Chapter 5
by @zahra48
💕
**ƘADDARATA*
*SANADIN* *HASKE* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*
```Page5 ```
*Free* *pg*
A hankali ya ɗago idanun sa masu kamar an diga mai a cikin su, ya zuba su kan kyakkyawar fuskar Fahrin da take masa kallon tsoro da razanar abin da ya kawo shi har cikin gidan su,kamar daga sama Fahrin ta tsinkayi Muryar sa cikin wata irin nutsuwa yana cewa ya jikin naki? Kusan daskarewa tayi a gurin saboda mamaki, to amma gudun kar agano ta sai kawai ta fiske tare da cewa da sauki" Yadikko ta ce" amma kam anyi dan albarka kayi kokari sosai idan wani ne ma ai gudu zaiyi ba zai ma tsaya ya saurareta ba, Allah ya yi maka albarka kaji" Fahrin sai zungurar Yadikko take yi, nuni ta ke mata shi fa bai san wan Nan albarkar ba , amma ina ga dukkan alamu dai Br BENJA ya matuƙar burge Yadikko tun da ga yadda take ta yabon shi, ɗan tura baki Fahrin ta yi cike da takaicin Yadikko kana ta mike tana cewa to an gode ku gaida gida"
Yadikko ta rakata da unbola tana cewa abu korar sa kike shakiya da kika samu yazo har gida ya duba ki" miƙewa ya yi yana gyara zaman cot din jikin sa , Yadikko ta ce" tafiya zakayi ne? Jinjina kai ya yi tare da dukawaya ajiye mata bandir na dubu yana cewa Allah ya bata lafiya" kai yaro zo ka kwashe kudin ka , zuwan da kayi ma ya wadatar" daidai nan Abban kasa ya shigo,gaisawa su kayi a mutunce , Yadikko ta ce" maza karbi lambar shi a dinga gaisawa yaron mutunci ai ba a rabu duka ba" har waje Abban kasa ya rako shi a nan suka haɗu da Dady shima ya yiwa Benja godiya suka karɓar wa Yadikko lambarsa kamar yadda ya buƙata,
Washe gari da Fahrin da walwalar ta ta tashi, bata kasance mai barin damuwa a ranta har tayi nasarar kwamushe walwalarta ba,gwana ce wajen mikawa Allah kukanta gwana ce gurin ibada, tana da ilmi me tarin yawa, cikin ƙananan shekarunta zakayi mamakin littattafan da ta haɗiye a ƙwaƙwalwar ta,dan haka take yawan amfani da ilminta da baiwar da Allah ya bata gurin kiyaye dokokin ubangiji shi yasa ko damuwar ce tazo ta kanyi sauri gurin mikawa Allah lamarin shi yasa sai wani lokacin kaga kamar bata tare da wata damuwa a ranta, duk da cewa da akwai ta amma tana ƙoƙarin ya kice ta da ƙoƙarin gayyato farinciki saman fuskarta ko dan ahlinta.
Tsaf ta gama hadawa Ummi karinta da duk wani abu da take bukata,ba tare da ta tsaya sauraran fitowar ta ba tayi ficewarta zuwa ɗakin Abba,zama tayi a kusa dashi tare da kama hannunsa cikin nutsuwa kamar ba Fahrin uwar giggiwa ba, ta ce "Abba ya kamata ka buɗe bakinka domin amsa min tarin tambayoyina,kai kaɗaine zaka zama shedata a duniya kai kaɗaine zaka tayani fahimtar da mutanen gidan mu wacece ummi,bazasu yadda damu ba har yanzu bani da kwakkwarar shaida akanta sai dai ina da tabbacin cewa akwai wani babban abu da take ɓoyewa a akwai wani kulli mara kyau a cikin zuciyarta a kwai abinda take son aikata mana Ni da kai akwai abinda kwanciyar ka anan ke nufi a kwai tarin abubuwan mamaki kunshe a tare da ita wanda nake son sani" amma Abba bazan iya Ni kaɗai ba ina da rauni dole sai da matai maki a tare dani,goge hawayen ta tayi saurin yi jin alamun takun dake nuna alamun shigowa ɗakin za ayi,sauri tayi ta ɓoye a bayan labulen window saboda tana da tabbacin Ummi ce tare da Dr Hisham,.
