ƊAN HAKIN DA KA RAINA.......

Chapter 1 to the end

by @ummindaddy77

ƊAN HAKKIN DA KA RAINA


ƊAN HAKIN DA KA RAINA......




Sanyayyiyar iskar asuba ta daminar marka-marka ce ta fara ratsa sassan jikina, na buɗe idanuwana da ƙyar, yadda na ji gari tsit ga duhuwa ya tabbatar mini ba farkon dare ba ne na tambayi kaina a zuciya, “A nan na kwana kenan? Hisham ka cuce ni. Ya Allah ka bi mini haƙƙina.” Na fara yunkurin miƙewa, sai na ji jikina ya yi mini nauyi, gaɓoɓina kamar ana sassara su, ƙara na sake sanadin zugi da raɗaɗin da gabana ke yi mini.

Na runtsa idanuwana haɗe da cijan laɓɓana kana na buɗe su, yanayin da na tsinci kaina da bushashshen jini da na yi tozali da shi a katifar da nake ya sa ni fashewa da kuka mai tsuma zuciya.


Hisham ya bi ni da wani irin matsiyacin kallo na raini da ƙasƙanci. Cikin tsiwa ya ce da ni.


“Ke dalla rufe mini baki! Idan ba haka ba na karairaya ki."

Wannan shi ne a dake ka a hana ka kuka. Bisa tilas na haɗiye kukan da ke ƙoƙarin yin galaba a kaina, saboda na san Hisham bai haɗa layi da abin da ake ƙira mutunci ba zai iya cin zarafina akan hakan.

Ya ci gaba da magana cike da izza. “Ni mutum ne wanda in har wutar sha’awata ta motsa akan duk wata ɗiya mace ko da jaririya ce sai na biya buƙatata ko ɗiyar wacece ita a ƙasar nan.”


Ya dalla mini muguwar harara cikin ɗaga murya ya ce . “To ɗiyar matsiyata, sai ki tashi ki yi gaba."

Ya watsa mini kayana a fuskata.

Ya ɗora ƙafarsa ɗaya bisa gefen gado yana kallona ya ce, "Ni mutum ne wanda duk abin da na ƙudurta a zuciyata zan yi shi mai kyau ne ko mara kyau to sai na yi shi. Masu faɗa a ji sun buga sun ka sa ballantana 'ya'yan talakawa matsiyata irin ki, idan kuma kin ga za ku iya ja da ni bismillah ga fili ga mai doki."

Ya sauke kafar tasa, "Na ba ki minti biyar a fice mini a gida kar in kai ga yi ma ki korar kare." Yana gama faɗin haka ya shiga wata ƙaramar ɗaki.

Wani abu na ji ya riƙe mini ƙahon zuciya saboda bakin ciki. Na miƙe jiki a sanyaye kamar wacce aka cirewa laka jiki babu kuzari na sanya tufafina zuciyata na tafarfasa na fice.

Tafiya nake zuciyata sai bugawa take kamar ƙirjina za ta fashe ta fito waje, yayin da idanuwana suka fara yi mini nauyi ina ganin wani dishi-dishin baƙi. Kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raji’un na dinga furtawa har na isa gida.


Da gudu na shiga ɗakin Kakata na hangota tana kewaye ɗaki muna haɗa ido fukanta ya nuna mini damuwar da take ciki na faɗa jikinta na fara rusa wani sabon kukan mai tsuma zuciya da fizgar rai kamar wacce ta rasa uwa da uba lokaci guda.

Wani ruwa na ji ya sauka ta bayana wanda ya ba ni tabbacin hawayen Kaka ne ke zirara.

A take na tsagaita da tawa kukar na juya ina mai goge mata ƙwallar tare da cewa, "Kaka zubar hawayenki ya fi ɗaga mini hankali fiye da halin da nake ciki don Allah ki daina."


Ta sauke ajiyar zuciya, "Shi kenan ba zan kuma ba Maimunatu."

Na nufi bayi don yin wanka da gabatar da sallar asuba da ta kufce mini.

Bayan na idar da sallar tare da yin addu'o'i sai na ji ɗan nutsuwa ta ziyarci zuciyata, Kaka ta dube ni da cewa. “Maimunatu, na shiga tashin hankali ta dalilinki. Na ka sa tsaye na ka sa zaune kwana na yi ban runtsa ba. Na shiga tsaka mai wuya tun bayan dana aike ki sayo maganin cizon sauro ba ki dawo ba. Ina kika je don Allah?”


