta da mutumin nan me zuwa kullun tace ai Baba ne binto ta kuma mai-maitawa aranta kamin ta kuma tambaya to ina ummanki naga bata ta6a zuwa ba ita.
Tsahare tadan sunkuyar da kanta tace ai bazata zo ba Binto tai saurin cewa sabida me bazata zoba ai nice yar fari inji tsahare awwo.
Hawaye tagani idon tsahare mene na kuka kuma umma ta na tuna ni banma santa ba kamar ya bakisanta ba inji binto aita mutu tun ina qaram ayya Allah ya jiqanta.
Dan zaman tsahare a asibiti sun saba sosai da binto wadda take kira aunty haka shima baban nata wato tsalha sun saba sosai dan sukan zauna suyi hira sosai yake jinta aransa musanman ma yadda yaga tana kula masa tilon yarsa.
Abu kamar wasa saiga shaquwa mai tsanani ta ta shiga tsakanin Binto da tsalha sun saba sosai wanda har gidansu yake zuwa su sha hirarsu duda an jima da sallamar tsahare dan ta warke sarai.
Wasa wasa sai ga soyayya mai qarfi ta shiga tsakaninsu irin wadda turawa ke kira da pure lada ada tsalha ya dauka bayan mutuwar salame matarsa bazai ta6a san wata mace ba.
Baima yi tsammanin zai iya kula wata macen ba sai gashi yanzu yanajin Binto aransa sosai fiye ma da ita Salamen.
Ita kanta Binto jinsa take sosai aranta gani take inbata aureshi ba bazata ta6a jin dadin aure ba bama tajin zata iya auren wani ba tsalha ba, duda dai jama'a suna kallonsa dan qauye bagidaje ita kuwa tasan tsalhanta na dabanne ya iya soyayya sosai yasan takan mace ya kuma san ta yadda zaiyi taso shi indai har zata saurareshi to zatasoshi duk matsayinta.
Dalhat sunan da Binto ta sauya mai kenan zaune yake yana jiran fitowarta Taslim ce ta fito suka gaisa dauke da turen lemo da ruwa tace kadan yi haquri gatanan ok bakomi yace tai ciki.
Bata jima da shiga ba Binto ta fito sanye take da shigarta ta gado wato riga da zani na atamfa super wax me yarfin ja batai wata kwalliya me yawa ba tai kyau sosai musan man a idon tsalhanta tunda ta fito yake kallonta yayin da ita kuma ta ke sakin murmushi.
Binto ba wata me kyau bace Baqa ce sosai mai matsakaicin tsayi dan bata cikin dogaye haka babu me kiranta qajera ita din mace ce me yawan sumar gashi wanda bai cika laushi ba wanda mutane kan kira da gashin Hausawa saidai ita nata yanada tsayi sosai wanda kuma yazo har gaban goshi.
Bata da qiba saidai baza'a kirata da ramammayiya ba ita din mace ce me yawan tsafta kwalliya da ado hakan yasa mutane bama sa ganin muninta ko kadan kunsan ance mace yar kwalliya ce.
Sai da ta zauna suka gaisa gami da tambayarsa diyarsu wato salame dan tace yarsa yarta ce.
Suna zaune suna hira yaya isma'il yaxo zai shiga ciki duda yagansu yai fuska danshi inda abunda ya tsana to be wuce ganin binto da wani ba.
Da sauri tace Yah ya juyo yama mance da kishin da yake danshi din yana san yaji ta masa magana shi kadai yasan dadin da yajeji aransa.
Daf dasu yazo na'am qanwar ta gaidashi cikin fara'a shima sosai ta masa kyau se ma ince fiye da yadda taima Tsalha kyau.
Dalhat ga yaya na ku gaisa tace da tsalha cikin girmamawa ya gaida Isma'il din duda kuwa zasu iyayin sa'anni.
Tace yah ga Dalhat shi ne mijin da zan aura yadan kalleta araze ta kuma mai maitawa to to masha Allah ya fada Allah yasa albarka yasa zamu gani suka amsa da amin.
Can isma'il yace to a ina yake kafin tsalha yace wani abu tace agaru yanama da yarinya daya mahaifiyarta ta tasu oh Allah sarki Allah yajiqanta suka ce amin bari naje ciki ko inji isma'il din.
