Chapter 5
by @mamanyusuf
♠️♠️ *HUSNA KO HUZNA* ♠️♠️
*MALLAKAR*
*Maryam Umar Abdullah (mmn Yusuf)*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*____________________________________*
*Littafin na kudi ne 200 maiso ta turo kudinta ta wannan account number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Account no 1647784887
Account name Access bank
Name Maryam Umar
Ko katin waya ta wannan number 👉🏻***
🅿️ 5
.....................Ana haka kwatsam sai Alhaji Hussain ya had'u da Hajiya Aliya , wanda cikin k'ank'anin lokaci soyayya mai k'arfi tashiga tsakaninsu , da yake macece da Allah ya hore mata iya kissa da kisisina duk wani Abu da tasan zai janyo mata hankalinshi shi takeyi , ai kuwa tayi nasara don lokaci daya ta shiga zuciyarshi ,sai dai yarasa yadda zaiyi ya fad'awa matanshi cewa zai k'ara aure musamman Hajiya Ni'ima da yake jin tsoron ta had acikin zuciyarshi , a haka har maganar aure ta kankama basu Sani Ba ,
Lokacin da suka samu labari kuwa haukane kawai Hajiya Ni'ima batayi Ba ,gaba d'aya ta d'aga hankalinta ta d'agawa mai Gidan ,Hajiya Lauratu kuwa wato Mamah ko kad'an bata d'aga hankalinta Ba hasalima ko a kwalar rigarta fatan ta dai Allah ya basu zaman lafiya ,
Hajiya ni'ima kuwa ganin masifarta batasa ya fasa komai Ba saima cigaba da shirye-shiryen shi da yakeyi yasa tuni ta kira k'awarta *Talatu bariki* suka shiga bin gidajen bokaye da malaman tsibbu ,sai dai da yake Allah ya nufa sai anyi sai basu samu nasara Ba tanaji tana gani aka d'aura auren Alhaji Hussain da Hajiya Aliya a wata safiyar assabar ,
Zamansu zamane irin na tsananin kishi tareda hassadar juna , da yake Hajiya Aliya itama Ba daga baya Ba wajan son kai da masifar tsiya sai ya zamana kullum Gidan acikin tashin hankali suke , sannan Alhaji Hussain wato *Abee* sam baya iya tsawatar masu musamman ma Hajiya ni'ima don komai zatayi *Abee* baya ganin laifinta koda itace batada gaskiya hasalima bayanta yake bi , ganin hakan yasa Hajiya Aliya canza taku ta hanyar kissa da kisisna inda cikin ruwan sanyi take rama bunda duk Hajiya Ni'ima tayi mata ,
Bayan wasu shekaru Hajiya Aliya wato *Ammi* kamar yadda yaran kece mata ta haifi yaranta hudu *Aliyu* shine babba sai *Jamil* sai *Safiya* da auta *Surayya* a lokacin haihuwar *Safiya* ne itama Hajiya Ni'ima wato *Umma* ta haifi yarta mai suna *Nasma* kwana arba'in ne tsakaninsu , *surayya* Nada shekara biyar Allah ya bawa *Mamah* ciki wanda tun bayan haihuwar *Mu'azzam* da *Fatima* bata k'ara haihuwa Ba sai yanzu , bayan wata Tara ta sauka lafiya bayan tasha bak'ar wuya wanda har yayi sanadin da aka cire mata mahifa ,inda Allah ya azurta ta da 'yan biyu mace da namiji , inda ranar suna yaran sukaci suna *Hassan* da *Hussaina* wanda tun daga Kansu ba'a k'ara haihuwa a Gidan Ba wanda yanzu haka yaran sunada shekara 8 a duniya shekara d'ayane tsakaninsu da su *Husna da Huzna* wanna shine cikakken tarihinsu a tak'aice ..........
