ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 7

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA* 

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page7 ```



 *Free* *pg*




FREE PG YA KUSA KAREWA GA MAI BUKATAR CI GABA DA KARANTA LITTAFIN ƘADDARATA SANADIN HASKE ZAI IYA SIYAN SA A NAIRA 300 KACAL GA MAI BUKATAR V I P GROUP KUMA ZAI TURA NAIRA 500 DAN SAMUN DAMAR KARATU HANKALI KWANCE CIKiN SAURI.


ZAKU TURA KUDIN KU TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0138541704 FATIMA YUSHA'U ADAM UNION BANK, KO KATIN WAYA TA WANNAN NOMBER *** MTN KO Ailtel TARE DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NOMBER *** 


INA MARABA DA MASOYANA A DUK INDA KUKE....




Washe gari da sanyin safiya Fahrin ta ja Salma suka nufi rugar Fulani,dan haka nan take jin ɗokin zuwa gurin a safiyar wannan rana,babu wanda yasan inda suka tafi, dan su Adda Kulsum suna can suna shaƙar bacci cikin kwanciyar hankali"Goggon su Halima kuwa tana can tana can tana zuba idon su zo su hada karin kumallo,sai da suka fara shiga wasu rugagen waɗan da dama tun jiya sun riga da sun saba da su, har ma su ka yi mu su alƙawarin komawa a yau ɗin, dan haka ne yasa ba su karasa rugar Jallo da wuri ba sai misalin biyu na rana a rugagen su ka karya da fura da nono masu kyau da gardi.




A ta bangaren su Br Benja kuwa,sai da yaran sa suka zaga rugagen sosai su ka bincike su,su kasan me suke bautawa,kafin nan su ka fara shirin far mu su,dan yaɗa manufar su.




A cikin wata sabuwar anguwa dake cikin garin na legas,a kuma cikin wani tan fatsetsen gida, wanda gaba dayan sa ya ke zagaye da masu tsaro,kai sai ka rantse cewa aikin Allah ake gudanarwa a cikin gidan saboda tsananin tsaron da yake da shi,zan iya cewa kusan gidan shine gini na uku a gaba ɗaya anguwar, a cikin gidan kana kuma cikin dan ƙareren falon da yake Barazanar kaiwa fuloti guda, wani matashi ne zaune bisa babbar kushin ɗin dake falon, wanda ga dukkanin alamu wajen nan anyi shi ne musamman don zaman matashin, a tsaye a kan sa kuwa wasu zaratan mazaje ne masu ji da karfi ko wannen su ka kalla zaka gane yana jiran ko ta kwana ne,tare da shirin sai da rai a ko da yaushe,zasu kai kimanin su biyar ko wanne da kusurwar da yake tsaye, sai kuma wanda yake zaune yana fuskan tar matashin,wanda ga dukkan alamu zai iya kasancewa na hannun dama,chekass ke nan matashin da ke ji da Naira matashin da yayi fice da shuhura a fagen Naira,sai dai kuma babu wanda zai iya cewa ga taka maiman sana ar sa,kowa abin da ya sani kawai shine chekass matashin mai kuɗi ne,kuma abin tsoro ga duk mutumin da wani abu ya taba shiga tsakanin su,mutane da yawa sun ce chekass abun tsoro ne sai dai kuma abin mamakin an rasa meye abun tsoran, to me yasa mutane suka kasa baiyana ainahin halayyar sa ta ban tsoro?da yawa abin da mutane suke faɗa kenan a lokacin maganar zuci,amma kuma Ni Fatima idan kuka bini a sannu zaku san komai a kan wannan labari,



Matashin saurayin da yake fuskantar chekass shi ne ya taso cike da girmamawa, ya ɗan rissina gaban ogan sa,kana ya miƙa masa hotan dake hannun sa tun shigowar sa, karɓar hotan yayi ba tare da ya dubi fuskar hotan ba,ya jehowa yaron na sa tambaya,Mande na gaya maka a duk lokacin da wata har ƙalla ta shigo mana,ka fara gabatar min da bayani kafin ka bani hoto,dan haka ina jiran ka ka koran bayani bayan nan sai naga wanda za ai harƙallar a kan sa"jin jina kai Mande ya yi tare da cewa Oga wannan aikin ai ka rigani sanin sa, wannan yarinyar ce da aka bada aikin sheƙe ta, shine na karɓo hotan"a hankali chekass ya juyo da hotan ya duba,zubawa fuskar matashiyar budurwar idanu ya yi,da ƙarfi ya maida idanun nasa ya rufe,sai kuma ya kuma buɗe wa ,duban Mande ya yi kana cikin yanayin sa da ya sauya a lokaci ɗaya,ya ce"wan Nan ɗin kashe ta za ayi ko me?Mande ya ce"Oga har ka manta wan da suka bada aikin kasheta suke so ayi"girgiza kan sa ya yi da ƙarfi kana cikin wata iriyar murya ya ce" Mande ban taɓa saɓa alƙawari akan harƙallata ba amma a wannan karon tabbas an gabatar da abin da ba zan iya shi ba"Mande ya zaro Ido cike da mamaki ya ce"Oga saboda me?wani irin shu umin murmushi ya yi kana hankali kwance ya ce"saboda ina sonta".



