FANSA 2022

Page 3

by @116641895905258309688

------------------------------------------------  *FANSA 2022🌹*


 


 *✍🏽 SA'ADATU (KHILISHI CEH)*




```Bismillahir rahamanur rahim```


```Sadaukarwa ga Hassan ATK, Hussain 8k,Abubakar saleh Kurami, Sdeen, Abubakar Ak Saraki, Muhammad Kareem```

    


       

        *Free Page 3*




   Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kalmar da Baba Umaru keta maimaitawa kenan, yayin da ya gagara zama,sai kaiwa da kawowa yake yi.


  "Sulaiman ka tabbatar da gaskiyar videon nan kafin ka kawo mani kuwa,ba irin hada hotuna da akeyi  ba ne?"


 "Baba wallahi sai da nayi bincike na tabbatar da gaskiyar videon nan sannan nazo na nuna ma ka."


"Kira man Hussain din,ka ce ina son ganin shi gobe idan Allah ya kaimu,kuma ya taho tare da Rahma."


  Nan take Sulaiman ya kira number Dady Hussain bayan sun gaisa ne ya sanar dashi da sakon Baba Umaru.


  "To insha Allah zan shigo din" Dady ya fada a sanyaye,don ya san dole akwai dalilin kiran,barin ma da ya ji an sako Rahma," Addu'a yake a zuciyar shi Allah ya sa ba wani laifin Rahma ta yi ba.


  "Bani wayar" Baba Umaru ya bukata"


 Sulaiman ya tashi ya mika mashi, 


videon ya tura a wayar shi ya yi deleting na wayar Sulaiman din.


  Mika mashi wayar ya yi tare da faɗin "zaka iya tafiya"


  Fita Sulaiman ya yi, a zuciyar shi ya na addu'ar Allah ya sa tarkon da ya haɗawa Rahma ta fada, Allah ya sa suce zasuyi mata aure,ba shi wani buri irin ya ga ya mallake ta a matsayin matar shi ta uku,tun tasowar Rahma ya ke bala'in son ta, amma Rahma duk idan sun hadu ko kallon arziki be isheta ba, saboda kawai ya na rayuwa cikin kauye, murmushi ya yi, Ya na hango kanshi a matsayin Mijin Rahma.


  WASHE GARI


Misalin ƙarfe sha ɗaya, Dady da Rahma suna cikin kauyen kadanya,yara sai oyoyo su ke yi masu an baibaye motar su, takaici duk ya bi ya lullube Rahma irin hakane kesa ta na kara tsanar kauyen,a fusace ta bude kofar, har sai da ta kusa ture wasu yara da ke kusa da marfin mota.


  Kai tsaye cikin gidan ta nufa tana dauke kai gami da shan kamshi,dan kuwa ba kowa ta ke gaisarwa ba,ta kan ce rashin aikin yi ne ke sakawa ayi ta wani gaishe gashe.


 Matan Baba Umaru sun amshe ta hannu biyu,aka sauketa a dakin amaryar shi, kasancewar sun fi shiri da Rahmar kuma tafi ruwan wayewa ga tsafta ta na da ita.


 Shi dama Dady falon Baba Umaru ya wuce daya ke akwai kofar da zaka shiga falon daga waje,draver kuma dama a nan kofar gida ya tsaya.


******************


  A can falon Baba Umaru,Dady ne duke gaban Babban Yayan su wato Baba Umaru,wata irin zufa yaji tana diga cikin jikin shi,be taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba,ya ɗago rinannun idanunshi da suka rikide da zallar tashin hankali, ya yi kokari sosai da ya hana kanshi fashewa da kuka.


  Bakin shi na rawa ya ke faɗin "Yaya ku gafarceni bacin ran da na saka ku a baya,ashe haka iyaye ke ji?" amma wllh Yaya ban taba keta alfarmar diyar kowa ba" Anan gabar be iya rike hawaye shi ba, kawai sai ya fashe da kuka,lallai Rahma babbar Jarabawa ce Allah ya bashi.


  "Ashsha bari yi mata kuka Hussain ai sai ta kara lalacewa" Baba Zakariya ke faɗin haka.


