Chapter 11
by @zahra48
💕
**ƘADDARATA*
*SANADIN* *HASKE* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*
```Page11 ```
*Free* *pg*
Ba yabo ba fallasa suka gaisa da James ɗin wan da kwata kwata basa jituwa ko meye dalili?mai da hankalin sa ya yi kan aikin sa sai dai kuma hakan da Dr Hisham ya yi shi ya kuma tabbatar masa da zargin da yake yi masa ,ji ya yi yana son sanin ko meye haka kuma yana ji kamar abun ya shafi rayuwar sa duk da yasan cewa hakan abu mai wuya a ce Dr Hisham zai cutar dashi, James ne ya matsa in da yake da nashi korafin wan da shi kuma Benja ɗin sam bai ma daga kai ya kalleshi ba ,da ya gaji da hayaniyar sa ne ya ce", in dai saboda wan nan muƙamin Pastor din ne to na bar maka kaje kayi duk abin da Ni na kasa" ya faɗa hankalin sa kwance ba tare da ya daina abin da yake yi ba,kallo James ɗin ya bishi da shi yana jin takaicin abun da Benja ɗin yake yi har cikin ran sa, ji yake yi da shine ya samu damar da ya samu ai da ba zai taba sake ya yi wasa da ita ba,amma dai bazai gaji ba zai cigaba da lallaɓa shi har zuwa wani lokaci,ya yin da shi kuma Dr Hisham ya yi amfani da wan Nan DAMAR ya fece.
Cikin kankanin lokaci Dr Hisham ya ƙaraso gidan, bai shiga ko wane vangare ba, kai tsaye ɓangaren Ummi ya nufa,
A dai dai lokacin Salma take sake ƙoƙarin guduwa daga dabaibayin da ummin ta yi mata,a razane ta dakata tana mai duban wanda ya tare mata hanya a karo na biyu,da ido Ummi tayi wa Dr Hisham magana, hannun Salma ya danka kafin salma tayi wani yunkuri tuni ya soka mata allurar da tuni ya riga ya haɗa ta tun daga mota, daga nan ta tafi luu ummi ta yi saurin taro ta , da taimakon Dr Hisham suka kaita wani daki dake can karshen falon, duban juna su kayi kana ta ce" Dr aikin ka na kyau Ni kuma zanyi sauran aikin, kaga daga nan kofa ta bude mana" na fara jiyo ƙamshin nasara, wan Nan matakin shine mataki na farko kuma kaddara ta farko da zata yiwa Fahrin tutsiye cikin rayuwarta".
Tun tana zuba idon shigowar Salma har ta fara kosawa,lokaci lokaci takan dan duban hanyar kofar falon yadikko,kamar Yadikko ta san abun da ke ranta ke nan,ta ce" farere ko wan Nan uwar san jikin kwanciya ta je tayi ne? Tura baki Fahrin ta yi tare da cewa gaskiya Ni dai Yadikko ki daina cemin farere sai ka ce wata fara ta faɗa tana mai ci gaba da zubawa hanyar idanun ta, sai kuma gaban ta da yake ta faduwa wan da sanadin ke nan da taji hankalin ta ya kuma tashi, Yadikko ta ce" yo Dan kaniyar ki ba sunan ki bane? Kuma Ni duk abin da na yi niyar faɗa sai na fada sai dai mutum kar ya amsa" a halin yanzu dai hankalin Fahrin ya kai kololuwar tashi dan haka ba ta fuskan tar ko mai a duk zantukan da Yadikko ke yi mata,tashi ta yi tana cewa Ni dai bari na duba Salma bana jin lafiya ce ta zaunar da ita" tana mai kara sa zan cen azuciyar ta da cewa duk abin da ya haɗa da Ummi to tabbas babu Alkhairi a cikin sa,ita dai Yadikko ci gaba ta yi da murza goran ta hankali kwance.
