ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 6

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA* 

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page6 ```



 *Free* *pg*



A ranar bata bar Adda Kulsum ta huta ba, haka suka fita rabon katin saukar haddar su,kuma

Har Fahrin ta gama yawan ta da yinin ta a cikin gidan ta dawo,Ummi bata nuna mata wata alama da za ta nuna cewa ta ji hirar su da Kulsum ba."



Jiki a sanyaye ta koma bangaren Ummi, farin cikin da ta kasance a cikin sa, sai take ji dama hakan ya ci gaba da dorewa, dama duk abin da yake faruwa mafarki take yi,sai dai ina, tasan cewa wan Nan ɗin ƙaddarar ta ce,


A cikin wan Nan rana ne kuma Benja ya tashi da karɓar baƙuncin aminin shi kuma ɗan uwan shi,wato james,a cikin mamaki ya kuma duban fuskar wayar tashi domin tabbatar da cewa lambar Najeriya yake gani ba ta Istanbul ba,kara wayar yayi a kunnen shi bayan ya danna ok,



Ya broth ka zo filin jirgi ka ɗauke Ni Ko ka turo drever"tashi zaune yayi daga kwanciyar da yake, fuskar shi cike da fara ar, da ba a fiya ganin ta akan kyakykyawar fuskar shi ba,amma duk da farin cikin da fuskar shi ta nuna hakan bai sa shi kasa sakin miskilar Muryar shi wajen yiwa ɗan uwan nashi tambaya ba,ya ce"James ar u serious"James ya ce"na taɓa yi maka irin wannan wasan?malam ka fito kawai ko ka turo a ɗauke Ni na gaji da yawa Ina son yin tozali da fafana da kuma ɗan uwana"cikin nutsuwa Benja ya janyo wata karamar waya dake gefan shi kan bedsite ya daddanna tare da karata a kunnen shi, kaje airport ka dauko James"daga can ɓangaren aka amsa da Yes Oga,tashi yayi ya fada toilet yana jin Ni shadin zuwan dan uwanshi kuma aminin shi.



James ɗa ne ga yayan Madam Rebicca,shi yasa ya kasance ɗa garesu ita da Mr Mathew tunda duk sun kasance dangi ɗaya,ya zauna a tare da su na wasu yan shekaru, James yana matukar girmama mutanen nan guda biyu shi yasa suke masifar sonsa, dan suna ganin shi tamkar su nala da Benja ne,



Duk irin shakuwar dake tsakanin Dr Hisham da Br Benja,Bata kai ta tsakanin sa da James ba,James ɗan uwan sa ne kuma aminin sa haka kuma addinin su ɗaya,shi yasa aminta da shakuwar su ta zarta ta Dr Hisham,james ya jima da tafiya ƙasar Istanbul yin wani cos Wanda ya shafi ɓangaren addinin su,James ya kasan ce mutum mai tsananin son addinin sa wanda hakan ne ya janyo masa farinjini da kauna wajen Mr Mathew,James ya sawa ransa da zuciyarsa sai ya gaji Mr Mathew ko ma ya fishi, dalilin ke nan da yasa shi yin kaura da taimakon Mr Mathew ya tafi bincike akan addinin su,sai kuma gashi ya samu nasarar samo abinda yaje nema,har gashi ya dawo lafiya cikin samun nasarar rayuwa.



Zaku so ganin Benja a yayin da yayi arba da ɗan uwan sa, haka Mr Mathew da madam Rabecca farin ciki suke tamkar zasu haɗiye james,kafin kace meye tuni an cika gabanshi da kayan abinci iri-iri.