Hawaye ne suka fara fitowa suna zarya cikin kwarmin idona. Na ce da ita. "Kaka, da na tsallaka titi don sayo maganin sauron, sai na ga shagon a rufe. Juyawar da zan yi sai na ji an ɗauke ni caɗak! An toshe mini baki an jefa ni cikin mota tare da damke idanuna. Ina ji aka yi parking aka ɗauke ni caɗak jefar da ni da aka yi kamar kayan wanki na fahimci cikin falo aka shigo da ni, Yayin da aka buɗe mini idanuna take na ji jijiyoyin idon na raɗaɗi saboda ɗaurin da aka yi musu, ganin kaina da na yi a kantamemen tsakiyar falo shi ya sanya zuciyata bugawa akai-akai na fara rarraba ido."


Nauyayyar ajiyar zuciya na sauke na goge kwallar da ke zirya saman fuskata na runtsa idanuwana, ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mini al'amarin da ya faru da ni a daren jiya.


*Tunani*



Tsaye nake a tsakiyar falo ƙafafuna sun gaza ɗaukata, sai keta zufa nake na durƙushe ƙasa ina rera kuka.

Takun tafiyar dana ji ne ya sanya ni ɗago kai, yanayi mafi muni dana gan shi ne ya sanya ni razana, jikina ya ɗauki rawa kamar mazari. Ya zo gabana ya tsaya da ruwan roba mai sanyi a hannunsa, ya kinne ido ɗaya.


Na sunkuyar da kaina cikin rarraunar murya na ce da shi. "Don Allah, don darajar iyayenka, ina roƙonka da murya mafi ƙasƙanci kar ka keta mini mutunci."


Wani irin dariyar mugunta ya sake, kana ya murtuke fuska ya watso mini sanyayyan ruwan roban da yake sha, sannan ya ajiye a gefe, ya yi mini wani irin mugun kallo tare da sharara mini gigitaccen mari a kuncina. Take naji dodon kunnena ya yi dum! Yayin da ganina ma ya ɗauke, sai dana ɗauki wasu 'yan daƙiƙu sa'ilin nan na dawo hayyacina.

Sai faman huci yake kamar wani kumurcin maciji. Ya ja kofa ya rufe yana mai cewa. "Wa ya ce da ke ana ba wa Hisham haƙuri akan abin da ya yi niyyar yi?" Ya cilla ni kan gado, da ƙarfin tsiya ya cimma burinsa.

Ina kawowa daidai nan da tunanina, na sake sakin kuka mai tsuma zuciya.



Kaka ta sauke ajiyar zuciya. "Kina nufin Hisham ɗan gidan Alhaji Tanimu ne ya keta miki mutunci?" Na gyaɗa mata kai.

Ta ɗora hannu a ka. "Yau abin da nake jin wannan yaron yana yi wa ‘ya’yan wasu shi ne ya yi wa jikata! Me ya sa 'ya'yan masu faɗa aji suke shuka tsiya ba a hukunta su? Yaushe za a samu sauyi a dinga hukunta duk mai laifi ba tare da nuna bambanci ba?"

Na yi murmushin da zan ƙira shi da yaƙe, domin yana bayyana takaicin da ke danƙare a cikin zuciyata ne. "Kaka, hakan zai kasance ne idan adalai ke jan ragama."

Bayan wata ɗaya da faruwar haka, na fara jin rashin kuzari a tattare da ni ga yawan jiri da zazzaɓi mai zafi, kakata ta umurce ni da na ziyarci likita. Bayan an yi mini gwaje-gwaje, likita ya shaida mini ina da juna biyu. Take hantar cikina ta kaɗa, na fara jin wani irin yuuu a tsakiyar kaina.

Na yi fatan mutuwa ga rayuwata, na so a ce mutuwa ta ɗauke ni a madadin na riski kaina a wannan yanayin. "Hisham, yadda ka jefa rayuwata cikin kangi, na lashi takobi kai ma sai ka shiga." Na faɗa a fili, bayan na ciji laɓɓa saboda takaici.

Tun kafin na kai ga zuwa gida na fara yakar damuwar da ke neman yin tasiri a zuciyata kar ya bayyana, saboda tun bayan faruwar wannan al’amarin jinin Kaka ya fara hawa. Da ta tuntuɓe ni mai ke damuna, sai na ce da ita zazzaɓin cizon sauro ne.

Haka rayuwata ta dinga tafiya cikin ƙunci da ƙunar zuciya. Amma duk da haka, na yi wa kaina alƙawarin duk runtsi duk wahala ba zan zubar da wannan cikin ba. Sannan kuma ko da mutane sun farga da halin da nake ciki, zan toshe kunnena akan duk abin da za su faɗa.

