8
by @fadimafayau
Binto
8
Wayar tace tai ƙara alamar kira na shigowa jin kiran nata faman shigowa yasata tsayawa ta ɗaga ganin me kiran ne yasa ta ɗan murmusawa gami da ɗagawa kamar me wayar na ganinta ta ɗan rissina gami da faɗin sir ina kwana ya amsa cike da jin daɗi kinfa makara tuni ina class karki shigo kiso kina min kuka kisani kuka nima gaban students innalillahi tahau kira gami da Allahumma ajirni seda ya bari ta gama sannan yadanyi dari.
Sarkin tsoro ina bayanki waye ya sauke ki wata ajiyar zuciya ta saki yaya nane ok Kabir a'a mansur ko Ɗaha a'a Isma'il eyya na kusa taddoki inna rigaki shiga bansanki ba bata jira cewarsa ba ta kashe wayar tai class ya yai murmushi yabi bayanta.
Zaune suke suna hira ita da su Maryam dan tuni malamin ya fice wayarta ce tau ƙara ta ɗaga ga mamakinta sunan yah Isma'il ke yawo kan screen ɗin wayar tama mance tana da wayarsa.
Sallama ta fara yi aɗan gajarce ya amsa sallamar dan wulaƙanci kinaji ina kiranki shine kika ƙi ɗagawa to ni nace a kirani ta faɗa ahankula me kika ce oho tace lallai yarinyar nan ni nama rasa inda kika koyo rashin kunya cikin ƙunƙuni tace inda aka koyo faɗa tsaki yaja kinga bana kira ki dan ki ɓatan rai bane in kin tashi tafiya ki nemi Captain ɗinku zai baki saƙo bai jira cewarta ba ya kashe wayarsa.
Ita kam ko kaɗan bata jin daɗin abinda yah isma'il ke mata kawai tana ɗan dannewa ne tana nuna masa bata damu ba.
Tana fitowa daga masallaci suka ci karo da mansur yawwa ke naketa nema mijinki yabani saƙo tai dariya yaya ne ba mijina ba shima dariyar yai oho ina nasani cewa yai ga makullin mota nan tana inda ya sauke ki ɗazu inzaki tafi gida dariya tai dan sosai taje daɗi dan tun ɗazu tunaninta inda zata iya bin layin mota da kuma zuwa gida daga kabuga.
Godiya sosai taima mansur kai kace shi ya kawo motar tasan halun isma'i' inta kirashi ma ba ɗagawa zaiyi ba "Nagode" shine abinda kawai ta tura masa.
Yau kam ko makaranta Binto taƙi zuwa tun safe take ta shirye shirye dan yau yan bording zasu dawo za'a bada hutu farin ciki ne fal ranta zata ga ɗiyarta salma danma mami ta hanata da tuni take ta ɗauko abarta dan ta ce ita tama fasa barinta tai ta kwanan.
Wajen tara suka fito tsaf ita da yaranta da zummar tafiya ɗaukota sedai Bala driver ke faɗa mata ai an tafi ɗaukota bata buƙaci jin waye ba ta koma ciki dan bataji dadi ba ko kaɗan taso taje da kanta sedai ba yadda zatai ko banza taɗanji daɗi aƙallah agidan akwai wanda yake damuwa da rayuwar ta da yaranta tunda ba'a manta da randa zata dawo ba.
Batafi minti ashirin da komawa ba salma ta shigo da mamaki sosai ya kama Binto har andawo sukaita murna seda aka gama murna sannan Salma tasa kuka haba ɗiyar albarka mene na kuka kuma bacin farin ciki zakiyi anyi hutu zaki ganmu.
Ummanmu ba ke bace tunda na tafi baki taɓa zuwa ba akwai visiting day ma baki zo ba kowa ummansa taso anman ni da Abba be zoba shi kenan bani da kowa gaban binto ya faɗi tahau innalillahi se yanzu ta tuna wai ana zuwa visiting itaman batasan tsarin bording sch ba kwata kwata anya kuwa wannan uzuri be ta faɗa anya naima Tsalha adalci anya na riƙe amanar da ya ban kawai saita fashe da kuka.
Ganin haka yasa salma ta hau rarrashinta ita zatonta ita tasata kuka tahau bata haƙuri wallahi ummanmu bazan sake kuka ba dan bakizo ba daman Abba ya faɗan abunuwa suka miki yawa ita dai Binto kukanta kawai take ba ƙaƙƙautawa.
