ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 2

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA*

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page 2```



 *Free* *pg*




Take jikin Fahrin ya shiga rawa har jakar islamiyarta na neman faduwa,laɓe kike min har yanzu ko Fahrin?Ummi ta jefa mata tambayar tana mai zuba mata idanu,da sauri Fahrin ta shiga girgiza kanta kamar marainiyar ƙadangaruwa yayin da idanunta suka cika taf da ƙwalla, Ummi tace"Fahrin ina mai kuma jaddada miki cewa zakiyi danasanin sakawa rayuwata ido, zakiyi danasanin kokarin sanin wani abu daga cikin sirrika,hakan ba karamar nadama zai janyo miki ba,amma dai har yanzu kina da damar gyara kuskuren ki ta hanyar kama bakinki da kuma gujewa ji da ganin sirrikana, wanda ji da ganin nasu zai iya zama sanadin taki ƙaddarar,dan haka ki gujewa kanki ji da ganin abinda zai jirkita rayuwarki daga dai-dai zuwa bai-bai, dama ce na baki ba wai gargaɗi nake miki ba,wuce ki bani guri" cikin sauri Fahrin ta wuce zuwa ɗakinta zuciyarta na wani irin bugu da matukar jin tsoron maganganun Ummi,ba tare da ta tsaya tunani ba ta cire uniform dinta ta saka doguwar riga,kana ta fito,ganin ummin ta bar falon hakan ya bata damar fita zuwa sashen Dada,tana zuwa ta faɗa falon yadikko,madafi ta nufa ta dauko abinci ta fito tare da zama gefan Yadikko da take faman murɗa rediyon hannun ta, Fahrin tana gamawa ta shige ɗakin Yadikko tayi alwala saboda kiran sallar magriba da akeyi,bayan ta idar saida tayi karatunta kamar yadda ta saba har aka kira sallar isha'i, bayan ta idar ta fito cikin sanyin jiki, Yadikko ta dubeta tace"au har yanzu kina ciki baki tafi ba!?ba tare da ta amsa wa Yadikko tambayarta ba ta ɗora mata da Tata tambayar tace"Abbu kuwa yashigo?Dada dake shigowa falon ta bata amsa da cewa ya dawo mana,yana can falonsa,"wucewa tayi tana cewa zan shiga na gaidashi daga nan zan wuce gida!''Yadikko tace"Allah ya bamu Alkhairi ya tashemu lafiya.



