ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 9

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA* 

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page9 ```



 *Free* *pg*




Tun da ya dawo bai bari ya hadu da mahaifin sa ba, duk yadda James ya so hakan ta faru kuwa,ko dan yaga BENJA ɗin ya gyara wasu kurakuran da yake aikatawa akan addinin nasu,dan a ganin shi sam wan Nan muƙamin ma bai da ce da Benja ba dan baya bin duk wasu ka idojin da suka zama a karkashin sa,hasalima shi aikin sa ya fi masa muhimmanci akan ko mai, zuwa choc shine abin da zai iya bugar kirji Benja kawai na yi, shima yana ganin dan ya zama masa dole ne,a haka dai kallon da ake wa Benja kallo ne na mai tsananin riko da addinin sa, to amma shi a zama sa da Benja ɗin sam baiga haka ba,dan haka dole ya ya yi tunanin hanyar gyara Benja ɗin tun kafin manyan malaman su su ankara,domin abin da Benja ɗin ya dauko zai iya jawo musu abin kunya babba cikin zuri'arsu.



 Shuru babu wani mataki da Ummi ta dauka tun Fahrin tana fargaba har ta zo ta ɗan fara sakin ranta,ga kuma shirye shiryen bikin su Adda Kulsum ɗin da aka fara yi,shi yasa ma sam basu sami sukunin tattauna maganar Ummi ba,ga bikin yanzu saura kwana goma shi yasa gaba ɗaya hankalin su ya dauke daga tunanin ko mai da fargabar abin da Ummi ke shirin yi,



Sai dai kuma a ɓangaren ummin ba wai ta manta ko ta kyale komai ba ne,ta yi hakan ne kawai dan ta basu kafa,saboda ta fahimci cewa Salma ma tana da matukar wayo dan tafi Fahrin wayo nesa ba kusa ba,ita Fahri baiwa ce da Allah ya bata ta saurin fahimta da gano abu ba wai wayon ta ne kesa hakan ba, kuma hakan ne ya ke bawa Ummi wani irin tsoro game da al'amarin Fahrin din, shi yasa yanzu ta sauya salo da taku dole tana bukatar basu iska, domin shammatar bazata.


Hakan kuwa ba ƙaramin tasiri ya yi a zukatan su ba,duk da cewa lokaci lokaci suna ta da maganar haka kuma Fahrin tana matuƙar ƙoƙarin ankarewa da duk motsin da Ummi zata yi,sai dai abin da basu sani ba shine, salma ta fisu zagewa da ƙoƙarin san gano abun da ake ɓoye mata daga ɓangaren ummin,duk da cewa yanzu tasani amma ba wai sun fahimtar da ita babban al'amarin da yake wakana ba,da kuma zargin da Fahrin ta kewa ummin wanda ita kadai ta barwa zuciyar ta sanin wannan,



A bangaren chekass kuwa tuni yaran sa ya gano masa mazauni da kuma bayanai akan Fahrin ɗin ,sai dai kuma a yadda bayanan ya zo masa ya gano a kwai matsala babba idan ya ce zai shiga rayuwar Fahrin kai tsaye, duk da cewa shi ba ya tsoran komai in dai akan ikon sa da izzar sa ne, amma kuma haka nan yaji yana tsoran rasa Fahrin ɗin, yarinyar da alokaci ɗaya ta shiga rayuwar sa ta ke kokarin sauya tsari da duk wasu dokoki na mu amalarsa, cikin ikon sa ya bawa Mande umarni na biyu, akan yasa sauran yaran sa gaba ɗaya ta ko ina a sawa Fahrin ido da duk wani motsin ta kafin ya baiyana a gareta wanda shine abu da zaiyi na karshe idan bata aminta dashi ba,zai yi duk abinda zai yi domin samun ta a rayuwar sa,cike da bin umarni Mande ya amsa masa kana ya fita dan isar da sakon ogan ga sauran yaransu.



