Page 16
Fito na Fito
AKAN SOYAYYA TA
Labari da tsarawa RAHAMA MUH'MD RUFA'I NALELE
Wattpad @rahamanalele
Haske writer's association
Shafi na 16
Ban yarda wani ko wata ya d'ora min labari na akan shafinsa ba, ban amince ba, duk wanda yamin hakan ya d'ora toko ya d'ora haramun tunda babu amincewata, ina magana ne akan koma waye macece ko Namiji
Ina da hakk'in mallaka na copy right domin haka a kiyaye.
Kiran Hauwa'u qawarta tayi a waya ta kisa Mata abin da take San tayi Mata yanzu, nanko Hauwa'un ta tabbatar Mata zatazo Mata da sakon anjima Insha Allah..
Wannan yasa RaHinAT d'in farin ciki sosai.
Can wajen la'asar bayan SafiYAH tayi sallah Bama wani meyi musu sharar tsaka kudi tayi kud'i Akan ya Nemo Mata zogale d'anye, lokacin daya dawo daga siyo Mata biyar tayi hakan yasa ta shiga kitchen, ta auni shinkafa yanda tasan zata Mata da b'arzata a bulanda tare da wankewa ta zuba ruwa a tukunyar Dambu tare saka shinkafar a tsakiyar tukunyar, kana ta markada attaruhu da gyara, ta yanka albasa ta b'are maginta da saka gishiri kad'an, duk tasa komai a gyefe, nan ta tsince zogalanta shima ta agefe, sanda shinkafar nan tayi laushi irin Saura baifi Rabin awa tayi ba, anan ta fitto da ita, ta zuba Mata kayan miyan nan da magi dasu Kori, da yankakkiyar albasan nan da zogalan nan, ta juya sosai sanda taga ta had'e jikinta, kana ta zuba wani ruwan a tukunyar Dambun ta qara maida wannan had'add'iyar shinkafar tsakiyar tukunyar... Kan kace me tuni kamshi ya Fara cika gidan..
Nan ta had'a wani kayan miyan ta had'a miyar jajjage me dauke da bushash Shan kifi da Nama wanda Sam bata bama miyar magi sosai ba biyu kawai tasaka da d'an gishiri kad'an, saboda ta saka magi a cikin Dambun shinkafar saboda Kar yayi yawa..
Nan ta kammala komai cikin tsari, ta zubama oganta cikin wani fulas me kyan gaske, Wanda yake d'auke zufa GA kuma riqe zafi, haka ta zubama su RaHinAT takai musu dasu Anna..
Kana ta nutsu ta had'a lemon kankana, sannan ta qara dana manguro, nan ta sakama ogan nata a furuji dan yayi sanyi, anan tayi wanka ta gyara kanta cikin qananun Kaya, Wanda daidai lokacin Ake Kiran sallar magriba. Nan ta gabatar da sallar ta jira akayi isha'i tayi, bayan ta idar ne ta cire Hijabin nata da zanin sallar nata ta linke Kenan ta ajiye taji kamar an ashigo falan nata, nan ta fitto RaHinAT ta gani Ashe itace ta shigo mata.
SafiYYAN tad'an ji wani iri da RaHinAT d'in ta ganta da shigar dake jikinta, Amma ta share, itako RaHinAT d'in gabanta ba qaramin fad'uwa yayi ba ganin shigar tata, duk da Riga da Wanda ne, rigar daidai cibiya wandon kuma daidai gwiwa, duk Kala daya ne Kalar ja haka wular data saka ma ja ce, tayi kyau sosai kamar Y'ar tsana...
Ganin irin kallan da RaHinAT d'in take binta dashi hakan yasa taje ta saka hijab tadawo falan tana cewa, "banyi tunanin kece ba, cikin sanyin jiki tace "dama d'azu da Hauwa'u tazo ta kawo min wasu hijabai ne, shine nace bara na kawo muku ke d'aya ReeYAH ma haka, tana zuwa nan cikin zancen nata ta miqa ma SafiYYAN d'aya daga cikin hijaban tana cigaba da cewa, saka nagani kamar wannan zai fi Miki kyau.