A can kuwa jahar taraba jalingo cikin rugar fulanin daji,me suna rugar Jallo" . Fahrin ce da salma sai kuma sabbin kawayen su da sukayi a cikin rugar Jallo, Zaune suke a bakin tafkin dutsen da ruwa ke ta gudana zuba yake kawai tare da ikon Allah,abun ba ƙaramin burge su Fahrin ya ke ba,salma ce ta dubi daya daga cikin kawayen su ta ce" shin kun san ta yaya ruwan nan take zuba kuma daga ina take?dariya sendal ta yi kana cikin kwarin gwiwar ta ta bawa Salma amsar tambayar ta da cewa, daga cikin dutse ya ke fitowa mana ko baku gani ba? Fahrin ta zubawa ruwan da yake ta zuba daga cikin dogon dutsen ido kana ta ce" mun gani mana amma abin mamakin shine ya akai ruwa ya samu daga cikin dutse ba daga cikin kasa ko rijiya ba?kai tsaye ɗayar mai suna bingel ta ce wan nan duk yana daga cikin aikin abin bautar mu",Fahrin ta ce me ye kuke bautawa, bingel ce ta nuna mata wani katon dutse dake dan nesa dasu anyi masa siffar mutum hannun sa dauke da wani katon littafi wanda ga dukkan alamu ɗora shi akai, Fahrin bata san sanda wata dariya ta kwace mata ba,yi take har da kama ciki,duk bin ta suke da kallo suna mamakin abin da ya sa ta dariya haka,sai da ta tsagaita da dariyar kana ta ce" yanzu wannan shine kuke bautawa kuma shine ya yi silar zubar ruwa daga cikin duwatsu?jin jina mata kai su kayi cike da tabbaci,girgiza kai tayi cike da tausayawa kana ta ce"yanzu kuna ganin cewa shine ya halicce ku kuma shine ya ba ku numfashin da kuke rayuwa a yanzu?kuma jin jina mata kai su kayi, ɗorawa ta yi da cewa to amma ya akai shi bai bawa kansa rayuwar ba ai kamata yayi a ce yadda kuke rayuwa shima haka yake rayuwa tunda ina ga kamar rayuwar da kuke ciki ta fi tashi inganci?duk zuba mata ido sukayi ita ma kallon su ta ke yi tana mai jiran amsa daga bakin su, bingel ce ta ce"ai su dukkanin su basa motsi kuma basa ci basa sha,to kin san dalilin da yasa basu wan zar da haka a rauyuwar su ba? Shuru duk su kayi suna mai nazarin maganar Fahrin,katse musu tunani ta yi da cewa kalli nan"duk sai suka bi ta da kallo, ta shi tayi ta buya a bayan dutsen da suke bautawa, kana ta daga murya ta ce"kuna gani na? Duk suka amsa mata da basa ganin ta, sai ta kuma cewa ku tambayi abin bautar ku shin yana gani na? Duk sai sukayi cirko cirko dan basu san ta yadda zasu tambaye shi ba tun da sun san cewa baya magana, jin sunyi mata shuru sai ta fito daga bayan dutsen ta ce" to kuzo ku duba cikin littafin tun da a nan yake rubuta muku sakon da ya aika muku ko kuma abin da yake faruwa, bayan kuma kun shaida baya motsi ku gwada ko zamu ga yadda yake rubutu da hannun sa" da sauri su duka biyun su ka matsa gaban dutsen tare da fara bude shafin da ya kamata a ce a nan zasu ga abin da ya faru yanzun kamar yadda suka saba,sai dai kuma bin ciken duniyar nan basu ga komai ba, Fahrin cike da kwarin gwiwa ta ce" bingel wannan ba Allah bane ba kuma abin da ya can canta ku bautawa ba ne,domin shima halittar Allah ne, duk abin da kuka zo kuka ga an rubuta ko an zana a cikin littafin nan to ba kowa ne ya rubuta ba face mutum dan adam halittar Allah irin ku, domin dai yanzu kun ga shaida da idanun ku da a ce shine yake yi da yanzu zaku ga abinda ya faru a ciki kuma shi Allah ba haka yake ba , tun farkon fari ubangiji ya aiko annabawa da sakon shiriya ga bayin sa daga karshe ya aiko Annabi Muhammad wan da shine annabin da ya watsa addinin musulunci yazo mana da gaskiya da shiriya Allah bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, amma yanzu ku bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu zaku dawo nan gurin ku duba littafin in atabbatar muku da cewa ko da an rubuta muku abin ya faru to ba komai zaku gani ba, saboda shima Allah ne ya halicce shi bai isa ya san gobe ba Allah ne masanin abin da zai faru da wanda bai faru ba, zan so kafin mu dawo gobe kuyi dogon nazari akan abin bautar ku, Ni kuma kuyi min duk tambayar da kuke so akan addunina insha Allahu zan wayar muku da kai akan abin da Allah ya ya sanar dani,



