ABIN DA YA BAKA TSORO

2️⃣

by @maidambu41

ABIN DA YA BAKA TSORO...🦋

              (Arrow Of Destiny)

بسم الله الرحمن الرحيم

*EWF*

2️⃣

  Gidan lailaye yake da siminti musamman yar karamar tsakar gidan, sai yar karamar madafi, da rijiyar da yake tsakar gidan, dan gaba da rijiyar yar karamar rumfa ce da aka saka injin markade,sai yar ban daki da yake tsakanin dakuan ta lungu. ko ina tsaf-tsaf gwanin ban sha'awa. Ga kayan sayar da kosai da kunun an wanke shi tass an kefe mata shi.

Da sallama ta shiga cikin gidan, tana rike da hannun mahaukaciyar, har dakin da yake dauke da tarkacen shirginta.

          Ta fita ta dauko taburma ta shimfida mata, sannan ta leka ɗaya dakin ta ce.

  "Sannu malam nasan Rabe ya gaya maka abinda ya faru?." Gyada kai dattijon yayi sannan ya ce mata.

"Sannu Balkisu, Allah ya albarkaci al'amarin ki, ya kuma sanya waɗanda zasu miki hidima kamar yadda kika mana"

    Cikin murmushi ta ce mishi.

"Amin Malam"

     Sannan ta mike ta fito waje, madafin ta shiga ta haɗa wuta, dake tayi sallah tun a asibitin ta shiga hada wuta ta daura ruwan zafi sannan ta koma dakin ta fara hada shirgin ta daure shi tam, sannan ta fita zuwa dakin ta. Ta dauko wata yar yaloluwar katifa, ta shigo dakin da mahaukaciyar take zaune ta shimfida mata. Sannan ta koma madafin ta hada wutar sosai, tana cikin aikin Rabe ya shigo da cefane.

"Assalamu alaikum! Baaba me kosai ya take da jikin ta?"

"Wa'alaikumunsalam, da sauki fa gata nan dai na kawo ta gidan nan"

"Anya Baaba babu matsala?"

"Eh idan ta warke sai a maida ita wurin ta ba"

"Hmm"

   Sannan ya sauke kayan da yazo da shi, ya fara aikin da yake ba shi ne, tana nata.

"Yau kan naso nayi shinkafa da wake ne toh Allah bai nufa ba"

"Kin manta kin dafa waken kafin ki fita?" Ya tambaye tana yana kallon yar tukunyar karfen gefen ta.

"Kai jama'a wallahi na manta."

"Gaskiya gara da na tuna miki, yawwa na cire kudin geron wainar yau, sannan na cire kudin mai da na wake da na kunu, sauran ne na yi cefane da shi ga kudin nan" ya shiga dakin ta ya dauko mata kudin da ya dawo dashi daga kasuwa, sakawa tayi a lalitarta. Ta sanya shi ya dibo shinkafa, ya kawo mata ta shiga gyaran shinkafar.

     Ita kuma ta kwashe ruwan ta nufi ban daki, ta kuma zuwa zata diba s rijiyar shi ya amshi bokitin ya diba mata.

    Da gudu ya shigo har yana haki. Ware idanu yayi akan Rabe. Ya watsa mishi harara sannan yayi salama.

"Assalamu alaikum! Baaba me kosai. Kin ga Rabe yau ma bai bani kosai ba sai tafiyar shi yayi abin shi " ya fada yana yana kafe Rabe da manyan idanun shi.

"Rabe yaushe ka zama haka?"

Dariya yayi yana faɗin.

"Wallahi ban hana shi ba, asalima masu kula da gidan su ne, suka hana ni shiga, ni kuwa na rabawa yara "

"Toh kin ji ba sai ya ajiye min abuna ai" ya fada yana tura baki.

"Aliyu gadanga kusar yaki, kayi hakuri gobe da kaina zan kawo maka ai nasan ba zasu hanani shiga ba"

"Insha Allah " ya fada yana niman wuri ya zauna.

Duk da bata san dalilin makale mata da yaron yayi ba, sai dai tasan ita uwar Yara ne.


    Kai ruwan ban daki Rabe yayi shi kuwa sai kallon kofar gidan yake.

"Kayi laifi ne?"

"A'a kawai na gaji da zaman gidan ne, shine zan fito Aunty Ummi ta biyo ni wai kar na fita " ya fada kamar zai yi kuka.

       "Toh shi kenan zauna nayi wani aiki sai na raka ka gidan an jima " ta fada bayan ta shiga ban daki ta haɗa ruwan. Sannan ta fito ta shiga dakin ta tashe ta, tana tsugune kamar yadda take kullum.

