Part 1
------------------------------------------------ *FANSA 2022🌹*
*✍🏽 SA'ADATU (KHILISHI CEH)*
```Bismillahir rahamanur rahim```
```Sadaukarwa ga Hassan ATK, Hussain 8k,Abubakar saleh Kurami, Sdeen, Abubakar Ak Saraki, Muhammad Kareem```
*Free page 1*
Karfe sha biyu na dare AHUTA CLUB, club ne da ya amsa sunan shi, idan kana ciki bazaka gane cewa darene ba,saboda tsananin hasken fitilun wajen ko'ina tamkar rana,a wani waje da naga an rubuta VIP wajene wanda babu hayaniya.
Wani saurayi naga ya fisge wayar dake hannun wata budurwa,"Magana fa zamuyi ba chatting ba" tunda muka shigo wajen nan kiketa latse latsen waya.
Ya fada hakan tare da ajiye wayar saman table din gabansu
murmushi budurwar tayi lokaci guda ta zuba mashi idanuwanta masu tsananin haske.
Ya jawo hannunta ya rungume a hankali yana fadin "Menene ya hana ki zuwa school Rahma tsawon one week?"
Takai hannu tadan bigi goshin tah tare da fadin kamar kasan abinda ya dami zuciyata kenan Dady ya sakaman takumkumi ya kunsheni cikin gida,tun kan case din nan na birthday din Ruky.
Usman ya sauke numfashi a hankali yana fadin "akan me? menene yashafi karatunki a ciki?Duk dai abinda zasuyi sai dai suyi hakuri tunda sun ruga sun haifomu,ni duk abinda suke magana banga wani abu me muni da muke aikatawa ba.
Ta daga kafada tana fadin abinda nagani kenan Usman ni kadai nasan takaicin da nikeji, abin kunya ne a gareni ,a ce kamar ni!!,da ajina,da wayewata,in rinka zama 'Order', zaman Controlling." Rahma ke wannan maganar da alamun abin yana bata Mata rai.
"Ya kamata dai kiyi Kokarin dawowa school don lecture's nata wuce ki Usman ya fada yana duba agogon hannunshi wanda ya nuna karfe daya da rabi na dare,ya mike yana fadin bari inje SAWABA hotel in kwana gida basu san na shigo garin a yau ba.
Rahma ta mike tana dariya Usman akwai ka da kumbiya kumbiya muje nima ka maidani gida kada Aunty ta lura bana nan,su Fauza ma sun shigo club amma inaga ba yanzu zasu tafi ba bazan tsaya jiransu ba.
Usman shima dariya yake ya gyada kai bazaki gane ba wallahi wasu abubuwan dole saida sakayawa muje in saukeki kema ai albarkacin maigadi kikeci da yake bude maki get,in ba haka ba kila ba ganinki zamu rinkayi ba.
Rahma ta turo baki tana fadin wllh Usman abin nan yana damuna kullum in zan fita na dunga sanda ina waige waige kenan kamar wata barauniya,
...........................................
Washe gari 10am
Babban falone da yasha kayan alatu daga can daning area baka jin karan komai sai na cokula, Dady ya ture filet din abincin dake gabanshi ya mika hannu ya dauko 'tissue', yana goge baki tare da fadin"Allah yayi maki albarka Rahma" Mami da Aunty amarya suka amsa da Amin Dady.
Abdallah dake gefen dama ya gyara zama yana fadin "Dady babu albarka ga wanda ya auri duniya!" Ya ida maganar yana huci kamar wanda ya fito filin daga,dama tunda ya zauna yaketa cin magani.
Dady ya zaro idanu waje yana fadin "wacce irin magana kakeyi haka Abdallah waye kuma ya auri duniya?"
'Rahma ce Dady'
Abdallah ya Fadi kai tsaye.
Dady ya kalli Rahma a zuciyar shi yana fadin ruwa baya tsami banza duba da yadda Rahman tasha jinin jikinta.
Mami ta katsesu da fadin Menene tayi har kake kira mata ta auri duniya,ka kuwa san wanda duniya ta aura?
