Chapter 8
by @zahra48
💕
**ƘADDARATA*
*SANADIN* *HASKE* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*
```Page8 ```
*Free* *pg*
A hankali ya kuma lumshe idanun sa da dama suke a lumshe , Muryar ta na saculatin wa jinin jikin sa, raɗam yagane Muryarta a cikin kunnuwan sa, a yadda ya ke ɗin babu wanda ya ke iya gano yanayin da wanzuwar Fahrin a wajen ya saka shi, saboda abu ne me wuya ka iya gano ai nahin zuciyar Br BENJA,buɗe manyan idanunsa ya yi wanda kai tsaye basu tsaya a ko ina ba sai cikin fararan idanun Fahrin, wani irin harbawa ƙirjin ta ya yi tsananin kyawun sa da kwarjinin sa da ya dame shi a sanadin gaskiyar sa su suka nemi sawa jikinta wata irin mutuwa da kasala har da dimuwa, cikin karfin hali ta ɗauke idanunta daga cikin nasa ta na maida wa kan su bingel da suke faman tambayar Salma dalilin rashin zuwan su da wuri,
James ma zuba mata ido ya yi fuskar sa cike da wani irin yanayi na tsantsar tsana,yana mai jin kamar ya je ya shake wuyanta, ya za ai suna gab da samun cimma nasara wata kucakar bafulatana tazo ta wargaza musu nasarar da suke murnan jiyo ƙamshin ta,tashi ya yi cikin wani irin taku na tsantsar iko da takama ya nufi inda su Fahrin ɗin suke, dakatawa ya yi a gabanta tare da kare mata kallo sama da kasa, sai yanzu ya hangi kalar birni a tare da ita ya kuma tabbatar da cewa ba acikin rugar nan ta ke ba,fuska a haɗe kamar wani tsohon kumurci ya ce me ye manufar ki ta zuwa wajen Nan domin rusa farin cikin mu?ke ɗin wace ce? Kuma meye manufar ki akan addinin mu da har zaki soke shi ki kira shi da mara amfani"?
Wani kallon ƙyama ta yi masa kafin ta kawar da kanta ba tare da ta bashi amsar ko daya daga cikin tambayoyin sa ba,ci gaba da kallon ta ya yi yana mai jin sabuwar tsanar ta da kuma daukar fansar wulakancin da ta yi masa a gaban daruruwan jama a da hadiman sa,bai kai karshen tunanin sa ba ya jiyo daddadar Muryar ta ta na cewa da su bingel ku kwantar da hankalin ku zanyi muku dukkanin bayanan da kuke so daga gare Ni,na kuma tabbata zaku gamsu ku gasgata abin da na zo muku da shi" wani matsiya cin kallo James ya ke bin Dan mitsitsin bakinta da shi wan da nbaifi ya yi masa rabin lima ba,matsawa ya yi inda Br BENJA ya ke kame tamkar bai san wainar da ake toyawa ba,ɗan ƙasa ya yi da murya ya ce" Ms Benja kana gani kuma kana jin abin da ke faruwa atlist ko da ba ka ce komai ba ka bada Umarnin hukuncin da ya kamata a yiwa wannan matsiwaciyar yarinyar" ya faɗa cikin takaicin da ya ke kara kume shi, a hankali Benja ya bude lumsassun idanunsa tare da zuba su kan dan karamin bakin Fahrin da ta samu damar karkato da hankalin mutane masu tarin yawa kanta da shi, miƙewa ya yi ba tare da ya ce" komai ba,yana shirin barin gurin ya ji james cikin Muryar fusata yana bada Umar nin a dauko Fahrin yau sai ya yi maganin ta kuma sai ya ga uban da ya tsaya mata,cak Br BENJA ya tsaya ba tare da ya kara taku daya ba, cikin yanayin sa na ko in kula ya ce" da James kar ka kuskura ka taba kowa a gurin nan" daga haka ya kara gaba cikin nutsatstsan takun sa,idanun Fahrin na kansa haka na James da ya kasa boye jin haushin sa da mamakinsa,wani ɗan guntun murmushi ta yi mai cike da samun kwarin gwiwa da kuma tura haushi wa abokan adawa,barin wajen yayi zuciyar sa cike da abubuwa na daukar fansa marasa kyau,gaba ɗaya sauran ma sai suka watse suka bar gayyar yan rugar Jallo da su Fahrin,
Cikin nutsuwa Fahrin ta ke ta janyo ayoyi tare da misalai tana fassarawa, ya yin da Salma ke ta yata cikin ilmin su na sanin Ubangiji wanda ya isa gamsar da darin mutanen rugar Jallo,kafin ka ce wannan Fahrin ta samu nasarar karkato hankalin fiye da rabin mutanen da ke tare da ita awajen wanda daga cikin su har da su bingel,a wajen ta miƙa musu kalmar shahada tare da nuna musu abubuwan da ya kamata su farayi, san nan ta tafi da alƙawarin zata saka a samo musu malamin da zai koya musu ibada,ba duka ne suka musulunta ba amma fahrin tana da yaƙinin cewa masu rabo daga cikin waɗan da suka rage zasu samu tsira ko bayan bata nan.
