Chapter 3
by @zahra48
💕
**ƘADDARATA*
*SANADIN* *HASKE* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*
```Page3 ```
*Free* *pg*
A cikin yanayin ne Ummi tayi tafiya zuwa garin su , hakan ne yasa Fahrin ta tattara ta koma bangaren Yadikko, duk wata walwalar ta sai da ta dawo , gaba ɗaya ta man ta da wata rayuwar Ummi , dawowar Ummin ne ya dawo mata da komai , har asalin ta , da rayuwar da ta ke kai halin yanzu.
Wan Nan shine asalin Fahrin da Br BENJA
Washe gari , Fahrin kasa fitowa ta yi , tana daki tana ƙullawa da sakawa , da kirga adadin kwanakin da yarage su Adda Kulsum su dawo,
Shigowar Ummi dakin shi yane ya katse mata tunanin ta , murmushi ummin tayi kana ta ce" zama a ɗaki ba shi zaiyi miki ba, ba zan hanaki yawo acikin gidan nan ba saboda na gaya miki ba gargaɗi nake miki ba,kiyayewarki tamkar kiyaye lafiyarki da mummunar ƙaddarar kine dan haka babu kashedi tsakanina dake!"daga haka tasa kai ta fice daga dakin,yayin da ta tafi tabar zuciya da ƙwaƙwalwar Fahrin cikin ruɗani da tunanin makomar rayuwarta, tsuka tayi kana cikin ƙasa ƙasa da murya ta ce" an gaya miki saboda ke naki fitowa , eh saboda ke naki fita saboda ina tunanin hanyar da zan ɗai ɗai ta mugun nufin ki, in Sha Allah sai na lalata duk wani burinki" ta faɗa tana bin kofar da wani mugun kallo kamar ummin na gurin.
Fitowa tayi kai tsaye ta nufi ɗakin Abban tsakiya,da shigar ta,ta durƙusa a gaban gadon sa tana kallon fuskarsa da bata da maraba da fuskar mamaci, duk da cewa bacci yake , amma ko da ido biyun yake idanun sa kawar zaka gani a tsaye , babu wani da yake da tabbacin yana kallon ko mai ko kuma yana ji, cikin rawar muryar ta tashiga magana a hankali,Abba dan Allah ka tashi karka bari abinda nake hasashe ya tabbata,samun lafiyarka shine zai hana mummunar ƙaddarata tasiri cikin rayuwata,saboda kai ɗin zaka iya zama wata babbar shaida a gareni "ji tayi kamar ana yi mata raɗa wan da kuma ta tabbatar da cewa zuciyar ta ce ke sanar da ita abin da yake gaskiya, Fahrin tashin Abban ki bashi ne zai hana ƙaddararki faruwa ba domin Allah subhanahu wata'ala ya riga ya zana miki rayuwarki tun kina cikin mahaifiyarki dan haka babu wani abu da ya isa hana faruwar abun da Allah ya rubuta miki,domin ita rayuwa ƙaddara ce,kuma kowa da yadda take zuwa masa,wani mai kyau wani akasin haka,dan haka ki rarrashi zuciyarki ki zama mai hakuri da daukar ƙaddara a duk yadda tazo miki,wata ƙil Ubangiji yayi miki kyakykyawan sakamako da ta dalilin haka,dan haka kisa a ranki cewa ko Abban tsakiya ya tashi ko bai tashi ba dole sai abin da Allah ya ƙaddara faruwar sa ya faru" dafe saitin zuciyar da take mata wannan kyakykyawan tuni tayi tare da share hawayen ta,da kuma ɗaukar aniyar bin umarnin kyakykyawar zuciyarta, addu'oi tayiwa Abba kamar yadda take masa a duk lokacin da tashigo wajen sa,miƙewa tayi cikin karfafawa kanta guiwa ta fita daga ɗakin.