         Mikewa tayi babba ta dauki wani mayafi ta rufa mata, suka tafi ban dakin. Hankalin shi yayi wurin Rabe dan haka hira suke bai ga matar ba shima.

               Sai dai ta cire mata kaya tsaf, ta zaunar da ita dauki jikaken ruwan kanwar ta, ta wanke mata kanta da yake cike da kwarkwata, cukurkude ta wanke mata shi tas sannan ta shiga mata wanka,  tana durje ta ga mace har mace amma ba lafiya. Haka ta wanke ta tsaf sannan ta zuba mata ruwan da zata shiga ta mata yadda zata iya shi ta taimaka mata ta shiga bayan sun gama ne suka fito. Sai lokacin ya ga fuskar ta.

"Baaba Bakuwar kika yi?"

"Eh Gadanga kusar yaki" ta kaita lokacin har Rabe ya wanke shinkafar ya zuba, sannan ya koma gefen Aliyu suna cigaba da hira.


  A dakin kuwa sai da Baaba tasha fama kafin ta iya taje mata kai bayan ta saka reza ta yanke wadanda ba zasu taju ba, ta shafe ta da mai, sannan ta dauko wata riga da zani ta saka mata. Sannan ta fito yar sauran kunun malam ta diba ta saka a cikin ruwan shinkafar yayi zafi ta kawo ta mika mata, kamar tasan tana jin yunwa ta shiga sha da zafi zafin shi. Har jikin ta yana rawa. Hawaye ne ya zubo mata me zafi sabida tausayin yarinyar, tana gama sha ta mika mata magani ta mata alamar ta sha, taunewa tayi ta hàdiye, sannan ta bata ruwa ta sha ƙwanciya tayi domin sai lokacin gajiyar abinda ya faru ya sauko mata. Tunda ta kwanta barci yayi gaba da ita. Share kwalla Baaba me kosai tayi tana faɗin.


   "Da sannu Allah zai bi miki hakkin ki." Fitowa tayi ta samu Aliyu da Rabe sai musu suke.

"Rabe Allah yasa ka mai da hankali akan abincin nan?"

Ta fada tana leka dakin Mijin ta.

"Malam kayi hakuri zata kwana biyu ne idan ya ji sauki sai ta koma inda take zama" duk da kasancewar shi makaho amma sai da ya d'aga kai ya kalli inda take zaune na wani lokaci kafin ya ce mata.

"Mai Gado kina ganin haka shine mafita?"

      Duk da kasancewar ta dattijuwa da ta manyanta amma haka bai hana tayi wani irin dabi'a irin ta mata da basu gama mallakar hankalin su ba, wato irin kayi shiru kana wasa da wani abu ko bakin zani ko bakin mayafi ko tsinke hallo dai ko zare. Baya ganin ta amma sai da ya sake murmushi sannan ya ce mata.

"Kar ki damu jarabawar rayuwa ce, idan aka samu lokaci sai muyi maganar ba"

"Toh Malam" ta fada kasa kasa, sannan ta cigaba da cewa.

"Lokacin la'asr yayi ko zan zuba maka ruwa a buta ne?"

"Ba damuwa kiyi yadda kike so"

"Toh Malam"


Duk da bata son haka , amma kuka bahu yadda ta iya. Sam ta tsani malam ya bata dama ko yace tayi yadda take so, yana masifar mata ciwo, kanta a sunkuye ta ce mishi.

"Malam kana son mu rike ta ne?"

"A wannan lokacin hakan shine mafi alkhairi a rayuwar ta sama da ace tana wajen tana garranba"


Kamar yasan tana kallon shi, amma cikin nutsuwa ya ce mata.

"Haka shine mafi alkhairi, lada biyu ga jinya ga ciyar da bayin Allah, kina tsammanin Allah zai bar ki ne haka?"

Wani irin nauyi da darajar mafi girma da girma ya kuma sauka bisa kafadarta, hango kanta a wani irin matsayi take.

"Malam kana nufin na taka matsayin..."

"Kwarai kuwa Maigadon zinari, duk lokacin da kika dubi ni'imar Ubangiji karki tuna da baki haifa ba, Allah yana sane ta sanadin haka sai ki yi murmushi "

Kwalla ne ya zubo mata, kafin yau bata tunanin haka, amma yau malam ya kara tuna mata da haka.

"Ko min kashin sa kiyi kukan nasan kina kuka ne ko ban ji sautin ki da amon ki ba,.nayi imanin Allah ba zai barki haka ba, balle ina hango miki dinbin lada da zaki samu gwabgwab'a."