Da wani irin farin ciki salma da Fahrin suka koma gida, a cikin wannan zuri'a kuwa zaka so kaga irin farin cikin da ke wanzuwa ta re da Alfahrin samun Fahrin da Salma a cikin zuri ar,washe gari kuwa a kai musu malami har ma da ginin masallaci wanda Abbu da Dady sama suka dauki nauyi, tare da alƙawarin ginin islamiya, hakan kuwa ba ƙaramin farinciki y saka Fahrin ba har ma ta manta da duka abinda ke damun ta da wanda ke faruwa,walwala suke da nishadi sosai kafin kuma suka fara shirin juyawa inda suka fi wayo wato Legas,cike da farinciki da kewa suka rabu da mutanen ta na rugar Jallo yi suke tamkar zasu yi kuka saboda kewa haka nan su ka yi sallama ta bankwana da kawayen su bingel,tare da fatan sake kawo musu ziyara a duk sanda suka shigo jalingo,da wan Nan alƙawarin suka dauki hanya Sai Legos.
Kai tsaye Br BENJA ya ba su umarni da su shirya masa komawa legon,James ne ya tsare shi da kananun maganganu akan ba su yi abin da ya kawo su ba,kai tsaye BENJA ya ce" ban hana ka ba zaka iya yin abinda Ni na kasa,juyawa ya yi ga Amintaccen yaron sa wato Adebayo kallo ɗaya daya ya yi masa ya kawar da kansa, da sauri Adebayo ya bar wajen dan tuni ya fuskancin umarnin mai gidan nasa.
Acikin kankanin lokaci ya yi musu buking ɗin jirgi su biyu kawai dan shima kafar sa kafar me gidan sa,hakan kuwa ba ƙaramin takaici ya karawa James ba,wasu abubuwa mara sa kyau na wanzuwa cikin ƙwaƙwalwa da zuciyar sa,fuskar Fahrin ka wai ya ke hangowa tare da cin alwashi me girma akan ta,nasarar da ta samu ta zama babbar faduwa a cikin tarihin rayuwar sa.
Tunda suka shigo garin na legos abubuwa suka shiga dawo mata,Ummi ita ta fara wadowa cikin zuciyar ta sai kuma Abba da halin da ya ke ciki,ga kuma Adda Kulsum da tunanin abun da Ummi ta ke shirin aikata mata,ji ta yi dama ta yi zaman ta cikin rugar Jallo da ta manta da duk wata rayuwar ta ta baya da kuma wadda zata fuskanta, sai dai kuma abinda ta riga ta sani shine mutum baya gujewa ƙaddarar sa,a jiyar zuciya ta saki tana maida idanunta kan bishiyun da suke ta tseren gudu bisa titin, ta tuna abinda ya faru wasu yan awanni, tana mai jinjina hikimar Ubangiji gashi dai ƘADDARAR ta ta kaita ga SANADIN samun wani HASKE na musuluntar da mutane fiye da hamsin,ko wann nan ma wani hikima ne ta Ubangiji gagara misali buwayi abin dogaro, Alhamdulillah abin da ta furta ke nan tana mai ci gaba da salati da hailala.
Cikin ikon Allah sun sauka lafiya duk da dai akwai tarin gajiya a tare da su,kasancewar cikin dare suka sauka, sai kawai su kayi wanka kowacce ta nemi makwanci dan sauke gajiya.
Kai tsaye driver ya wuce da su kebantaccen gidan sa da wasu lokuta ya ke zuwa dan hutawa, a yanzu dai ba zai nufi gida ba dan yasan mahaifin sa na can a kunne ya na jiran sa ya sauke masa, shi kuma a yanzu sam ba zai iya daukar hayaniyar komai ba,wanka ya yi tare da feshe jikin sa da turare n sa na joegos ya bi lafiyar faffaɗan gadon sa mai tsananin kyau da taushi, lumshe idanun sa ya yi yana son bacci ya dauke shi don ya huce gajiya.