  "Baba Ibrahim ya ce ya kamata a kira ta mu kara tabbatar da gaskiyar al'amarin nan"


  Duk suka yi na'am da hakan,Baba Umaru ya daga waya ya kira amaryar shi ya ce ta turo masu Rahma falon shi.


  Bayan kamar minti biyu Rahma ta shigo,ganin su su duka a falon yasa tasha jinin jikin ta.


 Saman kafet ta zauna tare da gaishe su wasu sun amsa wasu kuwa ko kallon arziki bata samu ba.


 "Matso nan" Baba Umaru ya fada da muryar bada umarni.


 Dajan jiki ta matso kusa da shi da yake nuna mata, tsoron ta daya ka da su rufeta da duka,da alamun fuskokin su,babu sassauci.....


  "Menene wannan?" Baba Umaru ya fada, lokacin da ya kunna mata videon ya na miko mata wayar.


  Tun fara jin taken wakar,ta gane ko wanne video ne,rawa jikin ta ya dauka,me ya kawo videon partyn da Nameer ya shirya masu a wayar Baba Umaru? Wane irin cin amana Nameer ya yi mata? Nameer ya tabbatar mata da cewa daga cikin wayar shi babu wayar da videon zai shiga, wannan ne dalilin da yasa ba abar kowa shiga da waya wajen partyn ba.


  "Zaki amshi wayar nan ko sai na tattaka ki a wajen nan? Baba Zakariya ya fada kamar zai rufe ta da duka.


Dama duk cikin su yafi zafin rai.


 Ta amsa tana, dukar da kai,sama sama take kallon videon,dai dai lokacin da takalmin ta ya kusan fadar da ita, Nameer ya dauke ta cak,ya rumgume ta a kirjin shi a haka ya rinka hawa step din,be ajiye ta ba,har sai da ya dangana da wajen da zasu zauna, bayan ya aje ta, ya bi fuskar ta, ya na sumbata, lokacin ne kuma hole ɗin aka ɗauki sowa gami da tafa mashi,dai dai nan ta rintse ido,zufa na kara wanke jikin ta.


  Ganin reaction din da ta nuna kaɗai ya isa ya tabbatar wa da su Baba Umaru gaskiyar videon.


 "Tashi ki fita"


 Baba Ibrahim ya fada wanda saboda tsananin bacin rai har fifita yake da babbar rigar da ke jikin shi.


 Cikin sauri Rahma ta tashi kamar ta kifa,ta fice a falon.


"Wacce shawara ku ke da ita?" Baba Umaru ya tambaya yana kallon dukkan su ukun.


 "Aure yakamata mu yi mata Yaya," Baba Zakariya ya fada.


  "Shawarar Zakariya ta yi" shima Baba Ibrahim ya fada.


  "Baba Umaru ya maido hankalin shi wajen Dady Hussain da har yanzu be dawo dai dai ba" . Hussain kai menene shawarar ka?"


 Cikin sanyin jiki Dady Hussain ya ce wannan shawarar ta yi Yaya.


 "To Alhamdulillah ina fatan baku mance da wasiyyar dan'uwan mu Hassan ba?"


"Wannan ai ba wata matsala ba ce Yaya" Baba Zakariya da Baba Ibrahim suka hada baki wajen fadi.


  "Idan mu ka yi amfani da wasiyyar marigayi Hassan muka hada Abdullah da Rahma aure mun cutar da shi Abdallah in mu ka yi duba,da Abdallah be da wata matsala da za'ayi kaico da shi, amma Rahma fah.....?" Dady ya fada cikin damuwa ya cigaba da fadin


 "Sannan duka duka Abdallah har yanzu be cika shekara biyu da auren su da Basma ba,inaga nan ma akwai cutarwa, Abdallah beyi girman da zai rike mata biyu ba.


 "Wadannan ba hujjoji bane Hussain ance mu kyautata zato,kuma Abdallah ai jinin daya suka fito da Rahma, dole duk yadda ta zama yayi hakuri da ita."Baba Umaru ke wannan maganar.


 " Baba Zakariya ya ce ni sai ingama auren ta da Abdallah zai taimaka wajen tarbiyyar ta,in muka duba yadda ta ke shakkar shi.


"Hakane Allah ya tabbatar mana da alkhairi"


Shidai Dady jinsu kawai ya ke amma Aure Abdallah da Rahma hadin nan beyi ba kwata kwata.


