ƘADDARATA SANADIN HASKE

Chapter 13

by @zahra48

💕

   **ƘADDARATA* 

 *SANADIN* *HASKE* 💕


        *NA* 



*FATIMA Y. ADAM*






_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***


*_____________________________________*




     ```Page13 ```



 *Free* *pg*


WANNAN SHINE KARSHEN FREE PG IDAN KINA BUKATAR CIGABAN KADDARA TA SANADIN HASKE ZAKI IYA SIYAN SA AKAN NAIRA 300 KO KI AHIGA VIP AKAN NAIRAR KI 500 ZAKI TURO A WANNAN ASUSUN 0138541704 FATIMAH YUSHA'U ADAM UNION BANK KO KATIN MTN AKAN WANNAN NOMBER ***



Last free fg



Hakan ne ya sa gaba ɗaya bata jin sha awar fita ko kofar gida, takura take fama da ita ta ko ina ,ga kuma Abbu da ta kula ya saka mata ido a kwanakin nan, dan haka sai ta shiga taka tsantsan akan sa da kuma haɗuwar su, 



A hankali ta tura kofar dakin Abban tsakiya , yana nan kwance kamar kullum, idanun sa abude suke kamar ko da yaushe sai dai baya ga kiftasu da yake babu abin da yake ƙara motsi ajikin sa,zama tayi a gefan sa daidai kansa ta ɗora hannun ta saman goshinsa , kana hankali ta fara magana, Abba ko sau ɗaya kayi magana ka faɗa min wani abu da zai bani haske akan abin da yasa Ummi take duk wannan abun, na rasa da me zan alaƙanta lamarin amma nasan bazaka kasa sanin wani abu akan hakan ba" tayi shiru tare da zuba masa ido tana mai fatan ace ya budi baki ya ce" Fahrin nadiya tana yin wannan ne duk akan abu kaza, sai kuma ina hakan bata samu ba wasu hawaye ne masu zafi suka sauko saman fuskarta, addu'oi ta shiga tofa masa kamar yadda ta saba yi masa daga nan ta tashi ta fita daga dakin.




Yau bakuntar Adda Kulsum suka samu , hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi wa Fahrin ba, ƙarin abun kuma Ummi bata nan abun sai ya kara armashi suka shige dakin su na bangaren Yadikko suka ƙule su kadai su ka san abin da suka tattauna, amma ga dukkan alamu sun fara samo wata mafita ne daga cikin matsalolin su,har Adda Kulsum ta tafi gida Ummi bata dawo ba, shi yasa Fahrin bata samu wata damuwa ba.



US  


Duk wani abu da yakeyi hankalin shi yana kan Fahrin, ya rasa me yasa kullum damuwar shi nunkuwa take yi akan al amarin ta haka nan yake ji kamar tana tare da matsala, shi yasa yayi matuƙar ƙaguwa ya gama watannin sa ya koma kasar sa, 



Sosai Fahrin ta saka kanta busy taki bari Ummi ta gano ko guda daga cikin abin da take son aikatawa, abun da ta riga ta sani ne dole ne ta kubutar da Salma daga hannun Ummi , shi yasa duk wani tunanin ta yanzu ya tsaya akan yadda za ai ta kubutar da ita ba tare da an samu akasi ba, 



