ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 4

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA* 

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page 4 ```



 *Free* *pg*



"Da sauri Dr Hishim yabi bayanshi,tun da yasan ba sanin dakin ya yi ba,tsabar miskilanci ne yasa ba zai iya tambaya ba,Br Benja kuwa kai tsaye ya ya nufi ɗakin da zuciyarshi ke raya mishi anan wannan fitinanniyar yarinyar take kwance,shi kansa yayi mamakin yadda akayi yazo dakin kaitsaye ba tare da ya samu tabbacin shine dakin ba.



Tana jin alamun taku tayi saurin dafe kanta tana juyawa a hankali kamar irin wadda take cikin tsananin ciwon nan, gajiya tayi da baccin pritendin din da take shi yasa ta sauya salon nata,zuba mata ido yayi bayan yasamu damar shigowa dakin zuciyarshi na ci gaba da bugawa kamar yadda ya saba tun lokacin da ya fara saka Fahrin acikin kwayar idanunsa, cikin yanayin wahala ta daga kanta dan ganin wanda ya shigo ɗakin ,zaro manyan idanunta tayi tare da dafe ƙirjinta kamar ba mara lafiya ba azahiri,dama wannan kyakkyawan ingarman namijin shine ƙasurgumin kafurin da ake cewa Pastor?Amma dai gaskiya abin ba kama,tunda take bata taɓa ganin me kyau da tsari kamarsa ba,gashi da wani irin kwarjini wanda ya kamata ace cikakken musulmi ne ke dashi,hakanan taji tana daɗa jin kishin kasancewarsa acikin addinin da bana gaskiya ba, duk da cewa ba gaya mata akayi ba, amma haka nan taji cewa ajikinta shine Br BENJA."



Yadda ya tsareta da shu uman idanun sa yasa taji wani irin sanyi jikin ta ya dauki wani irin rawa kamar mai zazzaɓi, yanzu dama wannan katon mutumin ta zazzagawa rashin kunya ranar?wata zuciyar tace"ai sa ar ki ma baya jin Hausa tunawa da hakan yasa ta sauke wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya,tare da maida kanta ta kwantar tana cigaba da satar kallon sa ta gefan idanunta,shigowar Dr Hisham ne ya katse shurun da ɗakin yayi, cikin sauri ya ƙaraso gaban gadon da Fahrin take yana cewa yaya dai Fahrin kin farka?me yake damunki yanzu?"baki jiwo a ko ina ba dai ko?"ya shiga jero mata tambayoyin a ɗan rude da alamun kulawa,kanta ta kuma dafewa tana yatsina fuska kana tace"kaina ne yake ɗan ciwo"yace"ayya sannu zai daina amma sai kin sha magani faduwar da kikayi ne yasa kan naki yake ciwo"kaji algungumi kamar wanda akayi agabansa ko kuma ya damu da rayuwa ta, Fahrin ta faɗa ƙasa-ƙasa wanda hakan yasa Dr Hisham yaɗago kansa yana kallonta,gabanta ne ya faɗi take ta shiga kame-kame ji tayi yace"me kike bukata kuma yanzu? Ajiyar zuciya ta sauke tare da maida idanunta ta rufe ba tare da ta ce" komai ba.


Br Benja kuwa ɗan tsaki yayi tare da yin gyaran murya yana mai Da ɗa cusa hannayen sa cikin aljihun cot dinsa,sai alokacin Dr Hisham ya tuna dashi a dakin,yana shirin yin magana aka turo kofar dakin kai tsaye kuma aka shigo,jin bude dakin yasa fahrin ta buɗe idanunta sosai ai kuwa caraf ta sauke su akan na Ummi da take nufo gadon datake kai,take idanunta suka cika da ruwan hawaye har ga Allah Fahrin bata kaunar ganin ummi a duk inda take,duk farincikin da take ciki gushewa yake,haka ba ta da wata sakewa indai Ummi na waje,hakan ne yasa bata san sanda hawaye suka fara gudu kan kyakkyawar fuskar ta ba.