Salma ta ce" bai kamata mu tafi mu barsu da iya wan Nan ba,Dan haka ta ɗora da cewa mu kuma Ubangijin mu yana ganin mu hatta ku da baku gasgata shi ba" saboda shi mai ji ne kuma mai gani ne, 


Fahrin ta dafa kafaɗar bingel tana mai duban yanayin ta, ta ce" bingel ku sani cewa babu wani abin bautawa sai Allah kuma Annabi Muhammad ma aikin sa ne,Allah shi kadai ne abin da muke bautawa domin shi ya halicce mu ya kuma halicci duniya baki daya, zan ci gaba da kawo muku misalai dan ku tabbatar da cewa wannan addinin da kuke bashi ne addinin da aka halicce ku dan kuyi ba, Allah ya halicci dan adam dan ya bauta masa ne"ba dan ya bautawa wanin sa ba".


Salma ta ɗora da cewa wai kun san cewa akwai wuta a kwai kuma aljanna wanda Allah subhanahu wata ala yayi su domin dan wuta da ɗan aljanna, girgiza kai su kayi, Fahrin ta ce" Allah ya yi wuta ne domin masu saba masa masu shirka da kafuri wanda yaki yadda da fadar Annabi Muhammad da wanda suka juyawa addinin sa da masoyin sa Annabi Muhammad s w a, baya, da muna fukai da fasikai da masu da duk wani wanda baya bin Allah,ita kuwa aljanna Allah yayi ta domin bayin sa da suka yadda suka Amin ce cewa shine Allah wanda ya halicce su ya kuma aiko Annabi Muhammad ma aikin sa da shiriya, masu salla da azumi masu wankakkiyar zuciya waɗan da basa cin haram, wanda basa munafunci masu gaskiya da rikon amana wanda suka bi iyayen su masu yada gaskiya da goya mata baya amma Allah yana yafiya ga wanda ya tuba ya koma kan hanya".



Allah shi kadai ne ba shi da ɗa ba shi da uwa ba uba, shi ne ma haliccin sammai da kassai, ƙur ani shi ne littafin sa da ya aiko mana Annabi Muhammad da shi kuma shine mu ujizar annabi,duk wani abu ba gaskiya bane shi kadai ne gaskiya karshen gaskiya,gare shi muke kuma gare shi zamu koma ".



Salma ta ɗora da cewa amma ai kun san cewa ana mutuwa,to ita ma mutuwar ta Allah ce rayuwa da mutuwa duk nasa ne,wuta da aljannar duk sai an mutu za a shige su masu rabo su tafi aljanna mara sa rabo su tafi wuta,addinin Allah sauƙakke ne akan ko wane addinni shine mai sauki a cikin ko wane addini kuma shine addinin gaskiya".