A hankali tashiga falon tare da ƴar sallama saman laɓɓanta, kyakykyawan dattijo ne me cike da kamala,akwai alamun addini a tare dashi,kana kallon sa zaka san cewa lokacin ƙuruciyar sa ya zuba kyau da gayu,haka kuma ganin sa shi zai kuma tabbar maka da cewa shine mahaifin Fahrin saboda tsananin kama da suke,babu abinda ta baro shi photo copy ɗinsa ce sak farin Dada da gashin ta ne kawai ajikin fahrin,amsa sallamar yayi fuskarsa cike da annurin ganin farin cikin zuciyarsa, hannu ya miƙa mata yana ajiye dan littafin addu'oi dake hannun nasa,yace"zo nan autar kirki alfahrina Maryama abar kwaikwayo, ina kika shiga tunɗazu nake ambatanki da yabon ki?durƙusawa tayi ta fara gaidashi kana ta koma gefansa ta ɗora kanta gefan kafaɗarsa,ɗora hannun sa yayi a kanta yace"meke damunki haka alfahrina? cikin jan numfashi ta buɗe baki dan sanar dashi abunda ke ranta amma sai gargadi da maganganun Ummi suka shiga yi mata tsere cikin dodon kunnen ta,hakan ne yasa ta canja akalar maganarta tace"Abbu kayiwa mutanen gidan nan magana su daina kira na da mahaukaciya,Ni ba mahaukaciya bace,na faɗa musu sunƙi dainawa duk wanda na yiwa kuskure sai yana cemin mahaukaciya!'A hankali Abbu yagyara zamansa kana yace"gaskiyarki alfahrina bazan yadda da wannan sakarcin ba Ni ban haifi mahaukaciya ba, dan haka zanyiwa kowa kashedi da babbar murya duk wanda ya sake faɗa miki wannan kalmar tabbas zaiga hukuncin da zai biyo baya!'Dada ce ta shigo bakinta dauke da sallama,sai da ta zauna kana tace"suwa kuma za ayiwa hukunci haka kararwa aka kawo?Abbu yace"ai kema har dake tunda kina ji ana kiran ƴarki da mummunar kalma amma baki dauki mataki ba"Dada ta ce"to nice uwarta? taje ta sanar da Ummin ta mana taga idan bata dauki mataki ba,to Ni banga wani abun daga hankali a kan wannan ba,tunda suma masu fadar faɗa kawai suke ba wai dan sun san ke ɗin mahaukaciya bace" kuka Fahrin tasa har da sheshsheƙa,kuka take kukan da kana jinsa kasan cewa ya daɗe yana son fitowa, murmushi Abbu yayi, cikin san lallashin ta yace"meye na kuka Fahrin ai na gaya miki zan ɗauki mataki,kinji ko? cikin wani irin kuka mai cike da fassarori da takurar zuciya tace"Abbu kanajin abin da Dada take faɗa wai babu komai,Ni kawai banaso inajin wani abu daban duk sanda aka dangantani da kalmar,inajin kamar wataran hakan zata iya kasancewa dani kamar abin zai iya zama gaske,inajin haka har cikin raina,Ni banaso na zama mahaukaciya banaso banaso!'ta faɗa cikin wani irin sauti wanda sai da yasa gaba ɗaya jikin iyayen nata ya mutu take wani tsoro yashiga zuciyar Dada,Abbu ma kansa saida kalaman Fahrin suka jefashi cikin fargaba,hakanne yasa ya janyo ta jikin sa ya shiga bubbuga bayanta, cikin sanyin murya yace"a'a Fahrin ki daina wannan tunani me zai maida ke mahaukaciya bayan Ni ba mahaukaciya na haifa ba? ƘADDARA mana Abbu ƘADDARA zata iya zuwa min ahaka idan suna faɗa zai iya kasancewa,kawai kukan Dada sukaji cikin kukan take cewa nikam maryam na rasa abinda ke damunki a kwanakin nan,dan Allah ki daina irin wannan maganganun ke yarinya ce har yanzu baki san kan rayuwaba,kuma insha Allahu ƙaddarar ki ba mummunar ƙaddara bace,tashi muje na rakaki ta faɗa tana goge hawayen fuskarta,Abbu ya kalli Fahrin yace"tashi kuje kar na kuma ganin ki cikin wannan halin zanyi maganin komai insha Allahu!'gyada kanta tayi tana goge guntun hawayen fuskarta,tare da miƙewa tabi bayan Dada.



A bakin kofar sashen nasu Dada ta tsaya, tace"to maza wuce ki tafi amma dan Allah,Fahrin ki daina damuwa akan wannan abun kinga ke yarinya ce karama karki saka damuwa a cikin ranki kinji ko?gyada kanta tayi tare da kakalo murmushi ta ce"shike nan Dada bazan kuma ba na daina" yauwa autar Abbu da Ummi maza tafi kar Ummi tajiki shuru"'juyawa tayi ciki tana jin rashin Dadin danganta ta da Ummi da Dada tayi, sai da Dada taga shigar ta ciki kana ta juya tana ci gaba da tausar zuciyarta akan halin fargabar da tashiga akan maganganun Fahrin.



