CHAPTER ONE
by @ummubasheer
MAHAIFIYA TA*๐น
*{A Romantic &Loving story of a nice Family}*๐
*NA*
*UMMU BASHEER*
*REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*{We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of readers}*
โจ *Devoted*โจ
*To*
โจ *All Mothers in the world*โจ
*Page 1~5*
*{My Beloved Mother}*
*Gurin* cike yake da d'alibai y'an makaranta da alama tashin su gida kenan kowa na nufar hanyar da zai sadda su da gidan su, wata kyakyawar budurwa ce na hango sanye take da dark blue and White uniform, fara ce mai d'auke da daradaran idanu farare tass, kmr madara, bakin ta d'an k'arami dai-dai da fuskar ta, tana da eyelashes da eyebrows masu cika, tana da tsayi dai-dai ba sosai ba, fuskar ta a yamutse ta kalla wristwatch d'in dake mak'ale a hannun ta mai kyau tayi, ganin har 2:20pm yayi yasa ta juya ta fara tafiya tamkar tana tausayin k'asa, tafiya take cike da natsuwa da kamun kai, tun daga nesa take jin ana k'wala mata kira sanin ko wace ce yasa bata tsaya ba.
" *NAJMA NAJMA NAJMA*" wata budurwa ce ke fad'in haka tare da nufan wannan budurwan na d'azu.
Wacce aka kira da *Najma* tsayawa tayi ba tare da ta waiga ba cikin sanyin murya mai cike da shagwab'a ta fara magana "For God sake Yusra har sai Yaushe zaki daina b'ata min lokaci idan mun tashi bayan kinsan idan lokaci yayi bana son ko k'ara one minute ne ban tafi ba"
Yusra ce ta dafa Najma tare da fad'in "Kiyi hakuri Aminiya na tsaya karb'an wani text book nane gurin Ummita"
Murmushi Najma tayi har sai da dimple d'in ta suka lotsa, wayyo fan's zo kuga yanda tayi kyau, "Ba komai Aminiya mu tafi kar mu b'ata lokaci"
Nan suka nufa hanyar unguwar su suna tafe suna hira, dai-dai wani gida Yusra ta tsaya tayi ma Najma sallama, sannan Najma tayi gaba gida uku ke tsakanin su da Yusra, wani d'an madaidaicin gida na k'asa Najma ta shiga bakin ta d'auke da sallama.
Wata kyakyawar Mata ce gaban murhu tana iza wuta, da kun ganta zaku gane MAHAIFIYAR Najma ce saboda tsananin yanda suke kama da juna, Da sauri Najma ta ajiye jakar ta, tare da nufan MAHAIFIYAR TA, karb'an Maficin tayi ta fara fifita tana cewa *MAMI NA* shiyasa nake ta sauri in dawo domin ki huta"
Murmushi Mami tayi tace "Allah yayi miki albarka"
"Ameen" ta amsa, wutan na kamawa taja hannun Mamin ta suka zauna kan tabarma sannan ta shiga wani d'aki ta fito rik'e da wani magani a hannun ta, zama tayi kusa da Mami tare da d'ago fuskar Mami ta matso wnn maganin Penicillin ta shafa mata a zagayen idanun ta inda sukayi bak'i da alama shaidar duka ne, tana gama shafa mata ta mik'e da sauri zata bar gurin, cikin sauri Mami ta rik'e hannun ta, juyawa tayi ta kalla Mami, hawayen da take b'oyewa ne suka zubo, Zaunar da ita Mami tayi tana girgiza mata kai Alamar kar tayi kuka.
Ai ko kamar jira take ta fashe da kuka cikin kuka take cewa"Mami na har sai Yaushe zamu daina irin wannan Rayuwar?"
Mami gefen zanin ta tasa ta share mata hawaye "Allah na tare damu Najma, hak'uri zamu cigaba dayi wata rana sai labari"
Ranta a b'ace tace"kullum haka kike cewa Mami sai Yaushe hakan zai zama labari? Meyasa zamu tayin hak'uri?"
Kafin Mami tayi magana ta bar gurin cike da b'acin rai ta shige d'aki, Mami bata bita ba domin tasan ko taje baza ta iya rarrashin ta ba yanzu da take cikin b'acin rai, mik'ewa tayi ta cigaba da aikin ta tana share k'wallan dake zubo mata.