Dafa kanta Ummi tayi cikin kulawa tace"Fahrin garin yaya haka ta faru me yasa bakya kula idan kina tafiya"? Shi yasa bana son tafiyarki ke ka ɗai!"ta faɗa tana gogewa Fahrin ɗin hawayen da suke ta gudu bisa kyakykyawar fuskar ta,duban Dr Hisham tayi cikin neman karin bayani akan matsalar Fahrin ɗin,fahimtar haka yasa Dr Hisham yayi gyaran murya tare da yi mata bayanin abinda ke da akwai, cikin gamsuwa ta gyaɗa kanta tana mai duban sashen da Br Benja yake tsaye ba um ba ummm kamar wanda aka rutsa da bakin bindiga,nuni tayiwa Dr Hisham da alamun san sanin kowayeshi,Dr Hisham ne yayi mata bayani har da wanda ba tanema ba wato matsayin Benja a gurin sa da kuma gurin mutane baki daya da irin nasarorin da yake takawa,dakatar da shi tayi ta hanyar daga masa hannu da cewa ya isa ban nemi sanin komai daga gareshi ba wannan ba hurumina bane ba kuma abinda ya dameni bane"ta faɗa cikin ya tsine fuska,sanin halinta yasa Dr Hisham yaja bakinsa ya tsuke.



Yadda taji idanunsa na yawo ajikinta shine ya dakatar da hawayey da take tayi tun shigowar ummin Tata,ɗan tura bakinta tayi tare da murguɗa shi tanajin wani sanyi na bin sassan jikinta da dukkan ƙashushuwan jikinta,a hankali ya kawar da idanunsa da kuma zuciyarsa dake kanta, ya juya kaitsaye ya bar ɗakin cikin yanayin takunsa na ƙasaita wanda hakan yaja hankalin su baki ɗaya,da wani matsiyacin kallo Ummi tabi faffaɗan bayansa dashi tana mai jin wani irin abu me kama da tsana akansa wanda ta kasa gane ta dalilin ta? tunda dai babu wata dangantaka tsakanin su,amma kuma haka nan takejin haduwarsu da juna ba Abune wanda zai zama Alkhairi ba,to meye zai zama matsala a tsakaninsu">? Saurin kawar da tunanin tayi a ranta ta juya tana maida kallonta kan Fahrin.


Da sauri Fahrin ta janye idanunta daga kallon da tabi Br Benja dashi kamar yadda Ummi tayi sai dai kallon kowa daban kuma manufarsa daban wanda kuma dukkan ninsu basu san manufar ba, cikin tsawa Ummi tace"tashi mu tafi gida munafuka Ni banma yadda dake ba sai mun koma zaki min bayanin inda kika samo wannan kafurin me zuciyar kafuran!"a hankali Fahrin ta tashi jikin ta a sanyaye,gyara hijabin jikinta tayi kana ta zura takalmanta da Dr Hisham ya dai-daita mata su a gabanta,zurawa tayi ta mike tare da bin bayansu,a yanzu dai ta riga ta kawar da wani nan matsalar dan taji a ranta cewa tayi nasara wannan tafiya ta fasu baza kuma ayita ba insha Allahu.



Suna zuwa kafin su shiga falon Yadikko Ummi tayi saurin rungumota jikinta,da sallama suka shiga falon wanda hakan yasa dukkan mutanen dake zaune a afalon suka miƙe tare da maida hankalinsu kan masu shigowa,Hatta da Abbu Abban kasa Dadyn sama ne kawai baya gari amma duk sun dawo Yayyanta kaf sai da suka dawo gida duk asanadin kururuwar Yadikko dan duk ta ɗagawa kowa hankali,Abbune ma ya dakatar dasu amma da tuni sunbisu asibitin, Anty Batul ce tayi saurin kama Fahrin tana duba ko ina na jikinta, Yadikko ma cikin sauri ta tashi ta kamosu gaba ɗaya tana ci gaba da zuzuta lamarin,Dada kuwa mace mai tsananin yakana da alkunya duk yadda takai da zumuɗin san ganin halin da ɗiyar ta take ciki amma haka tayi hakuri sai kallo da take binsu dashi,tana satar kallon ɗiyar Tata , to anan dai kowa ya samu nutsuwa ganin lafiyar autar Dada kalau kamar ma ba mota ce ta bigeta ba,nan akashiga tattalinta tana narkewa kamar wata jaririya abinda dama take buƙata kenan wannan soyayyar sai dai kuma tayi mata nisa, ga dukkanin alamu ma dai baza ta kara samun dorarriyar soyayya daga danginta ba.



