Kashi na biyu 2
by @shuraih99
BUDURWAN SIRRI
Gajeran labari
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 2
.
Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin na batare da iznin wannan shafi ba
.
Ba komai nagani ba face namun daji danginsu su Alfadari, Giwa, barewa,Zaki,maciji,damisa,kura kai duk dai wani dabba da kuka san yana rayuwa acikin daji, cikin gungunsu suka nufo ni ai koda ganin haka sai na juya da nufin na fada cikin wannan kogi dayake gabana
.
Amma me zan gani wasu kyawawan kananan kifaye na gani masu zakwa zakwan hakora lokaci lokaci zakaga suna kikkirta hakwaransu, abun yabani mamaki wai ace kifaye da hakwara amma sai na tuna wani american film din dana kalla mai suna PIRANHA
.
Koda naga haka sai nayi wani gefe da gudu don na tsere ma wayannan dabbobi da suka biyo ni da mugun nufi, gudu nake iya karfina don na ceci rayuwata daga hannanun wayannan dabbobin sai dana kai wajen mintin arba'in ina tsala gudu acikin wannan jeji amma wayannan dabbobin sai bina suke duk inda na shige, abunda zai baka mamaki da wayannan dabbobin shine
.
Su ba gudu suke ba don kuwa tafiya suke amma yadda kasan suna gudu domin kuwa duk lokacin dana waigo yayinda nake tsala gudu sai na hango su a kusa dani,
Acikin wannan gudun danake yine, nazo gaban wani katon kogon dutse, batare da wani nazari ko shawaraba na afka cikin wannan kogon,
.
Ai koda shigata cikin kogon sai wani narkeken dutse ya mirgino da kanshi ya kulle bakin kogon ta yadda ko digon haske baya iya shigowa cikin wannan kogo,
.
Take duhu mai tsanani ya mamaye wannan kogon don kuwa ko tafin hannuna bana iya gani nan nacigaba da karanto addu'o'I kala kala duk wacce tazo bakina karantawa nake, har saida na karance gabadayan addu'o'in dana iya haka na runga jawo ayoyin kur'ani maigirma har zuwa wani dan lokaci
.
Koda naga an dauki dan lokaci banga komai ya faru ba sai na dan fara tafiya amma bakina babu abun daya ke furtawa face karatun kur'ani,
.
Tafiya nake ban san inda nake nufa ba, nidai nasan ina tafiya domin kuwa duhun daya mamaye wannan kogo baya bari naga maine ne agabana, na tsinci kaina tamkar wani makaho
.
Ni dai babu abunda nake furtawa face karatun kur'ani mai girma, koda na cigaba da tafiya acikin wannan kogon ina cin karo da duwatsu akalla na fadi yafi sau goma
.
Don kawai sai ina kan tafiya sai naji nayi karo da dutsi take zakaga na fadi gefe, a haka sai da hannuna na dama ya samu targade,
Kukan zuci nake sosai ina tunanin lokacin da akeyimana wa'azi a islamiya zaka ji ana cemana muyi aiki mai kyau don kuwa akwai lokacin da mutuwa zata riskemu,
.
Sam sam bana son na mutu yanzu amma kuma gani nake tamkar tsakanina da mutuwata banfi zira'I daya ba zuciyata tana ta karantomin abubuwa da yawa na cutarwa da ka iya wanzuwa a cikin wannan kogon
.
ni ma'abocin karanta littatafan yakine nasha jin labarin yadda kogo take, kuma a yadda naga dutsin nan ya mirgino da kanshi yazo ya rufe kofar fita daga wannan kogo hakan ya tabbatar mani da cewa wannan al'amari akwai TSAFI acikin sa
.
Amma haka na dake na cigaba da addu'a da karatun kur'ani a zuciyana, kai in takai takawo ma har hadisai ma karantowa nake
.
Haka na kasance a cikin wannan kogon har na tsawon wajen sa'a daya wato awa daya sannan na fara tafiya, babu abunda yake zuwa zuciyana face tunanin ALJANNU
.
Don nasan inba lamari na Aljani ba babu ta yadda za'ayi na kwanta a gida cikin dakina bisa kujera mai laushi sannan na farka na ganni cikin kungurmin daji sannan ga wasu halittu na neman su halakani
.
Haka naci gaba da tafiya kwatsam ba zato ba tsammani sai cikin kogonnan ya gauraye da wani haske wanda koda Allura ne yafadi akasa toh za'a iya ganinsa
.
Hamdala nayi sannnan na gode ma Allah daya rabani da sharrin Duhu ya Allah karemu daga sharrin DUHU,
.
Toh sai a sannan naga ashema kogon nan cikinsa tamkar wani gidan hamshakin attajiri ne ko kuma mashahurin sarki , domin kuwa ganin kogon nayi a kawace da tsarin gida,
.
Shi dai wannan kogo dana afka sam daga ciki baiyi kama da kogo ba sai dai akirashi da fada domin kuwa wani kayataccen fada ne a ciki, nan na zama dan kallo nama daina mamakin yadda akayi na zo wannan daji na koma mamakin wannan fadar wanda tafi min kama da ALjannar duniya, sai a sannan ne na lura da komai dake cikin fadar fadan ya kawatu iya kawatuwa don kuwa tun da nake a duniya ban taba ganin wani fadan dayai rabin wannan kawatuwa,
.
Duk da na kasance masoyin kallon fina finan kasa shen waje irin na su yaki, toh ko a fina finan ban taba ganin irin wannan fada ba
.
Babbar fadace katuwa wacce zata iyacin wani karamin gari akarshen fadar wata kujerace ta zinare a girke wannan kujerar an kawata ta ainun don kuwa wasu irin takubba masu tsananin walkiya da kashe idanuwa aka sossoka su ajikin kujerar
.
A saitin kujerar daga gaba wata shimfida na gani itama kalarta kalar zinari an shimfidata takai har karken fadar, kai nan dai na tsaya ina ta kalle kalle ,
.
Wani abun mamakin kuwa shine babu kowa acikin wannan fada sannan kuma ga a kowanne kusurwa na fadar an ajjiye wasu irin gumaka masu siffar mutane cikin shigan yaki,
Koda na kare masu kallo dakyau sai na gane ashe wayannan kaman sojoji suke,
.
Nayi ta yawata wa acikin fadar har kafafuwana suka fara kuka, nan na zube kasa ina mai dafe da kafafuwana, sai a sannan idanuwa na suka kai ga wata, kofa wacce sam ban lura da ita ba yayin dana shigo cikin wannan fada,
.
Koda na ga haka sai na daure na mike tsaye na tunkari wannan kofa, ina isa bakin kofar na sanya hannu na bude , ko musu kofar baiyiba yabata wata kara "kikkir kikkirrrrrr" alamar ana bude kofar, kofa kofar ta gama wangamewa ta budu nan take nai arba da abun da ya tashi tayar mani da hankali ainun,kwakkwalwata ta kusan daina aiki,idanuwa na sukafara lumshewa a hankali tamkar me gyangyadi,gaba dayan lakar jikina ya mutu,!!!
.
Zazzakar muryace ta biyo baya "shuraih! Shuraih!! Shuraih!!!
.
SHIN A TUNANIN KU wai me nai arba da shine da har na rikice haka
BUDURWAN SIRRI
Gajeran labari