Dada ta dubi Yadikko ta ce"nikam yau Fahrin ko bazata islamiya ba ne? Yadikko ta ɓantari goronta, kana tace"kin san dai babu abin da zai hana Maryama zuwa makaranta, saukar haddar su fa saura sati biyu" Fahrin dake shigowa falon sanye da Kayan makaranta tace"wato Yadikko idan bana kusa gulmata kike ko? Ina shigowa sunana na fara ji kin ambata" Dada tace"kinga Ni bana son yawan magana wuce ki tafi tura baki tayi kana ta dubi sashen da dakin Yaya Karima yake tace" ai Ni kika iya sawa ido bayan ga wata nan agabanki tunda tayi Tata saukar ta daina zuwa ta sallama karatun sai Ni da nake zuwa ban dainaba!'yadikko tace"yi naji ikon Allah Ni da kaina kika ji na ce bakya don zuwa mkrt ? dan neman fitina zaki tasani gaba da mita , kuma ita karimatu da kike neman ta da magana kin san ko abanza tunda kin san auren ta za ayi Dada ta ce" shi yasa suke faɗa da kariman saboda rainin da tayi mata kamar wata sakuwar ta" tura baki tayi kana ta yi gaba.
A hankali yake saukowa daga up stairs, taku yake me cike da nutsuwa tamkar wani ɗawisu ko Sarkin da keji da tsantsar mulki, fuskar nan tasa kamar kullum a kirne babu alamar fara a,ɗan tsayawa yayi tare da bin mutanen dake falon da kallo,zuciyarsa a ƙuntacetake da wan Nan muƙamin da aka bashi,irin wan Nan yake gudu wato abin da zai iya shiga cikin lamarin aikin sa, ga kuma haushin yadda zai dinga shiga cikin mutane kuma garuruwa jiha jiha dan yin yawan da Awa,shi kam Allah ya sani yana matuƙar gaba da duk abin da zai shiga cikin lokacin sa , tabbas yana farinciki idan akace yau sun samu karuwa cikin addinin su,to amma surutu da faɗe faɗen ne zai zama aiki a gurin sa, sai dai babu yadda ya iya tun da hakan shine burin iyayen sa akan sa,kuma shima yana kwadayin ladan da zai samu.
Karfin takun sa shi bawa manyan mutanen dake zaune dan jiran sakkowar tasa tabbacin zuwan sa,dan haka cikin tsananin girmamawa suka mike gaba dayansu tare da sunkuyar da kai alamun gaisuwa ga Pastor din nasu,,hannu kawai ya ɗaga musu ba tare da ya ce" komai ba wajen cin abinci ya wuce ya barsu a hankali suka koma mazaunin su suna jiran gamawar sa,cikin nutsuwa ya ɗan tsakuri abinda yaga zai iya ci,yana shirin miƙewa Dadyn sa ya fito tare da momy Rabecca,ɗan rissina kanshi yayi alamun gaisuwa ga iyayen nasa,dafa kanshi mom tayi cikin alfahari take cewa my Benja I'm fraund for you, I hope God bless your life"ameen ya amsa a saman laɓɓan sa, Dady ma ya dafa kafaɗar sa,cike da bashi ƙwarin gwiwa yace"don't worry my son,and take care of yourself,,,,,,shima jinjina masa kai yayi,kana suka rankaya gaba ɗayan su zuwa cikin falon,anan Pastor Mathew ya kuma danƙawa manyan malaman da zasuyi tafiyar yawan da awa tare amanar tilon dansa namiji.
Cikin sauri gard ɗin sa suka shiga buɗe musu motoci da folisawan da zasuyi tafiyar tare,shiga yayi cikin yanayin sa na dan gaggawa,a hankali motocin suka shiga tafiya a jere , motar sace a tsakiya sai ta sauran mutanen su, ta yan sanda da masu tsaro a gaba da baya ya zamana sun sakasu a tsakiya.