"Allah yasa haka shine mafi alkhairi "

"Alhamdulillahi, uwar Marayu"

Da wannan ta zuba mishi ruwa yayi alola, sannan ya fito da tiren ta xubda ruwan a wurin wanke-wanke.


"Baaba duba shinkafar ta nuna?" Inji Rabe yana tsamo shinkafar.

"Tayi ku wuce masallaci, bari na karasa. Malam Ali ka dawo kaci fa"

"Gyada mata kai yayi sannan ya bi Rabe suka fita.


Sai da ya gama sannan tayi alola ta nufi dakin ta, ta tadda sallah. Tana cikin Addu'oin taji shigowar Rabe shi daya tasan za ayi haka domin dai bai zama dole Aliyu ya dawo ba. Fitowa tayi ta zuba mishi abincin tana tambayar shi Ali.

"Mutanen gidan su masu shegen kallon Wulakanci sun wuce da shi amma ya ce don Allah a kai mishi abincin shi"

"Allah ya kyauta" ta fada tana nufar kitchen din ta zuba mishi a wani ƙaramin kwanon dan china, me kyau da zanen dawisu. Sannan ta dauki mayafinta tana me leka malam ta ce.

"Bari na kaiwa Aliyu abincin nan yan uwan sun tafi da shi"

"Toh ba kome Allah ya tsare"

"Amin" ya fada yana barin dakin shi.

"Rabe ka kula da gidan don Allah"

"Toh"

Ya fada shima, yana cin abincin shi dan la'asar tayi kuma za a shiga karatun la'asar.

Dake Baaba mace ce me mutunci da girmama kai, tana zuwa kofar gidan aka barta ta wuce har cikin gidan yana zaune a katafaren falon da ya sha kayan alatu irin na manyan gidajen sarauta masu ƙarfin mulki, da sallama ta shiga ta same shi zaune yayun shi sun saka shi a gaba ya ci abinci.

"Assalamu alaikum! Sannun ku bayin Allah!" Ta fada tana tsare shi da idanun. Da sauri ya mike tare da nufota ya amshi kallon Abincin yana amsa sallamar ta.

"Wa'alaikumunsalam, yawwa Baabana Nagode shi yasa nake son ki sosai Allah ya saka da alkhairi duk ni daya" ya fada yana zama.

Wata babbar mace ce ta fito tana fara'a.

"Baaba balki kece a gidan nan? Lallai shigo ki zauna"

"Yarwa Hajiya Asma'u, wallahi gani nan dai na kawowa Aliyu abinci irin cimar mu"

"Kai Baaba Balki ai nima ina son abincin ki. Sayyid zuba min mana" tura baki yayi yana faɗin.

"Baabana ina cewa ni daya kika kawowa?"

"Yaushe Sayyid ya fara rowa ne?" Mikewar Baaba tayi tana faɗin.

"Toh zan koma, Malam Aliyu sai an jima "


"Sai an jima Baaba mun gode."

"Ba kome " ta fada musu tana me barin gidan, Hajiya Asma'u matar Uban su Sayyid ne, Alhaji Hamza Mansa. Asalin su yan kasar mali ne daga cikin gidan sarautar Mansa keita.

Alhaji Hamza shine yarima na bakwai a jerin gidan su da yake jiran gado. Ita kan ta Mahaifiyar su Aliyu me suna Hafsat Omar Mansa, Allah ya mata rasuwa ne tun bayan haihuwar Aliyu. Ta tafi ta bar shi a hannun kishiyar da yan uwan shi da yana da Yayu biyar da shi na shida, mata uku su maza uku Mazan sun hada da.

Abdullahi, Jabir, sai shi Aliyu kuma mazan sune manyan sai Jalilah tana auren a kasar Morocco. Sai Fadwah tana aure a can Mali. Sai Buhayyah wacce yanzu take karatu domin duk yaran gidan suna karatun su.


Haka Mazan suma Abdullahi yana da mata yana zaune a Niymia da Yaran shi biyu, Jabir yana can Mali yana aiki da Office din Embassy na Mali.


Sun dauki wani jarababben soyayyar Aliyu sun daura mishi,.shi kan shi Mahaifin su Alhaji Hamza Mansa ba karamin so yake mishi ba.


Haka Hajiya Asma'u ta dauki soyayyar duniya ta daura mishi kamar su taru su cinye shi dan kauna. Abu daya yake damun shi sun hana shi abota da kowa, shi kuma mutum ne na jama'a, haka Allah yayi zuciyar shi da son al'umma.


