ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 12

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA* 

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page12 ```



 *Free* *pg*




"Ni dai ina ga kamar aljanu ne suka shafe ta ko asiri shi yasa ma tun kafin na ƙaraso nan har nayi Wa malam magana yazo ya duba ta ko za a dace"ta ida fadar maganar tana kallon fuskokin su dan ganin yadda zasu karbi maganar,kana ganin su kasan cewa sun yi matukar girgiza da jin wannan al amarin rana tsaka, Yadikko ce ta iya tankawa da cewa innalillahi'wa'inna alaihi raji un allahumma ajirni fil musibati waka lifni khairan minha Allah ka ije mana ka shiga lamarin mu kayi mana maganin duk wata masifa da ke shirin tunkaro mu ka kuma yayewa wannan yarinya abin da ya ke damunta ka kasaukaka lamarinta tare da dana da kuma daukacin musulmi"Amin mama da Ammi, suka amsa wan da gaba ɗaya jikin su yake a sanyaye da wannan abun mamaki , Yadikko ce dai ta kuma cewa gaskiya ne abin da kika yi ya yi dai dai malam ɗin ya zo kafin iyayen nasu su dawo asanar dasu halin da ake ciki ? Ta faɗa da alamar tambaya ga Dada, jinjina kai Dada ta yi daga nan suka dunguma dan zuwa duba jikin Salma, ahankali take bin su kamar kazar da kwai ya fashewa, jin zuciyar ta take kamar ba Tata ba, ji take kamar an dora mata wani gungumem dutse saman ƙirjin ta, tasbihi kawai take yi tare da hailala shi yasa har ta samu karfin takawa zuwa sashen ummin.



Cikin jimami Yadikko take cewa tabbas maganar ki akan gaskiya take Nadiya, wan Nan abun sharrin jinnu ne kawai,ita dai Salma bin su kawai take da idanu dan yanzu hawaye sun kafe daga idanun ta kukan na zuci ne wanda yafi daci da ciwo, haka Fahrin bata da bakin magana sai abun da Ummi ta zartar ta faɗa wanda kuma take take cin nasara kamar wadda ke matsa laya duk abin da ta faɗa ya zauna daram,haka nan suka gama jimamin su suka fita daga dakin kafin malam yazo ya duba Salman,wani duba Ummi ta yiwa Fahrin cikin alfahari da kanta ta ce" to auta ta ya ki ga wan Nan salon nasan kema dai ya kayatar dake ainun" saura taku na gaba wan da shine zai fi girgiza zukatan masoyan ki" ta faɗa tana goge wa Fahrin hawayen da suka balle cikin idanun ta, taci gaba da cewa kiyi haƙuri fa ja da NADIYA sai an shirya"daga haka itama ta bar dakin zuciyar ta fes ji take kamar ta samu dukkanin wata nasara da take fatan samu a rayuwar ta.


Zubewa Fahrin ta yi gefan Salma tare da dafe tsakiyar ƙirjinta wanda take jin sa kamar zai ɓullo ya fito, da karfi ta runtse idanunta wan da take ji har wani yaji suke mata,a hankali ta buɗe su akan salma da ita ma Fahrin ɗin take kallo cike da wani irin yanayi mara dadi, zubawa juna ido suka yi, sai da ga can Fahrin ɗin ta buɗe baki da kyar ta ce" Salma ki yafe min dan Allah na roke ki ki gafarta min, domin duk nice wadda na jawo miki wan Nan ɗin kuma a SANADIN ƘADDARA ta ke ma ta ki ƙaddarar ta juye zuwa mummuna" girgiza mata kai Salma ka wai ke yi, tunda babu bakin magana sai kallo da ido.



Ko da su Dadyn sama suka dawo su ka riski wan Nan al amari ba ƙaramin da kaduwa su kayi ba, duk kan su kuma take suka zauna akan maganar Ummi na cewa jinnu ne suka shafi Salma, Amma dai Abban kasa ya kawo shawarar a hada da na asibi tun da suna da Dr Hisham, Yadikko kuma ta gargade su da su da yaran su akan kar a sake a sanar da mutanen jalingo, sai idan ankwana biyu ba asamu wani cigaba ba,