Tafe take a hanyar ta ta zuwa islamiya, kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa ta ɗan shiga duniyar tunanin,amma yanayinta na na tsiwa zai sa ka kasa gane damuwar ta, tana gab da tsallaka titin da zai kaita har islamiyarsu taji tashin jiniyar motocin yansanda,hakan ne yasa ta dakata tare da zubawa motocin da suke tunkaro ta ido,dan matsawa tayi kusa da wasu magidan ta saboda jin yadda suke zan can Br BENJA da taimakon sa da dai sauran abubuwa da ta saba ji akan sa, har ɗaya daga cikin su yana cewa , wallahi ina matuƙa yiwa bawan Allah nan sha'awar shiga musulunci saboda kar halayen sa masu kyau ne sai dai abun da ba a rasa ba tun da ɗan adam tara yake " dayan ya ce" kana gani fa yanzu haka yawan da Awa zasu tafi, da ace musulmi ne ai da an samu karuwar Musulunci ta dalilin sa"A hankali Fahrin ta sadada ta ta bar gurin tana mai jin kunar cewa zai tafi ne yawan kira , wata kila ma har da Musulmai a waɗan da zasu karo,take taji bazata iya bari wan Nan tafiya ta kasance ba,duk yadda za ai ta rusa tafiyar nan sai ta rusata , zakaga yawan da awa yanzu zan jaza maka masifa arnen banza arnen wofi ta faɗa a hankali tamai hararar motocin nasu da ke tunkaro su , saida ta shammaci magidan tan nan kana tayi wuf ta faɗa saman titin bayan ta daidai ci sun kusa zuwa inda take,zuciyarta na cike da tsoran wannan ganganci da ta siyasa kanta , to amma ji take ko da ajaline ya riske ta tabbas bata da kaico tun da ta hana yaɗuwar addinin da bai zama na gaskiya ba.
Ƙiiiiiiii,,,,,ƙarar taka burkin motar dake gaba kenan, cikin ƙanƙanin lokaci duk sauran motocin suma suka taka birki ,wan war Fahrin ta zube ƙasa tana wani irin juyi da shure-shure kamar wadda ake son zare ranta, motar dake gaba ita aka bude tare da fitowa alokacin har magidan tan nan sun ƙaraso kan Fahrin suna ambatan innalillahi, wani katon mutum ne ya fito daga motar yazo kan Fahrin ya tsaya , kana ganin sa kasan babu alamar ɗan ɗanon imani a zuciyar sa.
Daga can cikin motar Br Benja kuwa,jin antsaya ba tare da an sanar ba,hakan yasa driver Adebayo fitowa dan ganin abinda ke faruwa a tawajen,haka sauran yan sandan duk suka fito aka zagaye Fahrin wadda a yanzu ta ɗauke numfashin ta gaba daya kai kace matacciya ce, ɗaya daga cikin yansandan ne ya durƙusa gaban Fahrin ɗin yana cewa yanzu me ya kamata muyi tunda kunga sauri muke kuma ga abinda ya faru wanda dole sai an kai yarinyar nan asibiti dan duba lafiyarta!'wani daga cikin drebobin yace"sai dai idan wasu ne zasu kaita asibitin wasu kuma su wuce can, dan kun san ba zaiyu a fasa tafiyar nan ba tunda kowa yasan da yadda Oga ya amince da ita,Ade drevern Benja da yake tsaye a gefen wajen yace"amma ya kamata a sanar da oga saboda kar hakan ya jawo mana matsala kunsan halinsa bai yadda da jira babu dalili ba"yana gama faɗar haka ya juya da sauri dan sanarwa da ogansa abinda ke faruwa,
Fahrin dake sheme akasa duk tana jin abin da ke wakana, zuciyarta kuwa addu'a kawai take da fatan samun nasara akan waɗan nan kafuran, dan tasan indai suka fita da wuya ace koda acikin musulmai ba asamu wanda yayi musu mubaya'a ba to da wahala a rasa acikin kafuran tsaunuka da na kauyuwa musamman wadanda basu da takamaiman addini,ita kuma abinda bata fata kenan,samun karuwa a cikin addinin da bana gaskiya ba,dan haka insha Allah yau saita wargaza tafiyar nan,wata zuciyar tace da ita,to Fahrin idan kin hanasu yau zaki hanasu gobene? runtse idanunta ta kumayi tana mai fatan ace hakan ba zai kuma faruwa ba,ba zai je ko ina ba ,shiwa? Zuciyar ta ta kuma yi mata tambayar da bata da amsarsa domin bata san ko waye ba,amma tasan tana tsananin jin kishin kasantuwar sa cikin addinin sa, haka nan take jin bai dace da addinin sa ba,tabbas wannan mutumin zai matuƙar bada gudunmawa wa addinin Musulunci,to amma tasan cewa hakan Abune mai matukar wuya,kawai dai tana kidan ta da rawar tane ita kadai , mutumin da ko sanin fuskar sa ba tayi ba,sai dai duk wannan ɗin lamarine mai matukar sauki a gurin ubangiji.