A safiyar wannan rana ne Fahrin ta fito daga ɓangaren su tana ta ɗan dube dube da alama dai tana son aiwatar da wani abun da bata son wani ya ganta, sai da ta tabbatar da babu kowa kana ta zaro karamar wayarta da ta soke ta a kugunta , kira tayi , jim kadan aka ɗaga daga can bangaren, cikin sauri da rawar baki, ta ce"Adda Kulsum na gano komai dan haka yanzu zan yi miki test ɗin bayanan komai ,daga nan kuma sai mu tafi mataki na gaba"daga haka ta yi saurin kashe wayar tare da maida ta kugunta a daidai lokacin ne suka hada idanu da Abbu, kasancewar a bayan ɗakin sa take , shi kuma yana ta ciki daga bakin window dakin sa , ya zubawa Fahrin ɗin idanu cike da tuhuma da alamar rashin yadda ƙarara a cikin idanun sa, alama ya yi mata da tazo ,ganin zata zagayo ta kofa sai ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata nuni da tazo ta nan ba sai ta shigo ba, jiki a sanyaye ta ƙarasa bakin windown, hannu ya mika mata alamar ta bashi wayar , zaro wayar tayi ta bashi ta cikin window da ya zuge , duba wajen kira ya yi, dan ganin ko da wa tayi waya sai baiga nomber ba saboda ta riga ta goge, duban ta yayi cike da rashin yadda kana ya ce" dawa kika yi waya? Adda Kulsum ce Abbu" ta bashi amsa kai tsaye ,jinjina kai ya yi kana ya dauko wayar shi ya shiga kiran Kulsum ɗin, jim kadan ta daga , bai saurari gaisuwar ta ba ya mika mata tambayar sa da cewa dawa kika yi waya yanzu? Kai tsaye ta ce" da Fahrin nayi waya yanzun nan na mayi zaton itace ta kuma kira dana ga kiran ka"shike nan ya faɗa tare da kashe wayar , miƙa mata wayar ta ya yi tare da yi mata nuni da ta tafi kawai, juyawa tayi tana tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa sai take jin kamar Abbun nata bai yadda da ita bane, saboda yana yawan kamata a bigiren da yake nuni da rashin gaskiya,sauri tayi ta kawar da wannan tunanin dan bata son wata damuwa a halin da take yanzu na son ceton yar uwarta.



Fitowar ta daga banɗaki ke nan tana goge ruwan jikin ta yayin da idanun ta suke kan Salma wadda baba nana take shiryawa, yanzu Fahrin duk wani kulawarta yana kan Salma ne saboda tana ganin komai ta dalilin ta ya faru, Baba nana na gama shirya ta ta fice daga ɓangaren gaba ɗaya saboda wan nan umarni ne na Ummi a gareta da zarar ta gama yin aikin ta to tasan in da dare ya yi mata, tana fita Fahrin alokacin ta gama shiryawa cikin doguwar rigar abaya , a hankali ta ƙaraso gaban Salma ta zauna tare da kama dukkanin hannayen ta , cikin tausayawa da damuwar da take shiga duk lokacin da taga anayiwa Salman hidima irin wannan, ta ce" Salma kiyi haƙuri ko mai ya kusa zuwa karshe na roki Allah ya bani damar kubutar dake ko da hakan zai zama silar shiga ta cikin wata mummunan ƙaddarar ko da hakan zai zama silar rayuwata, jotar da take rubutu ta dauka tayi rubutu kana ta nunawa Salman yadda zata iya karantawa, mafi yawan lokuta Fahrin tafi yi wa salma magana ta hanyar rubutu saboda tsaro dan tasan Ummi tana yawan yi musu laɓe ko da kofar su a rufe take , shi yasa take rubutawa ta nunawa salma,fuskar salma ce ta nuna alhini da damuwa , cikin san kwantar da hankalin Salman Fahrin ta ce"karki damu sister Allah zai baki lafiya.



Yadikko ta dubi Ammi kana cikin damuwa ta ce" Ni yanzu gaba ɗaya na daina ganin Fahrin ko yaushe bata da wani lokaci kai Allah dai ya bawa Salma lafiya, Ammi ta amsa da Amin kana ta ɗora da cewa gashi dai ciwo ajikin salma yake amma Fahrin itake jin raɗaɗi da zugin sa wannan kauna tabbas ta girmama kuma muna fatan dorewar ta har abada,Dada dake cikin kiching ɗin Yadikko tana jiyo su , kada kai kawai take yi dan kuwa ita kadai tasan yawan damuwar ta akan diyarta da yar uwar ta,



