12
👨🏻😭SUN GUJE NI😭👨🏻🦽
(SANADIN CUTAR LAKKA)
IT BASED ON TRUE LIFE STORY.
LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
*Wannan shafin na ki ne Husna Aliyu lawan ki na daga cikin masoya na musamman Wanda bai yuwa in mance irin fashin bak'in da ki ke ma wannan labari tabbas sharhin ki na k'ayatar da ni had'e da ba ni karfin gwiywa Ina godiya🥰.
SHAFI NA GOMA SHA BIYU.
Rana ce da ba zai Yu ya manta da shi a tarihin kundin kaddarar shi ba,dan ya zamto rana mafi muni daga tab'a riska a tsawon rayuwar shi,
Rana ce da Ra'isat ta tashi ba ta da lafiya duk da yanzu alhamdulillah shi ya ji sauk'i shi amman a tsatstsaye ya ke gudanar da harkokin sa saboda Jinin shi da ya hau,
ganin ta a kwance ba lafiya ba karamin tashin hankali ba abin ka da mai zuciyar Imani,nan hankalin sa ya d'ugunzuma ya tashi dan haka ya d'auke ta kai tsaye zuwa asibiti mafi kusa da gidan su ,nan aka yi mata duk gwaje-gwajen da ya kamata, likitoci su ka tabbatar da samuwar ciki a jikin ta,
Murna a gurin ta abin sam ba ya faduwa,innar mu ma ko da ta ji wannan kyakykyawan albishir d'in nan ta ke ta zubda makaman ta ta fara ba ta kulawa na musamman,anan ta k'ara bud'e sabon shafin rashin mutunci ga kowa tunda a ganin ta yanzu za ta samu kaina.
ba laifi Yusuf ya yi murna sosai da samuwar cikin da ke jikin ta duk da zuciyar shi na tunanin wannan abar ba ta cancanci zamto wa uwa a gurin y'ay'an shi ba amman sai ya sa a cikin zuciyar shi wannan rubutaccen k'addara ne Wanda Allah ya k'addara mi shi na auren Ra'isat Dan haka sai dai hakuri da Kuma tsananta addu'a ko Allah zai jik'an shi ya bashi Y'ay'a nagari,
Da wannan tunanin ya sa ya cigaba da ba ta kulawa gwargadon iyawar shi duk da Shima ba lafiyar ke gareshi ba amman a Hakan ya ke kokarin ya kyauta ta ma ta sai dai duk abin da yi mata sam ba ya gwanin ta,a Rana sai ta girka abinci sama da kala biyar idan ta ci spoon 1 ta ji bai yi ma ta ba sai dai ta zubar ko Kuma ta kira yaran yayar ta da ke kusa da mu ta ba su ,duk da kyakykyawan gargad'i da Ta-sallah ta mu su akan shigowa gidan gurin k'anwar ta amman sam yaran na zuwa Kuma Yana ji yana gani ta ke kyautar mi shi da abinci ba tare da ta bashi ya ci ba ,Dan tun ranar da likita ya Sanya mi shi dokar hanashi cin mangyada Ra'isat ta daina amfani da manja dan ta ce" ba ta ga shegen da ya isa ya sa ma ta doka ta bi ba"ko da Yusuf ya yi magana zancen dai daya ne akan ya yi hakuri cewar innar shi,ita kuwa oganniyar ganin yanda innar Yusuf ke ba ta kulawa na musamman sai ta bud'e sabon shafi ba ta san albarkacin ta na dauke da jikan ta na farko ta bangaren babban d'an ta namiji ta ke ci ba tuni ta fice ma kowa a rai,
Tun daga lokacin da ta samu cikin matukar ka ga Yusuf ya ci abinci to innar su ce ta girka ta bashi amman bai isa ya ci na cikin gidanshi ba in Kuma zai ci to dole ya bi k'aidar matar gidan ya mance da na likita,
A dah sam bai damu ba amman ganin yanda ta ke facaka da Madara,bornbita,kwai da su Naman da na ke siyowa ta saci na sata ta kai ma uwar ta kawai sai ya ji ya zama dole ta girka ta ba shi yaci dan ya gaji da ciyar da katuwa tare da fita siyan abinci kullum gashi Kuma ba wadatacciyar lafiya ke gare shi ba,
dan haka ya kafa mata sharuddan yin girki da shi dan a lokacin ba bu laifi ta fara iya girkin saboda yanmata na makota da yaran yayar ta da ke cika gidan suna ta ya ta aiki dan haka tuni ta goge kazantar dai na nan amman ta bangaren girki an samu canji,
So ko da ya kafa mata sharadin yin girkin da shi kullum da mangyadan ta ke girki in ya yi magana ta ce manja na sa ta amai alhalin in ta tashi soya wainar fulawa da kwai yana kallon ta da manjan ta ke soyawa Dalilin hakan ya sa jikin sa kullum ba lafiya har a ranar da mummunar k'addarar ta same shi acikin Wani yammaci da ya fita da mashin d'i sa vesfa wanda a lokacin mallakar ta sai d'an wane da wance,
Lamarin ya faru ne bayan sun yi kaca-kaca da Ra'isat dangane da rashin mutuncin da ta ke ma yan'uwan shi in sun shigo wajen shi,a ranar albarkacin cikin da ke jikin da ta kawai ya hana shi yi ma ta dukan da za ta gagara motsi dan haka ya figi mashin da niyyar ya fita ko zuciyar sa za ta samu salama ashe-ashe kaddara ta ce ke kiran shi,
