ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 1

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA* 

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page1️⃣ ```



 *Free* *pg*




 *LAGOS* 



Tunda aka tsayar dasu a cikin cunkuson ababan hawan take ta zabga tsaki tamkar zata tsinke harshenta, Muhsin dake gefanta a cikin a daidaita ya juyo tare da zabga mata wata ƙatuwar harara,bai dai ce mata komai ba, ya juya ya cigaba da kallon motocin da suka zama sanadin cunkuson dake faruwa a halin yanzu,tsakin da ta kumayi akaro mara adadi shine abinda ya kuma fusata shi ya juyo afusacen tare da nunata da yatsa,wallahi Fahrin idan kika sake min tsuka cikin kunnuwa sai na tsinka miki mari, dame kikeso naji?da wannan jiran da kafuran nan suka haifar mana ko da tsakin ki?haba!" ya faɗa cike da kufula,ita ko yarinyar da aka kira da Fahrin murguɗa ɗan ƙaramin bakinta tayi,tana gunguni aciki ba tare da ta bari sautin ta ya fito ba gudun kar tasha mazga gurin yayan nata.



Daga can waje kuma kan babban titin Lagos ɗin, cike yake da zafafan motoci wan da gaba daya manyan pastoci ne tare wasu manya daga cikin mabiya addinin yahudawa, wasu tafe suke a ƙafa wasu a mashina,kana ganin su kasan cewa suna cike da farin cikin wannan rana,wata danƙareriyar mota ce tafi jan hankali na, wadda na kula daga dukkan alamu wanda yake cikin motar baƙaramin ƙusa bane ko kuma wani me muƙamin ko dai daya daga cikin manyan pastocin da ake ji dasu ,tun da gashi dai gaba ɗaya alamu sun nuna hakan , duba da yadda naga jami an tsaro sun da baibaye gaba da bayan motar,dana mota dana ƙasa kowa kaffa kaffa yakeyi da abinda zai rabi motar bare akai ga na cikin motar.


