AL'AJAB

Chapter :3

by @oumwalid

*AL'AJAB* by 🌹 OUM WALID KD 🌹



*Page 3*



Cakumar kwalar juna suka yi kowanensu rai a mugun bace suna naushin juna tare da shurin junansu,sannan suka kara da amfani duk wani abu dake dakin wanda yayi kama da makami dama wanda beyi kama da makami ba suna kwaɗawa juna ajiki sun yiwa junansu jina jina idan da wani zai shigo lokacin abinda idanuwansa zasu fara gani shine tagwaye masu tsananin kama da juna suna faɗa saidai wannan yafi karfin kama, gabaki ɗaya sun birkita dakin asibitin dan har sunbar cikin dakin sun koma falon shima komai a birkice, hayaniyar da taji daga dakin ne yasa zainab ta fito daga bathroom data shiga domin yin alwala, ganin Aliyu duk biyun da irin ta'asar da suka yiwa juna da jikunansu yasa tayi turus ta rasa abin yi ga babu kowa kusa ana haka haj laraba ta fado dakin itama yadda zainab ta tsaya turus tayi,dan bata san lokacin da suka shigo dakin ba,dake ta ɗan fita zuwa harabar asibitin inda tasa direba ya dauko mata jakarta daga cikin mota wanda dazu ta manta dashi, ganin sun koma shaƙar juna da iyakacin karfinsu yasa zainab ta fita tana ihu neman agaji yayin da haj laraba ta shiga tsakaninsu tana ƙoƙarin rabasu tana kuka saidai ko gezau illa hankaɗata can gefe da suka yi ta buge kwankwaso, nan ta zauna tana wani irin kuka mai ban tausayi,oh ita laraba bata taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba, ga Aliyu B ya sake fama karyayen hannunsa, a ranta haj laraba tana tunanin idan har wannan faɗan ya cigaba to lallai Aliyu B zai rasa hannunsa har abada idan dayansu bai rasa ransa ba kenan, saidai yanzu menene abin yi sam basa cikin hankulansu balle su kula da cewa itace suka watsar kamar shara a ƙasa,tana saƙe saƙen abinyi taji motsin shigowar mutane.




Securities na clinic da nurses maza da mata tare da doctor Bello da MD ɗin asibitin doctor kamal da wasu doctors dake aiki anan asibitin sune suka fado dakin zainab da rukayya a bayansu sai zazzare ido suke suna kuka, ana cikin wannan rikicin zara ta farka inda gabaki daya ta rasa abinda ke faruwa tunda ita dai abinda ta tuna shine tana banɗaki tana amai bayan wannan bata sake sanin inda kanta yake ba sai yanzu data buɗe ido ta ganta anan tsakiyar filin daga, da ƙyar aka samu aka rabasu saboda zaratan maza ne ga tsayi gasu karfafa dakin asibitin duk ya sauya ko ina ka duba kayane da suka karya,tv dake maƙale a bango sun fasashi yana lilo shima saboda wasu wayoyine da suka riƙe,ran doctor Bello yayi mummunan ɓaci ganin irin yadda suka maida dakin,ga fuskokinsu duk jini hakama rigar dake jikinsu duk sun yayyage ga jini ko ina,sawa yayi aka fitar dasu daga dakin sannan shima ya fice, kai tsaye kawunansa alhaji Umar da kuma alhaji Hamza sodangi ya kira inda ya labarta musu abinda ya faru yanzu a asibitinsa,suma nasu ran yayi masifar baci.