Bayan wasu a wanni,gaba dayansu a zaune suke a babban falon kana ganin Madam Rebicca kasan tana cikin farin ciki na kasancewar ta gata ga Benja yau a inuwa ɗaya har tsawon mintuna ana hira dashi,duk da dai ba kasafai ya fiya saka baki a hirar tasu ba, amma murmushi yana yawan subcewa daga laɓɓan shi,zuwan Dr Hisham ne ya ƙarawa hirar tasu armashi,sai a lokacin ne james yake jin labarin matsayin da Benja yake kai,dubansa ya kai kan Br Benja cike da farin ciki ya ce"am happy duk da cewa ya kamata ace nayi fushi kasan cewar babu wanda ya sanar dani wannan al amarin mai dadin ji,bayan kuma kun san bani da wani buri a duniya wanda ya wuce ɗaya daga cikin mu ya gajeka dady,amma hakan ta tabbata a kasa sanar dani duk wayar da muke yi, farin cikin da na samu kaina a ciki ne kawai ya goge wannan laifin da aka yi min"ya faɗa yana damƙe hannun Benja cikin nasa hannun,cikin sauri Dady ya ce"a'a kar kayi mana wata fassarar my son kawai dai an samu tan garda ne shi yasa babu wanda ya sanar da kai amma duka muna mai neman afuwar ka"ya faɗa yana mai haɗe hannayen sa,da sauri James ya kama hannun Dady yana cewa haba Dady babu komai nayi muku uzuri fatan mu Allah ya taya shi riko"gaba ɗaya suka amsa" yayin da kuma mom ta ɗora da cewa sai ka kuma yi masa faɗa da kara nuna masa muhimmancin nauyin da aka dora masa,san nan ka dinga taimaka masa tunda kaima ka zama babban malami mukami ne kawai baka dashi amma baku da wani ban-banci!'gyada kanshi yayi yana murmushi ya amsa da cewa mom kar ki damu in dai wannan ne zan kula da komai,a ko da yaushe ina tare da Benja babu wata matsala"duk abinda suke tattaunawa Benja bai ce komai ba sai latsa wayar sa da yake ta faman yi,Dr Hisham ne ya fara tashi yayi musu sallama ya bar gidan ba tare da ya samu damar ganawa da Dadyn Benja ba.




Dukan sityarin yayi da ƙarfi yana mai cije yatsa, tabbas yaso ai watar da abinda ya kaishi gidan a yau,sai dai kuma zuwan James shi ya dakatar da komai,da kuma kasancewar Benja a gida,amma yana da yakinin cewa burinsa yana dab da cika,domin shi ɗin bai kasance waɗaɗɗe ba,Dr Hisham kenan.



A cikin kwana biyu da James ya yi ya fahimci abubuwa da dama a game da Benja da kuma muƙamin Pastor da aka rataya masa,sam ya fahimci cewa Benja baya son wan Nan muƙamin,hakan da ya lura ne yasa shi ƙara kusantar Benja domin jan hankalin sa.


Ranar juma a akayi saukar su Fahrin,saukar da ta tara manyan malamai da gomnoni kai harda sarakai ma, Fahrin ta samu lambar yabo ta ko ina , duk inda ka.juya sunan ta ake faɗa , da irin burge mutanen da ta yi,malaman kan su sai da sukayi alfahari da Fahrin bare kuma iyayen ta, kyaututtukan da ta samu kuwa ba su kirguwa , sai dai Allah ya sa karatun ya amfani al umma allahumma Amin.



Ummi luf tayi ta ci gaba da yin bakan wa Fahrin da kulsum,ta kuma yi tunanin basu kafa domin taga iya nasu ƙoƙarin,shi yasa har yanzu ba tayi wani yunkuri da zai nuna mu su alamar cewa taji hirar su ba,sai dai kuma sanin da Fahrin ta yiwa Ummi yasa ta fara hasaso wani abu dan gane da shirinta a gare su, tabbas Fahrin ta ji a jikinta cewa akwai wani abu da ummin ke son ƙullawa,lokaci ɗaya kaifaffar ƙwaƙwalwar ta ta bata amsar da take nema,take tsoro ya shiga zuciyar ta tsoron da take jin sa har can cikin ƙasan ranta,tabbas a irin salo da wayo na Ummi zata iya tabbata ace ta gano abin da suke shiryawa ita da Kulsum,to idan hakan ta kasance kuwa lallai rayuwar Kulsum na cikin haɗari tabbas wani abu zai iya faruwa da Kulsum,guntse bakin ta ta yi a yayin da wani irin kuka yake son kufce mata,shin me yasa tayi hakan me yasa bata ji gargadin ummi ba? yanzu gashi zata saka rayuwar 'yar uwar ta cikin haɗari,kuka ta saka sosai zuciyarta na kuma cika da matsanan cin tsoro da fargabar da tunda take bata taɓa jin ta ba,shurun Ummi a gareta masifa ne yanzu ya zatayi ke nan? bayan aikin gama ya riga ya gama,me ya same ta haka da taurin kai? Gashi ta na shirin kara janyo wata cikin matsalarta,anya kuwa ya kamata ta sako salma cikin haɗararriyar rayuwarta mai cike da ƙalubale iri-iri?.