Tsaye yake jikin dankareriyar motar shi kirar mbw, jikin shi sanye da manyan kaya wan da suka haɗu suka lullbe ainahin shi, suka fidda zahirin shi na cikakken kanuri,ya yi kyau matuka tun da ba wai sabawa ya yi da shigar ba,amma ya riga da ya sawa ranshi zaiyi duk wani abu da zai samo masa SOYAYYAr Fahrin , da karfin shi yazo da kuma kwarin gwiwa wan da yake fatan ko da bai samu kulawa farat daya daga gurin FAHRIN ba to tabbas zai samu daga gurin iyayen ta, domin shigar sa ita za ta siyo masa mutuncin da yake nema, haɗuwar shi da Dadyn sama shi ya tabbatar masa da haka, dan bai zo gidan ba sai da ya fara nemar iso daga gurin su Abbu, su kuma suka bashi dama saboda kamalar da suka gani a tare da chekas ɗin ,
Kicibus ta yi da ya Muhsin dan haka ta rabe dan bashi hanya ya wuce,amma sai taji yana cewa yauwa dama ke zan kira kije farfajiya kina da bako" yana gama faɗa mata ya shige falon yadikko,ya yin da ita kuma ta bishi da kallon mamakin abin da ya ce" jiki a sanyaye ta cigaba da tafiya,tun da ya hango ta ya kafe ta da Mayun idanun sa tamkar zai cinye ta, ashe hoto rage mata kaso mafi yawa ya yi daga cikin tsantsar kyawun da Allah ya bata,tafiyar ta mai cike danutsuwa yake bi da kallo yana auna yawan adadin kaunar da take kara narkewa cikin zuciyar sa,ganin tana neman wuce shi ne ya sa ya yi saurin shan gaban ta kana ya haɗe hannayen sa biyu tare da ƙaryar da kai kamar wani karamin yaro,ya ce" haba Fahrin ko kin san wucewar da kike ƙoƙarin yi dai dai ya ke da wucewa da numfashi na? Hakan da ya faɗa sai yaja hankalin ta har ta kai ga duban fuskar shi da ke yalwace da fara ar da yake ta kokarin kawowa kan fuskar tashi saboda rashin sabo,kai ɗin waye ? Me kake nema a wajena ? Ni Masoyi ne kuma SOYAYYA nake nema a wajen ki" ya bata amsa kai tsaye kuma hankali kwance,dan ya tsina fuska ta yi kafin ta ce", kayi haƙuri ba zaka samu wannan daga gareni ba na gode da soyayyar ka gareni" bata jira abin da zai ce ba ta yi saurin zagaye shi ta bar wajen har da dan gudun ta Dan karma ya nemi kara tsaida ita,bin ta ya yi da wani irin kallo na tsananin kauna tare da ɗaukar alwashi, Fahrin idan baki soni ta sigar da nazo miki ba, to tabbas zaki soni ta ainahi na, zaki san koni waye kuma dole ki soni" ya faɗa yana mai shigewa motar sa.
Duk taku daya idan zatayi tana yin sa ne tare da bugawar zuciyarta , jikinta kamar an zare mata laka tasa hannu ta buɗe bude kofar falon Ummi, shuru falon babu kowa sai ƙarar fanka da ac da ke tashi a hankali, dakin su ta nufa gadan gadan tana mai jin tsinkewar zuciyar ta na karuwa, tana gab da shiga taji alamun taku daga bayan ta, ido biyu su kayi da Ummi wadda ta kewa Fahrin ɗin kallon kin shigo hannu , cikin rawar murya da fargaba Fahrin ta ce"Ummi sannu da gida"murmushi ta yi ummin tare da cewa yauwa Auta"Fahrin duk sai taji bata yadda da irin kallon da ummin ke mata ba ga wani irin murmushi dake blushing kan fuskar ta,dan haka sai ta ɗan gyara tsayuwar ta kana ta ce "zan kira Salma ne Yadikko ce take kiran ta"da gira Ummi ta yi mata nuni da zata iya tafiya,kamar jira take kuwa da sauri ta faɗa dakin tana kuma fatan samun Salma cikin koshin lafiya.
Turus ta yi ganin Salman kwance tana ta sharar bacci cikin kwanciyar hankali,ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙarasawa ta ɗan taɓa goshin ta da ƙirjinta ta tabbatar lafiya babu wata matsala kana ta kuma sauke wata ajiyar zuciyar,ta shi ta yi ta Wada toilet tana mai ɗan jin relief a ranta da zuciyar ta,
Sai da Ummi ta ga shigewar ta dakin kana ta saki dariya tana cewa auta kin kusa zuwa hannu wannan ma yana daga cikin kaddarorin ki dan haka sai ki shiryawa karbar ta hannu bibbiyu,daga haka ta fice daga sashen hankalin ta kwance.