Yana shiga ya bille ta qofar baya yai garden din gidan jiri na daukansa duk dauriyarsa kasa daurewa yayi ya fashe da kuka sosai yake san Binto har cikin ransa yakuma san kowa zai aura bazai ta6a dena santa ba.
Seda yai kuka me isarsa har ya godema Allah ya miqe yaje ya wanke fuskarsa gami da samin guri ya zauna dan yasan yanxu in yafita da matsala dan har lokacin be dena jin jiri na dibarsa yayin da can ransa yakejin wani irin baqin ciki na taso masa wayarsa ya dauka yahau karatun alqur'ani.
Binto ce zaune tana sana'ata wato karatun novels khadija ta dubeta yaya wai yaushe zaki kuma siyo mana irin kifinnan me dadi Binto ta dan kalleta aiko yau ma ta ajiye littafin ku tashi muje suka sa ihu duka yee that's our babbar yaya .
Kai ku tsaya to dama kudunwa kuke nufi suka marai raice haba babbar yaya aikinsan da kudinki muke nufi ta koma ta zauna ta6 kace zaku mutu baku ci kifi ba.
Mum dake zaune tanajinsu ta ce haba kekuwa yayan duwa inbaki siyawa yan qannenki ba wazaki siyawa ta turo baki kai momey sunfa fini kudi aike babbace babba juji inkinayi se su koya ta6 nidai bani da kudi.
Taslim tace to zanbada 1k seki cika to yawwa se yanxu naji batu ku tashi mu tafi ta zari mayafinta mum se mundawo.
Suna saukowa talon qasa inda TV ke akunne binto na kallon ta taja ta zauna wallahi bazani ba drama din data fi so ake Saloni wai yaushe ma suka fara maimaita shirin nan duk qannen sukai mata banza gami da komawa sama suna qunquni gami da Allah ya isa ga wanda yabar TV din akunne.
Tsalhane zaune yana jiran fitowar Binto hankalinsa duk atashe dan jiya ta kirashi take fada masa Abbansu nasan ganinsa hakuma komi ya ke daga masa hankali ba sai sanin matsayinsu dana binto ba daya bane ba kuma ko wani mai kudi irin na Binto bane zai bada diyarsa ga talaka irinsa.
Satin da ya wuce da yazo gunta kan jirkitaccen tsohon mashin dinsa duk yai futu futu dashi kayansa duk sunyi qura gashin kansa jar qasar garinsu ta rineshi zuwa ja mahaifinta ya fito zai fita yana sauri ya taddasu tana zuba masa ruwa yana wanke qafa.
Da alama sauri yake yakan yasa sama sama suka gaisa kamin yace Binto waye wannan din tadan sauke ido qasa Abba shine wanda nake baka labari yai saurin qara kallonsa sosai kamin yace ba laifi ya shige mota, baifi minti biyar ba ya dawo yai ciki tana Abba ya kadawo da wuri haka yai mata banza haka da zai kuma fita bai amsa ada lafiyar suba.
Ji yake kamar cewa mahaifin binton zaiyi ya fita harkar diyarsa gashi shi ayanzu yanajin rabashi da binto kamar rabashi da ransa ne santa a ruhinsa yake.
Tsoronsa kar iyayanta su hanashi ita duda bazai ga lefinsu ba matsayinsu ba daya ba ita yar birni shi dan qauye ita yar masu kudi illimi gamida mulki shi ba dan kowan kowa ba wanda aqauyensu ma ba kowa yasan dasu ba.
Ita yar boko wadda har takaiga kammala degree dinta yayin dashi secondary dinma daqyar ya kammala baida wata sana'a sama da noma se dan acabar da yake tabawa shima iya qauyensu yasan baushe ma kance qwarya tabi qwarya sedai shi so da qaunar Binto ta hanashi kallon tarin banbancin dake tsakaninsu balle yai tunanin kwarya tabi kwarya din.
Binto
F.A.Ya'u
************
Asalin Binto
Alhaji mahmud Hashin shine sunan mahaifin Binto haifaffen garin kano ne awannan unguwar mai dunbin tarihi da ta hadar da manyan mutane kama daga professors, Doctors da manyan yan kasuwa.