Gaba ɗaya ragamar Salma da hidimar ta ta dawo wajen Fahrin, hakan ne yasa Dadyn sama ya tausaya mata ya ce asamo mai aiki yar dattijuwa wadda zata dinga kula da wasu al amuran na Salma , Fahrin Bata musa hakan ba tunda itama tana san samun sukunin samowa rayuwar su mafita,


Sai daga baya ne Yadikko ta yi Umar Ni da a sanar da goggo salma amma kar wan da ya sani acan jalingon bayan ga iyayen salma,takanas Abbu ya sa aka dauko goggon salma da mahaifin ta suka zo suka duba ta, duk da cewa sun damuwa har kuka sukayi amma hakan bai sa sun juyawa ƙaddarar su baya ba, kuma basu nemi da salma ta koma jalingo ba, acewar su nan ma iyayen ta ne masu iko da ita goggon su Halima ba karamar jarumar uwa ba ce kwatan kwacin halin Dada , yan uwan ta sun basu karfin gwiwar cewa insha Allahu da izinin Allah za su nemawa salma lafiya su sa ran su tamkar salma n gaban su ne ,kuma da kafafun ta zata zo har jalingo kamar yadda su ka zo Legas, da wannan kwarin gwiwar da 'yan uwan ta su ka basu suka rungumi ƙaddara kwanan su biyu suka koma jalingo,



Br BENJA.



Ya daɗe yana jiran wannan dama, sai yanzu ya samu a kuma lokacin da ya riga ya fidda rai ya ke kuma jin ba zai iya matsawa daga kasar sa ba saboda wasu manyan dalilan da shi kadai ya san su, cost zai taifi torkey na tsawon shekara daya, tun da takardar ta iso gare shi yake jin zuciyar shi babu daɗi,, yana da manyan uzurorin da suka saka yaji tafiyar ta fita a ran shi ,yana ji kamar zai tafi ya bar baya da kura ne, cikin tsananin farin ciki James ya dafa kafaɗar sa ya na cewa amma man gaskiya kai mai sa a ne a rayuwa , duk abin da kake nema kana samu kuma abun da yake da wuyar samu , gaskiya kayi sa a sosai,"

Mr Mathew cikin alfahari da ɗan nasa ya ce" tabbas zan can ka haka yake kaga sai ya baka muƙamin sa kayi rikon kwarya kafin ya dawo ko,da sauri James ya amsa da cewa haba Dady me zai hana zan riƙe masa amana har yaje ya dawo"mom Rabecca da sai yanzu ta tsoma baki a maganar ta ce" son ya naga kamar baka murna baka farinciki da samun cigaban da kayi,? Benja bai iya share mahaifiyar tashi ba, saboda ya ji dadin yadda ta fahimci damuwar shi alokacin da da ba kowa ne zai fahimci hakan ba,( kai uwa wasa ce ita ka dai ta ke fahimtar damuwar ya'yan ta ko akasin haka duk wani motsi na ya'yan ta takan gano shi alokacin da ba kowa ne yake ganowa ba Allah ka sakawa da iyayen mu Alkhairi da aljanna madauwamiya Amin) a hankali cikin wata irin murya mai cike da kasala ya ce"mom bana jin zan iya tafiyar nan cos a kwai aiki mai muhimmanci da na daukarwa kaina" kai kam wan Nan ɗa ba kayi dacen zuciya ba , cewar Mama ke nan da suke shigowa ita da su nalah,zama tayi ba tare da ta lura da gaisuwar da surukinta kuma dan ta ke mata ba , ta cigaba da fadan ta kai Benja ka rabu da wannan bakar zuciyar taka dan bana jin ki a gaba zata shuka maka Alkhairi, haka kawai ka dauki dabo ar da basu dace da kai ba ka ɗorawa kan ka,to kankiyayeni wallahi idan su iyayen naka kafi karfin su to Ni baka fi karfina ba" Shuru falon ya ratsa kafin Mr Mathew yaja wata doguwar ajiyar zuciya kana ya ce"BENJA ko wane irin aiki ka ɗaukar wa kanka kuma ko wane irin muhimmanci ke da shi bazan taba bari ka rasa wan Nan damar ba,dan haka ka fara shirin tafiyar ka tun da ga yau din nan, idan kuma kasake a kasamu kuskure a cikin wan Nan tafiyar taka to tabbas zakayi matukar mamakin abun da zai biyo bayan hakan ! Daga haka ya tashi a fusace yana dogara sandar sa ya haura sama, yana saka muhimman ABUBUWAN da zai aikata in har benja ya ki bin umarnin sa a wannan karon, mama tayi tsaki kafin ta ce da dai kuna kamanta yi masa faɗa da nuna ikon ku akan sa da bai zama haka ba".