Duk yadda taso wucewa dan kar su ganta amma hakan bai samu ba,duk da cewa ba wani abu taji daga cikin abinda suke tattaunawa ba,amma saboda gargaɗin ummi agareta sai duk ta ruɗe tamkar wata mara gaskiya,zuba mata ido ummin tayi tana son karantar yanayin ta, cikin sauri Fahrin ta gaida Dr Hisham tare da shigewa dakinta,Dr Hisham yace"Hajiya anya kuwa yarinyar nan bataji kalmarmu ta karshe ba? girgiza kanta tayi tana ɗan cije lebanta na ƙasa tace"Dr bana tunanin taji amma duk da haka zan bigi cikin ta,yace"wallahi Hajiya haka kawai nakeji kamar yarinyar nan zata iya bamu matsala kamar Akwai abinda take nadewa a ƙwaƙwalwar ta game da abinda muke shiryawa, Ummi ta ce"kar kadamu Dr Fahrin yarinya ce karama shi yasa nabi wasu hanyoyi dan firgita ta da tsoratarwa a gareta, duk da cewa idan ta kuskure zan iya aikata mata dukkan abun da na lissafa mata har ma da dadi , amma na tabbatar maka da cewa akwai gabar da zatazo da bazan iya rabuwa da ita ta wargaza shirina ba ko tonon asiri a gareni,Dr Dr Hisham ya ce" to da me zata tona miki asiri bayan har yanzu bata da wata hujja akan abun da ta fara fahimtar , san nan har yanzu bata san gun Darin abun da muke gwagwamar maya akai ba" haka ne maganar ka, yanzu dai mubar maganar Fahrin bata da wani amfani muyi abinda ke gaban mu!'yace"haka ne Hajiya amma kuma karki manta ɗan hakin da ka raina shiyake tsole maka idanu ya kamata kiyi tunani akan yarinyar nan da matsalar da zata iya haifa mana"ɗan jim tayi kana taja dogon numfashi tare da cewa kaima kayi tunani mai kyau Dr dan haka zan san abunyi akan lamarin,yanzu dai kazo da allurar Alhajin saboda na gaya maka akwai matsala ance min Ɗazu Fahrin taga yana motsa hannun sa dan haka dole a ƙara karfin ruwan allurai dan samun cigaba" A hankali Dr Hisham ya dauko wata ƴar jaka irin tasu ta likitoci tare da nunawa Ummi yace"kingan su nan yanzu daga nan can zan wuce nayi masa su saboda jinkirin yinsu zai iya kawo wata matsalar"da sauri Ummi tace"maza tashi kaje amma kasan da haka shine kazauna ? me makon ka fara zuwa kayi masa daga baya kazo mu tattauna" miƙewa yayi yana rataya jakarsa tare da cewa ki kwantar da hankalin ki muna da sauran lokaci babu abinda zai sami mai gidan ki ya faɗa yana wani shu'umin murmushi,jinjina kai tayi ta bashi hanya ya wuce,ita kuma ta wuce zuwa ɗakinta.



Duk waɗan nan maganganun da sukayi a kunnen Fahrin ne da sauri ta koma saman gadon ta tare da shigewa cikin bargo ta dukunkune har fuskarta,jikinta har wani karkarwa yake saboda tsabar razana,wai shin me Ummi take shiryawa ne me take son cimmawa?tasan cewa a kwai allurar da akewa Abba,amma yanzu ta fuskanci wani abu akan allurar da ake masa,wace irin allura ake masa anya kuwa ta neman lafiyarsa ce?me yasa ba za a canjawa Abba likita ba, dan sam ita bata yarda da Dr Hisham ba,akwai abinda suke ƙullawa shida Ummi, me yasa su Dadyn sama baza su karbi ragamar ko mai a hannun su ba, tasan cewa ba Ummi ce ta kawo Dr Hisham gidan nan ba, dan haka babu wan da zai zargeta akan wani abu , runtse idanunta tayi tanajin wani irin tsoro Na Kamata tare da fargabar abun da Ummi take shirin aikatawa akan Abban tsakiya , da wannan tsoron tayi bacci wanda sam babu daɗi a cikinsa.



