πŸ§‘β€πŸ¦½πŸ˜­SUN GUJE NI πŸ˜­πŸ§‘β€πŸ¦½

11

by @111922694126240833629

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ˜­SUN GUJE NIπŸ˜­πŸ‘¨πŸ»β€πŸ¦½

(SANADIN CUTAR LAKKA)

IT BASED ON TRUE LIFE STORY.




LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).




Follow this link to join my WhatsApp group: ***





*Shafin nan na ki ne my sweet zee-zee ina nufin Zainab ta SUN GUJE NI fans group,albarka da alhairin Allah ya Kai gareki love you my sweet daughter😘πŸ₯°πŸ˜*




SHAFI NA GOMA SHA D'AYA.





KUNDIN KADDARA.




Nan Umman mu ta dinga sa Ra'isat na zuwa gaisuwa a gidan su Yusuf duk Juma'a saboda innar su Yusuf ta kyasa dan ta san babban burin ta ba ya wuce auren Tilon d'an ta namiji,to ga shi an yi auren bayan innar su Yusuf ita ta duba a matsayin madubi saboda yanda ta ga ta ke rayuwa cikin tarbiyya da yi ma Allah da'a saboda nagartaccen tarbiyyar da su ka samu daga Mahaifin su,


Amman a yau ita Umman su ke ma gori tare da kwance mata zani a cikin kasuwa?


Murmushi kawai ta yi Wanda ya fi kuka ciwo ganin za ta d'aura ma kan ta ciwon tunani da damuwa ya sa ta mike ta cigaba da sabgogin ta.



WANENE YUSUF(BAFFAYO)?

  Yusuf Muhammad Sani Haifaffen garin Bauchi ne a wata unguwa da ake kira Tudun wada,ya taso ne a hannun nagartaccen uba Wanda ya tsayu kyam akan y'ay'an shi da tarbiyya tare da sa Ido Dan kakan Yusuf babban Malamin addini ne Wanda ya Tara almajirai,Malam Sani shine d'a namiji na farko a gidan su Yana da matar aure guda 1 wacce ake kira Hauwa Kulu Wanda ita ce mahaifiyar su Yusuf,duk da kasancewar Kakan Yusuf Malamin addini Amman hakan bai Hana shi Sanya y'ay'ayen shi mata da Maza a boko ba dalilin hakan ya sa za ka ga rayuwar wannan ahalin cike ta ke da ban sha'awar.

 Mahaifin Yusuf Direban babban mota ne na mai dan aka iyalan shi ke zaune cikin rufin asiri, innarsu Yusuf kowa ta na sana'ar sai da kayan Miya na gida,su takwas ta Haifa yayun Yusuf biyu mata sai shi ya zo ana uku sai kannen sa 4 Maza,autar su mace.

 Yusuf ya yi makarantar firamare da sakandire du ka acikin garin Bauchi,Yana daf da kammala karatun shi na sakandire ya had'u da wata d'aliba Wanda su ka fara Gina tsaftatacciyar soyayya suna kammala wa aka nemi ya fito amman sai aka samu akasi saboda a wannan lokacin Mahaifin sa ba shi da k'arfi motar da ya ke ja tunda ta b'aci shikenan ake rayuwa cikin taskun rayuwa Sanadin hakan ya sa aka aurar da wancan yarinyar,


Ganin yanda iyayen sa ke rayuwa cikin k'uncin rayuwa ya sa Yusuf mikewa tsaye domin ya tallafa mu su duk da Yana da burin yin karatun zamani Mai zurfi Amman sai ya sadaukar dan haka ya je ya nemi sana'ar yaron mota na Tifa,



aka dauke shi aikuwa ko shekara bai yi ba ya iya,ganin kwazon sa da hazakar sa ya sa Maigidansa nema mi shi ta shi motar akayi sa'a ya samu dan haka ya fara da sannu-sannu,cikin hukuncin Allah kuwa

Aka dauke ni ko shekara banyi ba na iya kuma maigidana ya samamin tawa motar da nake tukawa,


Allah Kuma ya sama mi shi albarka Yana samu sosai ganin hakan ya sa Mahaifiyar sa Sanya shi a gaba da maganan aure saboda shine babban d'an ta namiji Kuma ba ta da Wani buri a duniya da ya wuce ta ga auren shi amman ta bangaren Yusuf kwata-kwata soyayya ya fita a ran shi tun da ya rasa Ma'eeshat,ga shi dai dan gayu na karshen lamba amman Yana cin gayun shi ya fito da yamma sai dai ya wuce cinema ya sha kallon sa Sam ba shi da damuwa,


Lamarin da ya d'ugunzuma rayuwar innar shi kenan har ya sa ta zaunar da shi ta bukaci ya fito ma ta da Wanda ya ke so Amman kullum amsar d'aya ne"Banda budurwa Mamana",


Dan haka ta buk'aci ya nema ko Kuma ita ta nemar masa ya ce ya Bata zab'i sanadin hakan ta nema mi shi Ra'isat y'a a gurin k'awar ta Tabawa saboda yanda ta ga su Ta-sallah sun samu kyakykyawan tarbiyya daga gurin Mahaifin su sai ta mi shi kwadayin samun zuriya daga wannan tsatson,


