Chapter 10
by @zahra48
💕
**ƘADDARATA*
*SANADIN* *HASKE* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*
```Page10 ```
*Free* *pg*
Kamar waɗan da aka saka salatif abakunan su sun kasa cewa komai sai jikin su da yake bari, Adebayo yasa ya haska fuskar yarinyar, dum haka ƙirjin shi ya buga, Adebayo ya ce"Oga kamar yarinyar nan ta wancan garin da,shuru babu amsa sai ma duban shi da ya maida kan saurayin da yake gaba yayi mashi alamar yana jiran amsar sa ta farko, cikin rawar baki macen ta ce" wallahi yallabai ban san komai ba hayoni aka yi"cikin zarrar shi ya nufi daya bangaren ya buɗe motar tare da sunkuyawa cikin nutsuwa ya janyo ta ya rungume ta ajikin shi kai tsaye ya nufi motar shi da ita,ba tare da ya kuma duban inda suke ba,kamar jira suke saurayin ya yi saurin fita daga motar ya dauki hanyar tsira haka ita ma budurwar bata tsaya sanya ba gurin barin gurin duk da cewa tana jin matuƙar tsoro kasan cewar dare ya tsala sosai,shiga mota Adebayo ya yi yaja bayan ya tabbatar ogan nashi ya kimtsa.
Dan duban ta ya yi ƙasa ƙasa, wan da idan ba matuƙar lura kayi ba ma baza ka ce ita ya kallaba, cikin Muryar shi da kamar anayi masa dolen magana ya ce"muje can gida"Adebayo ya gane gidan sa na sirri ya ke nufi dan haka sai ya yi ribas ya juya tare da ɗaukar hanya cikin wani irin mahaukacin gudu da suka riga suka saba dashi.
Bazan iya kwatanta muku ga irin kwanan tashin hankalin da akayi a wannan family ba,Dada kwana tayi tana kai kukan ta gurin rabbil alamin ya kare mata ɗiyar ta a duk inda take,Salma kuwa ta kasa katabus ita da Karima gaba ɗaya kwana su kayi kuka, mazan gidan su kaɗai suke da dan ragowar karfin hali,mama kuka tayi har ta gode Allah,Ummi kuwa sunturi ne aikin ta ya yin da idanun ta suka kada su kayi jajur, duk saboda gudun rushewar katangar da ta fara ginawa,tana jin matuƙar takaici da haushin wanda ya yi mata wannan abun ko da yan kidnafin ne kuwa tabbas sun cuceta ,
Allah sarki Yadikko tun tana sanbatu da kiraye kiraye har ta hakura ta koma jan carbi, sai dai idan ta ɗan huta ka kuma jin tashin kukan ta da maganganu wanda take yi tamkar wata Zararriya,haka abun yake gurin goggon su Halima saboda tana matukar son Fahrin Bata jin banbancun da Salma,a haka har aka kira yi sallar asuba suna zaune dungurgur babu wanda ya runtsa, duk da irin sata ta bacci amma bai samu nasarar daukar ko daya daga cikin su ba, gaba ɗaya mazan suka fita sallar da niyar suna idarwa su kuma bazama neman Fahrin da shiga filin cikiya, ko Allah zai sa a dace ....
A hankali take buɗe idanunta wanda su kayi mata nauyi, tun tana ganin dishi-dishi har ya bude gaba ɗaya,a zubure ta mike tana wurga manyan idanun ta lungu da sako na dakin da take kwance,lafiyayyen daki ne mai tsananin kyau wanda kallo ɗaya zaka tabbatar da irin gidan da kake ciki,innalillahi a ina nake nan? Waye ya kawo Ni ? Me nayi muku? Tambayoyin da take ta yi kenan bayan kuma babu wani a kusa da zai iya bata amsa,tashi ta yi a hankali ta taka zuwa bakin kofar dakin, murdawa ta yi kamar da wasa sai ga kofar ta budu, kai tsaye ta fita ba tare da ta yi tunanin in da zata faɗa ba,matsakaicin falo ne mai kyau da aka yi masa kawanya da wasu lexa ɗin kujeru irin ai nahin na kasashen ketare ,komai na falon babu wanda yake na nageriya,babu wasu yawan tarkace wanda zai hana ka kasa ganin kawatuwar falon, wani sanyi da kamshi ne ya bigi kofofin siririn hancin ta,duk da halin da take ciki hakan bai hana ta lumshe idanun ta ba,motsin da ta ji ne ya ankarar da ita inda ta ke.