A hankali yake cin chips din dake gabansa,sam babu fara a akan fuskarsa tamkar wanda akayiwa dole haka yake tura chips din,ƙaramin Pastor kenan Benjamin,A hankali Madam Rebicca ta ɗora hannun ta saman hanunshi wanda yake cike da gargasa cikin kulawa da soyayya tace"my son what happened to you?ta faɗa tana mai tsira masa kyawawan idanunta irin nasa,janye hannunsa yayi kana a hankali ya bude bakinsa kamar ana masa dolen magana yace"nothing"ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa tsaye da sauri ta rikeshi tana cewa haba my Benja,duk da cewa nasan haka yanayinka da halayyar ka yake amma ko ƙaƙa kasan ina gane damuwarka, nasan cewa wannan muƙamin da aka baka beyi makaba kuma bakaso amma ka kasa faɗa me yasa kake irin haka eye Benja? nifa mahaifiyarka ce me yasa bazaka faɗa min damuwarka ba?zare hannun shi yayi daga riƙon da tayi masa ya fara takawa ba tare da ya bata amsar tambayar ta ba,sai da yakai hanyar kofar da zata sada shi da harabar gidan kana ya ɗan tsaya kamar ba zaice komaiba sai kuma ya bude bakinsa a hankali cikin wata irin murya mai cike da kasaita da nuna ginshira da maganar da momin takeyi yace"momy sorry forgot ur this isue we can telk to you letter,daga haka yasa kai ya fice cikin takunsa na kasaitattun maza wanda yake nuni da mazantakarsa,Madam Rebicca tayi murmushi tare da cewa oh God halin Benja saini dana haifa kuma nasan kayana.



Yana fita kai tsaye officce ɗin ya wuce,duk yadda Benja ya kasance me tsananin san addinin sa amma hakan bai hanashi jin bakin cikin muƙamin da aka bashiba,shi mutum ne da baya san harkar da tashafi hayaniya duk abinda zaisa shi shiga cikin hayaniya ko takurashi bayaso,amma babu yadda ya iya tunda Mahaifin sa ya amshi tayin hannu biyu yasan bazai kaucewa hakan ba.



Pastor Matthew Babban malamine a bangaren su na karatun Christian, yana da tarin dukiya da kuma tsantseni akan addinin da ba nasa ba,matarsa itace"Madam Rebicca wacce sukayi auren zumunci dan iyayensu daya kuma aguri ɗaya suka tashi cristocin naija ne amma duk zama ya dawo da tushen su Najeriya ɗai ɗai kun danginsu ne suke can naija a yanzu, Fastor Mathew Babban mutum ne wanda ake matuƙar ji dashi acikin zuriyar su haka bangaren su na cristoci ana ji dashi saboda ya kasance mutum mai kin dukiyarsa akan alheri da yiwa addinin sa hidima,shi yasa ko acikin pastoci shi na musamman ne,basu da yawa a wajen iyayensu daga shi sai ƙanwarsa wadda yake matuƙar so da kauna,mahaifinsu ya mutu yanzu sai mahaifiyar su,shima baya da wasu tarin yaya yaransa uku ne Benjamin shine na farko sai nala da karah wadanda suka kasance yan biyu ne, Pastor Mathew yana matukar san yaransa shi yasa yayi kokarin ɗorasu akan turbar da yake bi,ya kuma samu nasara akan tilon ɗan nasa dan a halayyar sa kadan ya bari,


Haka Madam Rebicca ma kusan halinsu daya da mijinta sai dai ita tana da yawan faɗa haka kuma tana son benja sosai kamar ranta,nala da karah suna tare da kakar su , duk da cewa ba wani nisa ne tsakanin su da gidan nasu ba. 