Lokacin da kowa ya dawo gida akayi zaman cin abinci,yau Fahrin cike take da farincikin samun yancin wannan rana,dan haka sai ta fara tunanin hanyar kwana a bangaren Yadikko ba tare da an hanata ba duk da tasan tarin ƙalubalen da hakan zai jawo mata wajen ummi,sai da ta fuskanci dare ya farayisai tayi luf ta ɓuge da yin baccin karya,ai kuwa tashin duniyar nan taki tashi idan an dagota sai ta zame ɗan karma ace wani ya dauketa acikin yayyanta ya kaita,dole dai uwar naƙi haka Ummi ta hakura amma ta tanadar wa Fahrin irin rashin mutuncin da zatayi mata, Fahrin bata jin magana kullum kwanan duniya karawa kanta yawan zunubai take a wajenta, lokacin dai yana nan zuwa dazata cimma burinta" ƙwafa tayi tare da ficewa daga falon".



Duk juyin da zatayi sai ta ganshi cikin idanunta,haka nan yanayinsa yake bata tsoro da kuma tausayi na kasancewar sa kafuri,ɗan tsaki tayi tare da kuma janyo fulo ta rungume,tayi wannan dabara ne dan tasamu bacci amma wannan mugun ya hanata anya ma kuwa ba maye bane? to idan ba haka ba me yasa ya kasa barin zuciyarta me yasa ya kasa barin idaniyarta?me yasa ya kasa barin gangar jikinta wanda duk motsin da zatayi sai taji kaifafan idanuwanshi akanta?a fili tace"kai irin wadan na arnan fa basu maida tsafi abakin komai ba yanzu haka ma shan jinin mutane yake shi yasa yake son shanye nata jinin kuma shi ne dalilin da yasa ta kasa mantawa dashi,kuka ta saka tare da dukunkune kanta tanajin tsoran kar yazo ya dauketa,domin yanzu da ta kuma tunawa abokin Dr Hisham ne sai ta kuma tabbatar da cewa shi din matsafine tunda shi kanshi Dr tana zarginsa da shanye jinin Abban tsakiya,ranar dai baccin Fahrin kadan ne dan sosai ta razana da abinda zuciyarta ta saka mata akan Br BENJA.



Bakin Pastor Mathew har kumfa yake saboda tsabar masifa,babu wanda ya sanar dashi abun da Benja ya aikata kasancewar duk saida ya basu gargadi mai zafi a kan hakan tafiyar tun da yasan cewa Benja baya so dan haka yaja musu kunne akan kar su bari Benja ya kufcewa wan Nan tafiyar,Br BENJA bai ce komai ba haka Ms mathew bai sa ran zai tanka masa ba shi yasa yana gama faɗansa ya haura sama yabar Br Benja a wajen,Br ba tare da nuna wata damuwa ba ya maida jikinsa da kansa cikin kujerar da yake kai tare da lumshe gajiyayyun idanunsa da suke bashi haushi,saboda yadda suka kasa daina hasko masa waccen maras kunyar yarinyar,tare da tuna mishi halin da take ciki,ɗan tsuka yayi tare da miƙewa cikin sauri-sauri da yar sassarfa ya nufi apartment ɗin shi.



Da fargaba Fahrin ta tashi duk da cewa sallolin da tayi cikin dare da karatun da ya zame mata jiki duk bayan sallar asuba sun taimaka mata wajen rage mata damuwa da kunci,ta dau alwashin cewa bazata bari dukan su suyi nasara akanta ba,ta daura ɗamarar yaƙi da duk wani mai shirin ruguza farincikinta,hatta da Ummi ta ɗauki damarar rage tsoranta domin ta fahimci da tsoranta take amfani dan neman ruguza rayuwarta,tasan cewa bazata iya rabuwa da bangaren Ummi ba,shima saboda iyayen su da sukayi matuƙar yadda da ita babu wanda zai fahimce ta wata ƙil ma suce dan bata son zama a wajen ummin ne shi yasa zata yi mata kage, ba wan da zai fahimci abun da take nufi akan manufarta,da wannan kwarin gwiwar ta kimtsa ta fita dan yin sauran al amuranta na yau da kullum.



Ummi kuwa babu irin mugun abun da bata saka akan Fahrin ba,tana jin tsanar yarinyar har cikin maƙogwaron ta,abu ɗaya ne zuwa biyu shi yake dakatar da ita akan mummunan ƙudurinta akan Fahrin.