Sai da Benja ya yi kwana biyar cif kafin ya koma gida,shima sai da James da Dr Hisham suka ta kura masa kana ya koma,sai dai abin mamakin shine ko kallon banza Mr Mathew baiyiwa Benja ba balle a saka ran zaiyi masa fadan da kowa ya yi zato, 



Su Fahrin iyayen biki, yadda suka shige cikin manyan yanmata ana komai da su shi zai baka dariya su basu yadda ba sungirma, Karima ce kawai yar adawa tayi ta musu masifa, ita kuwa Adda Kulsum ta kancewa ai Ni su ne manyan kawayena,haka Adda zulfa ma take cewa dan dole bakin Karima yake mutuwa, su kuma su yi ta mata dariya da gwalo,


Gida ya cika taf da baki yan jalingo ma kaf sun ƙaraso ko ina ka shiga hayaniyar jama ace wadda hakan ya kuma mantar da su halin da suke ciki, ya yin da ita kuma Ummi a gefe ɗaya wannan damar ta ke ta jira a yanzu ta riga ta tabbatar da cewa sun shagala idanun su ya dauke daga kanta ,dan haka tana jin kwarin gwiwar fara aikata mugun nufin ta mataki na farko,



An fara gabatar da bukin al'ada wanda Yadikko bata yarda an zubda ita ba,kasancewar suna da babban fili a cikin gidan shi yasa basu cika fita waje ba, haka kuma su Abbu basu yadda da bidi o i a cikin aure ba, su ma sun san da haka,walimar ma da zasu gabatar tare da angwayen da kyar dadyn sama ya yadda suka fita waje suka kama waje saboda abokanan angwayen ne suka shirya ta,shi ma sai da aka daura auren a ka kai amaren kana aka shirya zuwa walimar,




Karfe biyar tuni guri ya fara dinkewa da al umma kowa ka kalla fuskar sa cike da annuri, sai dai haka nan Fahrin ta dinga jin wani irin tashin hankali wanda bata san daga ina ya ke ba, ko kuma dalilin yin sa,idanun ta shawagi kawai suke akan Adda Kulsum don kuwa damuwar ta da tunanin ta kaf ya na gun Adda Kulsum ɗin,Salma ce ta ɗan dafa ta kana cikin son kwantar mata da hankali ta ce"Fahrin ki nutsu insha Allahu babu abinda Zai faru da Adda Kulsum lafiya zasu tafi gidajen su, danni nafi tunanin Ummi babu abinda zata yiwa Adda Kulsum tunda yanzu aure akayi mata kinga gidan ta zata tafi don haka bata da wata fargaba akan Adda Kulsum"langaɓar da kai ta yi cikin wata iriyar fargaba da bugun zuciya ta ce" to amma Salma me yasa nake jin abin da nakeji? Me yasa nake ji kamar wani abu mara kyau zai samu dayan mu?babu komai kiyi ta maimaita innalillahi'wa'inna alaihi raji un zaki samu salama da nutsu a zuciyar ki",salma ta faɗa tana mai jan hannun ta dan su koma cikin mutane,maganganun salma ne su ka sa ta ɗan fara komawa walwalar ta,duk da dai ba wai ta daina jin abin da ta ke ji ba ne.