Kyawawan gaskene dan Rabecca idan ba sani kayi ba zaka iya sakata a sahun larabawa farace tas me manyan idanu,saɓanin Mathew da yake wankan tarwada sai dai shima ba bayaba dan har kama suke da juna,Benja kamar mamansa yayo sai dai kalar fatar babansa ce dashi kalar da take da tsada acikin mutane,



Benja yayi karatunsa na Br Wanda yanzu haka yana aiki da babbar kotun da take garin na Lagos,Benja mutum ne mai matukar tsantseni a kan duk wani abu da ya shafeshi,bai cika san hayaniya ba san nan ba ko da yaushe ne zaka same shi yana magana ba,ko maganar akayi masa sai yaga dama zai amsa,ba kuma wai dan wulaƙanci ba sai dan kawai maganar da take mashi wahala kuma bai saba da ita ba,baya harkar mata dan basa gabanshi,da kwai ƴanmatan da suke sanshi da yawa amma basu sami fuskar tunkarar sa ba,ko sun tun kare shi basa samun kallon mutunci balle ya nuna yasan dasu,rayuwar Benja badan sabanin addini ba sai nace rayuwace ta burgewa da sha'awa,abokan sa biyu ne dan uwan sa James sai kuma daya da ya kasance musulmi likitane mai suna Dr Hisham,su kadai ne aminan bayan tafiyar James karatu ne , sai ya kasance bashi da wani aboki sai Dr Hisham,wanda sukayi shakuwar da har iyayensu duk tsantseninsu akan mu'amala da musulmai sai da suka bada goyan baya akan abotar su,dan sun riga sun yadda da yadda Benja yake son addininsa, sun san babu abinda zaija hankalinsa akan wani musulmi balle har ya canja masa ra ayi,saima su da suke tunanin watarana shi Dr Hisham ɗin zai iya karɓar nasu addinin, hakan ne yasa basu damu da wannan kullin abotar ba,haka ta bangaren uban gaiyar Benja bayajin wani abu makamancin haka dan yanajin ƙololuwar kauna akan addini sa.



Har ya gama wayar yana sauraron shi amma baza ka taba gane cewa hankalinsa yana kan wayar da Dr Hisham yakeba,Br Benja duk da cewa Dr Hisham aminin sa ne na rai amma hakan baisa shi yana yawan shiga cikin al'amarinsa da ya fuskanci bayason Asani ba,amma haka nan yaji bai yadda da shurunsa akan wannan abun da yaji kamar babu gaskiya Acikinsa ba,haka nan yake jin al'amarin kamar yana Dan gantuwa dashi,har zaiyi magana sai kuma ya fasa ko wane irin tunani yayi oho,ci gaba yayi da danna laptop ɗinsa ba tare da ya tankawa Dr Hisham ba,miƙewa Dr Hisham ɗin yayi yana cewa Benja ni zan koma asibiti saboda akwai tiyatar danake da ita karfe uku idan na fito zan kira ka"jinjina kanshi kawai yayi ba tare da ya tankasa ba,tsaki Dr Hisham yayi yana ƙoƙarin ficewa daga officce ɗin yace"ayi mutum kamar kurma bakinka ko doyi bayayi saboda tsabar shuru yanajinsa ya fita yana mitar da ya riga ya saba da ita.



 Asalin mlm sulaiman bafulatanin jalingo ne anan aka haifi mahaifansu,basu da wani yawa a dangin su amma mahaifinsu yana da yara babu laifi saboda matanshi biyu malam sulaiman shine kusan na karshe a cikin yan uwansa kuma shine ya fita Zakka acikinsu saboda shi kaɗaine yayi karatun boko kuma wannan dalilinne yasa zaman jalingo ya gundureshi,yar uwarsa aka aura masa mai suna Maryam , bayan auren ne ya dauki matarsa sukayi kaura zuwa Kano basu fi shekara daya akano ba suka kuma komawa Kaduna saboda yanayin aikinsa da yake samun sauyin gurin aiki,yana zuwa gida akai akai har ya zamana iyayen sun rasu sai kuma yan uwa wanda hakan baisa ya yada yan uwansa ba duk da cewa su biyu ne kawai suke daki daya da yar uwarsa kulsumu,