Kwance yake yayi luf a bayan motar tamkar wanda yake cikin ɗakinsa kan saman haɗaɗɗen gadonsa,idanunsa a lumshe suke kamar koda yaushe,har drevern Ade ya shiga motar amma Benja bai motsa daga yadda yake ba hasali ma tamkar wanda baya cikin motar ko yake bacci, cikin tsananin ladabi Ade ya sanar dashi abinda ke faruwa,tsawon lokaci bai tanka ba kuma bai motsaba, sai can ya ɗan motsa laɓɓansa wanda Ni kaina banji abinda yace" ba sai dai kuma shi wanda akayiwa maganar tsaf ya fahimci abinda aka sanar dashi,dan haka cikin sauri ya kuma fita daga motar, yana zuwa yasanar dasu abinda Br BENJA yace"wani ɗan sanda dake gefan Fahrin ya ce"anya zamu bari yallaɓai ya bar tafiyar nan saboda wannan yarinyar?Ade cikin gurbatacciyar Hausar shi yace"idan kana iya hanata sai ka bada himma Ni kam abinda ogana ya umarceni shi zanyi,tunda yaga dacewar kaita asibitin da kanshi Ni bani da wata damuwa da hakan kuma motar da yake ciki ya umarceni dana kaita dan haka sauran tunanin abinyi ya rage maku"yana gama faɗar haka ya sunkuya dan daukar Fahrin,Fahrin kuwa zuciyarta neman tsagewa take saboda tsananin fargaba, dan fa tabbas taga wannan ƙasurgumin arnen neman daukarta yakeyi,ita kuwa da ta bari ya shafa mata dauɗar najasa gara ta hakura da komai,sai dai kuma shima abinda take yin fa Abune mai muhimmanci a rayuwarta Wato hana cigaban yaɗuwar wani addini bayan nata, addu'oi ta shiga antayowa kala-kala dan neman ɗauki a gurin ubangiji.
Ade yana shirin kai hannu jikinta yaji an buge hannun nasa,da sauri ya ɗago sai yaga wata mata bata kai ace mata tsohuwa ba amma ta manyan ta,tace"kai gafara nan a taimaka maka, baka ganin ita macece? kuma baka tunanin idan addinin ka ya baka damar taɓa macen da ba muharramarka ba,me yasa bazayi tunani akan nata addinin ba? duk da cewa sha ani ne na ceton rai amma ai ka gwada sa arka ko zaka dace da samun mace yar uwarta da zata taimaka maka dan kai maka ita motar"tana faɗa tana cicciɓo Fahrin da take cikin wani irin farinciki dan tabbas da zasu kula da yanayin fuskarta sai sunga canji alokacin saboda yadda ta yalwata da annuri,Ade da bai wani fahimci Yaren sosai ba sai hakan yasa baiji kaifafan kalaman matar akansa ba da kuma sukar addinin sa da tayi a fakaice,shi ya nuna mata motar tare da bude mata gefansa na mai zaman banza ta kwantar da Fahrin wadda Ade ya kwantarwa da kujera dan taji daɗin kwanciya,godiya yayiwa matar kana ya shiga motar Ba tare da ya kuma bi ta kan mutanen da suke tare ba,
Fahrin kuwa jin sanyin a.c. da na aifreshner da kuma sassanyan turaran Ms Benja,sai hakan ya kuma bata damar yin kane kane akan kujerar da take jinta tamkar katifa,take baccin da bata samu yinsa ba saboda damuwar ummi ya kwashe ta,
Bugun zuciyarsa ne ya karu akan na da,sai yayi saurin ɗora hannun sa kan saitin zuciyarsa tare da lumshe gajiyayyun idanun sa,kai tsaye Ade ya nufi asibitin da yasan dole nan zasuje wato Lasuth wanda anan babban aminin Benja wato Hashim yake aiki,mintuna ƙalilan ne suka kaisu dan dama shine mafi kusa kasancewar asibitin acikin anguwar ikeja yake,suna tsayawa Hashim wanda tun suna hanya Benja yayi masa text , ya ƙaraso bakin motar cikin sauri,buɗewa yayi tare da cewa abokina ya akayi haka ai da kayi haƙuri ka bari ankawota kai kuma sai ka wuce ku tafi"wani