_________________
Assalamu Alaikum *Mamah* tayi sallama ta shigo d'akin na maigidan su da yake yau itace da girki,
Zaune yake akan wata kyakyawar darduma gabanshi kuwa kayan ciye-ciye ne kala-kala ,ya lumshe idonshi yana aikin tunani wanda a zahiri ko sallamar Mamah baiji Ba yayi nisa sosai cikin tunanin halin da d'an uwanshi k'waya d'aya tilo yake ciki kuma yakasa taimaka masa yarasa abunda ke damunshi duk yadda yayi niyar taimakawa d'an uwanshi sai ya kasa lokaci daya sai yaji ko sunanshi bayason tunawa wanda sau tari ko ganin k'aramun d'anshi *Hassan* bayason yi don duk lokacin da ya kalleshi zaiga tamkar dan uwan nashi yake kallo tsabar yadda suke kama ga kuma sunasu da yazo iri daya ,yarasa miyasa yakejin hakan , abun yana damun zuciyarshi sosai amma yakasa sanarwa da kowa,
Alhaji ,Alhaji ,firgigit yayi yace na'am Maman yara yaushe kika shigo ne ?
.....haba Alhaji taya zakasan na shigo kana irin wannan tunanin! Mi yake damunka ne ? Na kula a 'yan kwanakin nan kana cikin damuwa yakamata ka Sanar dani abunda yake damunka ,kasani damuwarka damuwa tace pls Abban Mu'azzam ka gayamun abunda yake sanyaka Yawan tunani irin wannan , tayi maganar cikin sanyayyar murya tare da addu'ar Allah yasa addu'arsu ce ta kar'bu ,
Ajiyar zuciya yayi mai k'arfi kamun yace
.....…....wato Maman yara abunda yake damuna shine a 'yan kwanakin nan ina Yawan mafarkai da d'an uwana Hassan , narasa dalilin da yasa na wufitar dashi alhalin nasani yana bukatar kulawata , bayada kowa sai Allah sai ni sai Inna, ita kanta Inna ta tsufa da yawa sosai take buk'atar kulawata amma narasa miyasa na kasa taimakawa dan uwana da mahaifiyata wannan wane irin bala'i ne gani da dukiya mai tarin yawa amma ace wadan da nafiso a rayuwata suna cikin k'unci da wahala, !!! Wasu hawaye masu zafi suka zubo mashi, hakan yasa yakasa ci gaba da magana sai girgiza kanshi da yakeyi alamar abun nacin ranshi sosai ,
Tunda yafara magana banda Alhamdulillah Ba abunda Mamah ke nanatawa acikin zuciyarta , dama tasani Ba abunda yake d'orewa banda sarautar ubangiji , tajima tana jiran wannan ranar ,ranar da mijin nasu zai dawo cikin hayyacinshi akan mugun k'ullin da aka mashi wanda tajima da sanin shiga tsakaninsu akayi , wanda hakan yasa ta tashi tsaye wajan nemo mashi Maganin karya sammu batareda masaniyarshi ba kuma Alhamdulillah tunda alamu ya nuna ansamu nasara don a da Ba wanda y isa yayi ma Alhaji zancan dan uwanshi ya zauna lafiya ,sai gashi yau da kanshi yake zancan d'an uwanshi da mahaifiyarshi ,
Alhamdulillah Alhamdulillah Ba abunda zamuce da Allah sai godiya tunda har Allah yasa ka gane abunda kakeyi Ba dai-dai bane ,yanzu shawarar da zan baka Alhaji itace mi zai hana ka dawo da Inna da d'an uwanka cikin Gidan nan ,tunda Alhamdulillah kana da halin yin hakan , kaga sai su zauna a wancan 'bangaren da Ba kowa aciki naga shikenan magana ta k'are don indai yana tare da kai to duk irin haka bazata rink'a faruwa ba,