Daga nan zaman ya dawo Legas , wan da suna zuwa rabo ya fara zuwa, Auwal aka fara haifa kafin Abubakar ya biyo baya , sai kuma usman da Yusuf daga nan aka samu Halima daga nan basu kuma haihuwa ba,


Malam Sulaiman bai bar duniya ba har sai da yaga jikokin sa daga dukkanin yayansa, Alhaji Auwal Dadyn sama kenan matar sa daya safiya itace suke kira mama yaransa uku , Alkasim da A'isha wadda suke kira da nauwara sai kuma sulaiman, Abubakar wan da suke kira da Abban kasa , matar shi daya da yara biyu duka mata Kulsum da zulfa, sai Usman da suke kira Abban tsakiya, matan shi biyu saratu wadda ta kasance itama yar uwar sa ce daga jalingo malam sulaiman ya auro masa ita, daga nan ya ce ya fito da wadda yake so bayan shekara daya ya aura masa , NADIYA ita ce wadda ya auro, wadda suke kira da Ummi, bata taɓa haihuwa ba, saratu kuwa Ammi ƴaƴan ta uku sha Aban Fatima sai Aliyu, Yusuf shi ne me khadija, wato Dada , yayan su biyar Batul ce Babba anyi aurenta da yaya Alkasim , sai muohamud da kharima sai Muhsin Maryam wato Fahrin mai sunan Yadikko ke nan, goggon su Halima kuma a can jalingo tayi aure dan uwan ta malam sulaiman ya aura mata acewar sa idan ya yi hadin sai zumuncin sa da yan uwan sa yafi karfi, ƴaƴanta hudu itama biyu maza biyu mata, Salma ce sa ar Fahrin kuma kawar ta .


A cikin yan matan gidan su takwas Nauwara da Batul da fatima kawai aka aurar , sai kuma Kulsum da zulfa da suke makaranta da zarar kuma sun dawo duk za ayi bikin.




A yanzu gwagwago Kulsum ƙanwar malam sulaiman tana nan da ranta a can jalingo, kuma danta goggo Halima take aure , san nan kuma kawu jauro shima yaya ne ga malam sulaiman shima yana nan da ran sa , da sauran yan uwan sa da suke uba daya, zuriar kaf tana jalingo hakan yasa ko da yaushe suna hanyan jalingo hatta da yaran kaf ɗin su babu wan da bai yiwa jalingo farin sani ba, kai ko harin da ta kasan ce autar gidan gaba ɗaya tasan kaf ahlin ta na jalingo, yawan saboda suna zuwa akai akai haka suma na jalingo duk da ba kasafai suke zuwa ba sai sabga tun da gurine mai nisa, suna da matuƙar zumunci Tare Da alfahari da junan su da kuma jahar su jalingo, dan nan ne tushen su da nan suke da nan suke takama wannan kenan. 


Kasancewar Ummi bata taɓa haihuwa ba yasa Abbu ya ɗauki Fahrin tun tana karamar da bata fice shekara biyar ba,ya danƙawa ummi saboda tausayinta da suke ji,duk da yawan so da ƙaunar dake tsakanin Dada da autarta Fahrin amma hakan baisa ta hana Fahrin wa ummi ba,


Ummi taji daɗin wannan karamci da sukayi mata dan haka ta karbi Fahrin cikin farinciki da nuna mata tsantsar ƙauna a gaban ɗaukacin mutanen gidan,