Shima ta shi ya yi yana kokarin barin falon,dan sam baya fahimtar komai a maganganun kakarta shi , dan dama so da yawa idan sun hadu da faɗa suke rabuwa dan kanwar su bata jukuwa, maganar mom din sa ce ta ɗan dakatar da shi inda ta ke cewa kayi haƙuri son kayi abin da yafi dacewa ko dan mahaifin ka ga kuma ɗan uwan ka da yake son cigaban ka, i begging u na roke ka"! Ta faɗa cikin tausasawa da tausayawa irin ta ɗan da ake matuƙar so,jin jina mata kai ya yi kawai yana mai kar bar zan cen nata da hannu biyu, ya shige ɓangare sa yana mai niyar kyautata mata a matsayin na wadda take saurin fahimtar damuwar sa , da wani irin kallo James ya bishi yana dan sakin murmushi ƙasa ƙasa wanda take na saka masa ayar tambaya?.




Face mack ne a fuskar shi haka kuma jikin shi lullbe yake da irin ƙatuwar rigar nan baka ta fata, shi yasa ba zan iya tantan ce ko waye ba , haka kuma yanayin yadda yake magana bai bani damar gano murya ba, zaune yake a wani ƙaramin falo wan da ba a cika masa shirgi ba , babu ko mai a falon face kujera da senter table, sai wasu tarin takaddu da hotuna a kai, kan sa a kasa yake magana cikin Yaren Hausa babu karka tar harshe ko daya,ya ce" ina so ku zamana cikin shiri saboda lokacin daukar fansa ya kusa, ina da tabbacin ko mai zai tafi daidai, hannu yasa ya dauko hoto guda daya daga cikin tarin hotunan da suke zube kan table ɗin , ya zuba masa idanu wanda har sai da idanun nasa ya sauya kala ya nuna alamar ɓacin rai da kuma wutar ɗaukar fansar dake ruruwa cikin zuciyar sa, da ɗan karfi ya yi magana wallahi bazan taba bari ba sai na dauki fansa wannan shine babban burina aduniya, ko da zan rasa raina ko da shine abu na karshe da zan aikata a duniya amma tabbas ba zan kyale wan Nan ba , sai na rama zalunci da ukubar da akayi wa rayuwata" ya faɗa yana mai runtse idanun shi, abun da ya farun na dawo masa yana gani tamkar alokacin yake faruwa, a hankali yaran nashi duk suka dinga ficewa suna bashi guri tun da sun riga sun san cewa duk lokacin da abun ya tashi baya bukatar kowa daga gefan shi.




Duk wani shiri ya gama yin sa, kuma a gobe ne jirgin su zai tashi, sai dai abu guda da ya tsayawa zuciyar shi wan da yake neman sa shi bijerewa tafiyar, da dukkanin zuciyar shi yake ji da akwai matsala ta bangaren can, ya rasa me nasabar shi da rayuwar ta da ta takura tashi rayuwar har yake ji zai iya rusa wani babban tsani na samun cigaban shi duk a sanadin ta, ba zai iya tafiya ba dole sai ya tabbatar da komai lafiya,wan nan shine tunanin BENJA.



Tun da Fahrin ta tashi yau take jin ta wani iri, bugun zuciyar ta na karuwa kasala na bin dukkan jikin ta, duk lokacin da ta rufe idanun ta shi take hangowa cikin kamilallan yanayin shi da ƙawatacciyar shigar shi, duk da cewa muskili ne amma tayi yaƙini cewa yana da sanyin hali da uwa uba tausayi, a ɗan haɗuwar da suke yi ta fahimci wasu kebantattu kuma nagartun halaye da ga gare shi, wan da har take fata ace ya zamo daya daga cikin jagora a addinin Musulunci, tashi tayi cike da kasalar da ta ke da ɗa mamaye ta a duk lokacin da tunanin sa ya hana ta sakat,.