Da farko da murna Yusuf ya amince ma ta ko da ta sanar mi shi da ta masa budurwa Amman Yana bincikawa ya je ya samu Ra'isat tallan doya da kwai ta ke yi ya sa ya nemi janye wa dan ina shi Ina y'ar talla ai Sam ba ajin shi ba ce Amman Yana kawo korafi ma mamar shi sai ta ce ba wannan ne matakin da ya kamata ba,kamata ya yi ya raba ta da tallan tare da Sanya ta a islamiyyar tun da ya ce Bata zuwa dan haka sai ya yi na'am da wannan shawarar amman ko da ya Sanya Ra'isat Sam ba ta zuwa Amman ba tare da sanin shi ba,


Sannan da ya tsananta bincike dangane da tarbiyyar Ra'isat ya gano sam ba ta da kunya duk da a lokacin har an Kai kud'in sadaki da na gaisuwa Amman haka ya ce ya fasa Amman mamar shi ta yi ruwa ta yi tsaki har sai da ta tabbatar da an sa Rana dan da Neman har zuwa yin auren kwata-kwata Bai wuce wata takwas ba,


Dan Yusuf ya fuskanci sam-sam ba tausayi ba imani a lamarin su Ra'isat dan har kayan lefen da aka kai gidan su sai da su ka ciccire zannuwa da ya fi biyar da sunan za'a Bai wa yayun ta mata,


Kud'in dinki da na Walima ma da ya ba ma Ra'isat Umman ta karb'ewa ta yi Koda ta k'ara tambayar sa wasu kud'in ana gobe biki Hana ta ya yi nan ma ya k'ara ta-da ballin ya fasa sai da kyar aka shawo kan sa ya amince aka daura mu su aure Wanda ya zama shine tushen dukkannin wata matsala da ya ke ciki yanzu.


Dawowa kan Asalin labari.

 Yusuf wanda cutar zazzab'in sauro da typoith ya yi ma mugun kamu a Yan kwanakin nan yana zaman gida saboda Sam jikin ya k'i warware wa,


Sababbin halayen Ra'isat ya k'ara fitowa Fili a gareshi dan haka damuwa ya yi ma sa mugun yawa saboda ba bu Wani kulawa da ya ke samu daga gare ta duk da innar shi na shigowa kullum tana Kuma lura da yanayin zamantakewar na su da matar shi Amman hakan Sam Bai sa ta ji zuciyar ta ta rissina ba sanadiyar hakan ya sa Jinin Yusuf ya yi mugun hawa ga ciwo ga damuwa dan haka ko da ya koma ganin likita dokar Hana shi cin mangyada aka Sanya mi shi tare da magungunan da za su dinga Sanya shi bacci,


Yana komawa gida ya sanar ma Ra'isat dokokin da aka Sanya mi shi Amman bud'ar bakin ta sai cewa ta yi"To ni kam wallahi babu Wani k'aton da ya isa ya hana ni cin abincin da na yi niyya in ban da shegen iyeyin tsiya me shi mangyadan zai k'ara ma ciwon na ka Banda karyan banza da wofi",


"Kuma wallahi matuk'ar ka siyi ruwan gora a gidan nan da sunan ruwan Shan ka tare da ni da kai za mu shanye tun da nima ba daga itace aka sassak'oni ba",


Shiru ya yi ma ta Yana mamakin halin Ra'isat mutum ace har ciwo bai ragar ma sa ba to me zai sa ta yi sanyi ita kuwa a rayuwar ta,


"Mutuwa"cewar zuciyar shi Amman ko ma mutuwar tababa ya ke yi dan rashin imanin ta ya yi yawa matuk'a a gare shi.

 Aikuwa ba ta canza zani ba kullum kamar yanda ta saba haka ta ke girkin ta da mangyada idan yagadama ya ci in ma kashe sa zai yi ya yi ita dai Babu ruwan ta sai innar shi ne mai kok'arin ganin ta samar mi shi da abin da zai ci a kullum har ya dan fara samun lafiya amma zuciyar shi na nan kullum cikin jinya da tunanin mafitar da ya kama ce shi,


Kwatsam wata-rana Wanda ya kasance shine tushen rugujewar walwalar shi da ta masoyan shi ya gamu da babban kaddara,kaddarar da ya Sanya mutanen da ya fi kusanci da su su ka GUJE SHI tare da nuna mi shi halin Yan Adam na rashin tabbas.

 Rana ce da ba zai Yu ya manta da shi a tsarin kundin rayuwar shi ba,Dan ya zamto rana mafi Muni daga cikin ranar da ya riska acikin tsawon rayuwar shi.....




Shin wace Rana ce wannan Fans😭ku taimaka da sharhi zazzafa sannan Kar ku mance da wannan labarin ,labari ne da ya faru da gaske ba zai yu sharhin ku ya kunce faruwar wannan kaddarar ba akafta.








Sorry for the late update oga na gida ayyuka na min yawa Amman duk da haka....More comments......More typing.














Ummu-jiddah.