Kallo ɗaya za ka yi masa kasan cewa yana cikin tashin hankali da mummunan ɓacin rai,idanun nan tamkar zasu fito, kaiwa kawai yake da kawo wa tsakanin bedroom din sa da falonsa,shin wane irin abun kunya Benja ya ke son jawo masa, a tarihi ma ba a taba samun solobiyon Pastor ba kamar Benja,anya kuwa Benja ya da ce da matsayin da aka bashi?idan wannan maganar ta fito ta cewa Benja ya kasa bawa addinin sa kariya daga muzanci irin na mabiya wani addini,shin wai ma wacece wan Nan yariya me tsananin karfin hali haka?daga wayar sa ya yi kira ɗaya zuwa biyu aka daga, ina bukatar dukkan bayanai akan yarinyar nan"daga haka ya kashe wayar ya jefata gefe,yana mai furzar da iskar bakin sa.
Bude idanun shi da suka yi masa nauyi ya yi yana mai jin gajiyar da ya yi na dan warwarewa,a hankali ya zura fararen ƙafafun sa kasan tattausan carfet ɗin da ke malale cikin dakin,kana ya zura su cikin flat shue dake bakin gadon,tashi ya yi a hankali ya yi yar mika ya nufi bathroom din sa,ya jima a ciki kafin ya fito,daure da towel a kugunsa fatar sa sai wani kyalli ta ke, ruwan ma sun kasa zama a jikin saboda tsananin laushi da sulbin skin dinsa,gaban katon mirror ɗin sa ya nufa ya fara kalailaye fatar kai kace wata sauraniya ce,dan yadda ya ke lallaɓa fatar da gyare ta ko wata saurauniyar albarka,sai da ya shafe kusan mintuna talatin kafin ya gama shirin sa,ya fito tsaf cikin tsaddiyar cot dinsa kalar ruwan toka mai sheki,wayoyin sa ya dauka tare da kunnawa,kamar jira ake ya kunna kira ya fara shigowa babu kakkautawa,ba tare da ya amsa ko guda ba ya nemi Adebayo, fita ya yi cikin nutsatstsan takun sa mai kama da na sarakai,da sauri Adebayo da yake kame jikin motar da zasu fita da ita ya matso ya mika gaisuwa kana ya bude masa bayan motar ya shige, shima ya shiga ya figi motar da mugun gudu.
Duba daya zaka yiwa jama ar gidan kasan cewa suna cikin farin ciki ,tun da suka tashi a safiyar dawowar su a ke hada hada ta dawowar tasu , Yadikko kamar zata maida jikokin nata ciki saboda yadda ta yi kewar su Bama dai kamar Fahrin,haka Dada zuciyar ta fal take da farinciki shi yasa kowa ka kalla fuskar sa a washe,hatta da su Safwan da sauran yayun su maza sun sake da su a nata raha da maida zance,
A hankali Ummi ta zame ta bar su ta nufi bangarenta, hankalin Fahrin na kanta saboda yanzu duk wani motsin da Ummi zatayi ba abin yadda ne a gurinta ba,dan haka cikin dubara ta zame tabi bayan Ummin.
Kai tsaye ɗakinta ta nufa tana mai ɗora wayarta da take kira tun kan ta ƙarasa dakin akan kunnen ta,dai dai lokacin da ta shige dakin tare da rufowa,Fahrin da ke sadade ta bayanta ta ci burki a kofar dakin tana mai maida hankali kan wayar da Ummi ta farayi,sun dawo dan haka aikin ku daga yau zai fara ku tabbatar kunyi duk abinda na fada muku saboda bana san samun kuskure a wannan aikin, dan kuwa shine farkon tsanin da zan fara hawa dan kaini ga cimma nasara"dan shuru ne ya ratsa alamun daga can ɓangaren ake mata magana,yauwa to na gode daga haka ta kashe wayar, tana dariyar da ta saka Fahrin cikin fargaba, da sauri tabar gurin tana mai share zufar da ta fara tsatstsafo mata,can ɗakinta na ɓangaren Yadikko ta nufa tamkar zata kifa saboda rashin ganin hanya,idan lissafin ta ya yi dai dai to tabbas Ummi tana shirin cutarwa ga Adda Kulsum ne,sintiri ta fara yi tana tunanin ta inda zata fara gano shirin ummin akan Adda kulsum,tunanin ta dai Yabata tabbacin dole sai Adda Kulsum ta fita ne komai ma zai iya faruwa,to kuwa ita zata toshe duk wata hanya ta fitar Adda Kulsum ɗin.