Isma'il ne ya shigo riƙe da jakar salma yo ke banda shirme haka ake ko parker mota banba ki fito aguje ta miƙe cikin hawa Abbanmu dan Allah ka baima ummanmu haƙuri kace nadaina kuka yadan dubi Binto ta daketa faman kuka ya ɗauki yan Muhammad ya miƙawa salma ya ɗauki me sunansa yaja hannun kairat muje ku ƙyaleta seda ya kaisu Bangaren sa sannan ya dawo.
Wai malama mene haka ne kawai zaki saka yara agaba kiyi ta kuka bafa masan shiririta inza'a san angirma asan angirma yanzufa ki kalli sallama ko ita kika kalla aikinsan ke ba ƙaramar yarinya bace aƙallah kina da budurwa agabanki wani takaici ya ziyarce kuka ya kuma kwace mata Allah mutumin nan ya rainata miƙewa tai tayi ɗakinta dan ita kam yanzu zata iya zaginsa inta biye masa.
Sai yamma su salma suka dawo gurinta sunyi fes dasu se ayanzu maganganun isma'il suka dawo mata tabbas yarinyar ta girma ta kuma zama mutun dan tana da garun jiki tafi wasu sa'annin nata da yawa girma ta kuna hankali nutsuwa ta kuma shigarta.
Tun ɗazu ake baima Binto labarin sch da yan sch da yadda duk wata sai Isma'il yaje ya duba Salma daɗi duk ya cika Binto abinda ya dace ita tayi yake yi itakam ko ada tasan bayan iyayanta bata da ya yayanta me santa ta rasa me tai masa yanzu ya tsaneta.
Wayarta ta ɗauka ta rubuta saƙo ta tura masa Salma ta faɗan mungode yafi awa biyu da tafiya saƙon se can aka turo "badan ke nayi ba bans buƙatar ki ƙara cewa komi dan naima yarana wani abu bas" Saƙon nasa ya bata haushi anman ko ba komi ya bata amsa bakamar da da yake nuna bema gani ba.
Zaune take tana chat ita da sauran mutane saƙon prof. Ya shigo me kike ne fatan de karatu ake ta tura masa alamar murmushi zadai ayi ina hutawa ne ok yayi kyau yaushe zaki bamu lokaci ne zamuzo nida madam da wasa taɗauki batun koma yanzu ne ai ba laifi kuzo ok shikenan bamu awa biyu.
Bata wani ɗauki abin da gaske ba kitso take ma salma dan jibi take so su je ƙauye dan kaima dangin tsalha tsiyara wata sanyayyar murya ce tai salma da sauri binto ta ɗago dan muryar tai mata daɗi murmushi matar ke mata itama ta maida mata shigo mara mara binto ke faɗe duda bata gane taba sedai taso tasan fuskar.
Salma ce ta kawo mata lemo suka gaisa sannan Binto tace sedai kuma ban shaidaki ba tai murmushi eh fa bazaki sannin ba Sunana Safinat matar Salim Binto taɗan waro ido alamar mamaki ya bayyana afuskarta da tsoro har raɗan fara riƙe kuncinta tana jiran saukar mari tasan abinda ya kawo ta kenan.
Ko fahintar hakan safina tai oho taɗan murmusa tare muke dashi yace in shigo mugaisa se muje ku gaisa mu wuce karki damu ya faɗan alaƙarku tinda ya faɗan naji inasanki wallahi ni nake ta masa naci ya kawo ni yaƙi se yau yace kin bada dama ita dai binto kunya duk ta rufe ta ita va abin tace wace alaƙa yace suna dashi ba ita ba abin tace sharri yai mata basu da wata alaƙaba.
Munbar shi awaje kinsan baisan jira inji safinat ok muje inji Binto ta miƙe Muhammad yasa kuka, Walid ma yasa me sunan isma'il kenan Safinat ta ɗaukeshi sukai waje inda aka bar Salma da tattara gurin.
Yana zaune cikin daya daga runfunan da akai dan shaƙatawa na farfajiyar gidan sunata wasa da yaransa da kairi hankalunsa duk nakan yaran kamar ance ya ɗago suka ya ɗora idanunsa kansu Binto da ke tawowa yasakar musu murmushi inda safinat ta maida masa yayinda Binta tai yaƙe kawai.