SafiYAN ta kalli d'ayan kalan dake hannunta golden yellow ne sai black d'in data miqo mata, nan taji tafi San golden yellow din, Dan haka murmushi tayi da cewa, gaskiya wannan black d'in baiyi min ba, wannan golden yellow d'in yafi min kyau...
Cikin damuwa RaHinAT d'in tace "Dan baki saka black d'in bane, ki cire na jikin ki ki saka kiga...
Kan tayi magana saiga ReeYAH ta shigo tana cewa, "miyata bata kaini ba nazo a qaramin Dan Allah, murmushi SafiYYAH tayi da cewa, "Dambun yayi d'adi. Tace "ke ba'a magana wallahi yayi so sweet ko ba haka ba RaHinAT..
Murmushin yaqe tayi da cewe, "eh Kam yayi d'adi sosai.
Cikin Jin dad'i SafiYAN ta karb'i dukka hijaban daga hannun RaHinAT d'in ta wurgama ReeYAH black d'in tayi saurin cab'ewa kana ita kuma ta cire Hijabin jikinta ta saka golden yellow d'in tana cewa, "Dan Allah ReeYAH wannan baimin kyau ba..
ReeYAH tace, "subhanallah Wallahi yayi Miki kyau...
Tace "RaHinAT ce ta d'aukar mana wai da Hauwa'u tazo gunta d'azu, wai na d'auki black d'in da alama ke zata bama wannan d'in ni kuma gaskiya yafi min kyau, Dan haka saidai ke kiyi hakuri ki riqe black d'in..
Tace "ai ni ina da irinsa takai qarshen zancen da kallan RaHinAT tana cigaba da cewa, mun gode..
SafiYAN ma ta kalleta da cewa, "ALLAH ya saka..
Cikin murmushin yaqe tace "ba komai.. tana fad'in hakan ta fitta daga falan.
ReeYAH tace "sakamin miyar, tace "why sai ni, ki Shiga kitchen d'in ki iba mana.
Nan ta Shiga ta iba, bayan ta fitto tace "Ammafa wankan ki yayi kyau... Murmushi tayi da cewa, "wato daga d'an cire hijabi har kin gani..
Murmushin itama tayi kawai da ficcewa...
Sai wajen takwas da rabi HaYdaR ya dawo gidan, koda yaje duba lafiyar RaHinAT ganinta yayi a kwance Kan gadanta, Shi dai ayanda ya ganta tunaninsa ko bacci take yi, hakan yasa ya fitta zuwa part d'in ReeYAH, anan ya ganta falanta tana kallo, suka sakar ma juna murmushi yace "ke bakiyi baccin bane, tace "8:30 ne fa Yaya, da d'an sauran lokaci kamar zuwa 9:30 haka, yace "Gud, badai komai ko, tace "komai normal honey kaje ka huta, yace "tom Saida safe, tace "ALLAH ya tashemu lafiya. "Amiin yace da ficce
Gaskiya ya bada wankan SafiYAN, Yana San mace da qananun Kaya, nan ya rungumeta Yana cewa "zo muje ki tayani gyara kaina,
Murmushi tayi da binsa part d'insa...
ReeYAH tata Dan zuwa badroom d'inta bayan ta saka wata figigiyar rigar baccinta kawai sai idanta ya sauka Akan wannan Hijabin da RaHinAT ta basu nan qaddara ta sata jawo Shi wai tasaka taga yanda zaiyi Mata a jikinta, irin ta kalla a mirror d'inta.
Aiko tana saka hijab d'in da kallan madubin bad din nata taga yayi Mata kyau, Amma saidai me? wani saukar qaiqayi taji Wanda ya sata saurin fara Susa jikin nata..
Ai ba shiri ta cire Hijabin nan taga wasu qananun abubuwa kamar gashi gashi amma farare ne, ta kalli Hijabin taga daga cikin Hijabin suke, duk Sun b'ata Mata jiki kuma sun manne Mata sai qaiqayi suke Mata nan tahau Susa ko ina a jikin nata..