Cikin gaggawa ta gama shiryawa tana yi tana duban Salma da har yanzu ba ta tashi ba,kai ita idan ma ba gizo idanun ta suka yi mata ba sai ta ce ko irin juyin nan na cikin bacci bata ga Salman ta yi ba, cikin sakar zuci ta gama shirin ta a lokacin karfe biyu na rana kasancewar ba salla zata yi ba sai kawai ta fita daga dakin dan zuwa aiken da Dada zata yi musu su biyun, ba ta yi kokarin ta yar da Salman ba ganin duk tare suke itama ba sallar take yi ba,
Duban ta Dada ta yi kana ta ce ina salma ɗin ta ke? Dada bacci take tun ɗazu wallahi Ni kuma bazan iya tada ta ba"Fahrin ta bawa Dadan amsa wanda haka kawai take jin kamar ba daidai ta bada amsar ba,miƙa mata sakon Dada ta yi tana cewa sai kiyi sauri ki dawo kar ki kai yamma, kije baba na lado zai kai ki"ɗan tura baki ta yi kana ta ce gaskiya Ni dai a nafe zanje, cikin tsira mata idanu Dada ta ce"bazaki a motar haya ba, har kin manta da abin da ya faru ko Fahrin? Girgiza kai ta yi kafin ta juya tafita daga dakin gaba ɗaya.
Baba na lado yana sauke ta a harabar asibitin ta su Dr Hisham,kai tsaye ta nufi ɓangaren masu haihuwa,in da anan zata kai sakon zamzam ɗin da akayi tofin nakuda wa anty bishira faccalar yayar ta Anty Batul,da Anty Batul ɗin ta fara cin karo, da sauri Antyn ta tari Fahrin ɗin tana cewa ai inaga ma yanzu ta sauka amma bari mu bawa nos ɗin can ta bata dan shima babban taimako ne"zama Fahrin ɗin ta yi cike da tausayin bushirar, zaman ne ya soma gundurar ta dan haka ta mike ta fita reseption dan ta ɗan mike kafafun ta ta kuma shaƙi iskar subhana,daddan turaren sa wanda ta fara hadda ce shi cikin kofofin hancin ta shi ta fara shakowa, yadda zuciyar ta ta fara bugawa da sauri da sauri shi ne ya bata tabbacin shi din ne ba wai ƙamshin bane, lumshe fararen idanun ta ta yi kafin ta buɗe su fes akan hanyar da take sa ran bullowar shi ta nan,
Cike da wata iriyar izza da wani taku tamkar dawisun dake tafiya kan gajimare ya fara ketowa cikin reseption ɗin , cikin kankanin lokaci kallo ya koma kansa, idan ba cikakken sani kaiwa Br BENJA ba to tabbas zaka iya saka shi cikin sahun kimtsatstsu kuma managartan musulmai masu cike da tsantsar tsoran Allah,
Kallon shi take yi har bata son ɗauke idanun ta daga kanshi, hango shi kawai take yi cikin kamalantacciyar shiga ta alfarma a sahun gaba a matsayin limami ko kuma wani shahararren malamin da ya yi fice a fannin ilimin addini,har bata san sanda wani ƙawataccen murmushi ya shiga blushing kan kyakkyawar fuskar ta ba,tana jin dadin kallon shi tare da daddaɗan tunanin da take yi wanda bata ankara ba sai waigawa ta yi taga har ya wuce babu abin da ta kuma hangowa daga ƙawatacciyar fuskar shi sai dai ƙeyarshi wanda bakin gashi ke kwance yalayala tamkar dan asalin kasar Larabawa , sai abun ya bata dariya yanayin shirman ta da abin da take saƙawar duk shi yasa ta darawa wanda kuma har cikin zuciyar ta tana jin ba shirme bane tana fatan wata rana burinta ya cika hakan ta faru,zuciyar ta ta ce to daga wannan fa sai me? Samun kanta tayi da rufe idanun ta da tafukan hannayen ta tana jin kunyar shirman amsar da ta bawa zuciyar ta ta,tashi tayi cike da wani irin farinciki wanda sam bata san daga inda ta samo shi ba, komawa ta yi ɓangaren da su Anty Batul suke, anan ta samu Anty bushirar ma ta sauka, dan haka kawai sai ta fita suka juya gida ita da malam na lado.