Fitowar Fahrin daga dakin su shi ya dakatar da Ummi daga wayar da take yi da Dr Hisham, samun kanta tayi da bin Fahrin ɗin da ido , Fahrin ɗin na gab da fita daga falon Ummi tayi saurin dakatar da ita tana mai katse wayar da take yi da Dr Hisham, a lokaci ɗaya kuma tana zubawa Fahrin ɗin ido so take kawai ta gano wani abu a tare da ita, gani take kamar shurunta da abin da yake nufi, har Fahrin ɗin tazo gaban ta bata sani ba sai da ta kuma magana a karo na biyu Ummi gani" kawar da kai ummin ta yi kamar ba abin da ya taba zuciyar ta, zauna abin da tace da Fahrin ɗin ke nan, zama tayi zuciyarta cike da tambayoyi akan yau kuma dame tazo mata ? Muryar ummin ce ta katse ta da cewa Fahrin me kike so ki sani akaina wan da baki sani ba? Zuba mata ido Fahrin ta yi cike da mamakin tambayar da tayi mata, tamke fuskar ta tayi kana ta ce"nasan tambayar da take ta birgima cikin zuciyar ki da kwakwalwar ki, tambaya ta farko akan Abban tsakiya ne tambaya ta biyu kuma me Ummi ke nema ne ko take hari da har yasa take duk wani abu domin samun cikar burin ta? Dage mata gira tayi yaya dai Auta ko ba haka bane? Bata saurari abin da Fahrin zata ce ba ta ɗora da cewa, duk in da kike tunani na na wuce nan Fahrin duk wani shirin da zaki yi a kaina ki sani cewa a banza ne damin reshe ne zai juye da mujiya, Gara ki hakura ba kuma wai dan ina jin tsoran abin da zaki yin bane kawai dai ina jiye miki Bala o in da Zaki fuskanta ne, ɗan sunkuyawa tayi tare da kara yin ƙasa da murya kana ta ce" ko kin san duk akan me nake wannan ɗin ? Ba ta saurare ta ba taci gaba da cewa akan SOYAYYA ne " a wani irin mamakan ce Fahrin ta ke duban Ummin ba tare da ta iya furta ko mai wa Ummi ba, abun ya kada ki ko? cewar Ummi ke nan, kar ki yi mamaki domin soyayya babu abun da bata sawa mutum ya aikata , ku ɗin nan ke da ubanki ko nace wan ubanki kune wadan d kuka shiga tsakanina da farin ciki na , wan ubanki wato mijina shine ya fara shiga tsakanina da farinciki na ya rusa duk wani burina da tanadina akan kauna ta sai kuma akayi rashin sa a Ni ɗin bani da hakuri a kan duk wani abu dana ke so haka kuma bani da hakuri akan duk wan da ya shata layi tsakani na da farinciki na, ke kuma ina kokarin kawar da wan can matsalar kika sako rayuwarki cikin lamarina kina kokarin san gano dalilina da kuma ainahin dalilin cutar Abban tsakiya wan da hakan da kike yi yana daidai da kuma nisan tani da kaunata farincikina kinga ke nan babu yadda za ai kema na kyale ki allurar Abban tsakiya da ban take da ta salma ba irin su ɗaya ba saboda ita salma ko yanzu na gadama zan iya sawa a dawo da ita daidai ta hanyar kawar da waccen allurar da wata allurar, shi kuma maganin sa yana da nisan zango"so auta kinji abin da kike so kiji duk da cewa akwai saura wan da sanin sa da salma tayi shine dalilin fadawar ta halin da take ciki a halin yanzu" komawa tayi ta jingina da kujerar da take zaune akai tana bin Fahrin da kallon me zaki iya yi me kuma kike so kiji yanzu? 



A hankali Fahrin ta durƙusa gaban ummin tana mai haɗe hannayen ta , cikin yanayi na roko ta ce"Ummi idan kin san tun farko kina da wan da kike so me yasa kika auri Abba? Baki ji me nace miki ba auren Abban ku shine yayi min katanga da samun nawa muradin" to me yasa tun a lokacin baki sa ya sake ki ba sai kika gwammaci cutar da rayuwar sa? Cikin wani irin yanayi na sosuwar zuciya Ummi ta ke duban Fahrin kafin ta ce" hanyar da na dauka ita kadai ce zata hada Ni da muradina sakin sa gare ni tamkar kara katangar dake tsakanina da muradina ne" sam Fahrin ta kasa gane in da Ummi da maganganun ta suka dosa cikin jin tsanar ummin ta ce " to wai duk meye yasa hakan ? Waye muradin naki ? Me yasa sakin ya zama katanga a gareki da muradin ki? Fahrin na gaya miki iya abin da zan iya gaya miki kuma shima ba wai dan kiji daɗi bane a'a kawai sai dan radin kaina,har yanzu kuma ina kan bakana ki ci gaba da yakata Ni kuma zan cigaba da kare kaina ta hanyar maida takubban da kika watso min zuwa kanki , abin da kike yi tamkar kina ragen aikine ta hanyar bani damar juya wasan zuwa kanki, tashi ki bani guri ta faɗa cikin tsawa,