Kun ganku kuwa kamar wasu ƴan biyu ya faɗa ta dubi safinat dan ganin inda sikai kama Safinat fara ce doguwa me yar ƙiba bacan ba idanunta dedai fuskarta haka bakinta kyakkyawa ce ta ajin farko ita kuwa baƙa me kama da Hausawa itakam Prof zaginta yai basuyi kama ba bare akirasu tagwai safina taimushi ni ai nasa itakam Binto aranta cewa take wannan wane irin mutun ne da zai kwaso matarsa ya kawo gurin mace dan kawai tana student ɗinsa kai lefin ma matar tasa ne da har ta yadda ta biyoshi abinda take ta tunani kenan tun ɗazu wannan wane irin family ne.
Yadda suke ta barkwanci da raha jefi jefi sanins na sawo ta ciki ya bata mamaki sukam ba abinda ya damesu ta faɗa aranta anjima ana fira kamin ya miƙe mu zamu wuce sauran gobe a makara danna sani tai dariya ai tuni na dena makara nide na faɗa kar asake a makara ya ɗauki ƙaramin yaronsa yai gun mota ta bishi da kallo.
Safina ce ta dafo ta to Binta zamu wuce mu karki ɗauki ziyarar mu da wata manufa karki ɗauken mahaukaciya dan nazo gurinki wadda bata da aure kuna mu'amala da miji na nasan me nake kawai haka nake nagode ki kulamin da mijina a sch karki barshi yana kule kule duda nasan ba halunsa bane ta miƙe tana ɗaga mata hannu itakam Binto tama kasa cewa komi.
Tunda suka tafi tama kasa tashi daga wurin tinaninta kawai mene prof yace ma matarsa game da ita da har bataji komi ba ta iya yadda ta biyoshi dan kawo mata ziyara.
Tana zaune tuni tai nisa a tunani se ji tai an ɗauke yaron da ke a hannunta aɗan firgice ta ɗago kabir ne ya sakar mata murmushi matsoraciya kawai to nine tunanin me kike haka na jima a tsaye bama ki ganni ba tai murmushi kawai ina nazarin rayuwa ne yai murmushi Allah yasa dani a nazarin naki.
Ta basar da zancen da faɗin yaushe ka dawo kwana biyu munyi missing inka nida yara daɗi ya kamashi yanxun nan na dawo na hangeki anan na ƙaraso sun ɗan taɓa fira kamin ya miƙe bari in shiga ciki mami taga dawowata ina nan dawowa a haɗamin abinci dan yunwa nakeji ok itama ta miƙe tai ɓarin ta.
Hira suke sosai harda darawa Binto na faɗin Allah kabir baka da dama wannan ai sekasa cikina ya kulle ahto bari in shuru ya faɗa cikin kwaikwayon yadda take magana yadda yai ɗin ya kuma bata dariya wanda yai dedai da shigowar isma'il falon ɗauke da Muhammad daketa kuka.
Binsu yai da ido kamin ya miƙa mata yaron Kabir yace sannu yaya yawwa sannu da shiririta haushi ya kama Binto ko sannun ma kasa ce masa tai banda harara da ta watsa masa yanzu ku kuna ganin ya dace kawai ku zauna kuyita dariya sekace mahaukata eyyi ayi haƙuri baza'a sake ba inji kabir.
Wannan kuma ruwanku inma kun sake yai ficewarsa inda suka bishi da kallo kawai ganin yadda ya fice a fusace kabir ne ya cigaba da bata labarin tafiyar da yai ayayin da ita ko kaɗan tama dena jin daɗin labarin ta rasa me yasa aƴan kwanakin nan kome Isma'il yai mata inta ganshi cikin ɓacin rai se taji itama duk ranta ya ɓaci ji take kamar taje ta bashi haƙuri sedai zuciyarta me taurin rai na faɗa mata babu abinta tai masa kawai de ya tsaneta ne.
Ko fuskantar hakan kabir yai oho ya miƙe bari inje indawo tai saurin kallonsa kai yaya wai harka ƙoshi eh wallahi daman yunwar bata azo agani bace ok tom se ka dawo.
Wayarta ta ɗauka ta kunna Data dan ɗebe mata kewa duk yaran bass gurinta se Muhammad shi kuma yai bacci gashi bata san shiga cikin gida su haɗu da matar Isma'il domin indai suka haɗu seta ɓata mata rai yadda take harar ta wani zubin harda yada magana ta rasa me tai mata take mata haka saƙon ne ya fara shigowa taɗan saki murmushi kamar me saƙon na kusa kamin ta buɗe.
Ya muka barku ya faɗa lafiya lau fatan kunje gida lpy normal yace munfa gode da ziyara ama madam ban gajiya.