Duk da yanayin da take jin kanta hakan bai hanata shirya wa ba, tsaf ta kammala shirin ta cikin doguwar rigar atamfa blue me duhu wan da akayi mata ratsi da ruwan goro, ta dauki ma dai daicin mayafi shima ruwan goro da yar karamar pos ta hannu sai flat din takalmi , Masha Allah abun da Yadikko ta faɗa ke nan lokacin da Fahrin ta keto cikin falo da wani sassanyan kanshi wan da ya gauraya da ƙamshin turaren wutan da falon yadikko ya ke yi, gaskiyar Yadikko irin kyan da Fahrin ta yi sai dai kawai muce Masha Allah, Dan kam tsayawa faɗa ma bata baki ne ga doguwar rigar ta fita ta zauna daram a ƙayatacciyar surar ta ta cikakkar budurwa me tashe,Fahrin ɗin ce ta ce" Yadikko zan je na karbowa Salma maganin ta"ta faɗa tana mai jin dacin da yadda Ummi take ta sawa ana bankawa Salma wasu rubututtuka wan da ita sam ma bata yarda da su ba, Yadikko ta ce"maza tashi kije kar magriba ta yi"jinjina kai tayi tare da miƙewa ta bar falon,ya yin da Yadikko kuma ta bita da kallo na tsantsar tausayi, duk wanda yasan Fahrin a baya dole zai san cewa ba ƙaramin sauyawa ta yi ba, yarinya me kazarkazar da neman rigima mara damuwa da saka ta a ranta , amma yanzu duba ɗaya zaka yi mata ka gano yanayin ta na damuwa, wan da Sam a baya bata bari a a gano damuwar ta,to amma kuma ya za ai da ƙaddarar rayuwa me sauya mutum a kowane lokaci, hannu Yadikko ta sa ta goge guntayen hawayen tausayin Fahrin da salma tana mai addu ar Allah ya dawo musu da walwala da farincikin da suka rasa.




A hanyar ta ta dawo wa daga karbo maganin sai ta keto ta cikin unguwar su Benja, wan da hakikanin gaskiya bata san cikakken dalilin ta na yin hakan ba, tasan dai kawai tana son ganin shi ko da daga nesa ne ji take kamar shi kadai ne wan da zata iya gayawa damuwarta ,sai dai kuma har ta karaci muku nukun ta bata ga ko mai kama da shi ba,tana tafe tana waige har ta danyi nisa da gidan da har zata wuce gidan Aunty Batul Amma da tayi tunanin Salma sai ta fasa , juyawa ta kama yi wanda shima bata yi nasarar ganin ko mai gadin gidan ba, juyowar da zatayi taga mutum tsaye a gaban ta, razana ta yi sosai wan da har sai da hakan ya nuna kan kyakkyawar fuskar ta,kallon ta yake tamkar zai mai da ta ciki, yana kuma jin kan shi amatsayin mai sa a a duniya , domin ya tabbatar da cewa shi kadai ne namijin da zai yi nasarar ɗauke wannan kyakykyawar furanyar, tun da ya fara son ta bai taba jin karaya ta cewa zai rasata ba , dan ya riga ya san shi mai nasara ne a cikin dukkanin rayuwar sa , dan haka samun Fahrin tamkar siyan agogo ne a gurin sa, 



Matsawa ta yi cike da nuna alamun tsoro, dan ita sam bata gane shi ba, yo Fahrin ya za ai ki gane shi bayan yazo miki cikin shiga ta kamala yau kuma kin gan shi a cikakken chekass ɗin mai matukar ji da izza ga kuma iko na jin cewa shi mai nasara ne ba mai faduwa ba, daga ina kike ? Ya tambaye ta kai tsaye, sai abun ya bawa Fahrin dariya duk da cewa tana ɗan cikin yanayi na tsoro, to amma maganar sa da taji yanzun yasa ta tuna ko waye, cikin dakiya ta ce" daga in da ka aike Ni"zubawa dan karamin bakin ta idanu ya yi yana saka da warwara akan yadda zai cinye su duk ranar da ta shigo hannun sa, goce shi ta yi zata wuce amma sai ji ta yi ya cafko hannun ta tare murde shi , har sai da tayi kara kana ya ce " ina so ki shaida waye chekass kuma ki san irin maganar da zaki ɗin ga yi da shi , duk da cewa ina sonki to amma hakan ba shi zai hana duk lokacin da kika kauce daga kan layi na naci miki ba, dan haka ki sawa ranka daga yau duk in da kike chekass yana nan babu wani wan da ya isa kutsowa cikin rayuwar ki da sunan so in dai ina numfashi, zan iya kashe ko waye a kan ki , ki sawa ranki kina da miji abokin rayuwa , a gida ne kawai kike da ikon kanki amma duk kika fito waje kin zama ikona akan kuma umarni na kike," yana gama fadin haka ya sake ta tare da juyawa ya kalli Mande ya ce" maza Mande jeka kaimin lu' u, lu'u na har gida!" To Oga an gama cewar Mande ke nan, innalillahi'wa'inna alaihi raji un, kawai Fahrin ke maimaita wa an ya kuwa ita ce? Me ke shirin kara kunnowa cikin rayuwar ta? Me wan Nan mutumin yake nufi? Tunanin ta ne ya katse lokacin da taji ƙatuwar Muryar Mande a kan ta yana bata Umarnin shiga mota,ba ta san ya akai ba ko tsoro ne da tunani ya yiwa zuciyar ta banka banka , samun kanta ka wai ta yi da shiga motar zuciyarta na wani irin bugu kamar ana kwada guduma,


