Page 4
------------------------------------------------ *FANSA 2022🌹*
*✍🏽 SA'ADATU (KHILISHI CEH)*
```Bismillahir rahamanir rahim```
```Sadaukarwa ga Hassan ATK, Hussain 8k,Abubakar saleh Kurami, Sdeen, Abubakar Ak Saraki, Muhammad Kareem```
*Free Page 4*
Malam Abubakar mai shanu,ɗan asalin ƙauyen kaɗanya ne,Matan shi biyu A'isha itace Uwargidanshi, wacce suke kira da Yakumbo, sai Fatima wacce suke kira da Inna,yaran Yakumbo su biyar ne akwai Umar,sai Ibrahim sai Zakariya da Hauwa'u,sai auta Ahmad.
Umar da Zakariya da Ibrahim dukkan su suna zauna cikin garin kaɗanya da iyalan su,Aunty Hauwa Kuma na aure a garin katsina,sai autah Ahmad da Allah ya yi wa rasuwa tun yana shekara sha uku sakamakon haɗarin mota.
Inna Binta kuwa yaran ta biyu,Hassan da Hussain,wanda a wajen haihuwar su Allah ya yi mata rasuwa,sanadiyyar jini da ya balle mata,an kaita asibiti ba daɗewa ta rasu.
Rasuwar da ta tadawa mutane hankali ciki kuwa har da abokiyar zaman ta, saboda Inna Binta mutuniyar arziki ce gadaishi iyayen ta masu arziki ne amma ba ta da girman kai ga alheri hannun ta a bude ya ke.
Rasuwar Innah Binta yasa iyayen ta suka nemi alfarmar a basu riƙon Hassan da Hussain sai mahaifiyar ta da ake kira innoh ta shayar da su, idan sun yi wayau sai a dawo da su gidan mahaifinsu,haka kuwa akayi,bayan anyi addu'ar bakwai yan'uwan Binta suka hada duk wani abu na Hassan da Hussain,suka tafi kaduna da su kasancewar Inna Binta yar asalin garin kaduna ce, sanadiyyar tana zuwa kaɗanya gurin wata yar'uwar babanta gwogwgwo kuluwa.
Allah ya kaddara suka hadu da Abubakar soyayya ta shiga tsakanin su,duk da a lokacin ta gama secondary shi kuwa malam Abubakar ko primary be yi ba,sai dai ya na da ilmin addini sosai,hakan ya jawo cece ku ce,da ta kawo shi a matsayin mijin da zata aura,da yawa Yan uwan ta suna ganin ci baya ne,ta rasa mutumin da zata aura sai dan kauye wanda be da ilmin boko, amma a ɓangaren iyayen ta sun bata goyan baya,to a haka dai akayi biki amarya ta tare ɗakin ta sukaci gaba da zama cikin aminci ita da Mijin ta da kishiyar ta.
Bayan wasu shekaru
Saboda sabo da shakuwar da ke tsakanin Innoh da Yan biyu yasa koda ta yaye su ta kasa bawa mahaifinsu su,duk kuwa irin yadda malam Abubakar yaso hakan amma dole ya yi hakuri ya bar masu rukon yaran a hannunsu,kuma wannan ne dalilin da yasa Hassan da Hussain suka ta so cikin garin kaduna kuma suka samu ilmin boko da na addini,sabanin Yan uwansu dake garin kaɗanya da suka yi karatun allo kadai.
**********************
Zaman Hassan da Hussain wajen kakanninsu zama ne da ake kira da rikon kaka,Zama ne da ba kwaɓa ba zangwama.
Hassan da Hussain irin tagwayen nan da ba kowa ke iya banbance su ba suna tsananin kama, amma a bangaren halayya babu halayyar su ta tazo ɗaya, Hassan ya kasance mutum marason hayaniya, akwai tausayi gashi da hakuri yana da son yan'uwansa barin ma ƙaninsa Hussain,a bangaren rayuwa baya da girman kai sannan kyale kyale be dameshi ba.
Saɓanin Hussain mutum ne mai hayaniya ga saurin sabo baya da hakuri idan har ka tabo shi, sannan be damu da yan'uwanshi ba,ya kan ce "Abin kunya ne ace waɗannan kauyawan ne yan'uwana," Hussain mutum ne me kyale kyale shi irin matasan nan ne da basa son raini, wannan dama duk ya same ta ne tare da goyon bayan kakannin shi.
Duk wani abu da Hussain zai yi to fa zasu ce kuruciya ce, hakan ke kara bashi gudummawa sosai
lokacin da suna secondary malam Abubakar yakara yunkurin son ko Hussain ɗin ne su bashi ya dawo gaban shi, saboda wasu halaye da Hussain ɗin keyi na rashin tarbiyya
Tun suna secondary Hussain ke da ƴan'mata rututu,yau yana wajen wannan gobe yana wajen waccan,idan ka bari ya fara soyayya da diyar ka ko kanwar ka to bazaka gane kanta ba, irin samarin nan ne da suka iya kalallame ƴan'mata da dadin baki.