Mene kuma na godiya ai mune da godiya da aka yadda muzo alamar murmushi ta tura kin ɗauka da wasa nake zuwan namu ko eh wallahi banzata ba kun shammaceni irin sosai ɗin nan ai yai murmushi da mukai me komi ma banfa yi zaton har madam za'a zo ba yanzu da aka zo da ita ai kin yi zato tai dariya.
Hira suke sosai hakan ya rage mata damuwar da ta rasa ta mece kan kawai Isma'il ya ɓata ransa.
Salma ce ta shigo arazane mamanmu take kira Binto ta fito daga ɗaki arazane lafiya kike kwalamin kira haka aunty bata da lpy muna falo se kukanta mukaji towo muje sukai ɓangaren Isma'il.
Kai tsaye ɗakin da fiddausi ke ciki sukai yadda binto ta ganta ne ya tabbatar mata naƙuda take maza jeki falo yanzu zanfito to Salma tace tai falo hankalinta duk a tashe.
Ganin yadda take yasa binto ta fiskanci haihuwar tazo gab sosai take temakonta sedai ta galabaita leƙowa binto tai falo maza jeki ki ɗaukon zam zam ɗin su walid ki kawon da ajwa kifayi sauri to tace tai waje.
Tana kawo mata ta hada ta mittsike dabinon ajwan cikin zam zam din ta hada da habbatussauda ta tofa mata addu'a ta bata cikin ikon Allah tana sha ƙarfi ya dawo mata bata jima ba ta haifo yaronta Namiji da yake da hankalinta ita ta faɗawa Binto inda su reza sike ta yanke cibiya ta gyare wajen kamin sannan tace salma taje cikin gida ta faɗi haihuwar.
Salma se murna ake daman fatanta anti fiddausi ta haihu kan akoma makaranta ayi suna tana gida tana zuwa mami ta fara faɗawa murna gun mami tama mance sirikarta ce ta haihu tayo ɓangaren Isma'il ɗin kan kace me duk gidan sun tawo gurin me jego ɗin se godema Binto suke da ƙoƙarinta.
Seda aka kintsa baby me jego tai wanka sannan aka ɗaukesu zuwa asibiti dan duba lafiyarsu dan Dr kabir be gida Isma'il ɗinma baya gida.
Message Binto ta Turawa Isma'il Fiddausi ta haifi Namiji yanzu but muna hanya zamu asibiti dan duba lafiyarsu ita da baby .
Bata ko ajiye wayar ba kira ya shigo wayarta nasa ne ta ɗaga kuna wane asibitin ne bamu ƙarasa ba Nasarawa zamu ok kujirani pls ok tace Allah ya raya shi ta faɗa Amin amin nagode ya kashe wayar.
Yadda Isma'il keta nan nan da baby har kunya ya baima binto se kace shi aka farama haihuwa aduniya tace a ranta koda Fiddaisi ta fito komi normal bata samu matsala ba.
Gunta ya nufa ya wani ruƙota ana ta mata sannu ita kuma se wani lallafewa take a jikinsa tana shagwaɓa haushi duk ya rufe binto wanda bata san kona mene ba tama rasa dalin biyosu asibitin.
Ko fuskantar hakan Fiddausi tai oho seda suka zo kusa da Binton ta wani ƙara shagwaggwaɓe swt 💓 ama Binta godiya ita ta amshi haihuwa ta faɗe tana kallon binto tana wani maƙalƙalewa ajikin mijin ta ita ga matar So.
Yai ɗan murmushi ai basai mun mata godiya ba abinda ya ƙamata tayi ne tayi matsayinta na ƙanwar mijinki kuma fa haka muje ko yasa yace da Binto ta taso ta biyosu ranta suk a tunkushe wanda ita kanta haushin kanta takeji na ɓacin ran da rake.
Motar da suka zo da ita ta shige su suma suka shiga ta Isma'il ta jima a cikin motar tana tunanin me ya ɓata mata rai kafin ta tada motar ta bi bayansu.
Suna komawa gida aka tattara kayan Fiddausi se gidansu dan ta tubure ita se an akaita gun mamanta ita acan za'ai suna adole Isma'il ya barta badan yaso ba dan baisan abunda zai rabashi da matarsa da yaronsa.
Tunda prof ya fara lecture take kallonsa bata taɓa tsayawa ta ƙare masa kallo ba se yau ita kanta tama rasa kallon na mene ta kasa ɗauke idanta akansa tun bai fiskanta ba har ya gane.