Jimmm yayi yana tunani kamun yace tabbas Lauratu kin kawo shawara mai kyau , shiyasa a kullum nake alfahari dake don kullum k'ok'arinki na kiga kin sanya ni a hanya ne wanda hakan yasa sam bana iya 'boye maki damuwa ta Don nasan zaki bani shawara ta gari nagode sosai Allah yamaki albarka ,
"Abunda nakeso yanzu shine ki kira Mu'azzam ki gaya mashi komai take ya ajiye yazo yau ina nemanshi inaso gaba d'ayanku ku shirya daga ku har yaran zamuje k'auyen dala gobe zamuyi kamar kwana ukku a acan kamun mu tattaro mu dawo gaba daya ,
Cike da tsananin farinciki tace angama Abban Mu'azzam amma ka gayawa matanka da kanka ni bazan iyaba gaskiya , murmushi yayi don yasan halinta sosai sam batason raini shiyasa taja girmanta sosai don bata shiga shirginsu ,
" to ranki ya dad'e uwar gida ran gida yayi maganar yana janyo ha'barta cike da shauk'in soyayyarta , harga Allah yana tsananin sonta fiye da sauran matansa amma yarasa miyasa yake mata wasu abubuwan na rashin kyautatawa don ma tanada hak'uri sosai ,
........hmmm Alhaji dad'in baki ko ? Tayi maganar cikin wani irin salo na Jan hankali wanda hakan yasa baisan sanda ya janyo ta jikin shi ba lokaci daya ya sanya bakinshi cikin nata yafara bata zazzafan kiss kamar zai tsinka harshenta ,
Hmmmmmmm tsoffi ma sun iya love😜
Jikinta har rawa yake lokacin da ta bar jikin k'ofar bayan ta share mintuna masu yawa tana lek'ensu ,duk ta had'a zufa sai sambatu takeyi kamar tababba , Hajiya Ni'ima kenan da take la'be jikin k'ofar d'akin Abee tun lokacin da Mamah ta shiga d'akin ,
Duk abunda suka tattauna taji ,bata zarce ko ina Ba sai bedroom dinta , nanfa tashiga safa da marwa yayinda ta dunk'ule hannunta d'aya tana kaiwa d'aya naushi cike da 'bacin rai ta fara magana ,
"Lallai Laure bakisan wacece Ni'ima ba, jinta kikeyi , tabbas sai kinyi danasanin rusamun shirina , muje zuwa wallahi sai kinyi Dana sanin shiga lamarina da kikayi ,
Wayarta ta dauka ta kira k'awarta Talatu Bariki , ringing biyu aka d'aga
........." Hello ha..ja..jjuuu tayi maganar cikin in ina ,tsaki Umma tayi tace talatu kina ina, ??
......wani irin dogon nishi taja kamun tace ahhh Hajiya ina tare da Alhaji Hali lafiya dai ,
Wani irin dogon tsaki Umma tak'ara ja kamun tace wai nikam Talatu wace irin jarababba ce ke, ke kenan kullum cikin Abu d'aya to wallahi kidai bi a hankali tun basu hallakaki ba
.......hhhhhhhh wata irin dariya Talatu ta kece da ita kamun tace habadai Hajajju ai wallahi namijin da zai hallakani ban Ganshiba ...kedai bar wannan maganar mi yake faruwa ne? don nasan baki jiran banza da walakin wai Goro a miya .