Tun da ya shiga officce din Dr Hisham yana zaune ne shuru, ba tare da ya tanka masa ba,haka kawai yaji zuciyar shi na san kara kusanci da zama tare da Dr Hisham ɗin ko dan samun abun da zuciyar shi ke raya mishi wanda ya fara ganin alamun cewa tabbas Dr Hisham bashi da gaskiya akwai wani abu daban akasa, haka nan yake jin zuciyar shi na ingiza shi da shiga cikin lamarin, wanda sam hakan ba halin shi ba ne, wato shiga sabgar da bata shafe shi ko aikin sa ba, Dr Hisham ɗin yana kallon sa shima bai tanka masa ba ,Dan ya riga da yasan hali kawai dai ya ɗan so shiga mamaki ne akan zuwan bazatan da Br BENJA ya yi masa,kamar yasan abin da Dr Hisham ɗin ke tunani dan haka cikin dan gyara kashingidar sa ya buɗe baki a hankali kamar me lalubo abun da zai ce , ya ce" ina dan wani bincike ne akan wani case so inaga dole ya shafi nan ɗin , daga haka ya maida idanun sa ya lumshe su tamkar bashi ya yi maganar ba, ajiyar zuciya Dr Hisham ya sauke tare da jinjina kai wanda yake alamta cewa lallai ya gamsu da maganar Br tunda ya san cewa karya sam bata daga ɗabi un sa, shi kan shi Br sai da yaji wani iri saboda sam bai iya karya ba ,amma sai gashi yau wan Nan rasa kunyar tasa shi ya gillata.
Dada ta yi murna da jin cewa bishira ta haihu, har tana fatan Allah ya kaimu gobe suje suyi Barka ko ita da mama ne,ko Ammi , ita dai Fahrin Allah Allah take yi Dada ta sallame ta ta koma sashen Ummi dan ganin halin da Salma ke ciki ko ta tashi daga baccin oho?Dadan ce ta ce wuce ki bani guri dan naga gaba ɗaya hankalin ki ba anan ya ke ba,ta faɗa tana mai shigewa bedroom din ta,aiko Fahrin bata tsaya wata- wata ba ta fita da sauri kamar zata kifa.
Ahankali take bude dakin kamar mai tsoran wani abu,sai can kuma ta bude gaba ɗaya tare da sa kanta,ga tsananin mamakinta sai ta ga Salman zaune bisa gado ras da ita , babu wani alamun damuwa ko ciwo a tare da ita,da gudu Fahrin ɗin ta ƙarasa ta rungume ta cikin farinciki ta ce" haba tweeny yau kin kusa samun hawan jini"!! Shuru taji salma bata yi magana ba kuma bata maida mata martanin rungumar da ta yi mata ba, hakan ya sa ta ɗago da sauri ta zuba wa Salman idanu tana mai karantar yana yin ta,da ta nutsu sosai sai taga ne lallai fa akwai wani abu a tare da salma na ban mamaki, kama hannun ta tayi tana mai jijjigata salma kiyi magana mana wani abu ne ya faru ? Ce wani abu mana ko baki da lafiya ne? Shuru babu amsa sai idanun kawai da Salman ke bin Fahrin da shi, cikin tsananin kiɗima da gigita ta kuma cewa salma Ummi ta yi maki wani Abune? E nice Nan taji an faɗa daga bayan ta, wanda kuma kai tsaye ta tabbatar da cewa Ummi ce,a hankali ta juya sai tin kofar inda Ummi ke tsaye tana sakin wani munafin murmushi,kallon da taga Fahrin na yi mata na tsantsar tambaya, shi yasa ta ƙarasa shigowa dakin cikin takun ta na kasaita kana ta ɗora da cewa, Fahrin ba kince zaki ja Ni ba? Bakin ce lallai sai kin gayyato wani cikin kaddarorin ki ba?saboda duk baki san wacece Ni ba, kina kuma tunanin bazan iya aikata duk abin da naso ba,shi yasa Ni kuma na fara nuna miki misali akan wannan yar karamar kyikyiyon da kikaje har garken ta ki dauko ta, Allah sarki ashe da raban itama ta ta ƙaddarar tana cakude da taki duk da cewa ta ta ƙaddarar Bata kai ko rabin farcen ta ki ba, domin a ido biyu zaki fuskance ta"kallon ta Fahrin take da dukkanin zuciyar ta , tana kuma sauraren ta da dukkan kunnuwan ta, so take kawai taji wai shin me ummin ta yiwa Salma ne da ta zama gata nan kamar wata butum butumi, kamar tasan tunanin Fahrin din take yi dan haka ta hutashshe da ita ta hanyar warware mata abun da ta ke son ji,kinga wannan ta nuna wa Fahrin