Kai tsaye dakin su ta faɗa ta zube a kasa , abun da ya tsaya mata ka dai ya ishe ta bare akai ga tashin hankalin da take ciki , wannan wace irin Fitina ce ta shigo rayuwar su , tabbas Ummi Fitina ce babba a gare su, yanzu dama wai duk akan SO take wannan mugun halin , dama akwai mutane irin Ummi a duniya? Ita dai kam tana ganin wannan abun son zuciya ne kawai amma wane irin so ne zai sa ta jefa rayuwar mutane cikin hadari, dagowa tayi ta dubi Salma wadda a yanzu bacci take wan da kana kallo kasan ba na daɗi bane.



A yanzu ne Fahrin take jin wani karfin zuciya akan yakar Ummi, tsaf ta shirya da aiwatar da kudirin su na son fara ceto Salma kafin Abban tsakiya.



Yau da wani irin ciwon ciki Fahrin ta tashi birgima take yi kai kace ranta ake zarewa , duk tabi ta ruda mutanen gidan kuka take sosai tana zabura kamar mai aljannu, Ummi kanta sai da ta ɗan tsorata da yanayin ciwon Fahrin ɗin,sashen Yadikko aka tarkato ta , daga nan Momma (ayi min afuwa bana sako ta itace matar Abban kasa) ta kira Dady cikin mintuna kadan sai gashi, kai tsaye ya ce"da Ummi ta kira Dr Hisham ta sanar dashi zasu zo yanzu " saboda yadda Fahrin ta daga musu hankali babu wan da ya iya zama a gidan hatta da Dada Yadikko cewa ta yi tazo su tafi sai hankalin ta yafi kwanciya, dama Ummi zuwan ta ya zama kamar dole tun da itace uwar ta,kaf hankalin su ya gushe sun manta da Salma baiwar Allah da ma Abban tsakiya baki daya.



Ko a can asibitin ba sararawa ta yi ba, kiran mutuwa kawai take yi, yayin da hannun ta yake cikin na Ummi kamar wadda bata son rabuwa da ita,



A hankali ta fito daga maboyar ta fuskarta a lullube , baza ka taba iya gane ko wace ce ba, saboda yadda ta kai matuka wajen rufe fuskarta, baba mai gadi yana cikin dan dakin sa a kwance saboda shima da yau din da gudawa ya tashi , shi yasa ko da suka fita daga gidan ya kulle yayi kwanciyar sa , sai idan cikin ya motsa ya tashi ya shiga ɗan banɗakin sa, a hankali tasa mukullin da tazo dashi ta buɗe gate din Ba tare da ta bari tayi wani kwakwaran motsin da zai ankarar da Baba mai gadi ba, cikin sakanni ta shige gidan kai tsaye kuma ta nufi ɓangaren Ummi ta re da shigewa dakin ummin.



Sosai ta haɗa gumi wajen neman alluran, duba wayarta ta kuma yi , tabbas wannan ce durowar da allurar ke ciki to amma ya akai bata ganta ba karfa wankin hula ya kai su dare?



Dr Hisham ne ya fito daga dakin da Fahrin take yana cewa ciwon sune na mata gashi kuma bamu da allurar yanzun nan ta kare wlh" ya faɗa yana duban Dadyn sama, Ummi ce ta matsa tana cewa in dai wannan allurar ce ina da ita bari nayi sauri naje na dauko" karaf sai akunnen Fahrin cikin sauri tayi kamar zatayi amai ta Wada banɗaki , cikin wani irin rawar jiki da gaggawa ta dauko wayarta ta shiga turawa Adda Kulsum text.



Tana cikin haƙilon neman alluran taji alamun shigowar sako da sauri ta buɗe , Adda Kulsum kiyi sauri ga nan Ummi ta taho gidan kuma kin san ba tazara ne damu ba yanzu zaki ganta dan Allah Adda Kulsum kar ki bari Ummi ta ganki" cikin tashin hankali ta mayar mata da cewa Fahrin na rasa su basa in da kika ce suna nan , duk na duba ko ina wallahi muna cikin matsala" Fahrin da sauri ta fito daga banɗakin bayan ta karanta sakon Adda Kulsum , wani irin zufa ce ke sauko mata sai taji ciwon tashin hankali na gaske ya kamata da zaka saurari zuciyar ta kuwa tabbas sai kaji irin bugun da take yi tamkar zata faso ƙirjin ta ta fito.