Sosai take nazarinsa komi nasa a nutse yake dedai da magana a nutse yake abarsa bare kuma motsawa ta daɗe da sanin Salim ɗan gayune tun suna undergraduate sedai bata taɓa sanin yakai haka kyau ba kyakkyawa ne na ajin farko.
Tsintar kanta tai dayin murmushi yanayinsa ya tuna mata da tsalhanta komi nasa yana shige da tsalha wani fanni kuma yaya Isma'il she karu kawai zai ɗanfi Yayanta da mijinta ganin kallon yai yawa ne yasa Prof matsowa inda take yana Fadin Binta Mahmud tai saurin dawowa daga tunanin da take na'am sir.
Amsa tambayar da nai tai saurin nemo nutsuwa tasanshi beda mutunci zai iya rufe ido yaci mutuncinta anjima ya ce zai bata haƙuri eyyi tace eh answer now pls repeat the question ok ya maimaita mata bayan ɗan shiru kaɗan ta bashi amsa.
Ok class kun gane eh suka ce ok zaki iya zama tai ajiyar zuciya gami da zama ganin ta tsira da rashin mutuncinsa.
Binto
F.A.Ya'u
Tunda akai haihuwar Binto bata sami damar zuwa ganin baby ba sai yau kullin tana da lecture.
Tsaf ta kintsa su kairi Salma ke ɗauke da Muhammad ita tana ɗauke da Walid ɓangaren mami tai dan faɗa mata zasu ganin baby kamar ko yaushe mami na zaune Isma'il nagefenta da alamu shirin yadda suna zai kasance suke danjibi ne suna.
Sun gaisa da mama cikin kulawa kamar karta gaida Isma'il taɗan daure tace yah barka da hutawa barka yace bata kula da yanayin yadda yai maganar ba ta miƙe mami mu zamu ge ganin baby ne tun da suka tafi bamu je ba ok se kun dawo
Harsunkai bakin ƙofa Isma'il yace ku jirani jikin mota can zani se mu wuce no katafi kawai muna sauri cewa nayi ku jirani bawai roƙonki nai ba umarni ne ta watso masa harara alamar waye kake bawa umarni.
Ko kula da haka mami tai oho tace ku jirashin to tace gami da ficewa rai ɓace.
Yafi minti talatin sai tsaki Binto ke zubawa ranta duk ya ɓaci sannan ya fito muje ko ta ɓuɗe ƙofar baya ta shige me kike nufi ta masa banza ce miki akai ni driver ɗinki ne eyyi ta wasa masa harara to ni roƙarka nayi ka kaimu ko ce maka akai bamu da mota murmushi kawai yai gami da cewa Salma dawo gaba.
Yaja motarsa sukai gaba.
Yaron hannun salma ya karɓa ko da suka ƙarasa gidansu fiddausin tafe suke Salma na riƙe da hannun kairi wadda ke ta fama zuba musu surutu inka gansu kai kace wasu shahararrun masoyan nan ne ke tafe duda kuwa yadda dukkansu suka haɗe ransu.
Shi ya musu jagora zuwa cikin gidan kamar yadda gidan da akai haihuwa yake ƴan uwa da dama duk sunzo suna ganinsa tsoffi suka fara kiran angon ƙarni shi kuwa se wani wage baki yake yana jin daɗi.
Yaƙe kawai Binto take dan har yanzu ranta bai gama komawa dedai ba musan man ganin kallon wulaƙancin da ƴan uwan Fiddausi ke mata se ya ƙara bata haushi.
Ku zauna mana inji Isma'il yace wa Binto yana nuna mata kujerar gefen kujerar da aka masa masauki dan su ko gurin zaman ma kasa basu akayi gefensa ta zauna inda Salma da kairi ke ƙasa gefen ummansu.
Wai ina Fiddausin take ne yake tambaya tana wanka yanzu zata fito ok ace tai sauri muna sauri ne.
Wasa ya ci gaba da yima Muhammad da ke ta faman kyakyata dariya, Zainab ce ƙanwar Fiddausi ita da Hafsa sika fito riƙe da Baby ahannunsu Hafsa tasa hannu ta amshe Muhammad daga hannun Isma'il ta miƙawa Salma.
Yaya ungo shi ta miƙa masa ɗan jaririn yaro yanata kewar ka kai kuma ko ka tambayi yana ina kanata wannan ta nuna Muhammad da yai tsuru yana kallonta Isma'il yai murmushi aini na zata ko bazaku kawon shi bane tunda nasanku sukai dariya mu mun isa mu raba yaro da babansa.