Sai da sukayi dan dube-dube kafin Dr Hisham ya ce"Hajiya Nadiya Allurar nan kullum kara farashi take inajin tsoran ranar da zata zo ki kasa siyanta"wani irin mugun kallo ummi ta watsa masa cikin ɓacin rai ta nuna shi da yatsanta ta ce"ka dinga lura da irin maganganun da zasu dinga fitowa daga bakinka zuwa gareni,har yanzu baka san ko mai a kaina ba, shi yasa kake tunanin akwai ranar da zan gaza da siyan allurai,to inaso kasawa ranka cewa Ni nan Nadiya Sharif alƙali bazan taɓa gazawa akan siyan alluran da zasu dawo min da farinciki na ba dan haka ka cigaba da aikin ka yadda ya kamata ko dan ci gaba da samun abinda zaka siyi tsumman da zaka saka"duk da cewa Dr Hisham yaji zafin maganar Ummi ta karshe amma sai ya danne saboda abin da yake samu daga Ummin baza su fadu ba ,allurar ya haɗa yana mai sakin wani shu umin murmushi a saman lebban sa, yana sokawa Abba allurar yay wata irin mika tare da jan numfashi,wanda hakan ya kusa tonawa Fahrin asiri, saboda yadda ta firgita da yadda Abban yayi, hakan kuwa yaja hankulan su sosai,
Bin dakin suka shigayi da kallo loko da sako,kana a hankali Ummi ta shiga takawa zuwa bakin windown da Fahrin take ɓoye,take zuciyar Fahrin ta shiga dukan tara-tara, addu a ta shigayi bakin ta kuwa har rawa yake wajen ambaton Allah, Allah baji rokon bayin sa take a wajen Allah ya amsa ya kuɓutar da ita daga abinda Ummi zata iya aikata mata,Ummi tana shirin daga labulen kenan aka turo kofar dakin,a lokaci ɗaya tare da sallama, Ammi ce ita da Yaya Muhd hakan yasa Ummi ta fasa yin abinda tayi niya duk da cewa zuciyarta bata amince mata da cewa babu kowa a gurin ba kuma zaton nata akan Fahrin yake domin ita kadaice shu umar da take yi mata laɓe.mama tace"au ashe kuna nan? Dr Hisham ne ya gaida ta yana mai saɓa jakar sa a kafaɗa ya ce"to Ni na wuce asibiti Allah ya ƙara sauƙi yana faɗa yana mikawa Yaya sulaiman hannu fita yayi bayan sun gaisa zuciyarsa na mai ci gaba da raya masa abubuwa masu tarin yawa domin kara samun wadata daga uwargijiyar sa,yaya sulaiman ya gaishe da Ummi kana ya fara gyara Abban kamar yadda ya saba yi masa duk sfy fita ummi tayi tabar Ammi a ɗakin amma sam ranta babu daɗi.