Cikin wata irin murya me cike da sanyi da kuma yar tsiwar da ba wani iya ta tayi sosai ba, tace"wai dan Allah meke faruwa ne yau a garin nan?ko shugaban kasa ne zai wuce shine ya samu rakiyar ƴan maula? Fahrin ta tambayi me nafef ɗin,a dai dai lokacin da wani ɗan saurayi yazo shigewa ta gefan nafef ɗin yaji tambayar da Fahrin takeyi,dan haka tsalam sai ko ya shiga bata amsa da cewa,ai yaron pastor Matthew,,,aka bawa muƙamin pastor shine suke ta celebration kasan cewar sa yaro matashi da a wannan shekarar ya fara riƙe muƙamin fastor ne yasa abun ya Dada arna shi san nan kuma yaro ne uban talakawa Br BENJA ke kowa da ka gani san sa ya ke yi musulmi da kafuri kasancewar sa me gaskiya a fagen aikin sa mai kuma taimako talakawa na sane me kudi ma na sa ne in ɗai yana da gaskiya mai riko da addinin sa ne shi yasa Christian suke son sa mu kuma musulmi muna son sane saboda gaskiya da jin kan talakawa,yana da kudi kuma yana da aji uwa aba kyau,shi yasa yake da farinjini a wajen yan mata matuƙa" wani irin kallon wulaƙanci da kyankyami Fahrin ta shiga bin kyawawan motocin dasuke cushe akan babban titin da zai kaika anguwar su ta lakke da kallo , yatsanta ta ciza tare da yin ƙwafa kana tace"amma shine dan rashin kishin kai da addini, musulman mu suka tsaya kallon abunda bai da wata ma ana ko fa ida?har ma suna taya bera bari " Muhsin ya bige bakinta tare da cewa dalla rufe mana baki ke har me kika sani da zaki kawo wa mutane ƙauli da ba adi?tura baki tayi tare da ficewa daga a daidaitan,cikin sauri ya shiga ƙwala mata kira amma ina tuni har ta bace masa,kai tsaye motar da taga jami an tsaro nata faman kaffa kaffa da ita ta nufa, dan tana da yakinin cewa wannan kafurin yana cikin motar,kasancewar ta yarinya karama wadda bata gaza shekara goma sha shida ba yasa babu wanda ya ankara da zuwanta bakin motar duk kuwa da yadda suke tsaron motar kamar rai,a hankali ta ƙonkosa baƙin glace ɗin motar kamar wadda zata taya shi murna dan fuskar ta ɗauke take da wani sassanyan murmushi wan da ya kawa ta kyakykyawar fuskar ta ta,kamar wasa sai taga anyi ƙasa da glace ɗin,leƙa motar tayi ta shiga karewa mutane biyun da suke ciki kallo,da ta fuskanci cewa na gaban shine drivern sai ta maida kanta ga na bayan da bata gama ganin fuskarsa ba,baya ga kyakykyawar kirarsa ta santalelen namiji dogo mai ƙirar ƙarfi sai yalwatacciyar sumarsa da take a kwance kamar ta larabawa,jarida ce kife akan fuskar sa dan haka ba zaka shaida yanayin da yake ciki na ido biyu ko bacci ba,ɗan tsaki tayi tare da cewa wai kai kam ina baka da tunani?baka san cewa mutane sun cika titi suna jiran kubasu hanya ba?amma dan ɓatan rayuwa da na basira yana tare daku sam baku gane hakan ba,to idan ma murna kake bari na fada maka abinda baka sani ba wata ƙil ka hakurewa kan ka kasan cewa wannan abun da kakeyi bame amfani bane, wallahi tallahi da wan nan muƙamin naka gara muƙamin Sarkin kwasar kashi,dan haka ka daina murna,kuma kabamu hanya mu wuce tunda mu muna sallah kar lokacin ta ya kure mana!'kasancewar yadda Farhin ke magana cikin sanyi da kwantar da kai zakayi tsammanin cewa wani abun kirki take faɗa,dan shi driver bajin hausa yake ba shi yasa yayi tunanin murna take taya ogan nasu idan yayi la akari da cewa shine ya bashi umarnin zuge glace ɗin , kuma da yawan musulmi suna zuwa musamman dan kawai su gan shi, idanun sa ya kuma lumshewa bayan ya karewa ɗan karamin bakinta na tsiwa kallo, tana gama bayaninta ta janye daga jikin motar tana ɗagawa drivern hannu,duk atsammaninta fa babu wanda yasan me tace"tunda duk da Hausa tayi maganarta, dan haka cikin dariyar keta ta ce" na ci bulus"



Wani kallo Muhsin ya watsa mata tare da cewa daga gidan uban wa kike?banza tayi masa,dai dai lokacin ne suka ga ambada hanya, mai adaidaita ya kwashe ta da gudu dan kar wani sanadin ya kuma giftawa,basu tsaya ba sai cikin anguwar lakki inda anan ne gidansu yake,Muhsin ne ya tsaya ya sallami me nafef ɗin kana yabi bayan ƙanwarta sa,tunda ya doshi falon kakar tasu yake jin kwakwazon Fahrin tana bada labarin abinda ya faru har abinda ta fita tayiwa shi me girma Pastor ɗin bata rage ba,yana shiga ya sa kafa ya kai mata duka,da gudu ta buya bayan goggo Halima,ya ce"wallahi yadikko baza a kuma hada Ni aika da yarinyar nan ba neman tsokanarta yayi yawa,dan nasan wataran sai anyi mana duka akan ta!'yadikko ta ce"a'a muhsi bana son sharri yarinyar da magana ma bata dameta ba ina taga bakin yin tsokana?dan dai kawai kai dama ba kaunar maryama kakeyi ba!'harara ya watsa musu ita da Fahrin ɗin kana ya fice fuu kamar kububuwa yana cewa ai ke dama ba laifin ta kike gani ba shi yasa take wani abun,goggo Halima tayi dariya tana cewa to fa yadikko kin tabo Sarkin gida bakya tsoran ya yi miki yaji? Yadiki ta tabe baki kana tace" ya fashe karewar fushi haka kawai zai takurawa yarinya sai kace ubanta.



