KE HASKE CE

CHAPTER FIVE

by @ummubasheer

SAMEER* har ya isa bedroom bai bar tunanin LAILAH ba. Wato tana b'oye asalin ko wace ce ita domin tana da kyau sai ya samu kanshi da yin murmushi baiji haushin ta akan hakan ba. Har yayi barci LAILAH tana ran shi.



Bangaren AYAAN ko bai tashi barci ba sai around 10:00am koda ya tashi nan yayi K'okarin tuno da abin daya faru sai dai bai iya tunowa ba yana ganin abin kamar a mafarki sai ya fara tambayar kan shi wai wace ce wannan kyakyawar budurwan daya Gani tabbas kyakyawa ce. Ranar dai haka ya yini tunanin wannan budurwan wacce bai San ko asalin wace ce ba.




LAILAH tun daga wannan lokacin sai tana karantar halayen su kuma ta amince ta yarda ba mugayen mutane bane matsalar dai kawai AYAAN ne bata son halayen shi. Sau dayawa tasha ganin ya dawo a buge ko Idan taje d'akin sai ta tarar da kwalaben giya. Akwai wata rana duk sun tafi aiki sai va AYAAN ya dawo missalin k'arfe 1:00pm. Lokacin LAILAH tana aiki a kitchen sai taji an shigo koda ta fito parlour'n sai taga AYAAN rungume da wata budurwa suna hawa upstairs. Abin ya bata mamaki dan ko bata tab'a ganin wata mace a gidan ba, tasan lab'e babu kyau Shiyasa ma bata bisu ba.




Bayan kamar one hour sai taji tashin dariya a parlour'n tana fitowa sai ta gansu sun sauko kuma AYAAN ya canza kaya ba Wanda ya shigo dashi bane tasan dai zato zunubi ne koda hakan gaskiya ce sai tayi shiru. Ta gaishe su.



AYAAN yaji gaban shi ya fad'i domin dai baiyi tunanin wani abu bane Idan mai aiki ta gan shi da wata budurwan shi sai ya d'aure fuskar ya K'arasa gaban ta yace"kar ki kuskura ki fad'i wani abu dangane da abin da kika Gani ki d'auka ban shigo gidan ba. Rayuwa kawai nake holewa kuma lokaci nane dolle ne inyi kin gane ai" ya fad'a yana fita daga parlour'n yayin da budurwan ke faman hararran LAILAH tana tunanin ko ita ma budurwan shine.




Wato bayan giya da AYAAN yake sha har neman mata yake wannan wacce irin rayuwa ce yakeyi mai cike da kazanta. Haka dai ta cigaba da aikin ta tana mai fatan shiryuwa Idan mai shiryuwan ne.







Zaune yake a wani guri. Gurin na cike da tantabaru sai watsa musu abincin su yakeyi yana murmushi sau dayawa su ne ke debe mai kewar gida. Wani irin k'amshi ne ya ziyarci hancin shi lumshe ido yayi ba tare daya ga ko waye ba. Sai da tayi sallama sannan ya bud'e ido tare da amsawa yana kallon fuskar ta.



LAILAH ce sanye da doguwar riga na material blue yau fuskar ta yayi kyau kuma bata shafa gawayi da kyau ba dan Kad'an yayi saura ya kare.



"Ya SAMEER naga kana azumi ne shine Nazo in tambaye ka ko kana son in dafa maka wani irin abinci ne?"


Sweet voice d'in ta ya doka kunnen shi"LAILAH da kin bar halitar da Allah yayi miki da hakan yafi domin kina sa ma kanki muni Wanda ba haka Allah yayi ki ba"


Maganar shi ta razanar da ita da sauri ta fara K'okarin yin magana ya katse ta cikin sauri ya fad'a mata ya gano tana b'oye asalin ta. Tabbas tasan yayi gaskiya mene ne amfanin bata fuskar ta ita kan ta ta gaji dan bata saba da shafefe ba. Bata ce mai komai ba ta deba abincin tantabaru tana watsa musu can sai yayi musu wani irin kira da ake musu ai ko sai gasu kusa dasu suna tashi.