Bayan ya ajiye waya office ɗinsa ya nufa inda yasa aka kaisu, tangamemen ofishi ne mai dauke da katon tebur wanda akai akwai desktop computer da files sai stethoscope wanda yake amfani dashi wajen gwajin numfashi da kuma sphygmomanometer(blood pressure cuff)wanda ake gwada bp dashi, akwai wani ɗan kofi me ɗauke da pens akwai printer da fax machine, akwai kujeru uku kewaye da tebur yayin da daura da wadannan kujeru akwai kujerar da take na mamallakin me wannan office wato doctor kamal dan shine Md , daga can gefe lutsuma lutsuman kujeru ne da tebur a tsakiya sai katon centre carpet a kasa da katon flat screen TV, wannan ɓangaren su Aliyu A da B tare da doctor Bello suka zauna yayinda securities suka tsaya daga bakin kofar a tsaye saboda koda sun fara faɗa za'ayi saurin shiga tsakaninsu.



Aliyu A na zaune kan one seater sai cika yake yana batsewa, manyan idanuwansa sunyi ja saboda ɓacin rai ga jijiyoyi da suka fito akan goshinsa rudu rudu,jini ne ke tsiyaya ta gefen kyakkyawar fuskarsa sakamakon wani karfe da Aliyu ya buga masa akai, wani irin tuƙuƙi da baƙin cikin yake na shiga tsakaninsu da Aliyu B da akayi saboda so yayi ya karya ɗayan hannun dan ba ƙaramar kishin zaransa yake ba, lokacin da ya shigo yaga shege Aliyu B na shafar fuskar matarsa ji yayi kamar yasa bindiga ya harbe hannun daya taɓa ta dashi, duk da faɗan badan zaran kaɗai suke yi ba, faɗa ne na asali,da suna identity ɗinsu shine babban musababbin,

wani kwafa yayi aransa indai shine zai nuna ma Aliyu B shi ƙaramin ɗan iska ne,by the time ɗin da zai gama dasu sai sun zama abin tausayi. Doctor Bello wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka fuskanci ba ƙaramar gajiya ke tattare dashi ba, wunin yau yayi tane cikin operation theater inda yayi aiki ma patients har uku, shafa fuskarsa yayi yana tunanin lallai yana mutukar buƙatar hutu me tsawo rabonsa da samun isasshen barci zaikai sati,ga wannan al'amari Aliyu's daya tada hankalin sodangi estate baki daya,wani ɗan guntun tsaki ya saki tare da jan numfashi sannan yace cikin muryar dake bayyana ɓacin ransa.



"Irin wannan iskanci da zubar mana da mutunci da kima da kuka yi a asibitin nan is unacceptable,ku ba ƙananan yara bane,kunkai matsayin da saidai ku yiwa wasu faɗa amma kuna faɗa sai kace toddlers wadanda suke faɗa akan bebin roba, wannan shegantakar bazan lamunceshi ba especially here, this clinic is a reputable place da majinyanta suka zuwa dan a dubasu ba kawai yan sodangi estate bane kawai suke zuwa nan, irin wannan abin kunyar har ina, wannan ya zama the very last time daza kuyi mun faɗa a cikin asibiti i would not tolerate this kind of nonsense......"shigowar alhaji Umar da alhaji Hamza shine ya katse fadar da doctor Bello yake yi musu,bayan sun gaisa ya sake yi musu bayanin abinda ya faru sannan ya kara da cewa.



"Kawu ni a ganina a tsaresu waje É—aya har zuwa nan da kwana bakwai wato sati É—aya kenan, lokacin sakamakon DNA results din ya fito,kaga lokacin mun tantance ainihin Aliyun......."



"Gaskiya ni bazan iya kwana har bakwai banga iyalina ba yaya, saboda halin rashin lafiya da take ciki suna buƙatar kulawata ita da ɗa na dake cikinta saboda haka ku sake wata shawara."cewar Aliyu A fuskarsa a haɗe kamar hadari sam shi bazai bari a rabasa da zaransa ba musamman a wannan lokacin da tafi bukatarsa,rufe bakinsa keda wuya Aliyu B wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka fuskanci yafi jigata a cikin wannan faɗan musamman dake dama can yana fama da karyayen hannu wanda kullum cikin famata yake yanzu haka numfashinsa sama sama yake fita shima hannunsa yasa ya goge jini daga gefen bakinsa sannan yace yana zazzaro manyan idanuwansa.