Karfe bakwai aka tashi daga wajen walimar kowa ya fara kokari da haramar komawa gida,wani ne ya zo kusa da Fahrin da take ta raba idon inda zata gano salma wadda ta tafi nemo musu ya Muhsin dan ya maida su gida,a dan tsora ce ta dube shi kana ta ja baya tana ƙoƙarin wucewa ta barshi  ya ce" ko bake ce Fahrin ba ƙanwar Muhsin,kasa amsa mishi ta yi,sai binsa da idanu da tayi cike da rashin yarda,ganin kallon da take mashi ne yasa ya ɗan murmusa kana ya Ce shi ne yace na kiraki ga can motar da za amai daku yar uwarki na ciki dan ita ce ma ta nuna min ke"kallon motar ta yi sai kuma taji daga can cikin motar Salma na cewa taho mu tafi Fahrin nice Yaya Muhsin ne ya ce a kaimu gida" jinjina kai ta yi sai ta fara takawa a hankali zuwa inda motar ta ke,wanda kuma har yanzun dai bata ji jikin ta ya bata cewa ta shiga motar Ba,ga kuma Muryar da taji bata yi mata kama da ta Salma ba,kawai binsa ta yi zuwa ga motar dan tabbatar wa idan ma Salman ce cewa zatayi mata ta fito su samu na gida ko su hau nafef,sai dai kuma kafin ta gama tunanin da ya ke kaiwa cikin kanta tuni taji an shaka mata wani abu a hanci daga haka bata kuma sanin abin da ya ke faruwa ba.



Salma dai da Muhsin duk wanda suka tambaya ina Fahrin sai ace musu angan ta tare da wani sun shiga mota,suna kuma kyautata zaton ko saurayin ta ne,da haka su ka hakura suka nufi gida da fatan idan sunje gidan su sameta,duk da ran Muhsin yayi matuƙar ɓaci da yadda ya samu labarin saurayi ta bi dan ya kaita gida,da gudu yake jan motar yana kuma bambamin faɗa wallahi sai na gayawa Abban kasa ita mahaukaciyar ina ce ?har yaushe ta fara samarin da har zasu ɗauke ta zuwa gida,sai ka ce wadda ta taso a gidan marasa tarbiyya"ita dai salma shuru ta yi ba tare da ta tanka masa ba don ita bata jin zuciyar ta na sanar da ita lafiya ce rashin ganin Fahrin ɗin.


Suna isa kuwa ta fita da gudu,kafin ka ce me salma ta fara cikinta Fahrin a cikin gidan lungu da sako, cikin kankanin lokaci ta ankarar da mutanen gidan rashin ganin Fahrin ɗin, Yadikko tuni ta fara birki cewa, cewa take maza aje nemo mata jikarta,tuni labari ya iske su Dadyn sama da sauran yayun ta,babu shiri aka bazama neman Fahrin wadda ta yi batan dabo har kusan karfe sha biyu da rabi babu ita babu alamar ta,abun da ya kuma daga wa mutanen gidan hankali ke nan karamar magana na neman zama babba,duk inda ake zaton Fahrin an duba babu ita har gidan amaren Sai da aka je amma babu ita,tuni hankalin Adda Kulsum ya tashi yayin da kuma ta wani bangaren ta ɗora zargin ta akan Ummi wanda har take shirin idan ba aga Fahrin din ba dole ne zata fadi gaskiya dan baza ta taba bari Ummi tayi nasarar salwantar mata da rayuwar yar uwa ba.



Salma ma dai kwatankwacin tunanin adda Kulsum shi ta ke yi, to amma fa ita bata da wata hujja har yanzu, tunda a cikin su babu wanda ya sanar mata abun da ke faruwa yadda zata fahimta ta san kuma ta inda zata fara,shedar da ta samu a ɗan binciken da tayi baza su isar mata komai ba,




Dukkanin yayyun ta mata hankali. Su a tashe yake Adda Fatima sai zagaye gidan take Adda Batul kuwa sunturin ban daki ta fara yi, Adda Nauwara ce ta ɗan fisu karfin hali , goggon su Halima kuwa kuwa take Kashir ban an rasa mai lallasar wani ita da Yadikko sai da Dady ya tsawatar musu da yi musu tuni akan addu'a ya kamata su yi.