Tsananin mamaki ne ya hana ta motsawa daga in da ta ke, kallon shi take sosai kallon kurilla wanda yake nuna tsananin takaicin ta da kuma mamaki,bai damu da tsayuwar ta a gurin ba, kai tsaye wucewa ya yi tsakiyar falon cikin wan Nan takun nasa tamkar na sarakai, zama ya yi cikin kujerarsa yana mai daga daya daga cikin wayoyin sa, magana ya yi ƙasa-kasa daga nan kuma ya kashe ya janyo laptop din sa ya shiga opratin ɗin ta ba tare da ya nuna yasan da wata halitta a tsaye gurin ba,
Cikin tsananin jin haushi ta matso in da yake ba tare da ta zauna ba ta coge,me ye haka me kake nufi da sato ni da kayi me za kayi min ? Duk ma me nayi maka be kamata ka karya daraja ta ta diya mace ka sato ni ba"ta faɗa da ɗan karfi a saman kansa,tun yana gane abin da yake yi har ta sa ya dai na fahimtar komai, a rayuwar shi in akwai abun da yafi tsana bai wuce hayaniya ba balle kuma asaman kanshi,rufe laptop din ya yi tare da maida kan shi ya jingina, idanun shi a rufe, shi sam bai san meke damun wan Nan yarinyar ba,gashi nan saboda tsananin tsiwar ta ta janyowa kanta makiya kala-kala,yanzun fa ba da ban shi ba da yanzu tana can anyi garkuwa da ita,amma yanzu gata a saman shi tana yi masa hayaniya da maganganun da ya kasa gane kansu,yadda ya yin sai hakan ya kuma kular da ita, kuka tasa masa tana ci gaba da maganganun ta,dai dai nan aka yi norkin ɗin falon aka shigo, Adebayo ne dauke da wata leda me tambarin gidan abinci a hannun shi, cikin girmamawa ya aje ledar gefan da Fahrin ta ke, ɗan duban ta yayi kana cikin girmamawa ya ce" Madam ga nan break ki ɗauka sai a maida ki gida, ai Allah ne ya taimake ki da mutanen nan sun tafi da ke da yan zu ma sun kasheki dan ina da tabbacin ba yan garkuwa bane, saka su aikin sato ki kawai akayi dan tun jiyan mu kayi bincike mun sami tabbacin hakan mutanen ne dai bamu gano daga inda suke ba da kuma wanda ya sa su ba,,,kallon da Benja ya watsa masa shi ya dakatar da shi daga zubar da ya fara wadda ba a sashi ba,da sauri ya juya ya bar falon yana shafa sankon kanshi.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin nutsuwa da wata irin yadda na shigar ta,dama haka nan taji zuciyar ta bata gama gamsar da ita cewa shi ya sace ta ba,bayanin da Adebayo ya yi mata shi ya kuma fidda ta daga cikin duhu,a sadade ta nemi kujerar da tafi kusa da ita ta zauna tana maida numfashi,samun kanta tayi da yi masa kallon kurilla kyakykywa ne ajin karshe me cike da kamala ta gaskiya da ace a kwai hasken musulunci a tare da shi to tabbas da anyi kallon nagartacce kuma kamilallan mutum,wani irin sanyi taji yana ratsa ta da wani irin nauyi cikin ƙirjin ta,haka ta dinga jin shaawa ta kasancewar sa musulmi kwadayin hakan ya sa ta ɗin ga bin sa da wani irin kallo tana jin shaukin hakan cikin jiki da zuciyar ta,amfanin da zaiyiwa Muslunci yana da yawa ina ma ina ma,