Hussain ya hurewa ƴan'mata da yawa kunne,ya haɗa ƴan'mata da yawa faɗa.
Hassan yanayiwa Hussain wani irin so ,da har zamu iya cewa yayi yawa,a kullum zaka ganshi tare da Hussain zakayi zaton ya bashi ratar shekaru ne saboda yadda yake kulawa da shi,idan zai samu abu na ci ko na amfani to fah,sai ya fara bawa Hussain ya yi amfani dashi sannan shima yayi.
Hatta makaranta tun daga nursary har zuwa secondary shi ke kokari ta fannin taimaka wa Hussain a wajen jarabawa da assignment,sai da suka shiga jami'a aka rinka samun matsala saboda shi Hassan yana karantar "Faculty of Engineering",shi kuma Hussain "Politics" ya ke karanta. Yawan carry over da sukayi ta bawa Hussain, karshe da abun ya yi yawa hukumar makaranta ta kore shi,ba wai baya da fahimta ba ne, kawai karatun ne ba yada ra'ayi shiyasa baya maida hankali.
Hakan yasa,Kaka da,Innoh suka yanke shawarar fita dashi ƙasar waje,a cewar su karatun zai fi yi mashi sauƙi a can, wannan shine dalilin karatun Hussain a ƙasar malesia.
************************
MALESIA
Kallah! Kallah!wow matso dan'ubanka "Kaga yarinyar da nike fada maka"
"Kalli surarta sosai, cikin Ƴan matan da mukeyi ka taba ganin mai halittar da zata tsaya cak,ka ga fah siffar kwalabar lemon coke ne da ake fadi da ita". Hussain ne ke fadin hakan yana nunawa Abokin shi Nasir Bujawa hoton wata hadaddiyar Baby daya cika screen din wayar shi.
Nasir Bujawa ya kalli yarinyar sosai ya gano gaskiyar abokin nashi,ya ja dogon numfashi,tare ta jan tsaki to wannan ai daga ganinta balarabiya ce ko ba indiya,kasan kuwa sun yi maka nisa.
"Inji uban wa?" To Dan ubanka yar Nigeria ce kuma har nayi fallowing dinta,sunan ta Fateemah yar asalin garin gombe ce.
Aini insha Allah nayi mata, Hussain ya ida maganar ya na murmushi,be taba jin ainihin soyayyar diya mace ba sai akan Teemah wani irin so yake yi Mata,yana jin in ya same ta burinshi ya gama cika aka duk wata diya mace, Teemah ba abin da za a nema a wajen wata mace ba a samu a wajen Teemah ba.
Hussain ya fara ganin Teemah a Instagram, yawan bibiyar ta dayake yi yasa tun tana share shi har ta fara kulashi,a ranar da ta fadi mashi cikakken sunan ta da sunan garin su ranar wuni ya yi cikin farin cikin kulashin da tayi.
A hankali ya rinƙa cusa kan shi a wajen ta har suka dan fara sabawa,Anan ne ya yi mata tayin soyayyar shi,. Sai dai kai tsaye Teemah ta ce mashi "Bazan yi cinikin biri a sama ba" Kamar yadda na ce maka bana bukatar hatta picture din ka,ka bari inganka a zahiri to haka ma duk wani abu daya shafi soyayya,ka bari sai ka dawo Nigeria,( kasancewar Hussain baya dora picture din shi a social media)
A lokacin yaji ba dadi sai dai kuma da yayi wani tunani sai ya hakura yasan duk ranar data ganshi a zahiri ba zata iya ture soyayyar shi ba.
Kwanaki na ƙara mirginawa soyayyar Teemah na kara rugurguza zuciyar Hussain,ita kuma tana kara janshi a kasa, saboda kwata kwata halayyar Hussain batayi mata ba,tafison Nakiji miskili,wanda magana ba ta dame shi ba, batason namiji mai surutu kwata kwata.
********************
Kwance yake akan tafkeken gadon shi,sanye yake cikin kayan sanyi, kasancewar garin yau akwai sanyi,ya lullube rabin jikin shi da bargo,da ka duba fuskar shi za kasan ya na cikin damuwa.
Cikin sanyin jiki ya janyo laptop din shi domin yin wani research.
Ba a wani dauki lokaci ba yaji duk aikin ya gundure shi,ba abin da ya ke bukata irin son jin muryar Teemah.
Wayar shi ya dauko ya kara neman layin ta a karo na babu adadi,yanzu ma, haka ta gama ringing ba tare da an dauka ba.
Ya dafe goshin shi yana furzar da numfashi me dumi,yau kaɗai da basu yi magana ba ji yake kamar ba shida lafiya, yarinyar nan tana bashi wahala,ya kasa zuciya ya kyale ta ko ya yi niyyar hakan zuciyar shi bata iya jurewa.
Ƙarshe dole haka ya hakura ya kwanta,dan yasan ko zai yi mata misscall dari ba ɗauka zatayi ba,dama takanyi hakan in ƴan wulakancin sun motsa.