Gaba daya salis mijin Adda Kulsum ya kasa gane kanta, duk da kwantar mata da hankalin da yake amma abanza,tana ganin fitar shi ta yi saurin daukar wayarta ta fara lalubo lambar Abbu wanda kafin ta kai ga samun lambar,kira ya shigo wayar ta,hannun ta na wata irin karkarwa ta daga,wata kakkausar murya ta ji ana yi mata gargadi mai matukar zafi da razanarwa,me maganar ya cigaba da cewa idan kika sake kika fadi wani abu akan Hajiya Nadiya to tabbas zamu kashe yar uwarki sannan kema mu kashe ki dan haka sai ki zaba tonawa Hajiya Nadiya asiri ko rayuwar ku?kuma ba iya yanzu nake miki maganar nan ba, na baki wannan sharadin ne har zuwa lokacin da zamu gama cimma burin mu, dan haka zabi ya rage naki"daga haka ƙit aka kashe wayar,bin wayar tayi da kallo wanda sai alokacin ne ta ga ashe da ɓoyayyar nombar aka kira ta.




A bangaren Ummi kuwa cike da tsananin tu ajjubi take duban Karima da ke ta kuka tana sanar mata abin da ke faruwa,da kuma tsawon lokacin da ake ta duban Fahrin ɗin ba aganta ba,da sauri ta koma bangaren ta har cin kafa take saboda ruɗewa da sauri,wayar ta ta dauko ta lalubo lambar Dr Hisham, tana fara ringin ya daga cikin kwantacciyar murya wanda kana ji zaka san cewa hankalin sa a kwance ya ke,ya ce"hajjaju Barka da War haka ina fatan dai ba wata matsala aka samu daga ɓangaren majin yaci na ba? cike da ruɗewa ta ce" kai Hisham me ke faruwa ne? Ko kasan wani abu game da bacewar Fahrin? Tashi ya yi da ga kashingiden da ya ke,tare da cewa ban gane ba me kike nufi ? Naga dai duk wani abu da zanyi zanyi shine tare da sanin ki kuma abin da muka shirya yau din mun fasa ai watar wa,ina ce kuma ba akan Fahrin ba ne akan yar uwar ta ne? Haka ne Hisham mun canja shawara akan zamu rabu da Kulsum tun da tayi aure sai dai zamuyi mata baraza akan ɓoye sirrin da ta sani,to amma idan babu hannun ka babu hannu na ci kin batan Fahrin to waye? Gaba dayan su shuru su kayi na dan wani lokaci kafin daga bisani Dr Hisham ya ce" amma Hajiya abin da mamaki waye ya shiga rigar mu zai yi amfani damu dan cutar da Fahrin? Kuma akan wane dalili ne? Ummi ta ce" Ni ma tunani na kenan amma tabbas akwai matsala,bana son rasa Fahrin a yanzu domin ita ce makamin nasarata ta sanadin ta nake fatan cimma gaci,dan haka dole mu san abinyi tun kafin lokaci ya kure mana tunda yanzu an riga anyi mana shammatar bazata" motsin da taji kamar na faduwar abu shi yasa ta yi saurin katse wayar tare da nufar kofa.


Cikin sauri salma ta bar gurin kamar zata kifa,zuciyar ta cike da tsoran da Fahrin ta ke jin makamancin sa,wanda a tunanin ta ko mai ma bai kai taji masa irin wannan tsoran ba,amma ashe a rashin sani take jin hakan,yau ta tabbatar da abinda Fahrin take fada,ashe dama Ummi zata iya duk wannan abun? Me Fahrin tayi musu? Shin me take nema wanda dole sai ta cutatawa baiwar Allah zata same shi?wani irin tashin hankali taji wanda ya kuma hadewa da tausayin yar uwarta,dama ashe haka Fahrin ɗin ta ke ji duk sanda tayi ƙatari da mugun nufin ummi ? 