Kai tsaye suka wuce haɗaɗdiyar anguwar nan ta masu hannu da shuni wato ikeja,baka jin ƙarar komai sai na jiniyar yan sanda ,da sauri masu gadi suka buɗe tamfatsetsan get ɗin da yake neman cinye rabin anguwar,a hankali suka shiga ajere tamkar ƴan daukar amarya,lumshe idanusa yayi yana ɗan dafe kansa saboda tsananin gajiya da yayi da hayaniya,jinshi yake a matuƙar takure,sam bai saba da irin wannan rayuwar ba,yasan cewa shi mutum ne da yake da matukar san addinin sa,amma bai taɓa tsammanin cewa za abashi wannan muƙamin ba,buɗe mashi ƙofa da akayi ne yasa ya buɗe idanun da suka sauya kala saboda damuwa da gajiya ganin momin sa ne yasa shi langaɓar da kanshi kamar wani tsohon Maraya,amma har yanzu bai iya motsa bakinshi ba bare jikinshi, kama hannun shi tayi a hankali ta fito dashi daga motar kana ta shiga janshi har zuwa ƙatuwar kofar glace ɗin da take musu marhabin,taku yake ɗai ɗai tamkar baya son taka kasar,ita kuwa Madam Rabecca bata damu da hakan ba tunda tasan halin rabin ran nata kamar yunwar cikin ta,bata tsaida shi a ko ina ba,sai a katafaren ɗakinsa mai tsananin girma da ƙawatarwa,dubanshi tayi cike da kulawa tace"son nasan yanzu babu abinda kafi buƙata kamar wanka da hutu dan haka zamuji da bakin nida Dadyn ka kayi wanka ka kwanta ka huta na yanka maka kayan marmari suna fringe ɗin ka na falo"gyaɗa mata kanshi kawai yayi yana mai ƙoƙarin shigewa toilet,ganin haka yasa ta juya ta bar ɗakin cike da farin cikin abun alherin da yasame su a yau.



Fahrin Fahrin wai kina inane nake ta faman bude maƙogaro!'cewar Dada kenan dake tsaye a madafi tana juya miyar dake kan gas,da gudu Fahrin ta karaso har da ɗan nishinta,Binta da kallo Dada tayi kana tace"daga ina kike Fahrin?murza yatsun hannunta ta shigayi irin na marasa gaskiya,kafin Dada tayi yunƙurin cewa wani abu taji masifar Anty Karima daga bayanta,tana cewa Wallahi Fahrin sai na shuka miki rashin mutumci tunda kin maida kanki mahaukaciya mara hankali!'Dada tace"wai meke faruwane Karima?Anty karima tace"ina zaune tazo ta wuce ni tashige har ɗaki ta dauko min kit din kwalliya, garin giringiɗishi gashi nan yanzu gaba ɗaya ta fasa mun manyan hodojina daga na garin har na faundation ɗin,babu abunda zan amfana!'ta faɗa tana zabga wa fahrin mugun harara,Dada ta kalli Fahrin da tayi tsuru-tsuru tace"kin kyauta abinda kikayi dan haka babu wanda zai hanata baki kashi!'Karima tace"wallahi biyana zatayi dan bazan ɗauki asarar kusan dubu hamsin ba!'ta faɗa tare da kaiwa Fahrin ɗin duka,gocewa tayi ta samu damar barin madafin da gudu ta nufi falon yadikko dan tsira daga dukan Karima,Dada ta girgiza kanta tare da cewa kiyi haƙuri Karima kin san halin ƙanwar taki yarinta ke damunta zata daina ne!'karima ta tura baki tare da cewa haba Dada sai yarinya ta dinga yin abinda ranta keso a nacewa yarinta ba dole ta samu dama ba!'ta fita daga madafin tana ƴan mitocinta.