Kasancewar ina karatu a Jami'a fannin Shari'a, bayan na fito daga ɗakin jarabawar zangon ƙarshe da nake rubutawa, haka kawai na ji gabana na faɗuwa, ina doso daidai kofar gidanmu na hango dandazon jama'a.

Wani irin firgici ya kama zuciyata. Ina shiga gida idona ya yi tozali da makara, wata yarinya ta tare ni da cewa. "Kaka ta rasu."

Da gudu na zo kan makarar na durƙushe wani irin ƙara na sake, ina gunji tare da kuka na dafe kaina ina cewa, "Wayyo Allah na shiga uku na lalace! Kaka ke kaxai kika rage mini gashi kin tafi kin bar ni."

Nan take zuciyata ta fara bugawa da ƙarfi, wanda ya sa numfashina tsarkewa na ji jiri na ɗaukata. Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba, sai farkawa nayi na gan ni a gadon asibiti. Wannan abin da ya same ni ya zama sanadiyar ɓarewar cikin da nake ɗauke da shi.

Bayan wasu watanni na samu sauki an sallame ni a asibiti ana bikin ƙawata da muka gama Jami'a tare, Allah ya haɗa ni da Kwamishinan ‘yansanda ya sanar da ni da ƙudirinsa na son aurena. Ban ɓoye masa komai ba dangane da ni, ya ce ya ji, ya gani kuma yana sona a haka. Bayan mun xan fahimci juna na wasu ‘yan lokaci, sai muka nufi ƙauyenmu wajen wan mahaifina domin ya yi bincike a kansa. Da ya fahimci nagartarsa, sai aka ɗaura mana aure.

A gidansa na ci gaba da karatu na zama cikakkiyar lauya. Na bayyana masa lokaci ya yi da zan gurfanar da Hisham a kotu, ya goya mini baya aka tura masa sammaci.

Me zan gani! Hisham da mahaifinsa da 'yansandan da suka kai sammaci a gidanmu. Mahaifin Hisham da ya ga mijina abin ya ba shi mamaki ya nuna shi da yatsa. "Tahir! Ku kuka kai ɗana ƙara kotu? Matakin da kake kai a yanzu waye ya tsaya maka ka samu? Lallai dattin talauci da soyayyar mace suke damunka, har suke zuga ka kake ganin karanka ya kai tsaikon da za ka iya ja da ni. To ka sani, sai na gigita rayuwarka da duniyarka idan ba ku janye daga kuskuren da kuke ƙoƙarin tafkawa ba."

Mijina dariya ya yi, "Ikon Allah sai kallo! Wa za ka yi wa barazana, shege ka fasa. Ka sani, ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi."

Girgiza kai ya yi, "Haka ka ce ko? Bari murna karenka ya kama zaki, waɗanda suka fi ku da komai ma sun gaza yin nasara a kanmu."

Na yi murmushin takaici na mayar masa da raddi. "Ka daina bari bahaguwar zuciyarka tana zuga akan kullum kai ke da nasara. Ka yanke ƙauna a wannan karon, gaskiya da hujoji da adalci ne za su yi aiki."

Hisham, ya haɗe fuska kamar girar saniya. Ya ce, "Ke kuma ki rufe kazamin bakinki, mahaifina ba sa'an yin ki ba ne. Za mu je kotun ko don ku ga yadda za ku kunyata."

Guntuwar dariya na yi na ce, "Ɗan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido."

Ya dalla mini muguwar harara. "Dadi mu bar gidan matsiyata." Suka fice.

Shekara guda aka ɗauka ana shari'ar. Labarin shari’ar ya karaɗe ko'ina, waɗanda suke kufule da Hisham duk hankalinsu ya karkata ga shari'ar. Cikin hukuncin Allah na yi nasara aka zartas wa da Hisham hukunci daidai da laifinsa. Mahaifinsa a cikin kotun ya zube a ƙasa aka nufi asibiti da shi.

Na zo gaban Hisham, a ɗimauce ya ɗago kansa, ya haɗa zufa haikan na dube shi sama da ƙasa. "Ka ga yadda al'amarin Ubangiji ya kasance, ina fatan hakan zai zama maka izina da duk kuma mai hali irin naka."

Na kyalkyale da dariya na yi gaba na bar shi.

Haba! Wannan rana ta zama ta musamman gare ni, gani nake ko na gaban Ka'aba bai fi ni farin ciki ba. Na so a ce Kaka tana raye ta ga maƙomar Hisham, sai dai kash! Allah bai nufa ba.

Mahaifin Hisham waɗanda suke kusa da shi sun shaida mini dalilin faɗuwa da ya yi ya haɗu da larurar shanyewar ɓarin jiki.