Har kofar gida ya ajiye ta , ta bude gidan ta shiga jiki a san yaye kamar wadda aka yiwa duka,abu goma da ashirin ita sam yanzu ba damuwar wan Nan chekass ɗin ba ce a ranta, damuwar rashin Br BENJA ne yake neman zautata, ga kuma da muwar Ummi da kullum abun nata ƙara gaba yake yi .


Kacibus tayi da Abbu yana tsaye yana kallon ta tun da aka sauke , wani irin bugu ƙirjinta ya yi wan da har sai da ta dora hannayen ta saman ƙirjin ta tare da zaro manyan idanun ta wan da suke cike da tsoro, duban ta Abbun yake cike da tuhuma kafin ya magantu da cewa daga ina kike kuma suwaye suka ajiye ki?kasa bashi amsa tayi saboda bata san me zata ce masa ba , ganin hakan yasa shi cewa shi ke nan wuce amma ki tabbatar da cewa idan nayi bincike akan sabbin ɗabi un ki na gano akwai kuskure acikin su to tabbas zaki gamu da fushina" gingina masa akai tayi kafin tayi saurin shigewa kamar zata kifa.


Ummi da ke hango su ta sama ta ce" wannan ma yana daga cikin nasara ta duk da cewa ba shirina bane.



Duk yadda yaso yakice damuwar rashin ganin ta abun faskara ya yi , har lokacin da jirgin su zai tashi bai samu wata dama ta ganin nata ba, tun da James ya fuskanci damuwar Benja shi ke nan hankalin sa ya tashi, yasan kaɗan daga cikin aikin sa ne ya fasa tafiyar a cikin wannan lokaci , dan haka ya yi saurin dannawa mom Rabecca waya Dan yasan ita kadai zata iya tausar zuciyar Benja daga boren da take son yi , yana can ya yi zurfi cikin tunanin mafita yaji wayar shi na fitar da dan wani sauti mai daɗin saurare, shuru ya yi ba tare da ya dauko wayar ba, James da ya fuskan ci ba zai dauki wayar ba, shi sai ya yi saurin daga masa tare da sa wayar a amsa kuwa.


A hankali ya bude gajiyayyun idanunsa wan da suke a lumshe , ya zuba su saman fuskar James bayan Muryar mom din shi ta ratsa jijiyoyin kunnen sa, kawar da kai James ya yi yana kunshe dariyar dake neman kwace masa, bai katse mom din ba har ta gama lallamin ta , cikin muskilar Muryar shi ya ce is ok mon don't worry , daga haka ya mike kai tsaye ya nufi hanyar jirgin saboda kiran da aka farayiwa fasinja, zuciyar shi kwata-kwata babu so ko sha awar tafiyar, ko bankwana ba su yi da James ɗin ba , to dama ya lafiyar Giwa .



To mu dai sai muce matafiya a dawo lafiya .