Abu kamar wasa nan fatar jikinta tahau tashi, kamar an zuzzuga Mata bulala..
Hankalin ReeYAH ya tashi sosai nan ta fara hawaye, Abu yayi yawa AI bata San sanda ta Fara kuka wiwi ba, sabuta yanda gabaki d'aya jikinta yad'au qaiqayin....
Sai Kiran sunan ALLAH ya take ya kawo mata sauqi
Aiko cikin ALLAH dabara ta fad'o Mata tayi toilet ta tara ruwan d'umi ta Shiga ciki tar da saka sabulai nan ta dunga wanke jikin nata, ruwan zafin na qara kashe Mata qaiqayin, sanda tayi ruwa kusan uku, ana hud'un ne bata saka sabulan ba, tayi lub acikin ruwan Yana gasa mata jikin nata, nan taji dad'in jikin nata ta dawo ta shafa oil, lokacin zazzab'i ma ya fara kamata, Dan haka panadol tasha Kawai ta kwanta tana mamakin wannan abu...
Aiko zazzab'in ya kamata sosai, gashi bata San gayama HaYdaR haka ta qara duba akwatin magagun gunanta taza wani maganin zazzab'in, wanda tana sha Allah ya temaketa bacci yayi awan gaba da ita..
Anan ko RaHinAT baqin ciki kamar ya kasheta, tazo wannan qaiqayi ya saukarma SafiYAH ta yanda bazasu samu nutsuwa tsakaninta da HaYdaR d'in ba, saiga ReeYAH ta shigo, "banza kije ke kika sa'ni yayin da kika saka Hijabin... Ta hakan a bayyane..
Shiko HaYdaR ya qara more amarcinsa abinsa, yayi Imani Aure rahama ne, ba abin daya Kaisa nutsuwa da kwanciyar hankali..
Washe gari tare ita dashi suka had'a breakfast, haka HaYdaR din Yana ji Yana gani ta maidashi me aikinta, Amma bayan sun gama Shi kansa yaji breakfast d'in...
Ya kalleta da cewa, "Ashe haka Ake Shan wahala wajen girki, tace "No luv kawai dai Dan baka tab'yi bane, Amma Kasani duk wani aiki da zanyi idan har kana a ranar girkina to Kaine zaka tayani.. yace "what... saboda me, tace "saboda naji dad'in yanda Ka tayani yanzu..
Murmushi yayi da cewa Baki da matsala, indai zakiyi farin ciki Zan Miki abin dama yafi qarfin hakan, saboda ina sanki, ina qara sanki...
Murmushin Jin dad'i tayi da cewa, "I luv u..
Tashi yayi daga Kan dirning d'in ya sunkuyo da sakar Mata kiss da cewa, "luv u 2, akwai abin da kike San na tawo Miki dashi, tace "hmmm idan nayi tunani Zan kiraka a waya, sai dai yanzu ina San idan kaje gun RaHinAT da ReeYAH Ka dawo gareni na rakaka zuwa mota, wannan zai hana Idona manta cewa Naga Shigarka motarka..
Yace "badai kina San hakan ba, d'aga Mai Kai tayi, sai ya sakar Mata murmushi da cewa "tom jirani ina zuwa..
Tace "owkie luv, ina qara Sanka fah..
Ba tare daya kalleta ba yace "ni kuma ina qara qaunarki..
Da wannan yabar falan tabi bayansa da kallo tana tuna soyayyar daya nuna Mata daran jiya...