Koda ya tashi da safe bai tashi daniyar zuwa ƙauyukan da zasuje jiya ba,sai ma san sanin halin da fitsararriyar yariyar take ciki,babu wani abu aransa sai tunanin ta dan a ganin shi wannan hakkinshi ne tunda ta sanadinsa aka bigeta dan haka yazama dole ya kula da lafiyarta,waya ya ɗaga ya kira Dr Hisham domin yana da tabbacin ta wajensa kawai zai samu labarin da yake son ji dan gane da inda sai samu Fahrin din,kira ɗaya kuwa Dr Hisham ya ɗaga dan yasan halin abokin nasa baya kira biyu,shuru ne ya ratsa ta tsakanin su,sanin da Dr Hisham yayi cewa Benja bazai taɓa fara yi masa magana ba hakan ne yasa shi yin gyaran murya tare da cewa ya akayi ne sarkin bebaye na duniya me kake da bukata a cikin wannan safiya?dan na tabbata kiran nan yana da matuƙar muhimmanci!'ya ƙarasa maganar da sakin murmushi,ɗan tsaki Benja yayi kana cikin fuskar gizago da muryarsa me cike da nutsuwa yace"ya jikinta? Sarai Dr ya fahimce shi Amma sai ya waske yace"wa kenan? shuru Br yayi ba tare da ya amsa masa ba sai jan numfashi da yake a hankali,Dr Hisham yayi dariya tare da cewa tunda bazaka amsa Ni ba sai anjima"da ƙyar Br ya ce"I mean acsident girl"Dr ya ce aiyo wai Fahrin kake nufi?shuru yayi masa yana jin zuciyarsa na tafasa akan titsiyan da Hisham yake masa ya kuma kasa sanin dalilin da yasa ya kasa aje wayar tun farko kamar yadda ya saba idan yaga zai masa shaƙiyanci da rainin wayo,yana son katse wayar amma na tacciyar zuciyarshi na da ɗa dagewa da san sanin halin da yarinyar ke ciki,Dr Hisham ne ya katse masa tunani da cewa ai yarinyar tuni ta samu lafiya dama ai ba wani babban abu bane kawai yar buguwa ce da kuma raki irin na yara idan kuma duba ta kake son zuwa kayi bari na baka address ɗin su, su da ya bashi address ɗin kana ya dora da cewa idan kaje kace in,,,,ƙit yaji Benja ya katse wayar ba tare da ya barshi ya karasa maganar sa ba,bin wayar yayi da kallo tare da yin ƙwafa.



Maida kansa yayi ya kwantar tare da lumshe idanunsa,sai da ya samu mintuna biyar kana ya mike cikin nutsuwa ya fito babban falon inda a nan ya tarar da Dady da Madam Rabecca suna karyawa,zama yayi tare da gaida su fuskar nan babu fara a ko guda,mom tashi ce ta zuba mashi idanu tsawan wasu sakanni daga bisani kuma ta maida kan Mr Mathew girgiza kanta tayi tare da aje spoon ɗin dake hannunta tace"my son yaushe zaku kuma shirya tafiyar tunda wan can ya rushe? Shuru babu amsa sai chips and egg da yake ta ɗurawa a bakinsa,Mr Mathew ne ya dubeshi kana cikin haɗe tashi fuskar yace"U dont answer the question?a Hankali ya ɗago ya dubi mahaifin nasa kana cikin haɗiye takaicin dake ranshi yace"zamu samu time"when? mahaifin nashi ya kuma tambayarsa, miƙewa yayi tare da duban agogon diamon ɗin dake hannunsa alokaci ɗaya kuma yana goge bakinshi da tishue,ɗan duban su yayi a kai-kaice yace"I will telk you later"ba tare da ya saurari abinda zasu ce ba ya fice cikin tafiyarsa ta sassarfa,idan yana sauri,duban juna sukayi ko wannen su da abinda yake tunani cikin ranshi, sai can mom ta ce" bai ma tsaya yaji sakon kiran da mama ke mashi ba,(kakar su take nufi mahaifiyar ta?dad ya ce"yasan halin ta ki rabu dashi zasu haɗu ne"da wan Nan suka bar maganar Benja.



Har Abbu ya dawo Fahrin bata leka ɓangaren Ummi ba sai dai taje ta duba Abba wanda shima bata samu zama kamar yadda ta saba ba,saboda tana gudun haduwarta da Ummi,tana jin dawowar abbu bata je ba sai da ta tabbatar ya samu nutsuwa,kana ta nufi falon nashi tana mai fatan dacewa da abinda zata nema.