Ummi sai da ta kwankwasa ƙaramar kofar kana Baba mai gadi ya fito, yana shirin bude mata gate ta dakatarda shi da cewa a'a barshi kawai yanzu zan fito " to maida babbar kofar ya yi ya rufe yana yi mata ya mai jiki,shigewa tayi tana amsawa, 



Ƙarar bude kofa da Adda Kulsum taji shi ne ya kusa sa nunfashi ta zarce wa, zaro manyan idanun ta irin na Fahrin ta yi zuciyar ta na wani irin gudu suna tsere da numfashin ta,



A can asibitin kuwa yanzun kusan cutar Fahrin ta koma ta gaske, Dr Hisham kan shi sai da ya tsorata da yanayin yadda zuciyarta take bugawa, kai tsaye ya shiga bata taimakon gaggawa amma ina kamar turata suke saboda da tayi kamar zata dawo daidai sai ta tuna Ummi nacan a halin yanzu ta rutsa Adda Kulsum a dakin ta, tuna hakan da take yi ne fargaba take sawa zuciyarta ta kara saurin gudun ta yayin da numfashin ta kuwa ya ke wani irin sarkewa kamar wadda take neman shiɗewa,



Yadda hankalin ahlin nan ya kuma tashi abun ba mai misaltuwa ba ne, kafin kace meye dukkan yan uwan nan kaf har waɗan da basa kusa sun hallara a cikin asibitin , majinyata da kansu bayan likitoci yau sai da suka san cewa an kawo yargata cikin wannan asibitin , saboda duk wanda ka duba idan baka ga hawaye a idanun sa ba to tabbas zaka gano tashin hankalin da yafi kuka ciwo, su kan su iyayen nasu maza dauriya suke yi, Yadikko kuwa har ta gaji da kuka da kororota ta koma salati da hailala.



Allah sarki Dada Fahrin tana kwance ne kawai amma abin da take ji a ranta da zuciyar ta zai iya zama kwatankwacin na Fahrin, Dada jarumar uwa ce wadda ta zama abar alfahari ga dukkan iyalan ta , Allah ya yi mata juriya da dakiya akan duk wani abu da ya kasance na tashin hankali, tun da ta zauna a waje daya ko kwakwaran motsi bata cikayi ba, carbi ne kawai a hannun ta take ta dannawa , Muhsin ne da shima bai dade da sauka ba dan dama yana hanyar zuwa Adda Fatima ta sanar dashi abun da ke faruwa, zama ya yi agefan ta cike da tausayin ta , dan duk da Dada tana ɓoye san ƴaƴanta amma soyayyar Fahrin bayyananniya ce a gurin ta duk da itama tana ƙoƙarin ɓoye hakan saboda kawaici amma hakan bai hana mutum ya gane ba, Dada dan Allah kiyi haƙuri maryaman ki zata samu lafiya da izinin Allah"kallon shi kawai tayi ba tare da ta iya furta komai ba ta ɗauke kanta tana ci gaba da lazimin ta,



Adda Nauwara ce ta ce" anya kuwa Kulsum ta san halin da ake ciki? Momma ta ce" gaskiya bana tunanin hakan dan da ta sani ita zaki fara gani a cikin asibitin nan" Adda Nauwara ta daga wayarta dake hannunta ta shiga kiran wayar Adda Kulsum.



Tun da Ummi ta shiga dakin take bin sa da kallo sai take ganin kamar ba haka ta fita tabar dakin ba, kawar da wannan tunanin tayi tare da nufar durowar da take ajiye magungunan ta masu muhimmanci da allurai kai tsaye tasa mukullin ta buɗe , gurin laluban allurar duk sai da ta wargatsa kayan cikin durowar kana ta ganta , tana dauka tayi hayar waje dan fita daga dakin,ƙarar ringin ɗin wayar da taji shi yasa ta tsayawa cak.



Domin jin yadda zata kaya ku biyoni acigaban ƙaddara sanadin haske ta hanyar siya akan farashin da na zana tare da hanyoyin biya a saman fg


Fatima y Adam ce✍🏽