A hankali yake jin yadda idanun ta ke bin jikin sa suna jefa shi cikin wani irin yanayi na tsananin kasala,ƙara kwantar da gangar jikinsa ya yi saman wadatacciyar kujerar sa, tun yana jurewa har ta kai da ya fara bude fararen idanun sa wanda ba su sauka a ko ina ba sai tsakiyar idanun Fahrin,a wani irin bazata abun ya zo mata,diriricewa ta yi tare da ƙoƙarin kawar da nata ƙwayar idanun,samun kanta tayi da jin nauyin sa saboda yadda ya kamata dumu-dumu tana kallon sa, shi ma din kallon ta ya ke kai tsaye ,miƙewa ta yi da sauri kana cikin rawar murya ta ce"na gode da taimakon ka amma dan Allah ka sa amai dani gida nasan yanzu hankalin iyayena yana can a tashe" ta kara sa maganar tana mai ɗan rissinar da idanun ta da suka kawo ruwa, ba tare da ya ce" komai ba ya mike ya nufi hanyar barin falon hakan ne yasa itama ta bi shi da hanzari, dan a ɗan iya mu'amalar ta dashi ta fahimci rashin maganar sa ya fi maganar sa yawa,
Ga mamakin ta mota daya suka shiga Adebayo yaja su, wanda ita a tunanin ta Adebayo ne kadai zai kaita gidan,sai ta dinga jin karamcin sa ga dan adam yana matukar burgeta, tana kuma karajin san kusanci da shi ta bangaren gauraya a addinin Musulunci,zaman kurame su kayi tun bayan da ta gama yiwa Adebayo kwatancen gidan su,sai dai kuma haka nan take jin muradin kallon kyakykyawa kuma kauwamammiyar fuskar sa,dan haka lokaci lokaci takan dan saci kallon shi,a haka har suka kai kofar gidan su Adebayo ya saki hon, Baba sani me gadin su shi ya yi hanzarin lekowa saboda yanzu sam basa wasa da bako ko wani motsi da zai shin shino musu samun Fahrin din,
Adebayo ya samu guri ya yi fakin,da wani irin gudu Fahrin ta buɗe motar ta fito kai tsaye ta nufi falon yadikko, wanda dukkan mutanen gidan suke ciki,kamar daga sama Dada ta ji an fado jikin ta, sai kowa hankalin sa ya koma kansu wanda tuni su Ya Muhammad sun fara fadin Alhamdulillah,dagota Dada tayi kana ta kuma rungumota jikin ta kamar za akara sace Mata Fahrin ɗin,daga haka Fahrin ta dinga rungume yan uwanta da Abbun ta Salma da Yadikko su suka zama na karshe tana tsakiyar su kamar zata koma Cikin Yadikko,Abban kasa ne ya danyi gyaran murya kana ya ce"auta daga ina kike hankalin kowa a tashe ya ke tun jiya babu wanda ya runtsa a gidan nan"sai alokacin Fahrin ta tuna da Su Adebayo dan haka cikin sauri ta tashi tana cewa Abba suna waje wanda ya taimaka min yana waje tare muke"Muhsin ne ya yi saurin tashi yana cewa kinji matsalar ki da anyi magana kice ke mai hankali ce, zunbura baki ta yi tare da matso ƙwalla shi kuma ya fice dan shigowa da bakin,
Tun da ya sako kai cikin falon hankalin ta ya koma kansa, kyakykyawa ne ajin karshe,takun sa kansa abun burgewa ne, cike da wata irin nutsuwa ya kara so ya zauna a in da Dadyn sama ya nuna masa, babu wanda bai gane shi ba ,Dady ne yayi magana da cewa sannu yaro akaro na biyu ka kuma taimakon yarinyar mu mun gode sosai"Yadikko ta amshe da cewa Allah yayi maka albarka Duk da cewa ba mutsaya munji daga bakin ka ba amma mun san ko da yaushe taimako ne yake shiga tsakanin ka da yarinyar mu"shuru ya ratsa falon shi Br BENJA tunanin ta yadda zai fara magana mai tsawo cikin munen ya ke, su kuma jira suke su ji ta in da al amarin ya fara,wayar shi ya zaro ya yi wa Adebayo text message jim kadan kuwa sai gashi a bakin falon yana magana cikin gurbatacciyar Hausar shi,Abbu ne ya bashi izinin shiga , kamar jira yake tuni Adebayo ya fara zuba labari tun da ga yadda akayi suka tsaya har zuwa yau da safiyar nan, Yadikko salati ta saka tana tafa hannaye, Ummi kuwa tuni ta faɗa zuzzurfar tunani akan al'amarin da yake neman shige mata duhu,shin mutanen nan suwaye?idan ba masu garkuwa ba ne to su waye? tabbas al'amarin akwai rikitarwa a gareta kuma dole ne ta tashi tsaye dan gano su waye suke san shiga rigar ta, da kuma abin da suke nema a cikin gidan nasu,