Fahrin yarinya ce wadda ta tashi cikin soyayyar yan uwa da iyaye, ga kuma kakarta kai harma da inna kursum dake can jalingo,hakanne yasa take shuka tsiyarta da kuma taɓara son ranta,tana da tsiwa amma tana da sanyi shi yasa baka gane masifarta,tana da tsokana amma akwai tsoro kamar farar kura,ba wuya ka razana ta,tun bayan komawarta bangaren Ummi da wasu yan shekarun da basu wuce biyar ba, Abban tsakiya ya kwanta wani irin ciwo mai matukar zafi wan da har ta kaishi ga kwanciya kas , nan aka shiga magani da neman taimako amma babu wani cigaba , Dr Hisham shine likitan su na gidan kuma Abban tsakiya ne da kan sa ya kawo Dr Hisham amatsayin family Dr , Ummi ce ta ɗan ganta lamarin cutar tashi da mutan ɓoye , hakan yasa gaba ɗaya aka juya kan neman maganin wan Nan ɓangaren , sai kuma Dr Hisham dake duba shi akai akai , da manyan alluran da ya fara yi masa acewar sa sune zasu taimaka wajen warware jijiyoyin jikin sa da suka daskare , dan haka duk san da mutan ɓoye suka sake shi zai tashi ne kai tsaye da taimakon waɗan nan alluran.


Fahrin wata irin baiwa Allah Ubangiji ya bata, tana da matukar saurin fahimtar abu shi yasa ko amakarn ta take da wani irin kokari na ban mamaki, dalili ke nan da a cikin kananun shekarun ta ta fara fuskan tar cewa Lallai fa akwai lauje cikin nadi akan alluran da ake yiwa Abban tsakiya, hakan ne yasa ta yi matukar sa ido har sai da ta gano cewa akwai wani abu da Ummi take son aikatawa bayan wan da take tunanin ta aikata akan Abban tsakiya, a hankali Fahrin ta fara ban kaɗo wasu sirrika game da halayyar uwar goyan ta, wan da kuma a sannu a hankali tayi nisa akan gano manyan sirrikan da take ɓoyewa, Fahrin bata kai ga wan Nan gacin ba Ummi ta gano ta take ta fara fuskantar matsala daga gurin ummin,wan da hakan yasa Fahrin ta kuma gasgata tunanin ta da kaifaffiyar ƙwaƙwalwar ta ke zano mata, saboda mugun kalamai da Ummi ta fara amfani da su gurin razana ƙaramar ƙwaƙwalwar Fahrin gami da son birkita tunanin ta, sai dai kuma duk da yawan tsoro na Fahrin hakan bai sa taji zata saurara daga barin Ummi ta cigaba da aikata munanan halayenta akan ahlin ta ba.



Zuciyar Fahrin da tunanin ta gaba ɗaya sun tafi ne akan son gano wacece Ummi da kuma manufar ta da abin da take kullawa ita da makirin likita maci amana, duk da cewa Fahrin yarinya ce amma tayi matuƙar zurfafa tunanin ta akan hanyar da zata bi dan fallasa Ummi , wan da kuma tunanin ta ya bata tabbacin cewa babu mai yarda da ita kai tsaye ba tare data bada hujja mai karfi akan ummin ba , kuma a yanzu dai bata da shaida ko guda , dan haka dole ta yi tunanin mafita, Adda Kulsum ce kawai ta fado mata, ita kadai ce zata iya taimaka mata , Addan ta Kulsum itace best frind kuma yar uwa mafi soyuwa a ranta , duk cikin yayun ta babu macen da ta dauki sangarta da shagaɓar ta kamar Adda Kulsum,ita kaɗai ke tsayawa ta nutsu ta saurari Fahrin, bata gajiya da ko wane irin shirme da zata kai mata, tana ƙaunar Fahrin tamkar itace suka fito ciki daya ba zulfa ba,wan Nan tunanin da Fahrin tayi shi yasa ta kara dokan ta da dawowar su Adda Kulsum ɗin gida ...


F Y ADAM✍🏽