LAILAH dariya take sosai ba tantabarun gwanin ban sha'awa. Kawai sai SAMEER da LAILAH suka fara hira suna watsa ma tantabaru abinci abin ni kaina sai ya burge ni.




Can dai ta tashi ta Shiga kitchen ta shirya ma SAMEER abin shan ruwa.


Bayan sati biyu LAILAH tayi ma SAMEER magana akan tana son zuwa k'auyen su ita da Inna Mairo nan yace Hafiz ya kaisu bayan ya basu kud'i dan suyi tsaraba. Ai ko haka akayi Hafiz ne ya kai su sai da ya kai Inna Mairo Sannan ya kai LAILAH har gida.


Ba karamin farin ciki LAILAH da Hajaju sukayi ba da ganin junan su. LAILAH rungume ta tayi tana kuka yayin da Hajaju ke rarrashin ta ai ranar kwana sukayi suna hira LAILAH tana bata labarin inda take aiki da k'auyencin da sukayi tayi ita da inna Mairo sannan ta bata labarin su SAMEER har Hajaju tana sa mai albarka yayin da take kushe MAHEER.



Kwana biyu LAILAH tayi ko yaushe tana manne da Hajaju. Lokacin da Hafiz yazo d'aukar ta kamar za tayi kuka dan bata so haka ba bata son rabuwa da kakar ta ita ma Hajaju taji ba dadi amma ba yanda za suyi haka suka rabu cike da kewar junan su.




*__________________________*





Bayan wata biyu



Tunda LAILAH ta dawo daga k'auye ta daina shigar nan tana sa kaya masu kyau yawanci dogayen riguna ne kuma bata sa fitted sannan bata kwalliya dan baya burge ta suna zuwa gurin Fateema matar Hafiz suyi ta hira tana koya mata wasu abubuwan irin namu dai na mata dan Fateema wayayiya ce kuma y'ar boko ce. LAILAH da inna Mairo suna jin dad'in zama da juna.



Wata rana MAHEER yana saukowa daga upstairs ya hango LAILAH ta fito daga kitchen sai da ya kusa fad'i dan tayi mugun kyau sai da yayi tasbihi game Allah daya hallice mu. Bai tab'a tunanin ita bace sai dai kuma ya gane ta kasancewa lokacin da bata shafa gawayi sosai. Sai dai ya d'an kwana biyu bai gan ta ba dan ko yaushe yana busy. Tsaki yayi a ran shi yace tazo birni ta fara kyau may be ma bleaching takeyi. Ya d'aure fuska ya wuce ta ita ko ko kallo bai ishe ta ba tunda ta gane bashi da mutunci.




Wata irin shak'uwa ce mai k'arfi ya Shiga tsakanin LAILAH SAMEER da AYAAN. Domin kam wani lokacin hira suke irin ta y'an uwa SAMEER yana jin dad'in zama da LAILAH domin halayen ta nagari ne kuma yana Samun kanshi cikin farin ciki duk lokacin da suke tare. Suna yawan zuwa gurin tantabaru suna basu abinci ko su Shiga kitchen tare suyi girki yana taimaka mata. Yanzu har K'anwar shi tasan da LAILAH don har waya yake bata suna gaisawa. Ita kanta LAILAH sai taji tana son K'anwar shin.



AYAAN yakan sa wak'a yayi ta rawa a parlour LAILAH na Zaune tana mai dariya kullum sai yace ta fito tayi rawa amma tak'i wata rana ya k'ure volume sai cashewa yake LAILAH na dariya sai yace ita ma sai tayi suna ta gardama tak'i yarda Dole dai ta amince ta d'an fara takawa.


MAHEER dake bedroom yana barci music y ya hana shi sai fitowa yayi a fusace yana zuwa yaga LAILAH tana d'an taka rawa AYAAN na mata tafi ai sai yaji wani bakin ciki a fusace ya sauka yana zuwa ya d'aga hannu ya sharara mata wani mari ai sai da taga stars suna gilmawa. Sannan ta durk'usa dafe da kuncin ta.