irin kallo Br Benja ya watsawa Hashim ba tare kuma da ya furta komai ba,nos din da suka ƙaraso da gadon ɗaukar marasa lafiya su suka katse Hashim daga maganar da yaso yi,dan haka sai ya basu umarnin da su ciro mara lafiyar yaci gaba da cewa ku wuce da ita emagency basu da matsala da ƴan sanda zamu iya karbarsu saboda tare da yansan dan abin ya faru,jinjina kai sukayi tare da cicciɓo Fahrin,zabura Hashim yayi tare da nuna Fahrin da yatsa bakin sa na rawa yace"wannan ai Fahrin ce" kayan makarantar jikinta shine ya bashi tabbacin makaranta zata tsautsayi ya gifta da ita,jin Hisham ya ambaci sunan yarinyar da suka bige yasa Benja ya ɗago kansa sosai dan ƙara fahimtar abun sai kuma idanunsa suka sauka akan kyakykyawar fuskar Fahrin wadda ayanzu baccin ta kawai take shaka cikin kwanciyar hankali da kore duk wata damuwa dake fuskarta da karkashin zuciyarta,ji yayi ƙirjinshi ya buga da karfi fin na baya,wanda har sai da hakan yasa ya runtse idanunsa,Muryar Hisham yaji yana cewa maza ku kaita emagancy wannan ai ƙanwata ce nasanta Nine likitan gidansu "Benja yakewa wannan bayanin wanda shi kuma yayi halin nasa,dan kuwa banza yayi dashi babu wata alama da zai nuna maka cewa yaji abinda Dr Hashim yake faɗa masa,haushin hakan yasa Hashim ɗin ya zuba masa harara tare da bin bayan gadon da aka tura Fahrin.
Kwanciya ya kuma yi yana tunanin da yasan wannan fitsararriyar yariyar ce bazai fasa aikinsa dan ceton rayuwarta ba,sai dai kuma duk da ya samu damar fecewa ya kasa tafiyar haka ya cigaba da zaman jiran dakon halin da Fahrin ɗin take ciki, duk da shi ɗin dama mai taimako ne amma sai yake jin kamar da wani dalilin bayan na taimakon .
Abun da Dr Hisham ya farayi shine kiran Ummi ya sanar da ita halin da Fahrin take ciki,kafin nan ya shiga ɗakin da aka kwantar da ita dan dubata,maganganun da taji ne ya farkar da ita tare da ankarar da ita inda take da kuma tunawa da abinda ta aikata,a hankali ta ɗan buɗe idanunta ba tare da kowa ya kula da hakan ba ganin ba taga uban gaiyar ba yasa ta fara tunanin ko sun kawota ne su kuma sun wuce sabgar gabansu,duk da cewa ba tasan shi ba amma tasan shi din zai kasance na musamman ,ganin Dr Hashim bai firgita ta ko bata mamaki ba tunda ta riga da tasan shi din likitane,tunanin ta ya tsaya a inda taji Dr yana magana inda kuma anan ta samu tabbacin cewa arnen yana nan bai tafi ba , wato jira yake yaga farfaɗowar ta,hakan yasa ta samu nutsuwa tare da shan alwashin bazata farfaɗo yanzu ba,tana ji Dr Hashim ya karaci ƴan dube-duben sa ya fice daga dakin.
Samun Br Benja yayi tare da yi masa bayanin sakamakon da cewa my friend katafi kawai babu wata damuwa tare da yarinyar, dan ina tunanin firgita tayi kawai shine abun da yasa ta suma amma nan da wasu yan mintuna zata farka"ko kallonsa Benja baiyi ba balle Dr yasa ran yaji abinda ya sanar dashi,Dr Hashim ya harde hannu yana kallon miskilanci da tsabar wulaƙanci irin na aminin nasa,ƙwafa yayi tare da cewa Wallahi ina jiwa matar da zata aureka,dan ba karamar wahala zata shiga ba,wa yasani ma ko zakayi auren tunda bamu da tabbacin lafiyarka!'ya faɗa dan cusa masa haushi kamar yadda shima ya cusa masa,sai dai ko ajikinsa saima lumshe idanun sa da yayi yana cigaba da sauraran tsammani tare da bugun da zuciyarsa ke masa.