Ya dade yana juyi daker ya samu bacci ya dauke shi cike da tunanin ta, hakan yasa ya kwana yana mafarkin ta.
.............................
NIGERIA
Ƙwance ya ke a bayan ƙatuwar kirar Ferrari,baka sidik har sheki take yi, Driver ne ke tukashi cikin natsuwa da bin ƙa'idar tuki.
Matashi ne ɗan kimanin shekaru talatin,cokolate color ne irin kalar hutun nan,sumar kanshi tasha gyara, Idanunshi sanyi cikin farin gilashi, kyakkyawa ne na ƙarshe.
Hassan Abubakar Mai shanu kenan. Matashi wanda ke cikin ganiyar shi, bayan kammala digirin shi a fannin Foculty of ingenering ya samu aiki a wani babban kamfani.
Suna kan hanyar su ta dawowa daga kauyen kaɗanya ya kaiwa Mahaifinshi da ƴan'uwanshi ziyara.
"Malam Saminu kaɗan kara gudun motar nan kaga dare ya fara nisa"
To yallaɓa ina neman alfarmar in tsaya inyi bawalli,tun dazun nike rikeshi,naji yana neman gagara ta"
"Tsaki Hassan ya ja in banda abun ka Malam Saminu wake rike fitsari ai sai yayi maka wata illar".
Jingina bayan shi yayi jiki kujera,ya rufe idon shi yana shakar iskar da ke ta kaɗawa cikin dajin.
"Ya yin da Malam Saminu ya fita dan gabatar da buƙatar shi"
"Ya duka ya fara fitsari kenan yaji alamun nishi a kusa dashi,wayar shi ya fiddo ya haska fitalar wayar,abin da ya gani yasa shi saurin mikewa,da alamun gudu ya bar wajen.
"Ƙarar rufe ƙofar da akayi cikin rashin natsuwa,ya maido hankalin Hassan,
"Lafiya kuwa malam Saminu?"
"Da sauƙi dai yallabai" malam Saminu ya bashi amsa yana maida numfashi,dai dai lokacin ne kuma yaja motar.
"Meya faru ne?" Hassan ya ƙara jefo mashi tambayar.
Malam Saminu yace "Mutum ne kwance cikin jini yallaɓai.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine kuma ka zo kaja mota?
Yi ribos mu koma wajen me yiwowa akwai taimakon da zamu iya mashi,idan mun bar shi a nan wazai san dashi.
Malam Saminu ba dan ya so ba ya yi ribos dama basu wuce wajen sosai ba.
Hassan sauka ya yi ya nufi wajen ya yi amfani da wayarshi wajen haskawa.
Halin da ya riski mutumin yasa hankalin shi ya tashi.
Hannu yasa da niyyar ciccibar shi,sai dai jin bazai iya ba yasa dole ya nemi taimakon Malam Saminu.
A bayan mota suka sakashi lokaci zuwa lokaci Hassan yana lekawa ya haska mutumin gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake, gani yake Malam Saminu ba ya gudu hakan yasa ya yi ta azalzalar shi.
A guje motar tasu ta shiga Eroson hospital,gudu gudu ya fita ya na kwala kiran.
"Nurse!!"
"Nurse!!"
"Pls help!"please help!"
Gaba daya hankalin mutanen dake emergency ya dawo kan shi,da sauri kuma nurses suka turo gadon dora marasa lafiya,su ka fice aka dora mutumin aka shigo da shi.
Sai dai kuma suna ganin yanayin raunikan da ke jikin shi,suka ce ba zasu taɓashi ba sai an kawo Police.
Hussain ya ji ba dadi,amma ya yi masu uzuri yasan suna kan aikin su ne,nan da take ya kira wani abokinshi video call, police ne mai muƙamin DPO ya basu shi suka yi magana sannan aka shiga da mutumin domin ceto rayuwar shi.
Malam Saminu ya matso gurin Hassan ya na faɗin, "yallaɓai ko zamu tafi gida sai mu dawo gobe muga yanayin jikin na shi?".
"Eh amma mu jira fitowar likitan tukunna."
Sun shafe kusan awa guda kafin su samu nasarar tsaida jinin dake zuba tare da cire bullet da ke jikin shi.
A lokacin ne kuma likitan ya samu fitowa,gaba ɗaya jikin shi ya haɗa gumi.
Ya karaso wajen su yana faɗin, "A binciken da mukayi mashi munyi nasarar cire harsashi guda, ɗaya a ƙirjinshi amma daga ɓangaren hannun damansa, akwai gwaje gwajen da zamu yi amma wasu result ɗin duk sai gobe.
Zaku iya tafiya zuwa goben sai ku dawo, akwai nurse's da zasu kula dashi.
Dr.Mors ya ida maganar ya na mika masu takarda bill ɗin da zasu biya.
Nan take Hassan ya yi mashi transfer suka bar asibitin suna yiwa mara lafiyar fatan samu sauki.
#Khilishi ceh😍