Kwanciya yayi bayan ya ɗan sha kayan marmarin da mom ta kawo masa,lumshe idanun sa yayi daniyar yin bacci,amma sai hakan ya gagara bakin matsiwaci yar yarinyar yake kallo cikin idanunsa,yana mai mamakin karfin halinta,tsaf yaji abinda take faɗa dan shi ba baƙone a harshen Hausa ba,wato ita a tsammanin ta bai ji abin da tace ba,da tunanin karfin halinta yayi bacci.



Kwance yake kamar gawa babu wani abu dake motsawa a jikinsa baya ga idanunshi, Fahrin ce zaune a gefanshi tana bashi kunun tsamiya wanda kusan rabin sa ke zuba ta gefan bakinshi,zuba masa ido tayi ganin yana kallon ƙofar shigowa ɗakin,sai kuma ta maida kallon ta kan mai shigowar,mama ce hannun ta ɗauke da tire,tace"au Fahrin ashe kina nan?Dada nacan tana cigiyar autar ta!'fahrin tace"mama kunu nake bawa Abba nazo naga kamar yana son dauka!'wani irin kallo mama tayiwa Fahrin cike da tambaya kana tace"Fahrin kina nufin Abban ku ya motsa jikinsa?gyada kai Fahrin tayi cike da tabbatarwa, murmushi mama tayi,kana tace"insha Allahu gaba gaba dai zamu samu nasarar samun lafiyarsa!'ta faɗa tana karasawa gaban gadon da yake kwance,tace"Fahrin tashi kije wajen Dada ina ga wani aikin zata saka ki"'kwalƙwal tayi da ido tare da langaɓe da kanta tace"wallahi mama nasan Anty Karima ke nemana shine zaki min wayo!'mama tayi murmushi kana tace"haba Fahrin ai dai kin san Ni bazan goyi bayan me bata miki ba bare kuma a hada baki dani,ki kwantar da hankalin ki babu mai taɓaki da sunan duka a gidan nan in dai ina cikin sa!'da gudu Fahrin ta rungume mama tana cewa yauwa mamana love U so much!'daga nan ta sake ta tafita daga dakin, maman tabita da kallon cike da alfahari da kauna,



Kai tsaye sashen Dada ta nufa,bata sameta a falon ta ba sai can cikin ƙuryar ɗakin ta,tana haɗa kayan wankin Fahrin ɗin da aka kawo daga guga,a hankali ta kwanta a bayanta tare da cewa Dada gani mama ta ce" kina nemana Allah dai yasa ba Anty Karima zaki kamawa Ni ba!'murmushi tayi ba tare da ta juyoba tace"ke kam Fahrin naga ranar da zakiyi hankali,ke kam kina kamuwa ne?juyowa Fahrin tayi tana fuskantar Dadan ta ta,tace"Dada bana so kema da bakinki me albarka kina dan gantani da hauka,kefa uwace Dada bakinki zai iya bina,bana son kalmar nan dasu Yaya Muhsin da sauran ƴan uwana suke dangantani da ita da nayi dan abu na kuruciya sai su ce min mara hankali, Dada yau zaki so ki ganni cikin hauka?ta faɗa cikin wani irin sauti,Dada tayi saurin rufe bakinta tare da cewa shike nan auta bazan kuma fada ba nasan komai kikayi yarinta ce kuma wataran zaki daina!"murmushi Fahrin tayi har kumatunta na loɓawa,Dada tace"yauwa aikenki zanyi gidan Batul amma dan Allah Fahrin karki tsaya wasa ko jan magana a waje kinji auta ta abar alfahrina!'murmushi Fahrin tayi tare da cewa bazan yi komai ba Dada,me zan karbo gurin Anty Batul ɗin?wata leda ta mika mata tace"wannan zaki kai mata nayi mata bayani a waya karfa ki daɗe, zaki dawo ku tafi islamiyya!'fahrin ta amsa tana ciro gogaggen hijab daga cikin sip,