Fahrin dai ta gaji iya gajiya bata jin zata iya jurewa har sai sun fita kafin ta fito,tana cikin wannan tunanin ne Ammi ta fita yaya sulaiman kuma ya shiga toilet, hakan ne ya bata damar fitowa daga maɓoyarta tana sauke ajiyar zuciya,zama tayi daga inda ta tashi kafin shigowar ummi,yaya sulaiman ne ya fito hannunshi rike da roba da ɗan ƙaramin towel Wanda zai gogewa Abba jikinsa,ya ce"Fahrin banji shigowarki ba?cikin zubawa Abba idanu zuciyarta kuwa ɗauke da tauyinsa ta ce"eh yanzun nan na shigo"'gyada kanshi yayi kana ya ce" tashi kije zan gyarawa Abba jikinsa kafin nan kya dawo"tashi tayi tana cewa yaya ba kai zaka dauko Adda kursum ba?girgiza kai yayi tare da cewa bani bane, Safwan ne kuma ya tafi tun ɗazu? murmushi tayi wanda ke nuni da farincikin da take ciki,kana ta fice daga dakin,
Dafe ƙirjinta tayi, idanunta cike da tashin hankali, cikin matuƙar razana take duban Ummi dake tsaye a kofar dakin,tana binta da wani irin razanannen kallo mai cike da tsana da tuhuma mai zafi,a hankali ta daga ƙafafunta dan barin wajen Muryar Ummi tayi mata tsinke cikin dodon kunnen ta, tabbas kishiryawa fuskantar mummunar ƙaddarar ki wadda ke da kanki kike jawo ta, idanunki su shirya fara ganin bakin duhu hasken da suka jima suna gani zai yaye,ina mai da ɗa yi miki albishir a cikin rayuwar da zaki fuskanta, tabbas babu komai a cikinta sai baƙin duhu da kuma tarin ƙalubale!"daga haka ta wuce ta bar Fahrin cikin yanayin da tasaba barinta idan ta gasa mata munanan kalamai masu tsananin ɗaci da bauri,tafiya kawai take bata san in da take jefa ƙafafunta ba,magana take ita kadai wanda har saida ya fito fili ba tare da ta san da hakan ba, cikin yanayin fitar hayyaci take wulla hannayenta tare da ambatan sunan Allah, ya Allah me hakan ke nufi?me zatayi min?ya Allah me yasa bazan bari ba kamar yadda ta bukata ta kuma gargadeni?ƙarar waɗuwar abu a ƙasa shi ya ɗan dawo da ita hayyacinta, karo sukayi da Abbu wan da zai je duba dan uwan shi, cikin sauri ta duƙa ta kwaso masa karamar wayarsa da ta tarwatse ta miƙa masa tare da wucewa cikin sauri,kamar wata mara gaskiya,wani irin kallo Abbu ya bi Fahrin da shi cike da mamaki da tunanika akasin masu kyau,bai samu sharafin yi mata magana ba har ta shige falon yadikko, cikin yanayin rashin gamsuwa da ɗora ayar tambaya akan Fahrin ɗin Abbun ya shige sashen dan uwan nasa.
Yadikko tabi Fahrin da ido lokacin da ta waɗo falonta kamar an jehota,riƙe baki Yadikko tayi cike da masifa ta ce"ke hankalinki daya kuwa? haka ake shigowa gidan mutane a garinku?tura baki Fahrin tayi tare da cewa, garinku kenan jalingo"ungo nan Yadikko ta faɗa tana wara tafin hannunta akan Fahrin,ba tare da ta kuma cewa komai ba ta wuce daki dan bata cikin mood din biyewa Yadikko a yanzu.
Misalin karfe biyu na rana Safwan ya sauke Kulsum a farfajiyar tsakar gidan su, cikin wani irin zumudi da tarin farinciki,Fahrin dake dakon zuwanta tun ɗazu ta kwaso da gudu tare da rungume Kulsum har suna neman faduwa,Kulsum itama cikin dariyar isowar ta ga yan uwanta lafiya da ganin ƙanwarta abokiyar shawararta, ta ce" kai autar Abbu da Ummi karki yada Addar taki mana!"
A hankali Fahrin ta janye jikinta, kana ta rike hannun Kulsum ɗin bakinta yaki rufuwa,murna uku ne ya haɗe mata,ga na dauko salma ga kuma dawowar 'yan uwanta da kuma uwa uba saukar su da yarage saura kwana biyar,Dada dake nufosu tace"maraba da uwar masu gida, Fahrin dan Allah ki saketa ta shiga ta huta!'Dada ta faɗa tana maida kallonta ga Fahrin ɗin da ta fuskanci sauyi daga gareta akan yanayin damuwar da ta fuskanci ta na ciki ɗazu da safe, Kursum ta kuma rike hannun Fahrin tana cewa muje ƙanwale Dada ai Fahrin ita zata warware min gajiya da dadaɗan labaran ta na wauta da shirme da kuma ban haushi!'ta kare maganar tana rungumota jikinta ganin yadda ta fara tura baki tana haramar zubda hawayen da suka zamar mata dabi'a a kwanan nan.