"Mami har yanzu Rahma bata dena zuwa club ba"
What! su ka hada baki wajen fadi
ba suga mikewar Dady ba sai saukar maruka sukaji lokaci guda ya rufeta da duka yana fadin "kaico Allah yayi wadaran halinki wato fitar daren dana hanaki baki bari ba,ganin babu wanda zai ceceta cikinsu yasa ta tashi ta ruga da gudu,
wa je take neman fita hakan yasa Abdallah yayi saurin damkota janta yake keeee har ya dangane da dakin ta tunkudata yayi ta fadi kasa har saida kashin kafar ta ya lankwashe ta bude baki ta fasa wata kara kamar wacce aka yanka,shut up ya buga mata tsawa tsitt tayi kamar ruwa ya ci ta sai hawaye dake ambaliya a idanunta,ya bita da wani mugun kallo,ke baki isa kisawa mahaifinmu hawan jini ba,ni zanyi maganinki wawuya,kuma maigadin da kike hada baki dashi yau zai bar gidan nan shasha wacce batasan ciwon kantaba,yana gama fadin haka ya fice tare da bugo Mata kofar.
Gaba daya kukan nata nemanshi tayi ta rasa ita kuwa me zatayiwa Abdallah ta rama duk wani kunci dayake sakata,me yasa duk wani abu sai yace batayi daidai ba?
shine silar duk wani takumkumi da aka saka mata,duk wani motsi nata yana biye da ita,ta rasa wane irin sa idone wannan,tadan muskuta zata gyara zamanta lokaci guda ta fashe da kukan shagwaba tana yarfe hannu da alamun mugun nan yayiwa kafar ta illah.
Da dubara taja duwawu har zuwa kan gado anan ta baje tana maida numfashi tare da tunanin yadda zata kwatarwa kanta yanci da haka baccin wahala ya kwasheta .
A can falo tun barin Abdallah da rahma falon fadan Dady ya koma kan Mami fada yakeyi kamar itama zai rufeta da dukan,gani yakeyi duk wata lalacewar tarbiyyar Rahma Mami tanada hannu a ciki,shiru kawai Mami tayi amma wannan hali na Dady yana kona Mata rai babu halin Rahma tayi laifi idan ya tashi fada saiya hada da ita,Aunty keta bashi hakuri tana nuna mashi Mami na kokarin kulawa da tarbiyyar Rahma,Rahmar ce fitinan niyar yarinya,ganin dawowar Abdallah falon yasa duk sukayi shiru,duk da cewa wannan ba bakon al'amari bane a wajen shi Abdallah,a kullum Rahma zatayi laifi to fadan akan Mami zai kare wannan dalilin kesa yana kara tsanar yarinyar,gaba daya ta hana iyayen su zaman lafiya.
Dady zan je gida dagacan zan wuce asibiti akwai wadanda nayiwa aiki jiya inason ganin yanayin jikin nasu Abdallah ke fadin haka dai dai ya karaso wajen daning area, Dady yace "to idan ka dawo ka shigo akwai maganar da nikeson muyi"Abdallah yace ok insha Allah Aunty na tafi Mami saina dawo, dukkan su addu'a sukayi mashi tare da fatan dacewa ya fice daga falon.
...........................................
Tun bayan gama duba marasa lafiya da yayi ya koma office dinshi, ya kasa tsinana komài akwai aiyukan da yakeson shigarwa cikin wasu files, zuciyar shi gaba daya a cunkushe take tun ganin da yayi mata a jiya lokacin da maigadi ke bude mata get misalin karfe daya da rabi na sulusin dare, lokacin da yakamata ace kowanne bawa yana kan gadon shi yana bacci domin dare akace mahuta bawa,yayin da wasu ke saman abin sallah dan neman dacewa wajen ubangiji, amma ita lokacinne lokacin yawon ta kwararo kwararo,jin an dafashi yasa ya juyo dan ganin wanda ya shigo kasancewar ya juyawa kofar bayane, sannan tsananin duniyar tunanin daya tafi yasa kwata kwata beji karar bude kofar ba.
Doctor Ishak da ke kallon abokin nashi ya tabbatar ba lafiya ba saboda yanayin idanuwan Abdallah da suka canza launi zuwa jaa, Abdallah be iya magana ba sai nunawa Doctor Ishak kujera yayi da hannu, Doctor Ishak ya zauna yana kure Abdallah da kallon tuhuma tare da fadin "Menene matsalar ka Abdallah?" Tun shigowata naga alamun kana cikin damuwa wanda ya hanaka jin bude kofata da maganar da nayi maka kafin in dafaka.
"Rahma ce Ishak,"Abdallah ya fadi hakan a rikice idanuwan shi gaba daya sun rune sunyi jawur,yarinya daya tana neman gagara.