Nan Umma ta kwashe komai ta gayamata kamun ta k'ara da cewa Babbar damuwa ta itace kinsan *boka dan Manu* ya gargad'e mu akan kar mu bari Alhaji ya taka k'afarsa a wannan k'auyen inba hakaba duk wani aiki da mukayi masa zai warware ,yanzu gashi wannan munafukar Matar tashi ta sanyashi tafiya Garin kuma wai har yana cewa gabadayanmu zamuje , sannan ban isa nayi mashi musu Ba don gudun abunda Zaije yazo don nasani tunda har ya yarda da tafiya wannan k'auyen tofa abubuwa sun fara warwarewa ,
......to ki saurara kiji abunda zan fad'amaki , karki yarda kiyi mashi gardama kinsani sarai kokadan baya sonki kawai asiri ne ke aiki akanshi har yanzu ki bari insha Allah zuwa jibi zan dawo don yanzu haka muna Lagos ,da na dawo zankoma wajan boka sai musan abunyi ,
..........to shikenan zanyi yadda kikace amma dai an takurani wallahi zaman k'wauye har kwana ukku haba,
......kedai kiyi hakuri kiyi yadda nace zan kiraki da safe don yanzu Baby yana jirana bye, ta kashe wayar batare da tajira cewarta Ba
...mrtssss jarababba kawai daga haka tayi jifa da wayar taci gaba da tunanin mafita,
_________________
Yar d'iyata 'yar d'iyata mikikeso 'yar d'iyata inbaki madara zakisha tayi maganar yayinda take d'aga kazar Sama tana cillata wai a doli wasa ake mata , wanda gaba daya kazar ta firgice inda zata gudu kawai take nema amma Ba hali don turke na musamman aka mata aka d'aureta da igiya ,a cewarta wai kazar bata jin magana ko ance kartaje yawo sai taje shiyasa tayi mata rurke ta daureta kuma ahaka sai wahalar da ita takeyi duk kazar tafita hayyacinta , Husna kenan uwar rigima ,
.......duk isakacin da takeyi mama na kallonta batace mata komai Ba don ita so takeyi ma kazar ta mutu a huta, tunda aka basu kajin nan banda wahala Ba abunda suke basu ,don itama Huzna jiya har wanka tayiwa tata kazar a cewarta tayi Datti da yawa kuma tanason kazarta tafi ta husna Fari da kyau ,
Aikuwa k'iris ya rage kazar ta mutu don Ba k'aramun ruwa tasha ba wanda da k'yar aka samu kazar ta tashi gatanan har yanzu batada wani kuzari , to shine ita kuma Husna yau ta tsiri NATA iskancin , wai kazar batajin magana ,
Sosai mama taso ta yanka kajin a cinye kowa ya huta amma Suka aza rigima sosai Wanda a lokacin wuni sunayi suna mata rigima da koke-koke , ganin haka yasa Abba ya hana a yanka masu kajin , wanda wani abokinshi ne yayi masu kyautar su ,
Suna Haka Abba yayi sallama ya shigo.
....amsawa Mama tayi ,tace sannu da zuwa malam ,
.....yawwa Maman biyu ya jikin naki ? Da sauki ko don naga har kin fito waje ,
.....naji sauki sosai malam yanzu ma Ba abunda yake damuna,
....to Allah ya k'ara sauki , ai insha Allah kin kusa hutawa da wahalar nan tunda watanki ya tsaya ,
......hakane malam Allah dai ya raba mu lafiya suka amsa da amin,
Husna yau ko gaisuwa bazan samu ba?
.....turo bakinta tayi cikin siririyar muryar ta tace Abba Ba Kaine kak'i tafiya dani inda Inna ba . tayi maganar kamar zatayi kuka ,
....murmushi yayi yace hoo Husna rigima. To inda Innar bak'onkine ? Ko bakisan waje Ba sai na tafi dake ,
...zumburo bakinta tayi cike da shagwa'ba tace to amma Abba ai ka tafi tareda Huzna nice bazaka daniba ,
...Ba inda naje da Huzna tananan wajan Talatuwa mai k'osai tana wasa nima banje ba yanzu dai zan tafi don haka taso mu tafi tunda kin nace ,
Yawwa Abbanmu bari na d'auko takalmina , yawwa mama ki kulamun da kazata karki barta take yawo kinji mama kuma karki bari kazar Huzna taci zalunta don naga alamar muguwa ce kinji Mama, tayi maganar a marairaice ganin mama ko kallonta batayi Ba ,