Godiya mai tarin yawa Abbu da Dadyn sama Abban kasa da sauran iyayen Fahrin su kayi wa su Br BENJA,Wanda har ya bar gidan basu da masaniyar cewa shi din Christian ne,Abbu ne ya ce da su Adda Kulsum su tashi ya Muhsin ya maida su gidajen su, dan bazai yuwu da ga kai su jiyan nan ace har sun fito ba,daga nan ya nufi sashen bakin su yan biki domin sallamar su dan a yau zasu koma jalingo.
Fahrin da salma kuwa daki suka shige, tuni ta fara bata labarin abin da taji Ummi na tattaunawa da mutumin da bata san ko waye ba a waya,shuru Fahrin ta tayi cike da tunani,sai daga can ta ɗan sauke numfashi kana ta ce" to Salma ko dai masu garkuwa ne? Idan basu bane waye zai nemi salwantar da rayuwa ta bayan Ummi? Tabbas in dai ba Ummi ba ce to masu garkuwa ne" Salma ta ce" haka ne Fahrin amma dai dole ne muyi ta ka tsantsan, shi mutum mugu baka sanin ka aikata masa ko mai yake shiga rayuwar ka,yanzu ga misali me kika yiwa Ummi Take son ganin bayan ki ke da ahlin ki?shuru ta yi tana mai gamsuwa da maganar salma da kuma kara zurfafa tunani.
Fitowar shi ke nan daga wata shari a,ya ci karo da dandazon yan jarida,tun dazun suke fakon fitowar shi,saboda yau Br BENJA ya samu nasara akan wata doguwar shari a da ta jima, akan dan shahararren mai kudin nan mai suna Alhaji babayyo kwangila,ya yiwa yar aikin gidan su fyade wadda ta kasance marainiya bata da uba,sun yi yawan kotuna kimanin guda biyar ana korar shari ar, wata kuma a zuba kudi a take musu hakki, dalilin ke nan da yasa shari arta shiga bakin yanjarida, baran ma da Br BENJA ya karbi Shari'a kuma ya tsaya musu har zuwa yau da suka yi nasara , duk yadda ya so gujewa yan jaridar nan amma hakan bai samu ba, sai da ya tsaya ya saurare su, ya kake jin ka a wannan rana sakamakon nasarar da kasamu? Wani kyakykyawan murmushi ne ya subuce kan kamilalliyar fuskar shi,wanda shine am sar tambayar su, wanda kuma a take suka gamsu da wannan amsa domin kuwa murmushi akan fuskar Br BENJA Abune mai matukar tsada da wahala,kai tsaye dan jaridar ya kuma watso mashi wata tambayar da cewa ko zaka gaya mana meye sirrin nasarar ka? A hankali ya buɗe baki cikin taushin Muryar sa ya ce" gaskiya da rukon amana da kuma kaucewa cin hanci da rashawa"daga haka ya yi saurin zagaye su ya bar su sake da baki da matukar mamaki da burgewar da ya yi wan da dole hakan ta faru a matsayin sa na me bin addinin Nasara,(ba wai babu hakan cikin addinin su bane a'a ko da ace Benja musulmi ne dole za ayi mamakin hakan saboda abin da ya yi wuya kuma ya yi ƙaranci ne a cikin al ummar mu,wanda shine ya kawo yawai tar abubuwa mara sa kyau da dama Allah ka bamu ikon ci gaba da gaskiya da kuma yada ta tare da kareta Amin Ya Allah).