Cikin mamaki Doctor Ishak yace Rahma kuma Abdallah me kuma ta karayi inace kace hatta makaranta yanzu an hanata zuwa.
Abdallah yace club din da aka hanata zuwa ashe bata bari ba,jiya akan idanuna maigadi ya bude mata get ta shigo misalin karfe daya da rabi na dare ya ida maganar yana cije lebe.
'Ishak yace amma baba maigadi anyi tsohon banza duk yadda muke kyautata mashi shine shi zai cutar damu,wllh wayewar nan ta Rahma bata tsinana mata komai ba sai tabewa,itafa duk wannan abun da suke gani suke wayewane.
Abdallah yace harda ma gata Ishak,Ina takaicin soyayyar da Dady da Mami suke nunawa Rahma a baya yanzu gashi yarinyar nan tsaye muke a kanta amma taki tankwaruwa nayi dukan nayi hargagin duk a banza,tanajin tsorona amma be hanata zuwa tayi wata fitinar da zata bata mana rai.
Ishak yace inaga harda kuruciya ma na damunsu, Allah dai ya kyauta,kaga lokacin sallah yayi muje masallaci idan mundawo ma kara tattaunawa.
*. *. *
Maganar da taji sama-sama yasa ta farka daga baccin wahala da ya kwasheta ta bude idonta ta na kallon rufin dakin, kafin ta yunkura da niyyar tashi,azaba tasa ta koma ta kwanta tana matsar kwalla,dai dai lokacin Mami da Lauratu suka shigo cikin dakin, Mami ta karasa bakin gadon ta zauna tare da fadin Menene kuma har yanzu kukan be kareba? Rahma ta kwantar da kaita a kafadar Mami tana kara narkewa "Mami kafata ya karyaman kafa" ta ida maganar tana yarfe hannu.
Meya samu kafar taki ne? Mami ta fada tana yaye blanket din da ta rufe kafar dashi.
Dukkan mu kallon babban yatsan muke ya kumbura har wani kyalli yake, hankali na ya tashi banason abinda zai tabaman jiki nan da Nan na kara volume din kukan da nikeyi.
"Yi shiru fadaman me yasamu yatsan har ya kumbura haka?"
"Mami Yaya Abdallah ne"
Dukan ki yayi ko ya akayi?
A hankali na zaiyane mata muguntar dayayi man dazun.
"Lauratu ajiye tiren hannun ki kije daki ki dauko man wayata tana nan saman mirrow"
"Lauratu tace to tare da ajiye tiren dake hannun ta ta fita,batafi minti biyu ba ta dawo ta mikawa Mami wayar, "zaki iya tafiya Lauratu Mami ta fadi hakan lokacin da take Kokarin latsa wayar.
Allah ya kara sauki Aunty Rahma Lauratu ta fada tare da ficewa daga dakin.
"Ka dawo ko kana asibiti? Mami ta fada da alamun Yaya Abdallah ta kira, "a a Mami gani akan hanya yanzu zan koma gida, idan nayi wanka nadan kimtsa zan shigo anjima"
"Ka wuto gida yanzu inason ganinka"
'to gani nan shigowa insha Allah'
Ok Mami ta fada tana kashe wayar.
Da lallashi Mami ta samu ta taimakaman nayi wanka, sannan ta zubaman abinci wanda daker na samu na ci kaɗan ina yamutsa fuska,dama abinci ba wani damuwa nayi dashi ba,ga raki idan banida lafiya ciwo kaɗan sai ya wahalar da ni.
Wayar Mami tayi kara alamun shigowar kira ta ɗaga tana faɗin,"Ina dakin Rahma"
Befi ƴan sakanni ba Yaya Abdullah ya turo kofa a darare ya shigo yana kara tamke fuska dan beson shiga shirgin Rahma kwata-kwata.
"Harararshi Mami tayi tana faɗin "Shigo kaga illar da kayiwa yarinyar nan"
Abdullah ya hadiye miyau daker a zuciyarshi yana faɗin dama nasan maganar kenan yace "Me kuma nayi Mami?"
"Ubanka kayi, zaka matso ka duba mata kafar nan ko zaka tsaya tambaya ne!"
"Yi hakuri Mami Yaya Abdullah ya fada lokacin da ya duka saitin kafata"
Hannu ya kai yaɗan taɓa yatsan,na janye kafar ina matso kwallah.