"Matarka ko tawa,kawu sam bazan yarda saboda wani shege munafiki ku hanani ganin zara ba,tana mutuƙar bukatata a halin yanzu laulayin babyn mu ya hanata sukuni she needs me......"




"Kunci ubanku yan'iskan yara marasa tarbiyya, mu zaku yiwa yawo da hankali,kai kana matarka,shi yana matarsa, wannan iya shegen naku ya kusan zuwa karshe,na rantse da Allah wa billahilazi idan result ya fito kuma muka gane asalin Aliyun sannan na gane babu alaqqa ta jini a tsakaninmu da É—ayanku wanda ya zamto musababbin wannan rudanin sai nasa an gana masa azaba wanda nan gaba zai bawa yan baya labari,kai wallahi koda alaqqa saina azabtar dashi saboda wannan iskanci da rainin hankali tare da rudanin daya haddasa mana a cikin zuriya, sannan zara tana da masu kula da ita,bayan sakamakon ya fito kuma mun tantance mijinta daga cikinku sannan zamu bari ya ganta until then babu inda zaku sake zuwa har sai result ya fito,dan Allah dubi irin yadda kuka yiwa junanku rauni sai kace kunyi faÉ—a da zaki irin wannan abin kunyar yau a zuriyar mu wallahi bazan yafewa ko waye yazo da wannan shegantakar ba,yan'iska kawai." Alhaji Umar kenan yana gama wannan maganar ya fice alhaji Hamza shima zazzaga masu masifa yayi tare da kudunduma masu ashar sannan ya fice waje ya turo wasu murtuka murtukan karti suka shigo su shida,ya kuma basu umarnin idan su Aliyun suka yi gardama su tara musu gajiya, uku daga cikinsu suka kama Aliyu A wanda nan take wani mugun kallo da yayi musu yasa suka sake shi babu shiri cikin kasalaliyar muryarsa wanda kan yaudari mutane har suyi kuskuren tunanin shi É—in ba wani bane yace.



"Ku sake ni zan taka da kafata zuwa mota, wallahi idan kuka sake yin kuskuren tabani zan fasa muku hanci stupid kawai."miƙewa yayi ya fice daga office ɗin yana tafiya cikin izza da ƙasaita kamar bashi da wata damuwa, yayin da Aliyu B ya daddage yana zuba masifa.




"Kawu wannan ai zancen banza ne, matata tana bukatata saboda hakkin kula da ita nawa ne bana wani ba saboda haka bazan yarda ku hanani ganinta ba."haka waɗannan kartin suka damkeshi suka fice dashi zuwa ɓangaren da za'a duba hannunsa anan asibitin kafin su wuce dashi gidan alhaji Hamza, yana kunduma masu zagi karyayen hannunsa maƙale ajikinsa haka suka fice, doctor Bello runtse idanunsa yayi ya ɗora kansa akan hannun three seater da yake kai, yana kuma al'ajabi faruwar wannan al'amari, shi kansa ya matsu sakamakon DNA results din nan ya fito kowa ma ya huta.


***



A bangaren zara kuwa bayan fitarsu Aliyun da sauran mutanen,daga ita sai haj laraba dasu zainab da rukayya,daga inda take zaune bisa gado kallon dakin ta sake yi tana mamakin yadda maza biyu suka birkita dakin kamar anyi wani ɗan ƙaramin girgizan ƙasa hatta da bangon dakin bai tsira ba,filastan bangon dakin sun farfashe sun zube a gurare da dama,wani sabon ciwon ne taji kanta nayi,dafe kanta tayi tace hmmm saboda sarawa dakan yayi sai lokacin haj laraba ta kula da ita tasowa tayi daga inda su Aliyu suka watsar da ita ta karaso inda zara take, fuskarta ta sake yin jajawur idanuwanta sun kumburo,sai kace ba mami ba uwar kwalliya da kwalisa.