Karshe sun rufe maganar akan za a yi waya Abdallah ya zo gobe,dan Baba Umaru ya ce be son bikin ya dauki lokaci.


Dole kwana ya kama su Dady kenan


**********************


 Misalin ƙarfe uku na washe gari duk wanda ake bukatar zaman dashi ya kammala a falon Baba Umaru,in ka dauke Rahma da ke cikin gida, amma ita ma an aika kiran ta.


  Tun dosowar ta kofar falon gabanta ya yi masifar faduwa jin tashin kamshin turaren Yaya Abdallah, saboda bata san ya zo garin ba kwata kwata, kasancewar wuni ta ke cikin daki.


A darare ta shiga falon yanayin sanyin ta da natsuwar ta ya bawa kowa mamaki,ta nemi wuri can daga nesa ta zauna.


 Baba Umaru ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka.


 "Akwai wasiyyar da dan'uwanmu Hassan ya bari kafin ya rasu, wacce muka yanke shawarar fada maku ita ayau saboda lokacin fadin da ya yi,duk da lokacin ke Rahma ko cikin ki babu."


  "Marigayi Hassan ya bar wasiyya cewar idan har Allah ya bawa Hussain haihuwar diya mace,kuma ba Saudat ba ce ta haife ta to yana son a aurawa yaron shi Abdallah"


  "A takaice dai mun kammala magana za mu cikawa Marigayi wasiyyar da ya bari zamu hada kai Abdallah da Rahma aure."


  Da sauri suka dako kai suna kallon Baba Umaru, maganar ta yi matukar bugun zuciyar su, Rahma kam harda suman zaune na a kallah mintuna biyu ta yi, nan da nan zufa ta shiga keto mata,ita kam tafi yadda mafarki ta ke yi.



Abdallah ma ya shiga rudani matuka wanda ban iya misaltawa,ya fada tunani wanda ya kasa gane bacci ya ke ko ido biyu ne?.


Baba Zakariya ya yi gyaran murya tare da fadin" Ku sauraremu dakyau Abdallah ku rike wannan a ranku mun zamu hada auren nan naku badan komai ba,sai dan cika wasiyyar Marigayi, saboda haka ku yi Kokarin hada kanku.


 "Baba Ibrahim yace ku yi mana biyayya ka da muji kada mu gani."kuna fahimta kuwa ?. Ya tambaya ganin kamar sun fice a haiyacinsu.


 Kusan hakane kuwa dan Abdallah maganar da Baba Ibrahim din yayi da daga murya kusan firgitashi ta yi,ji yake kamar an jona mashi wutar lantar ki,kan shi ya shiga sarawa,nan da nan sanyi mai tsanani ya shiga ratsa jijiyoyin jikinshi,koma dai menene zai faru babu musu tsakanin su da iyayen su,sai dai in saɓon Allah ne wannan babu yadda za a yi su yi masu biyayya.


Lokacin guda kuma ya saukar da ajiyar zuciya tuna Rahma ce fah,yasan duk rintsi ba zata taɓa amincewa ba,don haka ya bita da kallo, babban burinshi ta bijirewa abin, amma babban abinda ya bashi mamaki shine ko ɗago kai batayi ba,sai dai zufa da take ta haɗawa.


 Sun dade suna yi masu nasiha da jan kunne.


  Dady kuwa ko tari beyi ba,addu'ar shi ɗaya kada yaran su ki amincewa,ya fi tunanin matsalar daga Rahma sai gashi batayi ko tari ba, amma akwai alamun firgici a tattare da ita.


 Ikon Allah ne kawai ya kai Rahma cikin gida tana shiga dakin amarya ta fada kan gado wani irin numfashi ta rinka saukewa, ta kasa gane halin da ta tsinci kan ta.


Bata dade da kwanciya ba aka aiko cewa ta fito zasu tafi,abin haushi kuma da ta fito Baba Umaru ya ce ta shiga motar Abdallah su tafi tare,shi kuma Dady sun taho shida driver.


  Takaicin hakan yasa tunda na shiga nike matsar kwallah,kwata kwata na rasa abin da ke min daɗi zuciya ta a cunkushe ta ke.