Dama wacce bata kaunar ganin shi yana shiga dakin mutane Buhayyah ce, gani take darajar shi ya wuce karfin wanda zai shiga cikin talakawa yana rayuwa, ko abincin nan da Baaba ta kawo da kanta sai da ta bata rai ita sam bata son yana cuɗanya da kananun mutane. Idan ka ga yadda ake tattalin rayuwar shi sai ka dauka kamar ba lafiyayyun mutane bane, domin kome da za ayi mishi hatta abincin shi daban ne, kome na rayuwa ware mishi ake yi a nunawa kowa yana cikin masu jiran gadon sarautar Mali.

---

Koda Baaba ta koma gida ta samu har Rabe ya gama ya wanke kayan ya kifa, sannan yayiwa Malam sallama, malam yake gaya mata. Zama tayi ta fara aikin surfen geron wainar gobe, tana gamawa ta wanke, suna hira da malam, har ta surfe wake. Tana cikin wanke waken ya shigo ya gaishe ta, sannan ya ja wata fantaka ya shiga jan ruwa yana zubawa a kai. Kafin ya cika ya wanke tass geron kunun gobe sannan ya shiga kitchen ya dibo citta da kanunfari ya zuba ya fara markade .


Yana gamawa ya nutsu sosai ya tashe mata su, daidai ana kiran magariba, yana gamawa ita kuma ta markada geron wainar, sannan ta ce ya tafi masalaci. Itama ta shiga tayi sallah bayan ta leka dakin mahaukaciyar nan ta samu har zuwa lokacin barci take.


Sai da tayi sallah isha ta fito waje ta haɗa wuta ta daura ruwan zafi, sannan ta shiga dakin ta tashe ta. Suka nufi ban daki. Wanka ta kuma mata bayan ta gasa mata jikin ta, sannan ta fito da ita. Ta bada kunun me zafi nan ma tasha sannan ta kuma zuba mata abinci, kadan taci ta juya ta kwanta, domin yanzun tana jin dadin jikin sosai amma rashin karfi yasa ta bata son dogon zama.


Sai da ta mata addu'oi sannan ta ja ta rufe ta, ta kuma rufe dakin. Tana fitowa Rabe yana gama cin abincin shi yayi mata sai da safe. Sanan ya bar gidan.

***

Anyi biki na fitar hankali, gefen shi Lawali yana kara nausar shi. Ga Amaryan shi yar dangi ce gata Kyakyawar gaske. Haka yasa shi jin wani irin, duk da zuciyar shi tana yawan tuna mishi laifin da ya aikata amma haka bai kuma saka shi jin kome a ran shi.


Haka aka gama bikin Lawali da wani abokin su,, Tanimu suka raka shi bayan sun yi yar barkwace sannan suka musu nasiha da zaman lafiya yab matan amare kuwa an basu kudi me yawan gaske, sannan suka fito da abokai baki daya, kallon ta yake sai wani kamshi yake tashi a jikin ta. Haka dai ua tattara yar nutsuwar shi suka raya daren amma tabbas Mahaukaciyar nan duniya ce, shi da kan shi ya tabbatar da haka, mahaukaciyar nan ta musamman ce, haka ya nufi ban daki ya sakarwa kan shi ruwan sanyi. Kamar zai yi hauka haka yake jin kana shi kamar zata tsage gida biyu..


Yana fitowa ya kwanta, Washi gari aka kira shi domin tabbatar mishi da abinda yake nima ana hasashen zai samu.

Abin mamaki duk da saura kwanaki kadan zaben sai yaji baya son haka a ran shi. Haka yayi ta rayuwa har lokacin zaben yayi a lokacin Lawali ya kuma zuwa mishi da wani batu, inda suka tafi makabarta suka binne jariri sabon haihuwa. Sannan suka kuma hako wani kabari suka ciro wani mutum da aka binne. Sannan suka nufi gidan bokan da shi. Anan aka mishi wanka da......


*TOP-NOTCH WRITERS*


 

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*


  _Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_


   _Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b'ata shiru_


   _Wani banzan dariya ta saka min tana d'age min gira_

 

_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_

   _Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_

     _Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_

    

_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_


   _Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_


      _hmmm lallai zata fashe... Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa... Kin ga last na ga The Governor's Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah.... Abun dad'i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_


   _Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_

_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_


_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_


   _Don Allah fa_

   _Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_


_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_

_TOP-NOTCH.... Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_


_Wow da gaske?_

_Zan Miki karya ne?_

_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status...._


_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab'a ni_


    _Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_


  _Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi....._


_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350

_Guda Biyu_700

_Guda Uku_ 1k


_Zaku iya payment ta  to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_


_and send evidence to does number_

*****

Or

**** or ****

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_


_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_


**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

*+22784506476*


_Welcome ta Top-notch Team_