Chapter 4
by @nimcyluv
Jikinta ne ya saki bayan sun sanya mata handkerchief a baki wanda yake ɗauke da powder mai gusar da hankali,gaba ɗaya idanun Zarina ya lumshe jikinta saki yaza mana bata san inda hankalinta yake ba,sabida ƙarfin powder da akai using da ita a kan handkerchief ɗin,cikin motar ya turata tare da shimfiɗeta a side ɗin baya,shi kuma ya koma side ɗin gaba,ɗan juyawa yay tare da zuba masa idanunsa yana kallon yadda ta rungome teddy tare da tura yatsanta cikin baki,murmushin gefen baki yay domin nan take wani abu ya caki zuciyarsa,juyawa ya kalli drever yace "let's go" da gudu drever yaja motar suka bar kan titin.
Ihu Dreve'n Zarina ya saka domin kan idanunsa suka sanyata mota,tsoran ransa yake shiyasa bai ƙarasa ba,domin babban titi ne mutane basu fiya zama wajan ba,cikin kuka ya faɗa mota tare da janta da gudu ya mara masu baya,yana dreving yana kuka tare da faɗin "Hajai ƙarama ubangiji ya kareki daga sharrin mutannan,Yarinya mai halin manya kenan😭idan na rasaki ina zan samu mai bani na kashewa😂"
Sosai dreve'n Zarina ke gudu tsakiyar makeken titin amma kafin wani abu tuni motar ƴan kidnapped ɗin sunyi masa nisa,haka yayta bulayi babusu babu labarinsu,sabida tsoron abinda zai faɗawa Hajia Sultanerh yasa ya kasa zuwa gida sai gefen titi daya nema ya zauna yaci gaba da rusar kukansa.
Basu tsaya ko'ina ba sai filitin tashi da saukar jirki dake garin Kogi,suna isa jet ɗinsu na sauka,gaba ɗaya suka shiga ciki babu wasting time pilto ya tada jet suka lula saman gaji mare.
Fargaba gaba ɗaya ya cika Mom ganin lkcn da Zarina ke dawowa harya gota,cikin tsoron data sami kanta ta danna number wayarta,tana ji tana ringing but amma babu picking cikin muryar kuka Mom ta shiga faɗin "why Zarina am so scared pls come back"da sauri kuma ta danna number wayar drever'n cikin sa'a ya shiga ana picking tace "where is my luv,where is she!?"ta ƙare maganar cikin ɗaga murya tamkar yana gabanta,shuru tayi tana sauraran abinda yake faɗa kafin ta ƙwala ƙara tace "What Zarina missing but how, no you're lie duk inda yarinyata take kayi gaggawar dawo mani da ita kai shashan inane mtwss" tana faɗin hakan ta juya a guje ta nufi sashin uwar mijinta a babban parlour tana zuwa ta faɗa jikinta tare da sakin kuka,sosai Mamu ta shiga tashin hankali ganin surukarta cikin wannan halin,a tsorace tace "kee! Lafiyanki mene haka kamar wacce akace Abdallah ya mutu"ta ƙara magana tana kallon Sultanerh.
Ƙara ƙanƙame Mamu Sultanerh tayi cikin kuka ta shiga faɗin "Na shiga uku Mamu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta faɗin hakan tana ƙara rushewa da kuka,hakan yasa Mamu ƙara ruɗewa cikin wani sabon tashin hankali tace "Waini zaki maida shasha kizu kina kuka kuma kimin shuru oyya tashi ban waje idan baki faɗin abinda yake faru"girgiza kai Sultanerh tayi kana ta sassauta Kukanta tace "Zarina missing Mamu"ta faɗa cikin wani sabon kukan,da mamaki Mamu ke kallon Sultanerh kafin tace "sorry! I did get u kamarya Zarina missing kamar wata ƴar tsana?"nan Sultanerh ta ƙwashe komai ta faɗawa Mamu har abinda ta cewa Drever'n,Salati Mamu ta fara dayin addu'ar duk dayazu bakinta kana tace "Kin faɗawa Abdallah da kuma brothers ɗinta?"girgiza kai Sultanerh tayi tace "bansan tayaya ne zanyiwa swrth baya ni ba,ina tsori domin nasan soyayyar dakewa Zarina kamar ransa,Sufyan da Taufik bansan sanar dasu sbd kinsan yanayin aikinsu na sojoji da wahala yake gashi wannan karan kona kirasu waya ban samunsu ina tsoro zan jira harsu dawo"shuru gaba ɗaya sukai domin babu wani mai sauran kuzari cikinsu,can Mamu ta nisa tace "ko za'a ɓoyewa kowa banda Abdallah domin shine mahaifinta so kowanne tashin hankali zai shiga dole ya sani,ɗaukan wayana a ɗaki"miƙewa Sultana tayi tare da ɗauko wayan ta dawo babu ɓata lokaci ta dannawa Abdallah kira.