Sallama tayi tare da ƙarasowa gabansa, cikin farin cikin ganin sanyin idaniyar tasa ya ce"Alfahrina ya jikin naki ina fatan dai babu inda yake miki ciwo?langaɓar da kanta tayi cikin yanayinta na sangartattun yara tace"Abbu naji sauƙi kuma nayi missing ɗin ka"dariya yayi tare da ɗora hannunshi saman kanta,yace" to ai gani Autar Abbu me zan samu ?dariya tayi har lobawar kumatunta da na kasan habarta suka baiyana,ta ce"Abbu dan Allah ka barni na zauna a gurin Yadikko tun da kaga yaya Karima aure za ayi mata" zuba mata ido Abbun ya yi kana ya ce"Fahrin anya kuwa babu wani abu a can kasa saboda naga yanzu gudun Ummin ki kike wan da kuma sam hakan da kike yi bai da ce ba, shuru ta yi idanun ta har sun cika da ruwa,tana shirin yin magana ya katse ta da cewa a'a auta dan Allah kar kiyi haka mu bar wan Nan magana ki nemi wani abu amma ban da wan nan"goge kwallar fuskarta ta yi kana ta ce"to dan Allah,kace "Yaya muhd ya dauko salma ( salma yar Goggon su Halima) wallahi sam babu daɗi gidan kaga yaya Karima ba kulani takeyi ba wai dan kar na rainata kuma kaga dama Aure za ayi musu,ita kuwa salma tunda tayi candy kaga sai muci gaba da karatun mu tare muyi zaman mu a dakina kaga Ummi ma zata kuma jin daɗi ta samu karin ƴa!'shuru Abbu yayi, yayin da Fahrin take ta jan suratul nasri har sai da Abbu ya kula dan har ta fara fitowa fili,dariya yayi a ɓoye ba tare da ya bari Fahrin ɗin ta kula ba,yace"to yanzu kina ganin iyayenta zasu amince su bamu ita tunda idan na fahimceki a wannan karon ba hutu kikeso tazo ba!"da sauri ta daga kai tare da cewa kai Abbu kamar ba ka da iko da iyayen nata?shuru ya kuma yi can kuma ya numfasa tare da cewa anya Fahrin wannan bukatar taki zata samu? Idan na isa da Halima ai ban isa da uban ta ba tun da a matsayin yaya yake a gurina"tuni har ta fara hawaye cikin san fashewa da kuka tace"dan Allah Abbu kayi haƙuri ka barni na bi Yaya Muhammad ɗin sai na roki umman jalingon zata bari mu taho tare!"ta ƙarasa maganar cikin kuka,Abbu yace"to kuma meye abin kuka tunda haka kike so tashi kije za muyi magana da Dadyn sama da na kasa,daga nan sai suyiwa yayan naku magana sai ku tafi Harda Kariman da goggona Kulsum tunda gobe zata dawo daga makaranta, cikin tsallen murna ta rike Abbun nata tare da cewa kai Abbu dama gobe adda Kulsum zata dawo amma babu wanda ya sanar dani, Ni ban ma san ya akayi na bari lissafi ya kwace min ba,to Adda zulfa ita kuma sai yaushe zata dawo"?Abbu ya ce"

" ita kuma sai wani satin zasu kammala jarrabawarsu kinga da kin hakura da dauko salma kawai tunda ƴan uwanki zasu dawo kinga zaki rage kewar da kike magana akanta"rau-rau tayi da ido tare da cewa"Ni dai a'a Abbu sufa bazasu yarda da zaman ɓangaren Ummi ba Ni kuma yar tayin kwana nakeso ba ƴan hira ba kuma ka manta duk Aure za ayi musu su duka?jin jina kai yayi tare da cewa au haka ne fa kina da gaskiya to ki bari kawai itama zulfar ta dawo sai ku tafi jalingon gaba ɗaya"bata musa masa ba saboda bata san yawan musawa mahaifinta dan haka cikin murna ta ce"yauwa Abbuna nawa Ni kaɗai godiya nake Allah ya bar min kai"a'a Fahrin banda san kai ke kaɗai fa kikace tura baki tayi kana ta ce" to mu duka amma nawa yafi yawa"ya ce"haka ne fa tashi maza kije kar dare yayi miki!'tashi tayi tare da yin salut ɗinshi kana ta fara tafiya cikin faretti dariya sosai Abbu yakeyi yana mai alfahari da yar tashi dan duk cikin yaran shi tafi kowa saka shi nishaɗi da farinciki tun randa tazo duniya ya fara samun wasu bododi da alkharai wan da har abin yaso bashi mamaki to amma ikon Allah yafi da haka, shi yasa da yasa mata suna Maryam sai yake mata lakabi da Fahrin,take kuma sunan yabita har kuma yau yana alfahari da haihuwar Fahrin.