"Ki tsaya induba ko in barki da abarki,inta rube kinga mun huta da fitinar ki,ya faɗa muryarshi babu alamun sassauci"
Ta Allah ba taka ba mugu insha Allah har tsufana da kafafuwa na,nayi maganar cikin gunaguni.
"Uban me kike cewa? Ya fada a harzuke"
Wanda bacin Mami da ke a wajen kila sai ya kai min mari.
Babu abinda yaya Abdullah ya tsana kamar tsaki da gunaguni.
"Mami ta ce Abdullah duba kafar zakayi ko biye mata?"
"Buguwace mami zan kawo magani ta shafa a wajen"
Ya fadi hakan ne saboda Mami ta kyaleshi,duk da yaga alamun targadene a yatsan,yafi son sai taci wahala ko zai gyara mata,yasan yau, wannan bajewar da take ta kwashi bacci sai rana ta fito tayi gatse-gatse ta tashi sallar asuba,yau kam bazai yiwu ba.
Jiya ta saka ya kwana beyi bacci ba itama yau baza tayi ba,ya ida tunanin yana murmushin mugun ta.
Mami ta katseshi da ce wa "ka rubutawa Lauratu sunan maganin taje khemis ta amso yanzu."
Yace "to"be kara kallon inda nike ba ya fice daga dakin,
Mami ta maido hankalin ta kaina tana ce wa"sannu yanzu ki kwanta idan Lauratu ta kawo maganin sai in shafa maki."
*. *. *. *
Kamar yadda Abdullah ya faɗa kuwa tsakar dare Rahma nason kwantawa kafa ta ce batasan wannan ba, kafin wani lokaci zazzaɓi ya rufe ta, gaba ɗaya ta rasa in da zata saka kanta taji daɗi.
A can ɗakin Abdullah ma,yayi nufin hanawa Rahma bacci,sai dai shima baccin ya kauracewa idanunshi.
Rahma ta na barazanar haukatashi da matsalolin ta,ya rasa wacce hanya zai bi dan ladabtar da ita.
Ƙarar da wayarshi tayi ne yasa shi saurin waigawa ya mika hannu ya daukota kasancewar tana saman bedside drowar,MY WIVE shi ke yawo a fuskar wayar,ya ɗan ja ajiyar zuciya tare da lumshe gajiyayyun idanunshi,"ashe fah yau,kiran da yake mata na dare kafin ya kwanta,be samu yinshi ba,fitinar Rahma ta mantar dashi."
"WIVE me ya hanaki bacci har yanzu?"
A sanyaye yake maganar har ya tsorata Basma
Ta ce"Dear yau inata sauraran kiranka shiru baka kira ba, yanzu kuma na ji muryar ka ba yadda na saba ji ba,tabbas akwai abinda ke faruwa menene Dear?
"Na tashi daga bacci ne WIVE" Abdallah ya bata amsa tare da kwantar da kafadar shi a jikin fuskar gadon.
Basma ta sauke numfashi,My Dear niko na kasa bacci rashin jin muryar ka ya kangarar mun da ido.
"Sorry WIVE nima wayar ce babu chaji,sai na sakata a chaji da niyyar idan chajin yaɗan shiga in kiraki sai bacci ya kwasheni," Kiran kine ya tasheni.
Abdallah ya yi mata ƙaryar hakan sanin cewa batason duk wata magana da ta shafi Rahma.
"Yakike,ina My boy yau beyi kukan dare ba?"
Basma ta kalli dan Babyn su dake kwance gaban ta,tana faɗin "Yanzun ba daɗewa na samu yayi bacci,ai kukan dare ƙa'idane kullum sai ya yi shi."
"Zai bari nan gaba tunda an duba shi ba wata lallura dake damun shi,kuka ne kawai da wasu jariran kanyi.
Fira suka yi sosai,basu ajiye waya ba sai wajen karfe biyu da rabi na dare, tsananin kewa da kaunar matar shi da yaron shi, ta mamaye shi,gani ya ke yi kwanakin sunki gudu,shi kam wannan wankan gida ba akan son ranshi Basma ta jeshi ba.
Ganin tunani zai ƙara cin ƙarfin shi yasa ya yi amfani da wannan damar ya ɗauro alwallah ya ida raya daren da sallar Nafila.
By.......✍🏽Khilishi Ceh😍