Kallonshi Abba yakai akan kazar , ido ya zaro waje yace "Husna mizan gani haka , kin kama kaza kin mata irin wannan d'aurin harga wuyanta in ta mutu fa , .......ai Abba batajine shiyasa namata haka ,
....mrtssss kinga kwanceta kizo muje karki 'batamun lokaci ,inaga gaba daya sai kunyi ajalin kajin nan wajan shegen rashin jin ku ,
....mama tace hmmm ai malam Halliru ya had'amu da aiki ni sam banji Dadin wannan kyautar Ba wallahi don nasan halinsu sosai yanzu gashi munaso mu d'an canza yawu amma sun hanamu k'arshenta sai sun kashe kajin sunyi mussai , dariya Abba yayi yace ai wad'an nan kajin mai cinsu sai ya shirya , itama dariya kawai tayi don ta kudurta a ranta sai ta yanka kajin nan don bazata barsu su mutu a banza Ba alhalin sunaso suma, ahaka sukayi sallama da Abba inda ya nufi Gidan. Inna , a hanya suka had'u da Huzna duk tayi butu-butu da k'asa ,tana ganinsu kuwa tace lallai lallai sai tabisu itama , Abba yaso taje gida ta wanke jikinta amma fafur tak'i doli a haka ta bisu ,
Sunyi nisa sosai da yake sunada d'an tazara tsakaninsu da Gidan Inna kwatsam sai suka had'u da malam ilya mai kifi ,ya na dauke da kifinshi a akai yana tafiya yana fadin Asai kifi kifi mai kyau mai dad'i , aikuwa kamar masu jira a tare sukace "Abba ka siya mana kifi , sai da zuciya Abba ta buga don bashida ko sisi sannan yana gudun rigimar da zasuyi janyo mashi , cikin muryar lallashi ya dubesu yace kunga kud'ina yana wajan inna ku bari muje sai na kar'bo in yaso sai naje wajanshi na siyo maku kunji 'yan albarka ,
Lokaci daya suka kwa'be fuska alamar rashin yarda , amma basuce komai Ba sai bin malam ilya dasukayi da kallo da alamar rashin yarda a tare dasu ,
Suna haka kamar daga Sama sukaga manyan motoci kusan 3 sun shigo Layin aguje. Motocine na alfarma dukkansu bak'ak'e sunzo GAF da su Abba ne da yake Su Abba suna kusa da wani wajan da ruwan kwatami yake kwanciya basu riga da sun tsallakaba kwatsam sai ji sukayi shaaaaa motocin sunbi ta cikin ruwan aikuwa nan take ruwan ya watsarwa Huzzna da Abba a jiki batare da sun ankaraba wani irin ihu Huzna tayi kamun tace kam Bala'i 😳😳motocin har sunyi gaba sai kuma gasu sun sawo da baya ,saida suka zo Dad dasune sannan aka zuge glass din motar na baya , Ba zato Ba tsammani kwatsam Abba ya had'a ido da Gudan jininsa kuma abokin tagwaicinshi wato Alhaji Hussanin ,
Nunashi Abba yayi da hannu amma yakasa magana yayinda shi ma Alhaji Hussain yake kallon shi bako kyaftawa ,yayinda Huzna ta kafe wajan da matuk'in motar yake da ido cikin tsananin jin haushi tana jiran taga wane dan rainin hankali ne wannan ,
Lokacin da Husna taga cewa gaba daya fa hankalin su baya kanta yatafi ga junansu aikuwa cikin sand'a tafara ja da baya kamun ta arce da mugun gudu tabi bayan ilya mai kifi tana cewa ai wallahi tunda raina ya biya sai naci kifin nan ........,.........✍🏼
*Na kawo karshen free pages maison cigaba ta turo 200 asata paid grp karku bari abaku labari chakwakiyar yanzu aka fara*
Mutara a gobe takuce Mmn yusup😍😍😍😍😍
💃🏻💃🏻 *HAMSHAKIYAR MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI*💃🏻💃🏻💃🏻
Hallau dai takuce Mmn yusup mai gyaran mata ciki da waje😉😉😉😉😉😉😉
Kadan daga cikin kayan da muke dasu👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Kalolin gari
Kalolin gumba
Kalolin na matsi
Kalolin tsumi
Matan gaske
Gigitashi
Emergency
Dan mannau
Butar mai jego
Rantse bakida kishiya
Kai abubuwan fa da yawa hajiyata wanda bazai yiwu na iya rubutasu gaba daya Ba gamaison ganewa idonshi kalolin kayan zata iya nemana ta PC ***
*Muna sayar da kayan hadin kaza ga wanda suke nesa sai a masu bayani su dafa da Kansu*
Sai kunzo. Ina maraba daku😘😘😘😘😘😘😘💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