Fahrin Sam Bata damu da jiran driver ya kaita guriba tafi ganewa shiga ɗan sahu ko tafiyar ƙasa yadda zataji daɗin tsokana san ranta,hakan ne yasa yanzu ma tana ganin sunusi driver Amma batace ya kaita ba,fita tayi cike da zumudi,tana kallon okada na wucewa amma bata tsayar ba,dan yatsina fuska tayi tare da cewa ai tsakanin mu da ikeja ba wani nisa dan haka aƙafa zani!"tana tafe tana wasa da tsokane tsokane,hakan ne yasa ta dauki lokaci ba takai gidan Anty Batul ba,tsayawa tayi tana karewa haɗaɗden gidan da a kullum sai tayi mafarkinsa kallo, ita dai a rayuwa ta dade bataga gidan da yake burgeta kamar wan nan ba,dan haka duk sanda tazo gidan Anty Batul sai ta tsaya a wajen gidan ta gama kallon sa kafin ta ƙarasa,yanzun ma ƙarasawa tayi gaban gidan tunda taga yau jarababban mai gadin baya ta wajen,rufe idanunta tayi tana emaginin itace a gidan tana tsula tsiyarta,hangota takeyi tana rayuwa acikin gidan kamar a gaske,jin kamar an bude karamar kofar get din gidan ne yasa tayi saurin bude idanunta,karaf suka haɗa idanu dashi,shikam sarai ya ganeta itace dai bata gane shi ba saboda bataga fuskarshi ba a wancan lokacin da take mashi tsiwa,zaro manyan idanunta tayi tana kallon haɗuwar mutumin a fili tace"kai wato yadda gidan yake da kyau haka masu gidan suma suke dakyau kai masha Allah!'daga nan taja da baya ta bar kofar gidan tana waiwayen sa.



Bai ɗauke idonsa daga kanta ba sai da yaga gidan da tashiga,ɗan tsaki yayi yana jin takaicin yarinyar har cikin ransa, sai dai ta wani bangaren kuma dariya take bashi a cikin ran sa,hakan ne yasa ya kawar da tunanin ta aransa,juyawa yayi ya koma cikin gidan yana tunanin tsautsayin da ya fito dashi dan haduwa da wannan rasa kunyar,


Da sauri ta bawa Anty Batul sakon kasancewar lokacin islamiyya ya gabato,ba tare da ta tsaya sauraren komai ba ta juya zata tafi , Anty Batul ta ce lallai duk abin da ya hana ki tsayawa wajen adil ba karami ba ne" Adil jariri dan watanni da Anty Batul ta haifa,kai tsaye Fahrin ta ce" wan nan zuwan bana sa bane zan yi masa zuwa na musamman , yan zu islmiya zanje mu tafi kin san an kusa ya ye mu saukar yadda na karayowa babu batun fashi,tana faɗa tana fita daga falon cikin sauri.



Tana wuce gidan tana ci gaba da kallo da waiwayen sa,tana aiyana badan makaranta zata ba sai ta Kuma tsayawa ta kalli gidan son ranta tare kuma da tsara rayuwarta acikin sa.