"Sannu zara kin farka,bari mu kira dakta,zainab jeki fadawa doctor zara ta farka."da gudu zainab ta fice dan aiwatar da abinda haj laraba tace.



"Bakya jin daɗi me yasa baki faɗa munba zahra'u? inda rukayya ko zainab basu shiga dakin ba, da haka zaki zauna cikin ciwo babu wanda ya sani, idan kika ji baka jin daɗin jikinki kiyi waya koda bana kusa wani zaizo tunda zainab bata nisa yanzu da suka gama exams kullum tana gida kinji ko."cikin kulawa haj laraba take wannan maganar da ‘to’ zara ta amsa tare da gyaɗa kanta inda nan take tayi dana sanin hakan saboda wani jiri daya ɗibeta dole ta sake komawa ta kwanta haj laraba da rukayya suna yi mata sannu,shigowar zainab tare da likita ne yasa haj laraba ta matsa kusa da zara ta bawa doctor waje saboda ya dubata,bayan yayi wasu yan gwaje gwaje tare dayi mata wasu tambayoyi wanda zara ta basa amsarsu cikin muryarta mai sanyi,drip ɗin da aka daura mata ya cire empty ledar ruwa ya sake da wani sannan yasa aka canza mata daki exactly irin wanda su Aliyu suka bata.



Kwanan zara biyu a asibitin aka sallameta, alhamdulillah ta ɗan ji sauki,an bata magunguna irin na masu juna biyu su folic acid da sauransu ciki har da na amai waɗanda baza suyiwa cikin dake jikinta illa ba sannan yace ta rinƙa cin abinci mai gina jiki, kuma ayi ƙoƙarin wajen yawan bata abu mai ruwa ruwa saboda lack of rehydration ne yaja ta suma, zara tana samun kulawa sosai daga wajen zainab,haj laraba da rukayya sannan duk dare Abba wato sanata muktar sodangi saiya shigo ya dubata saboda Allah ya haɗa jininsa da ita yana ji da ita sosai kamar shi ne ya haifeta,zara tana jin daɗin yadda abba ke zuwa dubata saboda zama yake suyita hira.




Da dare kuwa lokacin da take ita ɗaya kuka take sosai saboda kullum saiya turo mata text me ɗauke da kalaman soyayya masu zafi,haka zata rungume wayar a kirjinta kewar Aliyunta na nukurkusarta tana sharar ƙwalla hannunta ɗaya toshe da bakinta gudun zainab karta jiyota kasancewar yanzu tare take kwana da ita tunda aka sallamota daga sodangi clinic,haka zata yita juye juye saboda ya riga ya ɓata ta da kwana ajikinsa yanzu da babu shi sam barcinta baya nisa kuma babu daɗi da kuka take kwana dashi take tashi gashi yau kwananta uku da aka sallamota, kwana biyar kenan rabon data saka daya daga cikinsu idonta.




Tsakanin sanata muktar da haj laraba kuwa gaisuwa ce kawai saboda sam yaki yarda cewa duk wannan abin babu sa hannunta a cikin,koda dama shi ba mazaunin gida bane saboda al'amarin siyasa yanzu rashin zamansa gida ya ninnika da,koda yana gida baya nemanta,idan taje dakinsa,duk maganar da zata yi baya tanka mata, haj laraba taci kuka harta gode Allah saboda tunda suka yi aure basu taɓa raba makwanci ba sai yanzu tsofai tsofai dasu muktar yake yi mata irin wannan wulakanci.



_________________________



*🌹OUM WALID KD🌹*


Comments, comments kuyi comments don't be a silent reader! Me kuka fuskanta?wanene real Aliyu?wane ne mijin zara?shin wane mataki sodangi family zasu É—auka idan result É—in DNA ya fito?