Su takwas mahaifinsu ya haifa shine na shida gidansu ma na sahun jerin masu karatun boko kaf gidan babu wanda bai boko ba.
yayyensa mata biyu se maza biyu sauran qannensa duk maza ne se autarsu mace.
Lokacin da yai kammala degree dinsa ne ya hadu da karima wadda sika qulla soyayya bada jimawa ba aka daura musu aure.
Auransu aurene najin dadi gami da kwanciyar hankali se irin dai matsala da dole in an hadu mutun biyu za'a samesu anman da yake duk su biyun sun san me suke babu wanda ya ta6ajin kansu.
Aurensu da shekara daya karima ta haifi yaronta namiji abinka da masu bin al'ada duda bokonsu aka saka a cirema yaro beli sedai yaita zubar jini bai kwanba ya mutu.
Haka haihuwa ta biyu shima da aka ma yaron kaciya basu zo gida ba yaro ya koma alokacin suka gano ashe haemophilic suke haifa.
Lokacin suka tada hankalinsu sosai hakan yasa yayan Alhaji Mahmoud ya bashi dansa ganin yadda suka damu mafarin dawowar Isma'il gidan kenan.
Ahaihuwa ta uku ne suka haifi mace wadda taci sunanta Binta wadda suka dauki san duniya suka dora mata haka shima isma'il murna sosai dan yayi qanwa lokacin zai shiga Jss 1.
Komi ya samu na Binta ne duk kudin makarantarsa ma ya dena kashewa shidai kawai yasaima Binta kayan wasa.
seda tai shekara shida suka haifa mata qani wanda take sansa sosai.
Lokacin Isma'il zai shiga level 1 yana da shekara goma sha shida cif wanda alokacin ita binta zata shiga primary 1, qanin ta Bashir wato jaririn da aka haifa sosai suke sansa ita da isma'il se arasa wanda yafi sansa.
Danma in yan kishinta suka motsa setace ina bazai dauki isma'il ba se ita haka zaitai mata doki tanama jaririn qwalo.
Shekarar Bashir uku Binto na shekara tara hartayi jarrabawar tafiya qaramar secondary jira kawai ake ta fito ta fara zuwa.
Tun Binto nada shekara bakwai lokacin Isma'il na level 2 ya fara santa sedai shi kansa baida tabbacin wani irin so yake mata ba akullin zatonsa sone irinna dan uwa da dan uwa.
Bashir shine bai iya fadin binta ba cikin gwarancinsa yake kiranta da Binto tun bataso har sunan ya bita.
Bashir be cika shekara Hudu ba aka haifi taslim batai shekara biyu ba aka haifi kadija.
Binto na Ss 2 lokacin isma'il na shekarar qarshe akaratun likitancinsa alokacin tuni ya gama gane haqiqanin wani irin so yakema yar qanwar tasa sosai yake santa duniya bashi da wani tunani se nata.
Yayin da ita kuwa aduniya wani malaminsu ke burgeta sosai sedai shi din kokadan babu baqar mace a tsarinsa danko amsa in baqace ke bama zai nuna kiba balle ki amsa.
Lokacin da ya dena zuwa ne ta gane basansa take ba burgeta kawai yake.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya isma'il na mutuwar san Binto yayin da ita kuma zuciyarta akullun ke hango mata wasu daba.
Binto bata da wata qawa ko aminiya sama da isma'il yayanta komi dashi suke haqawa su binne ba me ji duda zurfin cikinta baisa koda dawasa ta taba fadawa masa gawanda takeso ba hakan yai masa dadi dan yasan kenan bata kula kowa.
Lokacin da tai candy yabayyana mata burinsa nan tai fur ina ita batasan zanceba babu ta yadda za'ai ta auri yayanta cewarta kallon sibling dinta take masa babu batun aure tsakaninsu.
Tun bai damuwa yana zaton yarinta ce har kawo yau da take nuna masa wani matsayin mijin aurenta da zuciyarta tai mata zabi ji yake kamar zuciyarsa zata fashe.
Cigaban labari
Da fara'arta ta qaraso inda tsalha yake cikin barkwanci take fadin kaidai kaqi zama dan gida kullin kazo seka tsaya afarfajiya yai dariya ai wataran dai zan shiga in huta da gorin nan tai yar dariya gami da dan rissinawa ta gaidashi ya amsa cikin jin dadi.