Officce ya shige ya Wada toilet tare da sakawar kan sa shaya,sai da ya kimtsa tamkar wanda yake gida, dan officce din nasa ba bu abin da babu na bukatar yau da gobe,zama ya yi saman kujerar falon da ke cikin officce din, lumshe gajiyayyun idanunsa ya yi,tare da zurfafa cikin tunanin da ya sarke shi a cikin waɗan nan kwanakin,sam ya rasa dalilin da yasa yake ta san lallai sai ya gano mutanen da suke bibiyar ta,to amma ya aje hakan amatsayin taimako wan da ya saba yi a matsayin sa na kwararren lauya mai yaki da duk wani kuskure,da wannan matsayar ya samu karfin gwiwar ci gaba da laluben abun da ke cikin duhu.
Ke Fahrin zo nan ki ga" Yadikko ta faɗa tana mai kara zubawa tv plazman dake falon ta idanu, Fahrin ɗin ce ta ƙaraso tana cewa haba Yadikko irin wannan kira haka sai kace mai ciwon makanta" Yadikko ta ce" dalla Ni zo kiga abin da nake son ki gani kamar wan nan bawan Allah da ya dawo dake gida" da sauri Fahrin ta maida hankalin ta kan tv a dai dai lokacin da dan jarida ya wurga mashi tambayar cewa meye sirrin nasarar sa,kuri Fahrin ta yi tana kallon dan madaidaicin laɓɓan shi yana motsawa a hankali ya na fitar da kalmar gaskiya da rikon amana cikin wani irin salo na burgewa wanda yake a cikin jinin sa,bata san sanda ta nemi guri kusa da Yadikko ta zauna ba tana mai ci gaba da kallon takun shi tamkar na dawisu ya yin da yake tafiya zuwa officce din shi , Yadikko ta ce" kai Masha Allah wan Nan yaro dan halak ne ashe ma lauya ne,sam Fahrin bata fuskan tar kalaman Yadikko hasali ma ita tuni ta tafi zuwa wata duniyar tunanin ta ya fara karkata akan tambaya daya anya kuwa Br BENJA ba musulmi bane? Me yasa duk wasu dabi un shi suke kama da Musulmin kwarai ko kuma irin manyan malaman da su kayi shura akan kyawawan halaye?lumshe idanun ta tayi tana mai jin dadin zurfafa tunanin ta akan Br BENJA.
Cikin tsananin fusata chekass ya dubi yaran shi, da idanun shi da suka yi wani irin ja, ya ce" ya zama dole ku nemo min su ko a ina suke, da su da wan da yasa su sato tan duk bazan kyale su ba ,babu wani wanda ya isa na yi tarayya dashi akan kauna ta ta farko a duniya ,ban sani ba so ne yasa akayi mata hakan ko kuwa wata manufa ce ta daban? to koma dai meye ina so a ne mo min su cikin gaggawa"sai kuma ya danyi kasa da Muryar sa ya ce "yan zu na shirya zan shiga rayuwar ta zan jure duk wata wahala zan aje matsayina yanzu lokacin SOYAYYA ne,hannun sa ya haɗe waje daya su ka yi wata kara kana ya juya ya bar su cike da tsananin mamakin sa.