  "Wai kukan kuma na uban menene ?" Uban wa ya hanaki magana dazun?"


Yaya Abdallah ya fada yana dukan sitiyari,ya gangara da motar ya tsaidata, idanunshi sun yi jawur,dama da alamun jira yake.


Tsoro ne ya kamata ganin su kaɗai ne,gudun kada tasha mari ta ja bakin ta tayi tsit.


 Yaci gaba da bala'i na huci kamar ya rufeta da duka,


 "Idan kin yi shiru ne danki kuntatani,kanki kika cuta."


"Inada mata kamar Basma me zan yi da ke,baka mai bakin hali,ko da kinada hali mai kyau ban taɓa sha'awar baƙar mace ba.


"Don haka ya rage naki ko ki bude baki ki faɗa masu su fasa auren,in ya zama dole sai an maki auren kuma su samu can irinki su hadaku,ko kiyi shiru ki cuci kan ki,da ke da hoto duk ɗaya ku ke in kin shigo gida na,inada kishi yadda na tsare kaina bazan iya zama da mazinaciya ba,kodan yaran da zan haifa, kada su tsotso mugun hali."



  "Tun da ya fara magana Rahma ta kureshi da ido hawaye na kara ambaliya cikin su"


Ashe zargin da ya ke yi mata kenan shi yasa ya tsane ta,shi kenan daga an ganta jikin namiji ko ta rike hannunshi sai a kira ta mazinaciya?."



Cikin sanyi ta ce " Na sani Yaya Abdallah ba sai ka faɗi komai ba."


 "Sai dai shirun bani kaɗai na yi ba,me yasa kaima baka yi magana ba,duk da cewa nima bana son ka!, Kuma abu daya bakadashi cikin kalar namijin da nike burin aure, sannan..........


 Marin da Abdallah ya kai mata yasa ta yin shiru," Rufeman baki munafuka,ke har kinada wani quality da wani namiji zai soki.


 Ya ja tsaki "Stupid shashashar yarinya ballagaza kawai"


Be kara kula ta ba har suka iso gida,suna iso ko gama parking be yi ba, ta balle murfin motar da gudu tayi cikin gidan,ya bita da kallon takaici.


 Tana shiga ta afkawa mami wacce ta rafka uban tagumi jin abin da Dady ke faɗi masu"Abdallah da Rahma wai aure".


Rahma ta faɗa jikin mami ta cukwikwiyeta tana sauke ajiyar zuciya.


  Dady yace" Menene haka?"


 "Maza ki tashi ki bamu waje"


 "Tashi ta yi tana tura baki a haka tayi ɗakin ta."


Aunty tace "Dady in akayi haka tabbas an cutar da Abdallah ka duba wannan al'amari da kyau."


 "Nima abinda na faɗa kenan amma ya zamuyi kamar yadda Yaya Umaru ya fada ne Rahma ba tada jigo kamar Abdallah,ba wanda zai rike ta da mutunci kamar shi duk kuwa a halin da ya risketa, Dady ya ida maganar yanajin ɗaci a zuciyar shi."


 "Mami da bata saka bakin ta a maganar ba,a zuciyar ta fadi take "Baƙin ciki yanzu ka fara ganin shi Hussain,insha Allah bakin cikin Rahma shi zai yi ajalin ka,kamar yadda ka silar mijina Hassan"


  "Takai hannu dan ɗauke kwallar da ta ɗan fito daga cikin idanunta,har yanzu ta kasa mancewa na tsohon mikin dake zuciyar ta.


 Dady da ke binta da kallon tuhuma,yace baki ce komai ba Saudat?"


 "Allah yasa alkhairi"


 ta faɗa tare da tashi ta bar masu wajen.


  Gaba ɗaya da kallon mamaki suka bita dashi,duk da cewa wannan ba shi bane farko, wasu lokutan sukan rasa me ke damun mami.


  Ranar kam Abdallah, Rahma,da Mami babu wanda ya runtsa,kowa da abinda yake ƙullawa.

 

A can bangaren Abdallah har wani zazzaɓi zazzaɓi ya ji ya na barazanar rufe shi,yana zaman lafiya da Basma za azo a juna mashi wahala.


  ASALIN SU


.........................

#Khilishi ceh😍