Fiddausi ce ta fito cikin takun isa da ƙasaita inda idanunta suka ɗoru kan Isma'il da Binto kan kujera guda Haushi ya rufeta ji tayi kamar ta juya ɗaki ta dai daure ta ƙaraso.
Tana zuwa ta hau jirin ƙarya yai saurin miƙawa Binto jaririn yai gunta ya ruƙota tana amsar yaron zainab ta kwace shi yana zuwa yace Binta tashi pls ta zauna jiri take wani ƙululun takaici ya zo ya tsayawa binto a wuya ganin yadda Fiddausi ke kanne mata ido da alamu iskanci ne kawai ba abinda ke damunta shi kuma ya kasa fahinta.
Kusa dashi ya ajiye Fiddausi zainab ta miƙa masa baby ɗin tana faɗin yaya bari inmaku pic Family pic.
Hajiya Basira ce tace nifa bangane baƙuwar da kuke tare da ita ba take tambayar Isma'il Kafin yace wani abu Fiddausi tai saurin cewa lah Hajiya Binto ce tsohuwar budurwarsa what ya faɗa ke mene haka ya faɗa a fusa ce yayin da takaici ya ƙara rufe Binto.
No ni ƙanwar sa ce ba budur warsa ba inaga koshi ya faɗa baifaɗi dedai ba danni maganar so bata taɓa shiga tsakanin ba bama tasan sanda ta faɗi hakan ba miƙawa Fiddausi yaron yai mu zamu wuce ku tashi muje yace da Binta.
Miƙa masu kayan da ta kawo nabarka tayi gashi nan asama baby ta faɗa ta miƙe sukai waje yayin da duk jikin Fiddausi yai sanyi ita fatan ta ma Allah yasa badan Binto tace bata taɓa sansa bane yaji haushi ita inta abinda ta faɗa ne ko kaɗan bata damu ba danmene zai kwaso mata ita ya kawo mata ita.
Ko da Binto ta shige baya bai ce komi da alamu ransa ya ɓaci sosai duk jikin Binto yai sanyi itakam tayi danasanin zuwa barkan nan dan ba abinda ta ja mata in banda takaici.
A ƙofar gida ya sauke su kuyi haƙuri fa da abinda sukai muku zani wani waje ne bata ce komi ba ta fito daga motar kar ka damu basu mana komi ba se ka dawo ya bisu da kallo kawai
Sai da yai tafiya me nisa kamin ya parker motar abakin titi shi kaɗai yasan me yakeji duk da kasan tuwar sa jarumi me iya daure wa abubuwa besan sa'adda hawaye ya hau zobowa a kuncinsa ba.
Shi yama rasa dalilin da yasa suka dawo Nigeria da ya sani basu dawo ba me yasa suka dawo cikin gidansu da zama shi yaɗauka zai iya daurewa sedai kamar haƙurinsa yanaso ya bashi kunya.
Ba abinda yake tunawa se maganar Binto tabbas ziciyarsa bata masa adalci da take so masa abinda baisan sa baima yasani sesai san Binto ya mutu dashi yayi iya yinsa ya fidda shi ransa ya kasa dole zanyi maganin Fiddausi dole sai na ɗauki mataki akanta.
Tun daga ranar Isma'il bai kuma bari wani abu ya haɗa shi da Binto ba ko abinda zai haɗasu hanya yai maganinaa yasan ganinta ke tayo masa santa in be ganta ba shi kenan ya gama shiryawa abu bazai ƙara haɗa su ba har yabar ƙasar.
Acan kuwa Fiddausi hakalinta bai tashi ba se ran suna dan tin ran da Isma'il yazo da Binto be kuma zuwa ba wayarsa bata shiga duk tabi ta damu.
Yau suna duk yan gida sun shirya dan tafiya sunan daurewa kawai Binto tai ta bisu dan kawai bata san a isheta da tambaya me yasa bazata ba.
Acan gidan suna wulaƙanci kam tasha shi dan ƙannen fiddausi da yayyanta habaici sukai ta mata yaƙe kawai take.
Ko da me dije yazo ma haka suka dinga mata habaici har waƙa suka sashi yasa yayin da inba ita ba dasu babu wanda yasan da wa suke dan sauran yan uwa sunyi zaton kawai cikin shagali ne.
Wayarta ta hau daddannawa tana chat Saƙon kabir ne ya shigo ta ɗan murmusa suka hau fira tuni ta mance da shirgin Fiddausi da ƴan uwanta.
Binto