A yau ne kuma Adda zulfa ita ma ta sauka,wanda sam Fahrin ba ta yi zumuɗi da rawar jiki akan yadda tayi a dawowar Kulsum ba,amma babu wanda ya tsaya bincikar dalilin hakan.


Dada ce take ta sunturi daga sashen ta zuwa sashen Yadikko,babu abin da take so ta kuma ƙagu dashi a halin yanzu wanda ya wuce ganawa da gudan jininta Fahrin,tana ji a ranta da zuciyar ta lallai ya kamata ta ji damuwar Fahrin,tana jin tsoron yawan damuwar da take hangowa a fuskar Fahrin,zargi kuwa har ta rasa wanda za ta yi akan abin da yake damun Fahrin ɗin,shi yasa yau ta kasa zaune da tsaye so take kawai ta jawo yarta daki ta saka labule.


Tsaf ummi take hankalce da Dada, dan tun ranar da ta fahimci abinda Dadan ke son yi, shike nan ta saka mata idanu, babu dama ko kiran Fahrin ta yi ta saka ta aiki sai Ummi ta karba tayi ko ta saka su a gaba da su nan gaidin ɗin Fahrin,yau din ma tun da ta lura da yadda Ummin take shiga da fita, kawai sai ta tsiro anguwa ta ce da Fahrin ta dauko mayafinta zata yi mata rakiya,turus Dada tayi lokacin da ta fito daga kiching ɗin Yadikko ta tsinkayi umarnin Ummi ga Fahrin, cikin sanyin jiki ta ƙaraso cikin falon tare da zama gefan mama zuciyarta sam babu daɗi, dan haƙiƙa yau taso ganawa da Fahrin ɗin, itama Fahrin ɗin cikin mutuwar jiki ta tsame jikinta daga tsakiyar su Adda zulfa dake ta mitar anyi sauka babu ita,ta shiga daki ta dauko mayafinta zuciyarta cike da tunanika iri-iri.


Ko da suka fito Ummi da kanta ta yi drevin, tunda suka dauki hanyar zuwa gurin da Fahrin bata sani ba, babu wanda ya tanka a cikin su, Fahrin ko tari ta kasa yi saboda tsananin damuwa da tsoro,ba kanta take jiyewa haɗarin Ummi ba,yar uwarta da ta jefa cikin lamarin shine abin damuwar ta,tana matukar tsoran abin da zai biyo baya idan hakan ta tabbata Ummi ta gano ta sanar da Adda kursum, Fahrin meke damunki ne haka naga kwana biyu kina yawan nazari bayan kuma Ni da nake saka ki cikin tunanin banyi miki komai ba ban kuma sanar dake komai daga mummunan ƙaddarar ki dake shirin tunkaro ki ba,hakan yana nufin ke nan da wani bayani ? ta ƙarasa maganar tana mai fidda wani ɗan guntun murmushi,tare da kara murza sityarin motar cikin nuna kwarewar ta akan tuƙi,shuru Fahrin ta yi tare da kawar da fuskarta zuwa waje kokari take ta dake zuciyar ta,bata son ta yi saurin nunawa Ummi gazawar ta,haka kuma bata da tabbacin abinda take tunani dan haka dole ta karfafa wa kanta guiwa saboda kar ta bata damar gano abin da take ɓoyewa a cikin zuciyarta,Muryar ummin ce ta kuma katse ta a yayin da take cewa Fahrin na daina gar gaɗinki a kan sanar da wani sirrina sai dai amma ina mai tabbatar miki da cewa duk wanda kika sanarwa halin da muke ciki da ke to kuwa tabbas kin jawo masa karƙarewar rayuwa ba tare da ya shirya ba,dan kuwa zan halakar dashi ne,daga nan ne zai shiga cikin littafin ƙaddarar ki"ɗan juyawa ta yi ta kalli Fahrin ɗin wadda ta kasa gane wane yanayi zuciyarta ta faɗa ,Ummi ta ɗora da cewa" naga alamar gyatumar ki tana son keɓewa da ke,dan haka ina ga ita ce farkon wadda zata fara shiga cikin littafin mummunar ƙaddarar ki!".