ɗin wata kwalba da ke hannun ta,kana ta ɗora da cewa salma ta riga taji abin da bana so kiji shi yanzu, kuma nasan ke ce farkon wadda zata fara gayawa, so na san cewa ko da baki fadawa kowa ba tabbas zaki ce kina da karfin yakata ta hanyar dakatar da Ni abun da na dade ina da burin aikatawa, kuma na shigo gidan saboda shi,dan haka nasa a kayi mata allurar daskarar da gabobi daga nan sai na antaya mata wannan ruwan wanda shi zai juya ƙwaƙwalwa ta ta manta komai san nan nasa aka kuma yi mata allurar sagar da jijiyar da take da mahada da makogwaro wanda ita ce take bata damar yin magana, duba kiga yanzu salma bata da maraba da katako" ta faɗa cikin kwanciyar hankali,kafin ta juya fuskarta kuma zuwa fuskar bosawa ta ce wallahi wallahi wallahi Fahrin nayi rantsuwa duk sanda naji kin budi baki da niyar tona sirrika na to aranar zan kashe salma zan kuma kashe Kulsum daga nan na karasa wan can nakasheshshen uban naku dan haka ki kula duk abin da zaki yi ki dinga tuna wa cewa rayuka uku ne suke karkashin fallasar sirrin NADIYA kuma suke karkashin ƘADDARAR ki" cikin daukewar zuciya Fahrin ta ce" na Amin ce amma ki sani cewa ƘADDARAR tana iya juyewa ta zama wani SANADIN na HASKE dan haka zan karbe ta tun da nasan ba daga gareki take ba, dan haka zan yi kokarin cinyeta ko dan samun wannan HASKEN"! Ummi ta ce" yauwa jaruma haka nake son ki shi yasa har yanzu na kasa juya rayuwar ki up and doun, yanzu abun da ya rage sanarwa yan gida cutar da takama salma dare daya waya sani ma ko Mayu ne ko kuma surkulle ne irin na fulanin jalingo, ta faɗa cike da wata shakiyiyar dariya tana yi tana fita daga dakin.
Yadda ta zubawa Salma idanu tana tsiyayar hawaye ita ma haka Salman ta yi ruwan hawaye ne kawai ke zuba daga kwarmin idanun ta,bata ita motsi bare magana yadda take anan sai dai komai a yi mata, ranar Fahrin ta ci kuka har se da ta bawa uku lada ta ki cin komai kamar yadda tayi tayi da salma ta buɗe bakin ta ta sa mata wani abu ko fura da nono ne amma ta ki har kuma lokacin hawaye basu bar zuba daga idanun ta ba, Fahrin ce ta yi mata komai a ranar har Auduga ita ta canja mata wanda ta ga alamun ma ta gama piriod ɗin nata dan haka ta kudurta a ranta da safe zata yi mata wanka, duk abin da ta ke yi kanta kawai take ɗorawa laifi wanda hakan ne kuma yake ƙara sa ta fashe da wani azababban kuka kamar zata shide.
Yadikko da Dada kai har ma da mama duk kallon ta suke cike da mamakin sauyawar ta , manyan idanun ta sun yi ja sun kuma kankance , har da wata ƴar rama da ta yi tsakanin jiyan da yau, Yadikko ce ta magantu da cewa, ke Auta me yake faruwa da ke ne haka? Kin ganki kuwa ? Zuba mata ido Dada tayi tana son jin amsar ta haka ma Mama, a daidai lokacin Ummi ta shigo ita ma kamar wadda akayi wa mutuwa ko mara lafiya, ahankali suka maida idanun su kan ummi Yadikko tana mai juya tambayar kanta,cikin wani irin pretendin ummin ta fashe da kukan da ya matuƙar girgiza Fahrin tare da kara sakan kanncewa cikin mugun halin ummin, cikin kukan Ummin ta fara da cewa Allah na tuba astagfirullah wan Nan wace irin masifa ce muka tashi da ita a cikin wannan safiya ta Laraba? Tuni Yadikko ta zaburo cikin faɗa ta ce" yo ai wannan kwane kwanen naku mu shi zai kashe mu tun da kunki fadar abin da ke faruwa" ta faɗa cike da tashin hankali, kai tsaye Ummu ta ce " wallahi Salma ce yau muka wayi gari bata magana bata koda motsi wato dai kwatankwacin halin da Abban su ya ke ciki, banban cin kawai shine salma najin duk abin da za a faɗa kuma idanun ta na ganin kowa,ban san meye ya faru ba, ban san daga ina matsalar take ba,ta faɗa tana rushe wa da wani irin kuka mai ban tausayi.