To yanzu kuma su waye suka kuma kutsawa cikin rayuwar Fahrin ɗin? Shin me ta yi musu? Me suke so daga gareta? Anya kuwa ba yan kidnapin bane?yanzu tana ina a wane hali take? Su ne rudaddun tambayoyi mafi muni da saka fargaba a cikin kwakwalwar salma,kuka ta saka saboda rashin samun mafita, tabbas Fahrin ta yi gaskiya ba kai tsaye ne zasu iya gabatar da wannan mummunar al'amari da ummin ke shiryawa ba, tabbas sai ayanzu ne take da ɗa fahimtar Fahrin ɗin tare da jin wani mugun tausayin ta.



Allah sarki uwa mafi kusanci ga da ko danta, kallo ɗaya za ka yi wa Dada kasan cewa zuciyar ta na cikin tsananin damuwa, tun tana kawar da abun saboda tsananin kawaici har ta kai ga ta fara karaya, ahankali ta sulale ta koma bangaren ta, ta re da kulle kanta a daki tana mai kokarin karfafa kanta da addu oi na kariya wa diyarta ta,alwala tayi ta fuskanci alkibla inda ta fara kai kukan ta gurin mai sama domin tasan shi kadai zata yiwa kuka ya da beta kuma tasan cewa addu'ar ta ba mai shamaki ba ce zuwa ga diyoyinta .



Abbu ma dai abun kusan yawa ya yi masa ga kukan Yadikko a kan sa ga kuma damuwar bacewar diya mafi soyuwa acikin zuciyar sa, dauriya kawai yake yi saboda ya karfafawa Yadikko da sauran yaran zuciya,ya kuma yi kawaici wa yan uwan sa da suka suke cikin damuwa, amma ina duk a banza domin tashin hankalin da suke ciki ba mai misaltawa ba ne,Ummi ma wannan karon da gaske tayawa take da jajen Fahrin ɗin karo na farko da abu ya faru akan Fahrin ɗin tayi wani abu da gaske ba amatsayin pretendin ba.



Kwance yake a bayan motar da cikin ta yake tamkar ƙanƙara saboda sanyi,kamar yadda ya zame masa jiki idan ba waya ce a hannun sa ko laptop ba to idanun sa zasu kasance ne a lumshe,buɗe gajiyayyun idanunsa ya yi yana mai jin yadda adebayo ke sharara gudu kan saman kwaltar da zata mai da kai ikeja,haka nan ya samu zuciyar sa da wani irin bugu tamkar wanda ake dakan sakwara, har saida ya maida manyan idanun sa ya runtse yana mai fatan raguwar bugun da zuciyar tasa ta keyi,sai dai kuma kamar ance ya bude idanun sa, haka ya bude su yana mai zubawa titin da motoci suke wuce wa tsalli tsalli kasancewar titin ba wani kyau ya cika ba shi yasa ba kowane ke iya biyo hanyar ba,bawai rashin kyau na hanya ba rashin kyau na mahaya hanyar,wanda shima ba kasafai yake biyowa ta titin ba, haka nan tun ɗazu ya samu kansa da bawa Adebayo umarnin bi ta hanyar,wanda shi kansa bai san dalili ba,acikin tunanin da yake ne ya lura da motar da tun dazun ta sharto da gudu ta wuce su,amma sai gashi har sun zo sun tarar da ita wanda ga dukkan alamu matsalar faci ne.


Kamar wanda aka bashi umarni,haka yaji bakin shi da ya yi nauyi ya bude tare da cewa Adebayo ya dakata su bawa motar nan safaya taya dan yaga tabbacin facin su kayi, Adebayo ya ce"Oga wajen nan fa bashi da kyau kuma ina ga Allah baza su rasa safayar taya ba"shima BENJA ɗin yayi tunanin haka sai dai kuma haka kawai wani bari na zuciyar shi ke ta angizashi da bashi umarnin tsayawa ga wannan mota,jin shuru tuni Adebayo ya shiga taitayin sa ya yi kuma gaggawar bin umarnin ogan nasa,a hankali ya gangara bakin hanya inda motar da suka gani ita kuma take daga bayan su kaɗan,