_Masarautar Bilhas_
A hankali ta shiga buɗe manyan idanunta wanda sukai mata nauyin gaske tana mamakin irin baccin daya ɗauketa,bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci kana taja idanunta ta ƙare kullesu,teddynta ta rungome sosai tare daci gaba dashan yatsanta ƙamar wacce ake feeding,cikin abinda bai huce 3mins ya farayi mata gizu kamar yadda ya saba yi mata cikin baccinta,amma a wannan karan tana mamakin yadda komai nasa yake bayyana abu ɗayane takeson gani hakan kuma ya kasa faruwa,a duk lokacin dataso ganin fuskarta sai kanta ya fara ciwo tare juya mata,ɗan ya mutsa fuska tayi cikin ranta tace "where are you haiding ne?"ta faɗa tana turo bakinta,sosai yake bata haushin ɓoye fuskarsa da yake mata,cikin nasarar da suka samu Zarina ta manta komai tama manta cewa satota sukai,ta manta Mom,Abbanta,Sufyan,Tufik,abu ɗaya take iya tuna ta kuma fahimta shine “Heart dream”
Turo ƙofar ɗakin da akaine yasa tayi saurin ware idanunta tare da zubawa ƙofar ɗakin idanun,saurin miƙewa tayi tare da zama waje guda ta ƙanƙame jikinta ta zubawa mutumin idanu,murmushi yay mata kana ya ƙarasu cikin ɗakin cikin so da ƙaunar ganinta yace "baby harkin farka?"kasa tankashi tayi domin haka kurum taci ta kasa yarda dashi,cije lips yay kana ya zauna kusanta yace "ohh baby badai harni kika manta ba,so how was ur night beby kin daɗe kina bacci harna gaji zarya"nanma shuru tayi masa ta ƙara ƙanƙame teddynta a jikinta ta shiga mutsa bakinta alamar tana son faɗin wani abu,ganin yadda bakinta ke motsi gashi gaba ɗaya sun jiƙe da saliva wanda ya ƙara hadda fidda asalin ƙyan lips ɗinta,yasa shi saurin lashe gefen bakinsa yana jin wani iri a ransa,cikin wata muryar yaudara yace "ohhya bebyna say something pls"hawaye ne suka wanke mata fuska cikin siririyar muryarta wacce bata fita sosai tace "who are u?"ɗan ware idanu yay alamar mamaki yace "Ohh bebyna ta manta lover ɗinta whatever dai i'm ur husband to be😱"kallonsa tayi da jiƙaƙƙen hawayenta tace "sure?"
“yeah” shine amsar daya bata cike da murnar nasarar daya samu,ɗan murmushi tayi wanda ya bayyana haƙorin makkanta cikin muryar nutsuwa tace "Thank God,amma da naji tsoro sai nake ganinka kamar mugu irin kumurcin majinnan"ɗan ɓata fuska yay baice bata komai ba yakai hannu zai riƙe hannunta tayi saurin jaa baya,cije laɓɓansa yay yace "ok bbyna take a shower and za kiga komai kamar a mafalki so ki ɗauki hakan matsayin sabuwar rayuwa zaa kawo maki white clothe ki sanya as from today shine kayanki daga nan banson wata tambaga kin gane"yana faɗin hakan ya fice a ɗakin.
Baki ta taɓe ita wani tsoransa ta keji haka nan,amma taji daɗi cikin ranta tunda yace shine zai zama mijinta tasan kuma miji never ya cuci matansa,miƙewa tayi tare shige wani ƙofa data gani gefenta ganin toilte ne yasa ta faɗa ta shiga sakarwa kanta shower tana gamawa ta maida kayan jikinta kana ta ɗaura alwala,sosai tai mamakin ganin dare ya ƙarayi cikin sauri ta gabatar da sallah sannan ta zauna zaman lazimi,tana iddar wasu Hadimai mata suka shigo kayan suka ajjiye mata sannan suka ajjiye mata kayan motsa baki danginsu fruit,wata Hadima ce tayi dariya tace "kice mun ƙaro wannan mai kalan aljanun ina aka sameta?" cewar ɗaga daga cikinsu kenan,Zaituna ce tace "kee! Saurara banson rashin ɗa'a meye haɗinki da ita?"Kuyanga Furare ta amshe maganar wajan faɗin "Babu fa,nidai ƴan matan duk abinda zaki ki ɗauke idanunki akan Lil prince domin shiɗin nawa ne ni ɗaya"Zaitunce ta maka mata harara tace "ke prince ya maida kuma iska na wahalan damai kayan kaba banda hauka irina Furera waya gaya maki tsarin mulkin Masarautar Bilhas jinin sarauta na kula baiwa,kima daina mafarkin samum prince domin yay maki nisa sosai"ta ƙare maganar tana kallan Zarina wacce taci gaba da laziminta cikin ranta idanunta rufe ba tare data kallesu ba,amma sosai maganganunsu ke damunta sbd bata sama da hayaniya ba sam.