Kadaran Kadaham yasami RaHinAT Sam bata Bari wata hira me tsayi ta Shiga tsakaninsu ba, haka yayi part d'in ReeYAH, anan ya ganta cikin bargo, kallo d'aya yayi Mata yasan bata jin dad'i, nan cikin sauri ya tambayeta Lafiya, anan take cemai daran jiya ne batayi bacci ba ta kwana cikin zazzab'in, nan cikin damuwa yace, "what, shine baki gayamin ba, cikin murmushi tace "Bana San takuraka ne Yaya, cikin rashin jin dad'i yace, look karki qaramin irin hakan bana so, aduk lokacin da kikaji Baki Jin dad'i kikirani cikin sauri, oya tashi muje asibiti yanzu, tashi tayi cikin murmushi tace, "ALLAH Yaya na warke, da ace jiyane Ka ganni cikin wannan halin tabbas dako bakace muje ba zance dakai muje, Amma yanzu ina lafiya kawai dai ina buqatar Hutu ne Dan maganin Dana sha Allah yayi zaiyi min aiki wallahi bana Jin ciwon Yanzu, yace "kin tabbata, tace "kwarai na tabbatar maka da hakan..
Rungumarta yayi cikin Jin Santa yace "I luv u, bazan so na ganki cikin wani hali ba, ALLAH ya qara miki lafiya, yanzu idan kinyi breakfast ki qara Shan maganin idan kikaji wani Abu please ko yayane ki Kiran muje asibitin kinyi, Allah ya qara Lafiya, tace "Amiin ba komai ma Insha ALLAH honey.
"Yanzu akwai abin da kike buqata ne, tace "no komai da sauqi, yace Masha ALLAH Zan tafi, tace "ALLAH ya bada sa'a Yaya.. yace "amiin nagode..
Da haka yabar part d'in nata, nan kuma ya tarar da safiya bak'in kofar d'akin ta tana jiransa, nan ta sakar Mai murmushi sukayo harabar gidan, anan ta miqa masa mukullansa da naqurarsa tana cewa, "Luv, ALLAH ya karemin Kai, ya bada sa'a, ya hana haram Shiga cikin dukiyarka ya Baka abin da kake nema duniya da lahira, cikin Jin dad'i yace "Amiin luv, nagode sosai, am Dan Allah ki Kula da ReeYAH kamar bata jin dad'i Dan Allah duk da nasan kema ba wani Jin dad'in kike ba, Amma zanso ki bada lokacin ki, tace "Subhanallah, Luv me yake damunta, yace "jikin da sauqi sosai jiyane wai ta kwana cikin zazzab'i, naso yanzu na kaita asibiti Amma tace tana normal, so ina dai San ki bata kulawa, tace "ba matsala to, Ka kwantar da hankalinka tunda tace yanzu tana lafiya ina ganin hakan ne, murmushi ya sakar Mata da cewa, "Tom sai munyi waya ko, d'aga masa Kai tayi, Kana yaja motar tasa...
Nan tayi part d'in ReeYAH da sauri
Yayin da RaHinAT ta sauke labulan windown ta, taga duk abin daya faru tsakaninsu tasan meyasata yin shashin ReeYAH da sauri, hawaye ne ya zubo Mata, tana San HaYdaR irin soyayyar da bata San ganinsa da wata y'a mace, wannan yasa take matuqar Jin tsanar SafiYYAH a ranta, gani take awane lokaci SafiYYAN zata rabata dashi kwata kwata, dole zatayi wani Abu Wanda zai bata damar rabasu, Amma bazata juri ganinsu cikin farin ciki da annushuwa haka ba, tana kawowa nan cikin zancen nata ta goge hawayen nata da nufar part d'in ReeYAN
"Subhanallah ReeYAH garin Yaya haka, bayan jiya mun rabu dake lafiya, Amma ji yanda kika fad'a kamar kinyi wani ciwo na kwanaki.. SafiYYAH ta Gaya Mata hakan tana me Zama gefan gadonta kusa da ita..
Tace "hmm kedai bari, Hijabin da kika ban jiya.. tace "Hijabin dana baki Mene, meya faru da Hijabin, RaHinAT ce ta bamu..
Zatayi magana sai ga RaHinAT d'in ta shigo, tana cewa, "meya faru da RaHinAT nace ana kiran Sunana, SafiYAN ta kalleta da cewa, "Barka da safiya ina tambayar ReeYAH Akansa..