Wai Fahrin na tambaye ki mana, cewar mama da ta rutsa Fahrin ɗin a bayan ɓangaren ta cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa, jinjina kai Fahrin ɗin ta yi tana mai kallon maman da idanun ta da suka koma ja saboda damuwa , dafa kan ta maman ta yi kana ta ce"auta shin wan Nan ƙaddarar da ta same mu daga wa take ? Kai tsaye ta ce" daga Allah ne"meye kuma cikar imanin musulmi? Nan ma ta ce " yadda da ƙaddara me kyau ko akasin ta" yauwa to amma duk kin san da haka me yasa ba za ki zamo daga cikin muminan bayi masu yadda da ƙaddara ba? Auta ke yarinya ce mai ilimi wan da sam mu iyayen ki Bama shakku akan cewa lallai zaki zama musulma mai amfani da ilimin ta na addini, gashi kuma na ga kamar hakan ba zai yiwu ba gashi tun yanzu kina neman zub da dabi ar da muka sanki da ita na yakice damuwar dake cikin ranki ko wace iri ce kuwa"dan Allah Fahrin ki samu nutsuwa Salma fa ba wai zata yi ta zama a haka bane cuta ce ke shiga farad daya amma sauki sai a hankali, kiyi haƙuri ki daina wan Nan damuwar kinji autar Abbu" murmushi Fahrin ta yi me ciwo kana ta ce " shike nan mama na daina bazan kara ba " yauwa ko ke fa muma kin ga duk kin samu a damuwa yan uwan ki da iyayen ki kowa walwalar ki yake so, Ga Addar ki Kulsum tana gidan ta amma gaba ɗaya ta kasa kwantar da hankalin ta duk saboda damuwar ki, ai ko dan mu da yan uwanki kya rage yawan damuwar nan" hannun ta ta kama suka bar wajen tana mai kara kwantar mata da hankali.



Ummi dake bayan su jikin fulawowi ta fito tana murmushi, kana ta ce" Allah sarki , baku san damuwar Fahrin yanzu ta tafi ƙarfin ta ɓoye ta ba,dabara ta gama kwace mata ƙwaƙwalwar ta tayi kan kanta da daukar manyan damuwowi kamar wa dan nan, ku ma dan baku san komai ba ne dukkan ku kuna cikin duhu, rayuwar Fahrin a yanzu tana kewaye ne da tarin makiya masu san cimma burika " ta faɗa tana mai juyawa da barin gurin .



Tun daga ranar Fahrin ta fara kokarin kawar da damuwar da ta fara fallasa kan ta a gaban mutane, tana yawan zama da Yadikko ko dan samun nutsuwar tsohuwar , duk da cewa idan ta kebe damuwar ta ta takan sabun ta kanta ne, kullum duniya mafita take kokarin samowa kanta , har kullum bata daina yunkurin sanarwa da iyayen ta ba, sai dai kuma da ta yi yunkurin hakan sai gargadin ummi ya dawo mata, tabbas ta yadda Ummi zata iya kisa kai in da abun da yafi kisa ma zata iya aikatawa, shine abin da yake saka mata matsanancin tsoro da fargaba tare da dakatar da ita daga abin da take shirin aikatawa,


A cikin haka ne a ka kawo sadakin Kareema sati biyu kawai aka saka, iyayen su kuma da Yadikko sun ce daurin aure kawai za ayi sai walima daga nan a mika amarya gidan ta, wan can ma takura musu aka yi , to balle kuma da abun ya kasan ce har da su sata , shi yasa abun ya kuma fice musu a rai , kai da kowa da kowa ma dake gidan,



Hidimar bikin ne yasa Fahrin ta ɗan saki jikin ta , duk da cewa ba wani rajin bikin take ji kamar na su Adda zulfa ba,kuma gashi tana kusa da dukan yan uwan ta mata ,haka a kayi biki aka gama, amaryar Dadyn sama ne da kan sa ya kaita gidan ta, dama yan jalingo basu zo ba, kasan cewar Abbu ya ce su yi zaman su tun da ba a dade da yin nasu Adda Kulsum ba, zirga zirga-zirga zata yi musu yawa guri ba tafiya kadan ba gashi basa son su zo sigar halin da Salma ke ciki.


Sai gidan ya kuma yin shuru , tun da mazan dama ba mazauna bane, dan yaya Muhd ba a nan Legas yake aiki ba, shi kuma yaya Muhsin ya tafi Jos bautar kasa,.


Hakan sai ya kuma takura Fahrin zaman gidan sam ba yayi mata daɗi , tun da salma ba magana take ba, sai kawai ta shiga bin gidan yan uwan ta tana kai musu ziyara, hakan ma sai ya zama matsala a gareta , duk inda ta yi chekass da yaran sa suna biye da ita kamar jela, har ya fara saka mata mugun tsoran sa,, da fargabar fita.