Dan kareriyar motar da tagani a harabar gidan nasu,ita ce tasa jikinta yayi sanyi tare da tsayar mata da duk wata walwala da farincikin da take cikin sa a kwana biyun,a hankali ta cigaba da takawa zuwa falon Yadikko,sallama tayi kamar maiyin raɗa can ƙasan maƙoshinta,tana kuma fatan ace ba abinda take zato ne zai tabbata ba, cikin zaro manyan idanunta take kallon matar dake hakimce saman kujerar dake fuskantar kofar shigowa falon,sai da ta dafe ƙijinta saboda bugawar da yayi, Yadikko tace"wai sanɗar me kike yi ne haka?bakiga Ummin ki ta dawo bane? cikin san dawowa hayyacinta ta washe baki ta gaiyatowa kanta dariyar dole tare da karasawa gaban ummin dake hakimce tana binta da wani irin kallo mai kama da tambaya,tsugunawa tayi tare da cewa Ummi barka da zuwa fatan kin dawo Lafiya?shafa kanta Ummi tayi tana cewa lafiya ƙalau Fahrin,yanzu dai kibarni sai zuwa anjima kafin kifara lissafomin mugayen da suka cimin zalunci bayan bana nan!"ta faɗa da murmushi kan fuskarta, Yadikko tace"ai kuwa kin san da akwaisu ko Ni zan tayata lissafosu!"murmushin yake Fahrin ta kumayi tana ɗan share zufar da ta tsatstsafo kan goshinta,bata iya cewa komaiba bayaga murmushin, ta miƙe ta nufi ɗakin Yadikko, yayin da Ummi ta kuma Binta da wani irin kallo da Ni kaina ban gane masa ba, Fahrin tana shiga ɗakin Yadikko ta shiga sunturi yayin da idanunta suka cika taf da ƙwalla sam ta manta da rayuwar da take fuskanta saboda rashin Ummi, idan tana tare da Yadikko da Dada mantawa take da komai shi yasa yanzu ma ta manta rayuwarta da kuma halin da take ciki,ita kanta tasan bata da saka damuwa arai amma ba dan haka ba tabbas halin da take ciki bazai bari tayi walwala da farinciki ba,ganin ummin ya tuno mata da komai,anya kuwa zata iya komawa sashen Ummi?shin ta wace hanya zata gujewa hakan?ya za ai abbu ya fuskanceta ya gane cewa rayuwa cikin su da yan uwanta ya fiye mata farinciki?ya za ayi ta fuskantar da mutane WACECE Ummi bare har agoyi bayanta abarta ta zauna da Dadanta?share hawayen fuskarta tayi tare da furtawa a fili, Allah shi kadai yasani shi kaɗai yasan sirrin ɓoye shine kuma yake da hanyar magancewar kowacce irin matsala!'jin kamar za a shigo ɗakin yasa tayi saurin faɗawa bandaki.



A sanyaye ta fito dan tafiya islamiyya,Dada ce ta dubeta cike da kulawa tace"meke damunki ne Fahrin? bazaki ci abinci ba zaki tafi makarantar?ɗan jingina tayi da jikin Dadan kana tace"sai na dawo zanci idan na tsaya zan makara"Yadikko tace"nikam bana son zama da yunwa ke kuma al'adarki kenan sai kinje wannan cutar ta yunwa ta kamaki!'fita tayi tana cewa ba abinda zai sameni Yadikkona sai na dawo,ta faɗa tare da barin falon.



A saɗade ta shigo tan gameman falon da yaji kayan alatu na more rayuwa,kana ganin tsarin gurin zaka tabbatar da cewa mamallakiyar gurin ba karamar hamshakiya bace"kamar daga sama ta jiyo Muryar Ummin tana cewa Dr lallai ina buƙatar ganin ka saboda akwai babbar matsal,,,,maganar ta tokare mata ganin Fahrin na faman zare manyan idanunta tana son shigewa daki,Wani irin miyau ta haɗiye kana ta cigaba da cewa bari zan sake kiranka!'daga haka ta datse kiran tana mai wurgawa Fahrin wani irin kallo mai cike da fassarori da ma anoni masu tarin yawa.



F Y ADAM✍🏽