Zaitun ce ta ƙarasu wajanta tace "ƙanwata sannunki kinji mune masu alhakin kula dake daga nan zuwa sati biyi ki koma ɓangarenmu baki ɗaya,amma kiyi hqr da rayuwa ki karɓeta a yadda tazu maki,amma mene sunanki?"sai lokacin Zarina ta ware jajayen idanunta da suka sauya kala lokaci guda sbd tsaɓar tension ɗin data shiga,sosai take kallon Zaitun kafin ta ware laɓɓa tace "heart dream"tana faɗin hakan taja idanunta ta rufe ta shiga tauna laɓɓanta,girgiza kai kawai Zaitun tayi tare da faɗin "Allah yasa mudace"hannu tasa ta dafe kanta dake sara mata tayi sosai take son tuna inda taji kalman ta,
“Allah yasa mudace”amma ta gagara tuna komai,cusa kanta tayi tsakiyan cinyoyinta ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita a haka wani sabon bacci ya ɗauketa yatsanta cikin baki.
Washe gari
Fada
Zaune Mai martaba yake kan karagar mulkinsa yana amsar bayanai daga wajan talakawa da kuma abinda ke faruwa a gari,wani dagacin baƙin da suka halarci Fadar wani ya numfasa yace "Allah ya ƙara girma yaja ƙwana muna da ƙorafi bisa babban filin da gwamna yay mana alƙawari bayarwa domin a gina makarantar islamiya yanzu kuma mun samu saƙo akan cewa ya fasa bada wannan babban filin,mu'alummu muna cikin tashin hankali bama da kuɗin saka yaranmu a manyan makarantu kuma muma munaso rayuwan yaranmu su inganta kamar t sauran yaran,wannan filin da za'a bamu jahadine kuma taimakon musulunci za'ai Allah yaja da zamanin sarkin sarakuna mai adalci a duba mana wannan lamarin"yakai ƙarshen maganar idanunsa na fidda ƙwaila.
Mai martaba ya jinjina kai tare da bada umarnin rubuta bayanai cikin peper,haka ya dingajin abubuwan da talakawa ke buƙata kana ya sallami kowa,Mai martaba ya kalli Tiraki sannan ya bashi umarnin yaje ya ƙona peper cikin girmama Tiraki yaje ya aiwatar da abinda Mai martaba ya umarcesa dashi,Ɗan aikena ya shigo da sauri tare da zubewa gaban Mai martaba ya soma kirari kafin yace "Ran sarki ya daɗe baƙwan U.S ya sauka yana airport yanzu haka" cikin farin cikin jin mai tsaronsa yazu ya bada umarnin aje a taho dashi,kana zaman Fada ya watse Mai martaba ya shiga tirakarsa.
Kilishi ta sami Jakadiya tace tana so ayi mata iso wajan Mai martaba,wajan 5 minutes Jakadiya ta dawo tare da zubewa gaban Kilishi tace "Allah ya taimaki uwar ɗakina saidai a tara nan gaba"cikin ɓacin rai Kilishi ta kalli Jakadiya tace "wai wannan wanne irin abune baka da ikon ganin mijinka a lkcn da kaga dama sai wanine zai baka dama?"Jinjina kai Jakadiya tayi tace "sai hqr haka tsarin Sarautar yake dole sai Fulanin Sura ta bada dama"rai ɓaci Kilishi tace "miƙomin Bakilawan can amma ni bazan iya lukutar masifa ba mata sai shegen iyayi kamar wani tafi"Kirara Jakadiya ta shigayi mata tare da zugata kana ta miƙa mata Bakilawan tayi waje.
A hankali wata babbar mota ƙirar Bugatti tayi parking tsakiyar masarautar,cikin sauri Drever'n ya fito tare da dawowa side ɗin baya ya buɗe ƙofa kana ya ƙame ƙam kamar wani dogari,wanda yake a zaune a bayan motar a hankali a ajjiye news peper ɗin hannunsa,gajiyayun fitinannun idanunsa yaja ya lumshe tare da taune jajayen laɓɓansa masu taushi,wani zazzafan numfashi ya fesar ta hancinsa kana ya shiga murza ring ɗin hannunta wanda ya kejin soyayyarsa kamar ransa,ƙyaƙƙyawane ajin farko Allah ya bashi murɗaɗɗan jiki kana ganinsa zakasan tabbas shiɗin soldier shi,hannunsa yasa ya shafi sajen fuskarsa kana yay ɗan gyara murya kaɗan wanda ya jawo hankalin drever'n cikin sauri ya amshi news peper ɗin tare da wayoyinsa,cikin isa da taƙama haɗi da izza ya zura da ƙyawawan ƙafafunsa waje ya ɗauki some minutes kafin ya fito da dukkan jikinsa,Sarki ya tabbata ga ubangijin daya tsara wannan halittar ni kaina na alƙalamina ya kusa faɗuwa,sanyen yake da farar t.shirt mai ƙaramin hannun hakan ya haddasa bayyanar murɗaɗɗiyar arms ɗinsa,sai dugun wandonsa na kakin sojoji yayinda ya ɗaura rigar uniform ɗinsa a waist ɗinsa,tsaiwarsa ya gyara tare zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,cije lips yay wanda hakan ya zama kamar habit ɗinsa,cikin wata zazzaƙar murya mai daɗi da taushi yace "Masarautar bilhas"