Fahrin ta ce idan zamu kwana a nan baza mu iya sanar da ku girman al arshin Ubangiji da buwayar sa ba, baza kuma mu iya siffan ta muku yawan dadin aljanna ba kamar yadda ba za mu iya kwatan ta muku siffar girman ubangiji ji ba,zamu bar ku da wannan ku je ku zurfafa tunanin ku ba tare da mun ba ku tamba ya ba,ko sama ku ka kalla ta ishe ku tunanin ban ban ce gaskiya.daga nan suka juya suka bar su bingel tsaye sake da baki da kuma shiga cikin wani irin zuzzurfar tunani akan wan nan abun mai kama da almara,,basu ɗauke kansu akan su Fahrin ba har saida suka kule cikin ciyayi".



Wan Nan abu da ya faru baƙaramin saka zuciyar su bingel ya yi cikin tunani da wasu wasi ba,duk juyin da zasuyi za su yi shi ne da muryoyin Fahrin da Salma cikin zakin Muryar su me saka nutsuwa da kashe jikin me sauraro,bingel ta juya ta dubi kawarta sendal da ita ma take cikin zurfaffan tunani,ta ce" sendal me yasa abin bauta baya rubuta duka abin da muke ai katawa? Sendal ta ce" to ke kin yadda shi ɗin ne ya ke rubutawa ? Bingel ta ce" anya maganar bakin birni babu ƙamshin gaskiya, sendal ta ce" to shi Ubangijin na su ta yaya yake ganin mu bayan kuma sunce shi ba a ganin sa? Bingel ta ce" ki bari sendal a kwai tambayoyin da nake so nayi musu wanda har idan sun bani gamsasshiyar amsa tabbas zan bi addinin su domin har na fara kwadayin Ni imomin da suke cikin addinin", cike da gamsuwa ta ce" nima ina da tambayoyi dan haka ina bayan ki, da wannan shawarar suka samu damar runtsawa suna fata gobe ta yi Lafiya.



Acan bangaren su Fahrin kuwa tunda suka tafi zuciyar su ke cike da kwadayin samun nasara akan su bingel,suna yi musu fatan da cewa da samun babban rabo,suma da tunanin suka yi bacci suna fatan Allah ya nuna wayewar gari lafiya,



A can cikin rugar Jallo inda su Benja suke, babu yadda James be yi da shi ba akan su fita yau ɗin amma ko kallo bai ishe shi ba, balle ya samu amsa, duk da cewa ba kasafai Benja keyiwa James irin wannan miskilan cin ba, amma yau din haka nan ya share da maganar da ya ke masa, da ya dame shi ne ma ya bar masa gurin yana mai cewa sai tomorrow daga haka ya bar James da shaƙar ƙamshin sa da yabari a gurin,



Legas



Cike da mamaki Mande ya ke duban ogan nasa, a iya sanin da yayi masa sam babu sosayayya cikin lamarin sa, kai matan ma sam babu su cikin tsarin aikin sa, abinda ya riga ya sani kawai shine kudi neman su ko ta wace hanya da kuma iko da sunan da yake nema ta wasu hanyoyin da ba kowa ne ya sani ba.



Duban Mande ya yi wanda ya ga no kallon tsantsan mamakin da ya ke yi masa, cikin isa da ikon da ya ke fatan samu fiye da wanda ya ke ciki ya ce da Mande,kashare tantamar da ke cikin zuciyarka ka yi aikin da ya juya zuwa kaina,Abune da kasani me wuya samun yarinyar nan ta ruwan sanyi,amma dai yanzu Ina son duk wani bayanai akanta kafin zuwan abu na gaba"daga haka ya mike ya shige cikin kuryar haddadan dakin sa wanda yake tamkar fadar shugaban kasa, murmushi Mande ya yi tare da ficewa dan fara aiwatar da umarnin ubangidan sa.



Taraba jalingo



Washe gari su Fahrin ba su yi sammakon zuwa rugar Jallo ba, kamar yadda sukayi jiya, saboda suna san bawa su bingel damar zurfafa tunani,



A can cikin rugar Jallo kuwa, cike da ɗokin safiyar su bingel su ka tashi,amma kuma sai su ka ji shiru har ya zamana sun koma bakin hanya dan sauraron ta inda su Fahrin za su ɓullo amma kuma kash har rana ta fito babu su babu labarin su, sai hakan ya saka zuciyoyin su cikin tunani masu yawa,



Suna zaune jigum har ma sun rasa abinyi,kawai sai suka jiyo wani sauti,wanda suka riga suka saba da shi a duk lokacin da ake son gabatar da wani muhimmin taro,hakan ne yasa suka mike jikin su na rawa, suka koma cikin ai nahin rugar cikin rashin jin dadin zuwan kawayen su.