Da ƙarfi Fahrin ta runtse idanunta wanda suke mata wani irin zugi da raɗaɗi tamkar an zuba musu barkono,sai kuma kaikawo da zuciyar ta ta shiga yi akan anya kuwa Ummi ta san wani abu game da tattaunawar da su ka yi da Adda Kulsum,in dai kuwa hakane to yanzu za ta fara kokarin gyara ɓarnar da ta yi,lallai ya kamata ta cire Adda Kulsum daga cikin lamarin nan domin tseratar da rayuwar ta,Ummi kuwa har yanzu murmushi ne akan fuskar ta,wanda kana ganin sa kasan na samun nasara ne, cikin dabara da mugun nufi ta samu ta kawar da hankalin Fahrin daga kan layin da ta fara hawa,tasan cewa idan Fahrin ta san cewa tasan komai akan maganar da suka yi da kulsum ɗin to tabbas zata san hanyar da zata bi dan kaucewa haɗarin da take shirin afkar musu.


Babu abin da su ka yi sai zagaye gari,ba Ummi ce ta dawo da su gida ba sai misalin goma na dare,dan ma Allah yaso Fahrin bata sallah da abin sai ya fi damunta,haka Ummi ta ja ta zuwa bangaren su ba tare da tabar Fahrin ta kusanci ɓangaren Dada ba.



Sai da ta gabatar da sallar asuba, kafin ta samu bacci ya dauke ta ,dan ba ta yi ƙasa a gwiwar kai kukan ta gurin mahalicci sarki jalla wa azza ba,harma taso ta manta da tafiyar su jalingo, sai da Adda Kulsum ta tunatar da ita ta hanyar zuwa ta tashe ta,cikin gaggawa ta gama shiri ta fita ba tare da ta sanar da Ummi tafiyar tasu ba,domin tana tsoran abinda zai biyo bayan sanin nata, haka ce kuwa ta faru Ummi tana can ta shanya baki su Adda Kulsum da Adda zulfa Da Karima da kuma uwar gayya Fahrin suka hau bisa kwalta yayin da ya Muhd ya zama shine namiji kuma drever a cikin su.



Br Benja ya shirya tafiyar sa a yau cikin kwanciyar hankali da taimakon ɗan uwan sa James,yau fuskar Mr Mathew cike take da fara a saboda yasan wannan tafiya zata kasan ce me dimbin nasara,dan yana da yakinin cewa James zaiyi duk wani abu da ya kamata dan jawo hankalin mutane gare su,baran ma da ya kasance cikin Fulani zasu shiga ya tabbata wasu ma basu da cikakken addini,shi yasa yake da yaƙini akan samun cigaban su,haka mom din sa da mama kajarsu ke nan duk sunzo dan yi masa ban kwana, bayan gama sallamar su ne motocin su ka yi conbai suka fita cikin tsari da nuna cewa e lallai manyan mutane ne a cikin waɗan nan tsula-tsulan motoci,kai tsaye suka dauki hanyar taraba tare da addu'oi na neman samun nasara.



Wani irin kallo Ummi ta bi Yadikko dashi a yayin da take bata amsar tambayar da tayi mata, Yadikko ta ci gaba da cewa ai yau zumunci ne ya motsa dan gaba dayan su sun tafi jalingon amma nayi mamaki da baki sani ba,gashi kuma kina tare da shugabar tafiyar tunda ina kyautata zaton cewa Fahrin ce ta tashi tafiyar"Yadikko ta faɗa tana mai ɓantarar farin goronta,tana kuma sauraron abin da Ummi zata ce,a hankali Ummi ta kawar da kanta daga kallon kuril ɗin da ta ke yiwa Yadikko,kana ta ce"wallahi Yadikko sha afa nayi amma duk da haka ban yi zaton dukan su ne a tafiyar ba, shi yasa kika ji ina tambaya"ta faɗa a lokaci ɗaya tana miƙewa dan san barin falon, yadikko ta ce"ayyo ai duk ɗin su suka tafi"ko sallama Ummi bata samu damar yiwa Yadikko ba ta fice daga falon cikin ƙara ɗaukar alwashi akan yaran,babu abin da zuciyar ta take tunani sai abin da take ganin shi zai kai Fahrin jalingo,cizon yatsan ta ta yi, tana mai zama a bakin gadon ta,cikin yin magana a sarari ta ce"wallahi Fahrin muddin a kaina kika tsiro tafiyar nan ke da Kulsum kin tarowa kan ki tashin hankali mara karshe,wato dole dai kin ce sai kin tonowa kanki abin da zai hana ki zaman lafiya karshe ma ya zama ajalin ki, Fahrin bin ciken ko Ni wacece ba shi zai sama miki kwanciyar hankali ba,domin sanin shi zai jawa rayuwar ki da ta ahlin ki shiga garari da tashin hankali sanin koni wacece ba abune da zai zama mai sauƙi a gare ki ba,ke yarinya ce bazaki gane komai ba kuma bazaki fahimta ba,Ni ɗin na wuce zaton duk mai zato na wuce tunanin duk mai tunani, yanzu ne lamarin zai soma mu je zuwa yarinya".