AYAAN ko sakin baki yayi dan abin yazo unexpected. Kafin yayi magana sai MAHEER ya fara zazaga mata ruwan massifa. Wai ai aiki tazo ba rawa ba ya zage ta sosai fa. Ya juya zai tafi AYAAN cikin haushi ya fara cewa ai bai dace yayi haka ba sai cemai yayi to yazo ya rama mata ya hau upstairs ya bar AYAAN da cewa"mugu kawai Allah ya isa d'in ta. Kai da Allah"😚



Sannan ya fara bata hakuri daga karshe ta fita parlour'n ta nufa Inna Mairo sai dai bata nuna mata komai ba.


AYAAN ko yana ganin SAMEER ya dawo ya fara bashi labarin abin daya faru Shima SAMEER Baiji dad'i ba amma ba yanda zaiyi dashi kawai sai a share yaba LAILAH hakuri sai ta nuna ai ba komai nan yaji ta burge shi dan tana da hakuri.



LAILAH ko tasa ma kanta hakuri dan dai aiki tazo yi dole tayi hakuri. Beside ma laifin ta ne.






Sau dayawa MAHEER Idan yaga LAILAH Dasu SAMEER sai ya dinga jin wani irin zafi. Tana dai aikin ta tana tabbatar da bata samun matsala gurin gyaran bedroom d'in MAHEER dan yanzu sai ya hau ta da fad'a. Sai dai fa yana jin dad'in girkin ta kawai dai yana basarwa ne.



Wata rana Granny tayi rashin lafiya SAMEER da AYAAN Inna Mairo da LAILAH suka je gaishe ta a can suka samu MAHEER Wanda yaji haushin zuwan LAILAH. Ai ko Granny taji dad'in ganin su dan ita mace ce mai kirki tana son masu aiki bata wulakanta su. LAILAH girki na mussaman Na gargajiya tayi ta kawo mata ai fa nan tayi tasa mata albarka.



Haka suka yini hira Wanda Granny har ta fara jin dad'in jikin ta. MAHEER ko sai hararran LAILAH yake. Ni ko Ummu Basheer nace sai muyi maka taron dangi dan kowa massoyan LAILAH ce.😂











Yau ta kama ranar Sunday da safe LAILAH ta gyara sauran bedrooms d'in sai ta Shiga na AYAAN dan nashi ne a karshen gyara saboda datin d'akin. Tana Shiga ta fara sallati kamar yanda ta saba Idan ta Shiga saboda ganin yanda d'akin yake upside down. Ga kwalaben giya nan a kasa can sai ta hango AYAAN kwance kan bed yana shak'ar barci.



Ba tayi tunanin yana nan ba kasancewa suna fita exercises da sasafe shine take samun daman gyara bedrooms d'in kafin su dawo. Kunna wutan d'akin tayi AYAAN ya tashi zaiyi massifar meyasa za'a kunna mai wuta sai yaga LAILAH a tsaye.



Cikin bakin ciki da halayen AYAAN ta kalle shi tace"shin kana ganin rayuwar daka zab'ama kan ka shine daidai shin ko kasan shan giya da neman mata zunubi ne? Shin kasan ranar da zaka mutu? Idan ka mutu a wannan halin mai zaka fad'a ma Allah Wanda ya hanne mu da aika sab'a mishi"





Yau ce rana ta farko daya samu kan shi cikin jin kunya yau ce rana ta farko da yaji Kyamar wannan halayen. 


LAILAH bata San lokacin da ta fara hawaye ba domin tana jin AYAAN tamkar yayan ta ne cikin hawaye tace"ka tuba zuwa game Allah ka nema gafara gurin Allah. Allahu gafurur rahim. Allah mai yafiya ne, AYAAN ina rokon ka ka tuba"




Jikin shine yayi sanyi domin yau ce rana ta farko da yaji wa'azin da ake mai yana shigar shi. Duk da SAMEER da MAHEER suna K'okarin ganar dashi.



Juyawa LAILAH tayi ta bar d'akin yayin da AYAAN ke jin ya tsane kan shi.......