Gida tuni ya dauka da karadin Fahrin,ta hana kowa zance da Kulsum,saboda taki matsawa ko can da nan daga gareta,To ai dama kowa yasan shakuwar dake tsakanin Kulsum da Fahrin, dan haka babu wanda yake mamakin zumuɗin Fahrin din,
Ummi kuwa ganin take taken Fahrin,yasa ta maida kanta wata kalar tausayi,saboda tana matukar jin fargabar kar dawowar Kulsum yasa Fahrin ta samu damar kufcewa daga hannunta,bayan kuma zaman Fahrin ɗin a hannunta tamkar wani tsanine na hauhawan nasarar ta da kuma samun mafaka wa sirrinta da Fahrin ɗin ta fara bankadowa,hakan ne yasa ta kara maida kanta abar tausayi a matsayinta Na wadda bata taɓa haihuwa ba,kuma jama ar gidan suke matukar tausaya mata.
Hakan ta kuwa ya cimma ruwa,domin daga Dada har mama zuwa Yadikko kallo suke Binta dashi na nuna tsantsan tausayi,a yayin da take cewa Fahrin , Autar Abbu naga tun da Kulsum ta dawo kin kasa barinta,amma dai ina fata bazaki min kaura ba,domin jikina ya bani kina kokarin gujemin ganin 'yar uwarki ta dawo!"tsit falon yayi bakajin komai sai ƙarar fanka dana a c,sai kuma zuciyar Fahrin da take wani irin bugu da sauri da sauri,tabbas da ace hankulansu akan Fahrin yake to da zasu iya jin ƙarar bugun zuciyarta,sai dai kuma ina dukan su zuciyoyinsu sun tafi ga tausayawa Ummi akan maraicin rashin haihuwa,
Yadikko ce ta numfasa gami da cewa,ayya ai ita bata soma ba, sai kace ba gida daya suke ba, duk sanda taso zasuga juna!'Mama tace Fahrin bazata yi hakan ba, tunda tasan bacci ne kawai zai raba su, Yaya muohamud dake saman dinnin ya ce"to ban da shirme ma ai su ɗin ba mazauna bane duk Aure za ai musu,Karima ta kyalkyale da dariya tare da yiwa Fahrin ɗin gwalo,ai kuwa kamar jira take ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya da ban mamaki ga wanda bai san asalin kukan ba.
Cike da mamaki kuwa suke kallonta,sai dai kallon da mahaifiyarta take mata ya ban banta da wanda sauran suke mata,kallon mutane biyu ne ya ban banta da kallon dake kan fuskokin mutanen dake falon.
Tabbas Dada tana zargin a kwai abinda yake damun ɗiyar ta ta,jikinta ya bata cewa akwai babban dalilin da yake yawan saka autar ta kuka, lallai ya kamata ta binciki damuwar diyarta kar taje garin kawaici ta cuci kanta da yarinyar ta,
Abunda ummi ta fahimta a kan fuskar Dada,ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,duk da cewa tasan a yanzu Fahrin bata da ta kamaiman abinda zata faɗa a kanta,amma tasan ko yaya uwarta zata saurareta kuma zata taya diyarta ta yakin da ta dauko domin wargaza mata shiri da ƙoƙarinta na ta tona mata asiri,abu ɗaya ne bata da tabbaci a kan sa, shin Fahrin tana ɗaukar huɗubarta da gargadinta tare da barazanar ta ne? ko kuwa tarko ne take son Dana mata dan kaiwa ga samun nasara? tabbas Ummi bata da wannan yakinin bare ta cire fargaba akan Fahrin na cewa bazata iya sanarwa da uwarta abinda takeji take kuma gani ba.
Adda Kulsum cikin tausayawa da kuma tsananin shakuwar dake tsakaninsu,ta kuma jan Fahrin ɗin zuwa jikinta,a hankali ta shiga shafa bayanta,kana cikin raunin da itama bata san daga inda ya fito ba, ta ce"haba ƙanwali meye ne na kukan? naga dai muna cikin gida daya,to meye kuma kike tunanin zai iya rabamu? cikin rage sautin kukan da take ta ɗago da fuskarta dake sharkaf da hawaye,ta bawa Adda kursum amsa, da amsar da ta girgiza zukatan iyayenta da 'yan uwanta,Adda akwai mana Ni nasan akwai abinda zai rabamu ku baku sani ba,amma tabbas Ni nasani kuma inaji a jikina akwai ƘADDARAR da take shirin rusa farin cikina da kuma na masoyana!'