Sai misalin ƙarfe bakwai na magriba suka isa asalin cikin garin, Fahrin tana tsintar kanta a ƙofar gidan kakannin ta, ta sauke wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya, cikin a zama suka duru zuwa cikin tan gamemen tsakar gidan wanda yake gari guda,kai tsaye suka nufi sashen goggon su Kulsum cike da ɗokin ganin ta, goggo kulsum da maɗaukakin farin ciki ta rungume su,sai faman shafa kan su take yi kamar wan da aka ce za su bace mata, cikin kan ƙanin lokaci aka shiga hidima da su,kawo mu su a binci da zabbi da nono kawai ake, ko wane sashe da irin hidimar da za a aiko mu su da ita,



Lokacin da Fahrin da salma suka haɗu bazan iya kwatan ta muku halin farin cikin da suka shiga ba,saboda lokacin da suka zo salma bata nan,a wan nan rana Fahrin ta manta da duk wata damuwar ta, farin cikin kasancewa cikin danginta ya mantar da ita kalubalen rayuwar da take shirin fuskanta,karin farin cikin ma shine fatan da ta samu gurin gogon su Halima ta ko ina ta zama yar gata ga shi kuma sun yarda salma kan ta bi su zuwa Legos,duk da cewa hakan ya ɗan saka ta far gaba to amma ta sha al washin cewa ba za ta taɓa saka Salma cikin haɗarin Ummi ba,



Washe gari su ka shiga gari, sai da suka fara zaga dangi kafin nan su fara kutsawa cikin rugage da manyan tsaunikan da fulanin daji masu bautar ruwa da dutsuna suke zaune, duk da cewa tafiya ce mai dan nisa tsaka nin su da gida,a nan Fahrin da salma suka shiririce saboda sun sami wata rugar Fulani mai tsananin kyau ga dutsuna da manyan tsaunika sai dai kash mutanen dake zaune a rugar ba mabiya addinin musulunci bane dutse suke bautawa,gurin ne ya ba su sha awa saboda Ni imar dake ƙunshe a gurin,Fahrin ta dubi Salma yayin da su ke dawowa gida ta yi ƙasa da murya ta ce"Salma gobe idan Allah ya kai mu mu dawo kar mu bari su Adda su biyo mu tun da takura mana suke akan sai mun tafi gida"karima dake gaban su ita da su Adda zulfa, ta ɗan waiga ta harari Fahrin ta ce"wai ke uwar yawo ko? To idan za kiyi yawo a nan ki ɗin ga tunawa ba a gida kike ba,dan a nan tsaf za asamu masu cinye mutane,Ni dai babu in da zan kuma zuwa"Fahrin ta murguɗa ƙaramin bakin ta tare da cewa to waye ya saka dake dama mun ce ki biyo mu ne? Ta faɗa tana figar hannun salma suka wuce su, Kulsum ta harari Karima ta ce ke dai sam baki da jan girma wallahi".



Br Benja ba su sauka a ko ina ba sai wata rugar Fulani dake cikin garin jalingo wanda yake jahar taraba,tsaunikan dake wajen da koramar da take gudana shi ne abin da ya dauki hankalin Benja har ya bada umarni da su yi masauki a gurin,kuma da ɗin da dawa yana ganin zasu iya fadada addinin su a cikin rugar, saboda yadda ya yi la akari da mazauna rugar cewa basu da wani taka maiman addini hasali dutsen da su ke bautawa shima ba su dauke shi da wani muhimmanci ba,balle ya yi tunanin za su sha wahalar karkato da hankalin su,sauran mutanen da suka zo tare tuni suka shiga shawagi suna bi ruga-ruga suna bincike tare da bawa idanun su abinci,



Wannlittafin na kuɗi ne Naira ɗari uku kacal nomal group ke nan idan kuma kina buƙatar v i p shima baki da damuwa zaki biya Naira 500 ki sha karatu,zaku iya biyan kudin ku ta wan nan account nomber 0138541704 Union Bank Fatima yusha'u Adam sai ku turo shaidar biyan ku ta wannan nomber,*** ko katin waya ta wannan nomber *** 

 Tare da yin screen short na kudin da kika tura zuwa wan Nan lambar ***


Free pg