Kallan ReeYAN RaHinAT tayi da saurin waro Ido tana cewa, "Ya ALLAH ReeYAH meya sameki haka idanki suka fad'a, tace "wallahi da zazzab'i na Kwana jiya, kinga Hijabin da kika bamu jiya waini in gwana kafin na kwanta shine fa ina sakawa qaiqayi yayi ram Dani, kamar an saka wani Abu mesa qaiqayi a cikinsa, wallahi baku ganni jiya ba kamar zanyi hauka.. takai qarshen zancen tana me nuna musu Hijabin da tunda ta wullar dashi a qasa jiya bata qara bi ta kansa ba..
RaHinAT ta kalli Hijabin kamar gaske ta b'ata fuska, tace "too ikwan ALLAH, kinga ni tunda na zab'a mana agun Hauwa'u banci karo da wani abu makamancin hakan ba...
SafiYAH ta kalli Hijabin tare da d'agasa taga wasu fararen abubuwa kamar gashi kamar dai yanda ReeYAN tagani, nan tace "ko way'annan abubuwan ne suka haifar da qaiqayin, kungansu fa, ni ban tab'a ganinsu ba..
RaHinAT tace "aikuwa dai, kamar sune masu saka mutum yaji qaiqayin, niko agun wa na tab'a gani kuwa ya gayamin, tabbatar an samu kuskure ne, qila zai iya yuhuwa a ledar da Hauwa'un ta kawo a ita ne suke, ita kuma bata lura ba tasaka hijaban aciki, kuma wannan d'in shine na qarshe acikin ledar qila shiyasa yafi mannewa a jikinsa.
ReeYAN tace "inko haka ne ba mamaki kam.
SafiYYAH ta kalli ReeYAN tace "sannu fa, kice kinga haza, tace "AI Bari kawai kamar zanyi hauka fa, gashi nasa kayan bacci Kenan ba wani kayan arziqi a jikina na kama na saka, shine fa bayan nayi wanka zazzab'in ya kamani, bayan nasha magani koda na tashi danyin sallar Asuba nima nayi mamakin fad'awar da naga nayi, Amma yanzu jikin da sauke sosai....
Atare sukace Allah ya qara lafiya, tace amiin
SafiYAH tace, "Ya kamata yanzu kici abinci, saiki qara Shan maganin ki kwanta, tace "ok, Insha ALLAH yanzu kuwa..
Nan suka d'an tab'a hira daga bisani ko wacce tayi part d'inta...
Sosai SafiYYAN tayi qoqarin bama ReeYAH har sanda ta tabbatar ba wani abin dake damunta sannan hankalinta ya kwanta, Dan koda HaYdaR d'in yayi waya da ReeYAH yaji tana lafiya sosai, wannan yasa shima hankalinsa kwanciya...
A kwana bakwai din SafiYAH HaYdaR yayi Imani ya samu farin cikin daya dad'e Yana fatan samu agun matar auransa, ta bashi nutsuwa da kwnaciyar hankali, ga magana me dad'i ta soyayya, GA cikamai ciki da cima Kala Kala, ga d'aukar wanka me sashi farin..
Ita kanta tasan yayi farin ciki da kasancewarta Mata a garesa, wanna ya qara Mata jin dad'i ta kuma d'aura aniyar zage dantse wajen basa farin ciki musamman aranar da yake da ita..
Yayin da RaHinAT duk ta d'orama kanta damuwa da tashin hankali, a kwanakin nan kullum idanta nakan SafiYYAN da HaYdaR d'in yayin da take rakasa mota danyimai rakiya, haka take ganin Yanda suke tsula soyayyarsu, tayi Imani Basu da matsalar komai Dan gane da ma'amalarsu..
Shi kansa HaYdaR d'in ya fahimci akwai abin dake damunta, d'aya tambayeta cemai tayi ba komai, yace tatabbata tace Mai eh, wannan yasa ya zuba Mata Ido kawai..
Yau ReeYAH ce dashi, tun safe bayan fitarsa ta rasa me zata dafa musu da daddare..