Cikin farinciki Ummi ta karbi karin kyautar da Abbu ya kuma yi mata ta salma,kai idan ka ga yadda take hawaye da godiya wa Yayyan mijin nata zakayi matukar mamaki da shakku idan aka ce maka tana da wani boyayyan hali da kudiri a zuciyar ta, Fahrin kallon ta kawai take tana jin wani irin sagewar gwiwa akan shirinta na tona wa ummin asiri,ta maida duban ta kan Abbu da ya kewa ummin wani irin kallo na tsantsar yarda da tausayi,take ta ji wasu tarin ƙwalla sun cika kwarmin idanunta, cikin sauri ta gogesu dan a yanzu dai bata da wata mafita sai a wajen Allah,
Sosai Ummi ke jan Salma a jiki tamkar yar cikin ta, amma abun sam bai shigi Salman ba saboda a kwana biyu kawai da tayi ta fuskan ci cewa a kwai abin da ke faruwa tsakanin Ummi da Fahrin ,Salma yarinya ce mai matukar bin kwafkwafi da saurin fahimtar abu, kusan halin su ɗaya da Fahrin ɗin shi yasa ma tasu tazo kusan daya,amma dake Salman tana da wayo ta fuskan ci cewa sam Fahrin bata son ta san wani abu da ke faruwa,hakan kuwa shi ya bata kwarin gwiwar zurfafawa cikin san gano abun da ke boye,a ɓangare guda kuma damuwar Adda Kulsum ita tafi sako Fahrin ɗin a gaba, saboda duk wani motsin Kulsum ɗin tana ankare dashi bata son ta matsa ko ina bare ta samu damar fita ba tare da ta sani ba.
Wani uban wanki na ba gaira ba sabar Ummi ta haɗa Fahrin da shi,Salma ce ta dage sai ta taya ta,wankin suke amma gaba ɗaya rabin hanlinta ba a gun wankin ya ke ba, wani irin faduwar gaba ta ke ji mai tsanani,haka nan ta ke jin wannan wankin da Ummi ta sakata ba a banza yake ba, tabbas a kwai manufar sa,da sauri ta ajiye wanda ke hannun ta tare da dauraye hannun, duban ta salma ta yi da alamar tambaya akan fuskarta, cikin sauri ta ce"Salma akwai matsala bari na je yanzu zan dawo"daga haka ta figi hijab dake jikin window ta fita da ga backyand ɗin cikin sauri kamar zata fadi,Binta da kallo Salma ta yi kafin ita ma ta mike cikin nata saurin tabi bayan Fahrin ɗin,
Yadikko ta dubi Fahrin da ke watsa mata tambayar ina Adda Kulsum, ta ce"yanzu ummin ku ta aike ta saboda ta ce ku ta saka ku wan,,,,,cikin wani irin zafin naman da bata taba sanin ta na da shi ba ta fita daga falon yadikkon,kai tsaye waje ta nufa tana fatan a ce Adda Kulsum ɗin ba tayi nisa ba,Salma ma binta ta yi hankali tashe,tare suka fara bin hanya ko zasu ga inda Adda Kulsum ɗin ta yi sai dai ko alamar ta babu, zubewa Fahrin ta yi ta na mai sakin wani irin kuka mai taɓa zuciya da ran mai sauraro,Salma ce ta kama hannun ta tana cewa me ya ke faruwa Fahrin faɗa min mana"wani irin fincikewa tayi daga rikon da salma ta yi mata ta zabura ta dauki hanya, da sauri Salman ta kuma Binta tana rokon ta da yi mata magiya, cikin wani irin kuka mai haɗe da sheshsheka ta ce Salma rayuwar Adda kulsum tana cikin hadari dole sai na nemo ta duk inda ta shiga, cikin tsawa Salma ta kuma riketa tare da cewa Fahrin ki daina kokarin boyemin a bin da na riga na fara ganowa dole akwai matsalar da take faruwa kuma na fara sunsuno matsalar,zan kuma sanar da kowa abin da ya ke faruwa"
Karaf sai a kunnen Abbu wan da ya gano su tun da ga nesa hakan ne yasa ya fito daga motar ya biyo bayan su, me za agaya mana ? Me kuke ɓoyewa ne haka iye maryama? Ya faɗa yana mai zubawa Fahrin ɗin ido zuciyar sa cike da wasi wasi akan halayyar da yake tsintar Fahrin a cikin kamar tana yin wani abu da bata son su sani, cikin sauri Fahrin ta ce" babu komai Abbu wani ne fa yake so na Ni kuma bana son sa shine yake takura min to akan sane Salma ke magana" to yanzu me kuke yi a waje? Ya faɗa ba dan ya gamsu da abin da ta ce masa ba,Salma ta ce" Adda Kulsum ummi ta aika shine ta ce" mu fito mu jirata anan da akwai kayan da ta karbo mana na biki to bata son gulmawiya ta gani Adda Karima, shi yasa ta ce mu fito mu jirata" jinjina kai kawai Abbun ya yi kana ya juya ba tare da ya ce" komai ba.