Hankalin Ummi a matuƙar tashe yake neman mafita kawai take idanun ta sun rufe, tana tunanin ko ma waye ya shigo rayuwar su Fahrin da rigar ta tabbas ba ƙaramin kwararre bane, kuma sai da ya san komai akan ta, amma abin da mamaki a ce an san abin da take shiryawa a cikin gidan wanda kuma babu wan da yasan da hakan face Fahrin ɗin,to ko dai Fahrin ce take son yin wasa da hankalin ta? Kai an ya kuwa tunanin Fahrin ya kai nan ? Zama ta yi gefan gadon ta tare da kara wayar ta akunne bayan ta fara ringin,
Dr Hisham da ke zaune cikin officce din Br BENJA ya ɗaga wayar da sauri, samun kansa ya yi da tsaida tunanin sa akan wayar da Hisham ɗin ke yi abin da bai taba yi ba tsawon rayuwar sa,in dai abu bai safe shi ba baya saka kan sa aciki, shafar ma irin ta aiki,amma sai gashi a wan nan karon al amarin ya sauya, sai dai ya yi la akari ne da rashin gaskiyar da ya kula Hisham ɗin nayi,kamar da wani abu da ya ke ai katawa na rashin gaskiya,Br BENJA yana da saurin fahimtar mai laifi ko dan hakan ya zama daga cikin aikin shi ne, dalilin da yasa ke nan Dr Hisham bai cika sake wa a gaban shi ba in dai zai yi irin wadan nan wayoyin,yan zun ma kasa tashi ya yi dan gudun kar ya kama kanshi duk da ya lura hankalin Benja ɗin sam baya kan shi a na sa ganin kenan.
Daga can ɓangaren Ummi kuwa cikin ɗan daga murya ta ce"Dr Hisham maza kazo akwai matsala ina bukatar ganin ka, kuma kazo tare da wannan allurar ina ga lokaci ya yi da zamu fara gabatar da aikin mu na gaba" Dr Hisham ya ce" daga cikin su wa za a fara yiwa Fahrin ɗin ko Abba?
Amsar da ta bashi tayi daidai da zubewar farantan da salma tazo nuna mata wan da ta ce" su siyo mata su a kasuwa,tsananin ruɗewa ya hana ta matsawa daga bakin kofar har sai da ummin ta fito ta sameta anan.
Me kake yi haka? Dr akwai wani abu da ba daidai ba da kake aikatawa? Maganar Br BENJA ta dira tsakiyar kunnuwan sa wan da kuma bayan diriri cewa da ya yi har da dimbin mamaki ma akan yadda har benja ɗin ke son fuskantar wani abu cikin aiyukan da yake shiryawa ,bayan ya riga da yasan cewa shi ba mai shiga hurumin da bana shi bane,kawar da maganar ya yi ta hanyar duban kofar officce din da James yake shigowa,
Wani irin duba Ummi take mata, tamkar wadda zata hango hanjin cikin ta,wani irin ruwa ne ya taru cikin idanun Salma jikinta da zuciyar ta kuwa babu in da ba ya rawa, ta yi matukar girgiza da jin abin da ummin ta ke shirin aikatawa,idan kuwa haka ne baza ta taba bari hakan ta faru ba,juyawa ta yi cikin sauri zata bar gurin sai dai ina ta makaro dan tuni ummin ta ankara da hakan har ta yi saurin shan gaban ta, cikin wani irin rikitaccen kallo ta ce"Salma kina tunanin zaki ji sirrina Aban za ne? Kina tunanin zan barki kici bulus? To lallai kuwa zuyarki ta gaya miki karya"domin jin sirrin NADIYA dai dai yake da zuwan mala ikan daukar rai,,,,,,