Hakan yasa batayi girman Kai ba, tazo gun SafiYAH tace, "Y'ar uwa, Dan Allah me kike ganin ya dace na dafa mana yau da daddare..
Shuru SafiYYAN tayi, can ta kalleta da cewa, "kiyi kunu da alala, ina ganin kamar luv zai so hakan sosai, tunda kinga shi komai Yana ci..
Tace owkie, idan baici da yawa ba Zan hukuntaki..
Murmushi tayi da cewa, "ba komai Amma please idan zakiyi kunun Dan Allah kiyi mana na gyad'a kinga kin iya sosai ni kaina inaso idan naga kinyi tun a gida ai kin tuna ko, tace "tom in haka ne, ki tayani yin alalan ni kuma nayi kunun, Amma karki gayama honey ke kika tayani fah, dariya SafiYAH tayi da cewa nayarda, tace ba yarda nake San ji ba, kawai kice kinyi alqawari, tace tom nayi, Amma wane irin alalan kike San yimai, shuru ReeYAH tayi, alamar tunani, ganin hakan sai SafiYAN taci gaba da cewa, akwai na hanta dana kifi, dana kwai, Dana nama, idan kinso ma AI duk zaki iya hadawa, Amma kiyi na ganye, Naga yafi qamshi, sai kiba Musa ya siyo Miki ganyen yanzu.. tace okay, Amma bara na Kira Yayan naji wanne yake so aciki Allah yasa yace na Zama yake so, d'an shuru SafiYYAN tayi Dan tasan yafi San kifi fiye da Nama a fahimtar da tayi masa, zata Gaya Mata Kenan sai taga har ya d'auki Kiran da ReeYAN tayi masa...
Tace "Honey ina San yi maka kunu da alala, da fatan zakaso hakan, yace "wallahi Amaryata kamar ko kinsan rabona dashi nafi shekara, kwarai zanji dad'in hakan sosai, tace am na kifi kake so Kona Nama ko hanta... Katseta yayi da cewa, no kifi, tace Masha Allah, ALLAH ya dawo mana dakai gidan lafiya, yace "ina murna yau Ango nake da fatan kina tayani murna, tace "um ai kullum ma Ango kake, Ango Mata uku, yace dace na cike ta hud'un fa, tace Kai... Tab ni zakama kishiya fa kenan, Kana ganin Yaya yadace yama qanwarsa kishiya, murmushi yayi da cewa, "ALLAH ya baki hakuri, daga ke babu qari Dan duk kin rufe musu kofa, tace yauwa ko Kai fah, yace I Luv u, tace luv u 2..
Daga nan suka ajiye waya..
SafiYAH ta d'aga mata Gira da cewa, wannan soyayya haka, tace ke har kina da bakin magana idan ana magana akan soyayya, dariya SafiYAN tayi da cewa, "zuwa 4:00pm sai mu Fara ko, tace "ba damuwa Y'ar uwa nagode sosai, bara naje na kintsa wasu kayana, tace "ok tom..
Biyar suka Fara aikin, tare sukayi komai cikin tsari, SafiYAN ta koma shashin Dan yin wanka
Haka ReeYAN ma qara tsaftace kitchen d'in nata tayi itama ta Shiga wankan..
RaHinAT na Lura dasu, ta fahimci zasu iya had'e Mata Kai akowa ne lokaci, Sam bata damu da hakan ba, domin tunaninta shine duk ta fittar dasu wannan shine a gabanta.
HaYdaR yaji dad'in girkin na ReeYAH sosai, bayan sun gabatar da sallar godiya ga ALLAH, sunyima juna addu'a, tare da Shan madara me sanyi, lokacin da sukazo aikata Sunna tsoro ne ya bayyana muraran a idan ReeYAH, HaYdaR ya tambayeta Lafiya.
Tace "Honey ina jin tsoro, ance da zafi.. yace "wayace Miki, tace "SafiYAH, murmushi yayi da cewa, "kawai ta Gaya Miki hakan ne da wasa, kinga mu kwanta kawai bazan miki komai ba sai gobe tunda kina jin tsoro ko..