Kana ganin yanda ya ke tuk'in ka San ba bu nutsuww a tattare da shi dan ko gaban shi ba ya gani tsabar yanda tunanin hatsabibiyar matarshi ya yi mi shi katutu nan wani Keke(adaidaita sahu)ya shawo kwana ba tare da lura da wadanda ke zuwa ba nan ya dauke Yusuf wanda ke sharara gudu nan Mai afkuwa ya afku Dan ya samu mummunan buguwa a wuya nan da na aka dauke Yusuf da ke kwance magashiyan zuwa babban asibitin da ke garin cikin bauchi rai a hannun Allah dan ban ko san in da kan shi ya ke ba bai yi ba sai surutai ya ke yi Wanda ke nuna Yana cikin matsanancin hali,
Kasancewar Yusuf mutum sananne acikin garin Bauchi ya sa ko kafin a kai shi Emergency akwai Wanda ya waye shi Kuma har ya je ya sanar da Innar mu wannan mummunan sak'o,
Labarin ya riske ta a bazata dan ya bar ta ne zaune tana k'ulla Yan kayayyakin ta na saidawa ta ji bugun mashin din na sa Amman Kuma ace ma ta ya yi hadari Yana asibiti,
"Yanzu-yanzu fa yarona Yusuf ya fita" ta mik'e tsaye tana mai fad'in hakan cikin mugun tashin hankali Jin ya tabbatar ma ta da faruwar lamarin ya sa ta fasa kuka tana maimaita Kalmar nan ta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" a d'imauce ta lalubi gyale ta nemi hanyar fita har tana cin karo da Garu Amman ko Jin zafi ba ta yi ba ta ta fi,
Ra'isat wacce ke lab'e tun da ta ji sallamar mutumin nan ta na sauraron duk abin da ake cewa ko a jikin ta hasalima cewa ta yi"Allah ya k'ara ya d'auka ni d'in ta wasa ce?
"Yanzu ma aka fara wasan"
nan ta cigaba da sabgogin ta har da y'an wake-waken ta tana yi tana shewa tsabar dad'in da ta ke Jin Yana surga ta,(bangaren Innar Yusuf kuwa ta k'i sanar ma ta ne saboda yaron cikin da ke jikin ta dan Sam ba ta son abinda zai tab'a shi,ba ta san sahoramar tana Jin komai da ke faruwar ba hasalima murna ta ke yi).
Innar Yusuf kuwa tun a hanya ta ke Rusa kuka har idon ta ya kumbura dan haka duk Wanda ta had'u da shi ya tambaye ta sai ta fad'a mi shi wannan mummunan kaddarar da ta afka ma Yusufun ta, nan da nan matasan cikin unguwa,manya da kanana su ka cika asibitin tare da yan'uwa dan tuni an bubbuga mu su waya amman kowa ya je sai dai ya dawo da kuka saboda irin sumbatun da Yusuf ke yi na zafin ciwo,
Fad'in tashin hankalida yan'uwa da abokan arziki su ka shiga ma b'ata lokaci ne,dan acikin kwana uku rak in ka ga yanda innar Yusuf ta koma sai ta ba ka tausayi sam-sam ba ta runtsawa,ba ta iya cin abinci Banda sallah ba bu abin da ya ke tasar da ita daga bakin k'ofar da aka ajiye shi dan tana iya hango shi ta d'an Wani huji kwance magashiyan an Sanya mi shi neckcoler(abin da ke rik'e wuyan mutum).
Tabbas da kuka na magani da ya Dade da warkar da Yusuf dan ko Mahaifin shi sai da ya koka duk k'arfi zuciya irin na namiji ,saboda yanda ya ga Yusuf dauke da neckcoler dan asibitin sun ce wuyar shi ya karye,
Cikin zuciyar shi ya ji cewa k'ashin bayan shi Wanda ya rumgumi katangar gidanshi da ke niyyar rushewa Yana Shirin barin duniya Dan tabbas Yusuf d'a ne nagari ya tallafi rayuwar ahalin sa,wannan dalilin ya sa ya rasa dukkannin wani k'arfin gwiywar dan haka Shima kullum cikin kukan zuci ya ke yi musamman da ya ga asibitin ba Wani kulawa na musamman su ke ba Yusuf din ba,
duk wannan matsanancin halin da ake ciki Ra'isat Sam ba ta girgiza ba dan ko da aka ga yanda jikin na shi ya ke bayan innar su Yusuf ta je asibitin dole ta sa aka je aka kawo matar sa dan Babu Wanda ya yi tunanin Yusuf zai k'ara ko da kwana 1 a duniya saboda Sun ce wuyar shi ya karye Kuma babu wani alama da ke nuna sai rayu Dan likitocin da kan su sun kawar da Kai da lamarin na sa dan haka ba ta shi su ke ba dan haka,
Amman sam Ra'isat tamkar ba zuciya ce a jikin ta ba dan ba bu wani tausayi ko shiga Wani hali da ta yi ita hasalima zaman asibitin gundirar ta ya yi saboda ba ta samun damar yin girke-girken ta na banza da wofi da ta saba a kwanaki ukun farko da mijin ta ke cikin comma(tsakanin rayuwa ko mutuwa)dan Umman ta ko da ta zo ta ga halin da Yusuf ke ciki murna ta ke dan ta tabbatar da Yusuf ba zai k'ara ta ka Doron k'asa ba karshen shi ne ya zo dan haka ta yi ma Ra'isat famfo sosai tare da daura ta akan mummunar hanyar da ta ke tunanin shine hanya mafi sauk'i da za su samu cikar burin su.
A cikin kwana na ukun Yusuf ya..............😭😭😭
More comments......
More typing......
U
mmu-jiddah.