Yana daya daga abinda ke qara masa sant shine girmama mutanen isso tai masa zuwa dakin mahaifin nata.
Cikin mutunci ya amshe shi suka gaisa yai dan masa tambayoyi abinka da masu illimi awayance ya kammala nazarinsa kan tsalha tuni ya gano mutumin kirkine matsalar sa kawai talauci toh malan tsalha ka iya tafiya zakaji komi gurin ita binto din yamiqe yana godiya ya fito.
Yadda mahaifinta ya amsheshi ya gano inda ta gado karamci ko kadan bai wani nuna masa kyama ba ko irin danme zai ce yanasan yarsa duda baice masa yabashi ko zai bashi ba sai yakejin fargabarsa da yawa ta ragu.
Duk wani bincike da yakama sunyi babu wata matsala dan tuni ma suka ce sun bashi matsalar daya ce ita ce inda binto zata zauna qauyene gidan yawa tace ita taji ta gani zata iya tuni akasa bikin wata biyu.
Tuni gidansu tsalha ya dauka ai tsalha zai auri yar birni yaqi auren yar qauye duk tarin matan dake sansa na garin.
Ita kuwa diyarsa murna take sosai dan zata samu umma musanman ma dataji wace Abban nata zai aure.
Yan gulma basu qara tsorata da lamarinsa ba seda sukaga uban kayan lefen da ya hada wanda ko a auren farinsa be rabinsa ba dan wani dan birnin ma ba lallai ya iya suba.
Umma bilki ta kirashi tace yakamata arage yace ina shi inda yanada abinda yafi hk wallahi shi zaima binto dan ta fi qarfin haka agunsa.
Lokacin da dangin tsalha suka kai lefe se suka raina abinda suka kai tun daga qofar gidansu binto yadda suka ga girman gidan tukwicin dubu dari ala basu banda soye soye.
Tuni qauyensu ya dauka wata sabuwar gulma wai anasan cutar tsalhane kodai yarinyar tayi cikin shegene ko kuma yar tsuntuwa ce inba haka wani me kudinne zaikai diyarsa qauye shidai tsalha ya toshe kunnensa kamar besan anaiba.
Danshi yasan samun kamila kamar bintonsa sai antona duda kasantuwarta yar birni yar boko anman su yan qauyen nasu da suke ganin kamar sune masu tarbiyya tafisu sosai.
Yarinya qarama da batafi sa'ar tsaharensa ba sekaji suna kawo masa hari wai shi takeso wasuma har girke girke suke masa abin bai fara tsorata shiba seda wasu cikinsa suka fara kawo masa kansu kan su koda bazai auresu ba sunasansa sosai yake mamakin yaran hakan yasa ko kadan bai sakar musu fuska.
Tun saka ranar Binto isma'il ya tattara yabar nigeria inda ya tafi china dan yace yanasan karanta likitancin gargajiyarsu yayinda azahuri kuwa ya tafine dan yasan zuciyarsa zata iya tarwatsewa indai aka daura auren bintonsa da wani.
Duk yadda akaso ya zauna ayi biki yaqi yace in time din yayi zaizo yayin da dangi suka rabu biyu gidansu Isma'il na asali suka haujin yaushin mahaifin Binto kan yaqi dan uwa yabaima bare.
Sosai family dinsu suka dau zafi dashi yace shifa bemasan da isma'il nasanta ba ko kadan zatonsa shaquwar yan uwantaka ce kawai.
Dayawa cikin dangi sunce ya fasa baima tsalha yabaima Isma'il yace ina shi bazai zama qaramin mutin ba ko kadan ai tun farko isma'il yai nauyin baki.
Rana bata qarya yau aka daura auren Binto da angonta tsalha biki sosai aka sha na gani na fade dan kunsan in abu ya hadu tsayawa bada labarinsa qauyanci ne kawai.
Ranar lahadi da yamma aka dauki amarya se garin garu da yamma liqis aka kai amarya dakinta bayan ankaita bangare bangare aka dawo da ita barinta yayinda yan kai amarya kowa yaqi zama kowa nafadin ina ai su bazasu iya ko rabin awa aqauyeba.
Haka suka tafi suka bar Binto amarya zaune ita kadai saman gadonta adakinta da yasha gyara wanda inkana ciki bazaka taba cewa kana kauye bane.