A cike suka samu faffaɗan filin da rugagen su ke cike, kusan duk wani da ke cikin rugar ya halacci gurin, cike da san sanin abin da ke faruwa suka dinga kutsawa har su ka sami damar zamowa a asahun gaba,


James ne zaune kan wata kujera fuskar sa cike da walwala, yayin da a tacan bangare guda kuma ,Br BENJA ne zaune kan wata ƙayatacciyar kujera tamkar ta sarauta,haka suma sauran manyan da suke tare kowa yana hakimce bisa kujera sai kuma tarin kayan masarufi da duk wani abu da ya danganci abinci , kallo ɗaya za kaiwa Benja ka hango tsagwaran kyawu da isa a tare da shi, fuskar nan a shake ta ke babu alamun digon fara a cikin ta, amma duk da hakan tsantsar kyawun sa bai kasa bayyana cikin idanuwan mutanen da su ke zagaye da shi ba,gurin ya yi tsit baka jin komai sai ƙarar koramar da take ta ambaliya da gudana cikin dutsunan da suke rayuwa cikin buwayar Ubangiji,gyaran muryar da James ya yi ita ta kuma nutsar da zukatan su domin dukkanin su ƙagauce suke da jin abun da ya kawo waɗan nan mutanen masu tsananin kyau da iko,ga kuma tarin dukiyar da ke jibge saboda su, cikin Hausar da ya kware a cikin ta ya fara yi musu bayanin Bible tare da kawo manyan misalai akan addinin yahudu cikin kwantacciyar murya da lallama da nuna sadaukarwa gare su, bayan nuna musu cewa abin da suke bautawa ba komai ba ne kuma ba zai taba taimakon su a komai ma,face ma lalacewar rayuwa ta rashin amfani,idan suka yadda da su da addinin su zasu basu tarin dukiya wadda zata ishesu rayuwar yau da goben su,wani daga cikin fulanin ne ya jeho masa tambaya da cewa to shin ku waye Allah ku kuma yana ina? 



Kai tsaye ɗaya daga cikin Pastor din da suke tare , ya bashi amsa da cewa Yesu shine Allah n mu saboda shi ɗin ɗan Allah ne ".



Ƙarya ne waye yace maka Allah yana da ɗa ko shi Annabi isah bai fada muku haka ba , ko ɗaɗɗoyar basirar ku ce ta gaya muku haka , Annabi isah dan aiken Allah ne, kuma Allah ya halicci Annabi Isa acikin Maryama ne dan nuna buwaya da isar sa , ta haifi Annabi isah ba tare da uba ba bare ciki , Annabi isah ba dan Allah bane na fada muku , bayan da aka haifeshi sai Ubangiji ya turoshi cikin mutane domin ya basu shiriya hakan ne tasa Ubangiji ya lamunce masa War kar da marasa lafiya da masu makanta, da masu cutar jinnu kuma Allah ya yi hakanne da ikon sa dan ku bada gaskiya wa abun da Annabi isah ya zo dashi , amma sai kuka juya lamarin kuka canja littafin Annabi isah da abubuwa na san ranku, Annabi Isa bai taba tada matacce ba saboda bai da wan Nan ikon Allah ne kaɗai mai kashewa da rayawa kuma Allah bai kadarto cewa matacce zai tashi ba dan da hakan zata faru to da tabbas shi kadai ne mai ikon hakan, Annabi isah bawa ne na Allah bawan da haihuwar sa ko nace samuwar sa tazo da buwayar Ubangiji".


Duk sai kowa ya zuba mata idanu, wanda suka santa suna mamakin furucinta da kuma saka musu kokwanto akan dukkanin addini nan, waɗan da basu santa ba kuwa kallo suke mata na rashin fahimta da tunanin daga inda ta fito sai dai kuma kalaman ta ba ƙaramin tasiri su kayi wa daywa da ga cikin su ba kai harma da wasu mutum biyu daga cikin yan gaiyyar su benja,su kuwa mutanen Benja duk sai su kayi zaton yar cikin rugar ce sai dai mamakin su anan shine dama a kawai waɗan da suke bautar Allah a cikin rugar amma basu sami masaniyar hakan a cikin binciken su ba?su kuwa su bingel cike da farinciki suka ƙaraso inda su Fahrin ɗin suke tsaye,ta ke kuma sai yan maganganu suka fara ta shi baka jin komai sai tashin fillanci da Hausa kadan kadan a cikin filin gurin.