Najma ko tana shiga d'aki ta saki kuka mai k'arfi, ta jima tana kuka sannan ta cire uniform d'in ta tasa wani doguwar riga na atamfa, ta fito tsakar gidan, Wata mata ce zaune tana gyaran zogale, straight Najma gurin ta taje ta zauna tana taya ta, tana cewa "Tsohuwa mai ran k'arfe"
Inna kenan kakar Najma, turo d'an kwalin kanta tayi tace"Fad'i ki k'ara y'ar nan, sai naga y'a y'an ki"๐
"Nidai ki mutu inci gumba, kinci zamanin ki muma kina so kici namu zamanin ne"๐
Mami dake zaune dariya tasa domin ta saba da irin wannan hiran na Najma da Inna.
Mami ne ta d'auko abinci ta ajiye ma Inna a d'aki sannan tace Najma tazo suci nasu.
Turo baki tayi tace"Mami ni banci tunda baki rarrashe ni ba"๐
Inna dariya tayi"Karki rarrashe ta d'in ki kyale ta"๐
"Ke kuma Inna ina ruwan ki damu ne?"๐ cewar Najma.
Dariya Mami tayi yayin da Najma ta d'auko musu abinci suka fara ci cike da k'aunar junan su, bayan sun gama ta kwashe kwanukan tayi wanke-wanke sannan tayi alwala tayi sallah la'asar, tayi shirin islamiyya, light green d'in hijab tasa, yayi mata kyau, tayi ma Mami da Inna sallama ta tafi, gidan su Yusra ta shiga, dai-dai lokacin ita ma ta fito cikin shirin tafiya, wucewa islamiyya sukayi.
Sai k'arfe 6:00pm suka tashi, a hankali suke tafiya har suka shigo unguwar tasu, tun daga nesa suka hango yanda Samari suke zaune a k'ofar gidan su Yusra,
Yusra ce tace"Da alama Yaya *MUHSEEN* ya dawo dan na hango abokanen shi"
Wani irin Murmushi namusaman ne na gani d'auke a fuskar Najma har dimples d'in ta sai da suka lotsa "Ya Muhseen ne ma dan yace ai ba zai wuce week d'in nan ba"
Dariya Yusra tayi kafin tayi magana suka hango shi yana nufo su. Kyakyawan saurayi mai jini a jika, wankan tarwad'a ne fuskar shi na d'auke da saje,dogo ne mai d'an jiki, murmushi yake har ya k'araso inda suke.
"Ya Muhseen barka da dawowa" cewar Yusra
Da fara'a ya amsa"Yauwa sisi na, ya kike?"
Amsawa tayi tana kallon yanda Najma ke ta faman zuba murmushi,
Kallon Najma yayi "Beauty nah hope na same ki cikin k'oshin lafiya?"
Sunkuyar da kai tayi"Alhamdulillah ya aiki?"
"Fine Beauty na, ke meye kika tsaya kina kallon mu" yace ma Yusra wacce ta k'ura musu ido.
Dariya tayi"Uhm kaji lovers nidai na wuce gida"๐
Kallon Najma yayi tare da mata sallama ta wuce gida akan sai yazo da daddare, dan yaga yanda abokanen shi suke faman kallon mai Beauty'n shi.
Bayan sallan Magriba Najma na zaune a parlour tana duba Wasu litafan makaranta, yayin da Mami ke zaune a kujera, buga k'ofar parlour'n akayi Wanda sai da gaban Najma ya fad'i, kasancewar lokacin sauro ne shiyasa suke rufe k'ofa, kallon juna sukayi ita da Mami sannan Najma ta mik'e ta bud'e k'ofar.
Shigowa yayi yayin da Najma tace"Sannu da zuwa Abba"
Ko kallon ta baiyi ba ya nemi kujera ya zauna, a ranta cewa tayi dama bai dawo ba!
Mami cikin rawar jiki tayi mai sannu da zuwa, taje ta kawo mai abinci.
"Dan wulak'anci ina ta buga k'ofa kunyi banza dani koh?" Cewar Abba.