Sosai Fahrin take murna shi yasa ba tare da fargaba ba ta wuce ɗakinta kai tsaye ta cigaba da murnar dawowar yan uwanta,ga kuma zuwan salma tasan ko da bikin ne yazo zatafi yin walwala tunda da salma,tana cikin shagalinta taji anturo ƙofar dakin tare da shigowa,cak ta tsaya da birgimar da take a tsakiyar gadonta tare da zubawa Ummin ido, ƙarasowa Ummi tayi cikin ƙara tsare Fahrin da mugun kallo,yayin da Fahrin ɗin tayi kokarin bawa kanta dakiya da jarumta,hakan ne ya hanata ruɗewa yayin ganin ummin kamar yadda ta sabayi,zama tayi gefan gadon tana ci gaba da aika mata saƙonni ta cikin idanunta,sun jima a haka kafin Ummi tadanko kunnen Fahrin da ƙarfi cikin matuƙar ɓacin rai ta ce"Ni zakiyiwa wayo Fahrin Ni zaki rainawa hankali saboda kawai kin shirya tozartani kikayi hakan ko kuma saboda mugun nufin ki na kokarin tonawa rayuwata asiri yasa kikayi hakan?da sauri Fahrin ta shiga girgiza kai hawaye kuwa tuni sun wanke kyakykyawar fuskar ta farincikin da take ciki ya juye ya koma bakinciki,duk da tayi kokarin dakewa amma hakan ya gagara,wata irin tsawa Ummi ta daka mata tare da kara jan kunnen ta tamkar zata tsinke matashi,ta ce"ok to me kike nufi da hakan ko dai so kike ki nunawa yan gidan nan bakya farinciki da zama dani?nan ma girgiza kanta tayi tana mai wani irin kuka mai sosa zuciya,ga raɗaɗin zuciya ga kuma na azabar zafin da kunnen ta yakeyi,ok to wallahi Fahrin ki kiyaye ni har yau ina mai tabbatar miki da cewa bani zaki taimaka ba kanki zaki taimaka domin yin duk wani motsi dan tozarta Ni dai-dai yake da kin bada fansar rayuwarki ne dan haka sai ki kiyaye idan har kina son ci gaba da yin rayuwa mai kyau,Fahrin idan kika bari sharrina ya fara bibiyar ki zaki shiga tasku"jan kunnen ta kuma da karfi kana ta saketa ta fice a dakin cikin fusata.



Wani irin kuka take mai cike da damuwa da neman ɗauki,tabbas ta fara hangarwa kanta wata irin rayuwa mai cike da tarin kaddarori ma banbanta,tashi tayi ta waɗa toilet ta ɗauro alwala ta shimfida sallaya ta fara miƙa kukanta gurin sarki zuljalalu wal ikram.



Shigowar Adda Karima dakin shi yasa tayi saurin kimtsa kanta , tare da saita kanta, duban ta kariman tayi kana ta ce" kizo ɓangaren Yadikko anzo dubaki"dubani kuma waye yazo dubani? Dalla idan zaki fito ki fito idan kinje kya gani"daga haka tayi ficewar ta,da sauri Fahrin tabi bayan ta dan kar ta yi mata nisa ta tafi ita kaɗai,



Tun kafin ta shiga falon ta fara shako wani sassan yan ƙamshin turare , hakan yasa ta ɗan lumshe idanun ta , kafin sanyin jiki da bugun zuciya su biyo bayan kamshin da taji, Sallama tayi Dadyn sama ya amsa, zuba masa ido tayi yana zaune cikin kujera kamar wani sarki Wa ce a hannun shi yana taɓa ta kamar kwai,zama tayi a gefan Yadikko tana mai ci gaba da mamakin ganin sa, zuciyarta kuwa sai bugawa take, Allah yasa dai ba baya da kura ta bari ba.