Cikin sauri da ƙoƙarin cika umarnin mai gidan sa ya fito daga motar kai tsaye yana nufar inda motar take tare da mutumin dake tsaye yana ta faman rarraba idanu domin hakikanin gaskiya babu safayar taya abayan motar sa shi yasa gaba daya yake a rude gashi wayar da yake ta san kira ta ki shiga,zubawa Adebayo ido ya yi yana san fuskantar abun da ya tsayar dashi har kuma yake san zuwa inda yake, Adebayo ne ya katse shi da cewa kana bukatar taimako ne? Ga nan ogana ya bada umarnin a taimaka maka" ya faɗa yana duban mutumin, da sauri da kuma alamun rashin gaskiya dake tare dashi ya ce" to madalla dama taya nake bukata" jin jina kai Adebayo ya yi tare da cewa ok bara na dauko maka,yana juyawa shima mutumin ya juya zuwa cikin motar tare da dan zura kanshi cikin motar kamar yana magana da wani,hakan da Adebayo ya gani shi yasa masa shakka da tsarguwa, dan haka cikin sauri ya leka inda Br BENJA yake ya ce Oga inaga fa kamar mutumin nan bai da gaskiya akwai abinda yake ɓoyewa " kafin ya rufe bakin sa tuni Br BENJA ya zuro zaratan kafafun sa zuwa waje wanda dama hakuri kawai yake yake zaune cikin motar amma ji yake tamkar ana mintsinin zuciyar shi,yana ji ne kamar ana sanar dashi cewa da wani abu mai muhimmanci da ya kamata ya yi a wajen,nuni ya yiwa Adebayo da ya dauko tayar, cikin azama da sauri ya bude but ɗin motar, a hankali Benja ya ke nufar motar kansa tsaye ba tare da wani tsoro ba cikin kuma takun shi mai bawa yan maza tsoro,a daidai lokacin da mutumin ya bar jikin motar yana tsumayin Adebayo ya kawo masa tayar,sai dai kuma kiris ya rage bai hadiyi zuciyar shi ba saboda ganin irgarman namiji zakin zakuna a gaban shi ba tare da tsammani ko zato ba,duk da cewa dare ne amma hakan bai hanawa mutumin gane miskilalliyar fuskar BENJA ba,ina zai iya manta Br BENJA mutumin da ba wani br da zai iya takara dashi in dai a fagen nasara ne, wanda kuma ya sameta ne a sanadin gaskiya da tsayawa akanta, cikin dan rawar jiki mutumin ya ce" Br da kanka ai da ka kirani zanzo har mota na sameka" ba tare da ya saurari abin da mutumin ke faɗa ba ya wuce shi dan zuwa inda zuciyar sa ta ke kada shi, cikin sauri mutumin ya bi shi yana maganganu marasa kai,a hankali ya ɗan duka ya rage tsayin sa kana yasa dogon hannun sa ya bude murfin motar,ga tsananin mamaki sai ga mutum har biyu aciki,bayan na gaba da akwai mace a baya sai wata macen dake kwance kamar me bacci,ido ya ɗan lumshe kana ya bude su fes akan mutumin da gumi yake ta faman zubowa , idanun shi kuwa tamkar zasu fado saboda tsananin tsoro, cikin husky voice din shi ya ce su waye waɗan nan? Zare ido ya karayi a hankali kuma yana neman hanyar tsira, kwarjini da gaskiyar BENJA su suka saka gaba ɗaya ya rasa hanyar kare kanshi ko da dabara ce,ga kuma rashin gaskiyar da ke tare da shi,kafin wasu sakanni ya bawa kafafun shi iska ya bace bat daga gurin, ganin haka sai na cikin motar ma jikin su ya dauki rawa karma macen taji labari,wa kuka sato tambayar da ta doki tsakiyar kawunan su kenan.