Ammi ce ta katse Fahrin din daga zan tukan da ta keyi wanda suke kama da na mai kwance War kai a cikin kunnuwan su,ta ce"haba Fahrin me yasa kike son saka mana shakku a kanki?me yake damunki wanda kika gwammaci kiyi mana jurwaye a kan ki faɗa mana asalin abinda yasa kike wan nan fade-faden!"Fahrin na shirin buɗe baki dan bawa Ammi amsa, amma sai Ummi tayi saurin taran numfashin ta da cewa,haba dan Allah maman zulfa, kuma sai kace baku san halin sakarci da kuruciyar Fahrin ba,kawai tana yin duk wan nan ne saboda na barta ta kwana da Addarta, juyowa tayi ga Fahrin ɗin da ta zubawa Ummin idanunta tun farkon fara maganarta, cikin san kawar da shakkun da Fahrin ta saukar a zukatan yan uwanta da iyayen ta ummin ta ce" haba Fahrin ai ba sai kin yi min dabara ba idan kina so na barki ki kwana tare da 'yar uwarki?
To in dai ni ce na hakura dan yau ɗaya dai ki kwana gobe in Allah ya kaimu sai ki koma,kinji maza share hawayen ki,duk kin daga mana hankali da wannan hawayen naki da babu wanda yake bukatar zubarsu,ta faɗa tana wani ɗan murmushi da ita kadai tasan manufarsa.
Da wannan kalaman na Ummi zuciyoyi suka nutsa,amma fa ban da uwa mafi kusanci da jin raɗaɗin dake zuciyar diyarta,Dada har yanzu jikinta a sanyaye yake da lamarin sanyin idaniyarta,kuma tana nan akan bakanta na lalubar damuwar Fahrin.
Ummi ta gano hakan a tare da Dadan,hakan ne yasa, take ji kamar tayi wauta na barin Fahrin ɗin ta kwana a nan,duk da cewa ba a bangaren Dadan suke ba,lallai ya kamata a daren nan ta samarwa kanta mafita bazata taɓa barin Fahrin da Dada su keɓe guri ɗaya ba,domin hakan yana nufin abubuwa da dama na asara a gareta.
Dabara ce ta faɗo mata,dan haka cikin kulawa ta ce"Kulsum ya kamata Ku tashi kuje ku kwanta,dan ki samu ki huce gajiya,ga kuma auta itama tasha kukan taɓara ya kamata ta kwanta dan kar ciwon kai ya samu damar kama ta"Yadikko ta ce"haka ya kamata su yi,ke Kulsum maza ku tashi ku wuce daki saura ku tsaya surutu kar kuyi bacci!'ba tare da musu ba Kulsum ta kama hannun Fahrin suka shige dakinta na asali wanda ya sha gyara saboda dawowarta.
Abunda ummi bata sani ba, shine sam Dada bata mata wani kallo bayan na me kyautatawa a gareta a matsayin wadda ta rike mata diya amana,dan haka zargin abinda yake damun Fahrin sam bai dan ganci Ummi ba a zuciyar ta,ba ta tunanin Ummi ce sanadin damuwar Fahrin,wani abu can daban take kawowa,wanda take son jinsa daga Fahrin ɗin,kuma bata da niyar tuhumar Fahrin a wannan lokacin,saboda Dada mace ce mai kawaici,sau da yawa tana son kebewa da diyoyinta amma bata iyawa a idon mutane sai ta faki ido.
Ummi ba ta samu nutsuwa ba, saida ta tabbatar kowa ya nufi makwancinsa, a hakan ma sai da ta kuma leƙawa ɗakin Kulsum ta tabbatar da cewa sunyi bacci,kana ta juya ta tafi ɓangaren ta.