Ajiyar zuciya suka sauke lokacin da suka ga shigewar sa cikin gidan .
Cikin wani irin rawar jiki Fahrin ta ke duban Salma ga wani irin tashin hankali da ya kuma kunno mata,Salma me kike shirin aikatawa ?me ki fara ganowa? Wa zaki sanarwa? Salma ki rufamin asiri ki kawar da duk wani abu dake zuciyar ki,saboda hakan zai iya jawo mana makamancin tashin hankali da muke ciki yanzu,ko kin san cewa abun da ke faruwa yanzu yana da nasaba da abinda kike son yi?kai tsaye Salma ta amsa mata da cewa eh na sani mana angaya miki kaunar da nake miki ta wasa ce da har zan ga abinda ke son ta kurawa rayuwar ki na koma gefe na yi shuru?sam hakan ba mai yuwuwa ba ne, Fahrin na gano matsalar da kike ciki kuma akan Ummi ne dan haka Ni zanyi maganin komai bazan bari rayuwar ki ta lalace saboda barazanar Ummi ba,da sauri Fahrin ta katse ta da cewa Salma ba barazana Ummi ke min ba baki san ko wacece ba zata iya aikata duk abin da ta faɗa zata aikata,dan haka ki cire kanki daga wannan lamarin Adda Kulsum ma gashi nan rayuwarta tana cikin hadari,dan Allah na rokeki salma bana son wani abu ta sanadi na ya kuma faruwa da wani nawa dan Allah ki bari"kinga yanzu mun fara saka Abbu cikin kokonto dan nasan bai wani gamsu da abin da muka sanar dashi ba,wani irin kallo Salman ta yi mata kana ta ce amma Fahrin kin bani mamaki ban taba sanin cewa ke matsoraciya ce ba sai yau,na dauka yadda kike jajircewa da rashin tsoro a ko ina haka zaki kasan ce a anan ma, sai kuma na ga sabanin haka"Salma bazaki gane ba bazaki fahimta ba saboda baki san komai ba amma da,,,,,,tsayuwar me a daidai ta da fitowar da Adda Kulsum ta yi shine ya hana ta ƙarasa fadar abin da zata faɗa,da gudu ta ƙarasa gun Adda tare da fadawa jikinta,ɗago ta ta yi tana goge mata hawayen fuskar ta kana ta ce" Ni ma na fuskan ci akwai manufa cikin aiken da tayi min shi yasa na yi kokarin kufce mata ta inda ba tayi zato ba,kar ki damu auta komai zai wuce"duban Salma ta yi tayi mata murmushi tare da cewa haba maza ku gyara fuskar ku mu shiga kar ku bari a fuskanci wani abu dake faruwa zamu san yadda zamuyi mu shawo kan matsalar insha Allahu tun da mun karu za a fuskanci damuwar mu", jinjina mata kai su kayi kana su ka nutsu kana suka shige cikin gidan.
Cikin wata irin murya wadda ke nuni da tsananin ɓacin ran da ta ke ciki ta ce" wallahi wallahi wallahi Fahrin sai na ga bayan ki sai na maida rayuwar ki abar kwatance su waɗan nan ba komai ne ba duk zanyi maganin su, baku san wacece Nadiya ba har yanzu kallo na kuke da sauran imani,ke ma salma kin shiga rigimar kenan to babu damuwa yanzu wasan zai fara yanzu zaku san ainahin ko ɗin wacece tunda har yanzu bulayi kuke yi, ita kadai take surutan ta can cikin kuryar ɗakinta.
Cikin girmamawa ya mikawa ogan nasa duk wani bayanai da ya kunshi Fahrin kamar yadda ya buƙata,buɗe emblof ɗin ya yi ya zubawa hoton Fahrin idanu na tsawan wasu sakanni,kafin ya ɗan yi murmushi ya ce" ashe ma yarinya ce karama da aikin manya,Mr Mathew ya faɗa yana maida hotan dagowa ya yi ya dubi yaran nasa tare da cewa shi kenan babu wani abu da zan iya yi akanta nayi tunanin wata babbar halitta ce shi yasa ita kuwa wannan babu komai a tare da ita fa ce tsantsan kuruciya,"daga haka ya mike da eblof ɗin a hannun sa ya haura sama.