Cikin sauri da rawar jiki Ummi ta nufi falon yadikko,inda ta samesu har da mama da Dada sai Mami (itace matar Abubakar Abban kasa kuma maman su Kulsum da zulfa) duk a zaune, Yadikko ta dubeta cikin kulawa tace"ya akayi ne Nadiya?cikin yin fuskar tausayi tace wallahi Yadikko Dr Hashim ne yake sanar dani cewa yanzu wasu suka kawo Fahrin asibitin su sun bigeta!"a rikice Dada ta dubi bakin Ummi dake bayanin an kade mata fahrin, Yadikko kuwa kuka tasa tana tafa hannu yanzu Fahrin ɗin tawa aka kaɗe da mota?ke kam Nadiya baki iya kawo sakon arziki ba,da sauri Ummi tace"a'a Yadikko kar ku tada hankalin ku babu abinda ya sameta Dr Hashim ya tabbatar min da cewa tsorata kawai tayi shine dalilin da yasa ta suma amma yanzu haka ma ta farko bacci takeyi shine zanje na taho da ita"mama tace" to Alhamdulillah bari nazo muje Allah ya kiyaye gaba"duk da haka Yadikko ba tabar shan majina ba tana sharce hawaye tare da cewa Ni dai ku faɗa min gaskiya ko dai wani abu ya sami jikata kike ɓoye min dan kwana biyun nan ina yawan yin mafarkai Barka tai akan Fahrin dan Allah ku faɗa min gaskiya"ƙirjin Dada kuwa banda dukan tara-tara babu abinda yake, Allah ya sani dauriya da alkunya kawai takeyi amma zuciyar ta tana gab da kasa jurewa lallai tana san sanin gaskiyar halinda autar ta take ciki,tunanin ta ne ya katse yayin da taji ummi na cewa a'a maman yara ba sai kinje ba zanje Ni kaɗai kinga bai kamata abarsu a cikin wannan halin ba dan daga Yadikko har Dada suna bukatar lallashi"mami tace "ai da kunje ɗin zan kula dasu a nan"mama tace ke mami yanzu kika ɗora girki abin zai yi miki yawa , kije kawai Ummi Allah ya jishshe mu Alkhairi, Yadikko tace Ammi kuma bata nan da kun yafi tare"Ummi tace a'a Yadikko babu wata matsala yanzu zamu dawo, to Allah yasa muji Alkhairi cewar mami kenan"Ummi ta amsa tare da saurin ficewa daga falon.
Fahrin kuwa tunda ta samu tabbacin sai ta farko zai tafi sai ta samu damar shantakewa tana shaƙar baccin ta hankali kwance,dama ba salla zatayi ba dan haka ta samu damar bacci bayan ta lallaɓa ta shiga bathroom ta gyara jikinta,dan ta ƙudurta a ranta sai la asar zata nuna musu ta farka,dan tasan lokacin babu yadda za ayi ace za ayi wata tafiya duk da tasan a yanzu ma da karfe biyu ta buga ba lallai ne tafiyar ta yuwuba,Dr Hashim kuwa duk shigowar da zai yi sai yaga Fahrin bata farka ba sai hakan ya shiga bashi tsoro dan haka bai daddara ba yakuma zubawa Br Benja bayani,wanda hakan ne yasa Br Benja motsawa daga zaman jiran tsammani,kai tsaye Dr Hashim yaga Br BENJA ya fito daga motar ya fara takawa cikin nutsatstsan takun sa, daga dukkan alamu dai dakin da aka kai Fahrin ya nufa, bin sa da kallon mamaki Dr Hisham ya yi, eh mamaki mana yasan cewa Benja mai kula ne mai kuma tausayi ne , amma baza ka same shi da abin da ya aikata yau ba tun da yana da waɗan da suke kula masa da wani nan ɓangaren da duk wani abu na taimako,to amma wan nan na musamman ne kular ta musamman ce , damuwar ta musamman ce, jinjina kai ya yi tare da bin bayan sa.
F Y ADAM✍🏽