D'aga Mai kai tayi..
Shiko murmushi kawai yayi
Haka sukayi baccinsu batare da yayi mata komai..
Washe gari suna breakfast ya sakar Mata murmushi da cewa, "Zanso ki haifamin y'a mace me kama dake, domin kina min kyau sosai ReeYAH..
Tace "ALLAH Yaya, "ALLAH da gaske, tace "Insha ALLAH Zan Haifa maka, ina mana fatan alkairi dukkan mu..
Yace "ALLAH ya yarda..
Bayan yayi Mata sallama part d'in RAHEEMA nan yaji motsinta a toilet, haka ya zauna zaman jiran fitowarta har ta fitton, ta kallesa da sakar Mai murmushi Dan taji dad'in zaman jiran fitowartan da yayi, domin taga yayi latti Amma hakan bai hanasa tsayawa domin ganin lafiyarta ba, wannan ya sata Jin dad'i mara misaltuwa..
Tace barka da sa fiya sweetheart, tashi yayi d rungumarta Yana cewa, "barka dai my sweetheart da fatan kin tashi lafiya tace, "Lafiya Lau, yace "tom zani office ina buqatar addu'a, tace "Allah ya kaika lafiya ya kuma dawo dakai lafiya ya baka abin da kike nema, yace "Amin nagode sosai my love, akwai abin da kike buqata tace, "eh wasu kudi haka ba masu yawa ba.
Murmushi ya sakar Mata Yana me raba jikinsa da nata ya bata Yan dubu dubu tayi mai godiya sosai, kana yayi shigin SafiYYAH.
Taci adonta Yana shigowa taje ta gudu ta rungumesa tana cewa, "luv nayi missing d'inka, I luv u bansan haka nake Sanka da yawa ba, bakaga yanda nadinga juyi akan gadona jiya ba, Sam kasa rintsawa nayi, ALLAH ne dai ya temakeni baccin yazo kad'an haka...
Cikin matuqar Jin qaunarta yace, ”sorry luv, mijinki zai dawo gareki nan ba dadad'ewa ba, tace "I love u, yace l love you 2, jiya nayi makarki dake Baby kin haifamin Yan biyu, dukkansu Maza ne, cikin murmushi tace "subhanallah, Allah ya tabbatar da alkairinsa luv, zanfi kowa murna da farin cikin hakan..
Yace "tom Zan tafi office gashi bansan rabuwa dake, gashi nayi latti, murmushin Jin dad'i tayi da sakinsa tana cewa, "Kaje Allah ya bada saka luv, ni d'innan takace ba abin da zai rabamu sai ikwan ALLAH, kaje ina tare dakai cikin zuciyarka..
Murmushi ya sakar Mata da ficcewa daga part d'in naka..
ReeYAH ya gani a harabar tsakar gidan, nan ya sakar Mata murmushi da qarasawa Inda take, nan suka jera zuwa wajen motar tasa, tace, "Nima Inasan na samu ladan rakoka zuwa mota, tare da qara yi maka akan Allah ya dawo mana dakai gida lafiya..
Yace "nayi ko farin ciki da hakan, nan ya danna rimot din motar ta bude masa murfin motar ya Shiga tana cewa "tom saika dawo ALLAH ya saukeka lafiya, murmushi ya sakar Mata da cewa Amin nagode sosai..
Da haka yaja motar ita kuma ta nufi komawa cikin gidan..
RaHinAT ta sauke labulan ta, da ta fari da taga fitowar ReeYAN taga tafiyarta bata canja ba sai tayi tunanin Anya kuwa sun raya daran nasu, Amma da taga fitowar HaYdaR din daga part d'in SafiYYAH ta yanda ya sake da ReeYAN na Y'ar kulawan da sukaba junansu sai tayi tunanin kawai sun raya..
Har kuka sanda tayi, ganinta ya dace ya Fara da ita, ya kuma Gama da ita, Amma yanzu gani take kamar itace kashin Baya...