Najma tace"kayi Hak'uri Abba"
"Kayi hak'uri ba muji bane" inji Mami
"Ku rik'e hak'urin ku ban so"
Shiru sukayi yayin da Najma ta cigaba da duba litafin ta,
Tsaki Abba yayi"Kin wani Tara litafai a gaba sai kace abin arzik'i, a wannan k'wakwalwar kifin naki har abada babu abin da zaki gane!"
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata, Mami ko shiru tayi har ya gama ya bar parlour'n.
Kamar jira Najma take ta fara kuka, Mami ta k'arasa kusa da ita ta rungume ta tana shafa bayan ta,
"Mami meyasa Abba ya tsane ni haka, meye ne nayi mai a Rayuwa, meyasa yake jifa na da mugayen kalamai? Nifa y'ar shi ce" ta fashe da kuka.
Mami share hawaye tayi "a kullum ina k'ara miki nasiha kome zaiyi miki kiyi hak'uri dan shi MAHAIFIN ki ne, a Rayuwar nan komai mai wucewa ne, bana son ki k'ulaci mahaifin ki a rai"
Shiru kawai Najma tayi zuciyar ta na mata zafi.
_________________
*Adamawa State*
*Barikin sojoji*
Tafiya yake cike da izza irin na jaruman mazajen nan, Kyakyawan Saurayi mai tashen kyau asalin bafulatanin Adamawa, dogo fari tass mai d'auke da siririn saje kewaye a fuskar shi Wanda yake d'auke da sexy eyes da red lips, yana da d'an jiki dan baza a kira shi ramame ba yana da fafad'ar kirji, Sanye yake da kakin sojoji yana tafe ne fuskar shi a d'aure babu alamun dariya, Wasu sojoji ne majiya k'arfi ke take mishi baya suna d'auke da bindigogi, *CAPTAIN SAIFUDEEN ALIYU SULTAN* Kenan cikaken soldier.
Da sauri wani Soldier ya bud'e mai k'ofar mota ya shiga sauran kuma suka shiga wata motar, yayin da driver yaja suka nufa wani Unguwa, da ganin unguwar kunsan na manyan masu kud'i ne.
Bud'e mai k'ofar sukayi ya fito tare da yin mai salute, a hankali yake tafiya har ya isa parlour'n gidan. Masha Allah nace domin gidan ya tsaru iya tsaruwa, Wata mata ce hakimce a kan kujera hannun ta rik'e da Newspapers, karasawa yayi ya zauna kan kujeran dake facing d'in ta, cike da ladabi da biyayya ya gaishe ta, cire medicated glass tayi fuskar ta cike da fara'a ta amsa tana tambayar shi ya gurin aikin nashi.
Da gudu wata kyakyawar budurwa ke saukowa daga upstairs tana cewa"Welcome ya *Saif*"
D'aure fuska yayi ba tare da ya amsa ba, Ummi ce tace "Sister'n ka na gaishe ka"
A hankali ya amsa kamar baya son magana, ita ko ko a jikin ta dan ta saba da halin yayan nata na muskilanci, Mik'ewa yayi ya nufi part d'in shi, sai da ya shirya yayi sallah magriba da isha'i sannan ya nufa cikin gidan, Gaba d'ayan su sun hallara a dining table domin fara dinner, karasawa yayi ya gaishe da Daddy'n shi yayi ma Ummi barka da dare sannan sukayi dinner, bayan sun gama ne Daddy yace yana son ganin shi a parlour'n shi, yana tafiya Saif ya bi bayan shi, da sallama ya shiga parlour'n, sun d'an tab'a hira irin na d'a da Uba sannan Daddy ya gyara zama ya fara magana.
"Son by now ya kamata ace ka ajiye iyali, Alhamdulillah tunda kana aiki kaga sai kuma maganar aure ko, ya kamata ka fito da matar aure"
Sunkuyar da kai kawai yayi domin a Rayuwar shi ya tsane ayi mai maganar aure cause har yanzu bai samu wacce yaji yana son ta ba, shi mata basa gaban shi ma kwata-kwata,
"Kaji abin da nace dai dan haka kayi tunani ka samo mace ta gari, Duk sa'oin ka sunyi aure saura kai"
A hankali yace"Insha Allah zanyi tunani domin kuma in faranta muku rai"
"Toh Allah yayi muku albarka"
"Ameen" yace suka cigaba da hira.
*Wace ce NAJMA?*