Da sassafe Ummi ta dako sammakon zuwa bangaren Yadikko,ba ta taɓa kwana cikin fargaba ba sai jiya,ba ta kuma taɓa sanin cewa 'yar ƙaramar yarinya kamar Fahrin zata iya zama barazana a gareta ba,a safiyar yau din ta tashi ne da nunka azabtar warta ga Fahrin ɗin tare da matso da burinta kusa, tabbas Dr Hisham yayi gaskiya da ya ce Fahrin zata iya zama ɗan hakin da ka raina,da wan nan tunanin ta kai ga sashen Yadikko,ta kuwa ci sa a babu kowa a falon dan haka kai tsaye ta nufi ɗakin kulsum,.
Murɗa hadle ɗin ƙofar da zatayi kenan taji Muryar Fahrin cikin kuka tana maganganun da suka razanar da zuciyarta, bata dawo hayyacinta ba,ta tsinkayi Muryar Kulsum,Ummi ta dafe ƙirjinta tare da zaro idanu daga bisani kuma tayi wani shu umin murmushi,juyawa ta yi ta fasa shiga ɗakin,to me zata shiga tayi kuma yanzu? bayan aikin gama ya gama,saura kuma ya rage nata,muddin a yanzu su Kulsum suka san cewa taji su,to lallai bazasu bata damar hukunta su ba,lokaci ne yayi da zata fara nunawa Fahrin asalin wace ce Nadiya,lokaci ya yi da za ta san abinda ta dade tana son sani, murmushi ta kumayi,kana a fili ta ce"kaza garin tone-tone ta tonowa kanta abinda zai zama ajalinta, Fahrin watan uƙubarki yayi watan mummunar ƙaddarar ki ya kama."
Kulsum ta kuma rike hannun Fahrin kamar bazata saki ba,ta ce"Fahrin kiyi haƙuri kuma kiyi shuru da bakin ki,ki ci gaba da rike sirrin nan kamar yadda ta gar gade ki,idan ba haka ba hakan na iya jawo tashin hankali mara misali,kamar yadda kika sani ne a yanzu babu wanda zai yadda da maganar ki a kan ummi, tabbas Ummi ta san abin da takeyi shi yasa ta kama kowa na gidan nan da fuskarta ta karya,ta kuma ɓoye ai nahin fuskarta ne domin samun damar cimma mummunar manufar ta ,naji daɗi da kika yi tunanin sanar dani wannan al'amarin Ni kuma insha Allahu zanyi iya kokari na na ganin na taya ki zaƙulo manufar ummi a kan mu baki ɗaya domin kawar da baragurbi daga cikin ahlin mu."
Benja dole ka yi tafiyar nan Umar Ni ne wannan nake baka ba wai shawara ba!'maganar da Ms Mathew ya farayi kenan lokacin da yake kusan tar Benja dake tsaye jikin karamar durowar littattafai dake babban falon gidan,dan dakatawa ya yi da abin da yake yi, daga bisani kuma ya zaro littafin da yake son ɗauka ya fara takawa dan barin wajen ba tare da ya ce"ko mai ba, Benja magana nake maka fa"Ms Mathew ya daka masa tsawa ransa a matuƙar bace, hakan ne yasa shi ɗan dakatawa tare da bawa mahaifin nasa muhimmanci,kana kuma a hankali ya motsa tattausan lip ɗin sa, ya ce"yaushe ka ke son nayi tafiyar?sai a lokacin Ms Mathew ya dan sauko daga fushin sa, ya ce" ko gobe ma ina so ka tafi"jin jina kai Benja ya yi kana ya ce"amma dad kayi min afuwa zuwa kwana hudu saboda ina da shari ar da zan gabatar a cikin satin"shuru ya yi yana jiran abin da dad din nasa zai ce" ok ba damuwa in dai zaka din kayi kokari bana so a kuma samun a kasi har tafiyar ta kuma rushewa" dady ya faɗa yana hayewa sama,shima Benja wucewa ya yi ban garensa, yana ci gaba da jin yanayin da yake ji duk lokacin da ya tuna fuskar fitsararriyar yariyar.