FreeArewaPen original
MAHAIFIYA TA
- 1views
- 17chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Ina Alfahari da kasancewa ta Marubuciya
Sample · CHAPTER ONE
MAHAIFIYA TA*🌹 *{A Romantic &Loving story of a nice Family}*💍 *NA**UMMU BASHEER**REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *{We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of readers}* ✨ *Devoted*✨ *To* ✨ *All Mothers in the world*✨*Page 1~5* *{My Beloved Mother}**Gurin* cike yake da d'alibai y'an makaranta da alama tashin su gida kenan kowa na nufar hanyar da zai sadda su da gidan su, wata kyakyawar budurwa ce na hango sanye take da dark blue and White uniform, fara ce mai d'auke da daradaran idanu farare tass, kmr madara, bakin ta d'an k'arami dai-dai da fuskar ta, tana da eyelashes da eyebrows masu cika, tana da tsayi dai-dai ba sosai ba, fuskar ta a yamutse ta kalla wristwatch d'in dake mak'ale a hannun ta mai kyau tayi, ganin har 2:20pm yayi yasa ta juya ta fara tafiya tamkar tana tausayin k'asa, tafiya take cike da natsuwa da kamun kai, tun daga nesa take jin ana k'wala mata kira sanin ko wace ce yasa bata tsaya ba." *NAJMA NAJMA NAJMA*" wata budurwa ce ke fad'in haka tare da nufan wannan budurwan na d'azu.Wacce aka kira da *Najma* tsayawa tayi ba tare da ta waiga ba cikin sanyin murya mai cike da shagwab'a ta fara magana "For God sake Yusra har sai Yaushe zaki daina b'ata min lokaci idan mun tashi bayan kinsan idan lokaci yayi bana son ko k'ara one minute ne ban tafi ba"Yusra ce ta dafa Najma tare da fad'in "Kiyi hakuri Aminiya na tsaya karb'an wani text book nane gurin Ummita"Murmushi Najma tayi har sai da dimple d'in ta suka lotsa, wayyo fan's zo kuga yanda tayi kyau, "Ba komai Aminiya mu tafi kar mu b'ata lokaci"Nan suka nufa hanyar unguwar su suna tafe suna hira, dai-dai wani gida Yusra ta tsaya tayi ma Najma sallama, sannan Najma tayi gaba gida uku ke tsakanin su da Yusra, wani d'an madaidaicin gida na k'asa Najma ta shiga bakin ta d'auke da sallama.Wata kyakyawar Mata ce gaban murhu tana iza wuta, da kun ganta zaku gane MAHAIFIYAR Najma ce saboda tsananin yanda suke kama da juna, Da sauri Najma ta ajiye jakar ta, tare da nufan MAHAIFIYAR TA, karb'an Maficin tayi ta fara fifita tana cewa *MAMI NA* shiyasa nake ta sauri in dawo domin ki huta"Murmushi Mami tayi tace "Allah yayi miki albarka""Ameen" ta amsa, wutan na kamawa taja hannun Mamin ta suka zauna kan tabarma sannan ta shiga wani d'aki ta fito rik'e da wani magani a hannun ta, zama tayi kusa da Mami tare da d'ago fuskar Mami ta matso wnn maganin Penicillin ta shafa mata a zagayen idanun ta inda sukayi bak'i da alama shaidar duka ne, tana gama shafa mata ta mik'e da sauri zata bar gurin, cikin sauri Mami ta rik'e hannun ta, juyawa tayi ta kalla Mami, hawayen da take b'oyewa ne suka zubo, Zaunar da ita Mami tayi tana girgiza mat...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.