FreeArewaPen original
HUSNA KO HUZNA
- 1views
- 30chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Book writer
Sample · Chapter 1
♠️♠️ *HUSNA KO HUZNA* ♠️♠️*MALLAKAR**MARYAM UMAR (MMN YUSUF)**____________________________________**🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼**🇦SSOCIATION🤝🏻*'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''*____________________________________*_Wannan littafin na kudi ne gamai buk'ata zata biya 200 ta wannan account number din 👇🏻👇🏻2400915841 Maryam Umar zenith bankSai ku tura shaidar biyanku ta wannan number 👉🏻****Zaku dinga samun post sau biyu a Rana ba d'aga k'afa insha Allah**LABARIN HUSNA KO HUZNA LABARI NE AKAN WASU YARA 'YAN BIYU MASU MATUK'AR KISHI DA JUNA ,LABARINA K'AGAGGEN LABARINE BANYI DON WANI KO WATA BA , KU BIYONI DONJINA WATA IRIN CHAKWAKIYA*~YADDA NAFARA LAFIYA ALLAH YA NUNAMUN NAGAMA LAFIYA~BISMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM🅿️ 1Zaune take tayi tagumi , abun duniya duk ya isheta, ga kuma k'aton cikinta da yakai ko'ina akan girma, zama dak'yar, tashi dak'yar , tayi zurfi sosai cikin tunanin matsalar 'ya'yanta, tsakanin Husna da Huzna tarasa wayafi wani mugunta , yara k'anani sai muguntar tsiya , tunda ta haifesu bata huta ba ,mahaifinsu bai huta ba , duk da yana iyakar k'ok'arinshi a kansu.Ya fito daga Band'aki ya dubi matarshi Hafsi yace "lafiya dai Maman Biyu tunaninmi kikeyi haka? Nisawa tayi tace "bakomai Baban Husna ,kawai dai........... Batasamu damar k'arasa magarba suka ga Huzna kamar daga Sama tafito daga d'akinsu tana tunzuro baki, yarinya ce 'Yar shekara biyar mai masifar kyau kamar aljana , tace , " Mama naji kin kira Abba da Baban Husna ,wai miyasa kikafi son Husna a kaina ne , tana maganar kamar zatayi kuka , tsaki mama tayi don ji take kamar ta shak'eta don haushinta da takeji, kallon uwar tayi tayi k'wafa tace " to naga yanda za'ayi nikuma ki haife wannan cikin , kuma wallahi Husna ma bazan barta ba" Dukkansu a razane suka d'aga idonsu suka kalleta don sunsan duk abunda Huzna ta ambata to kamar yankan wuk'ane , Abban ya kalleta cikin sigar lallashi yace Haba 'Yar Baba karkiyiwa mahaifiyar ki haka kinji , ai dake da Husna duk d'aya ne duk muna sonku ba Wanda yafi wani acikin ku , don haka kar nak'arajin kinwa mahaifiyarki iri wanan furucin kinji ko, Wani narke fuska tayi Wanda hakan ba k'aramun fito da kyaun ta yayi , cikin shagwa'ba tace " wallahi ni ban yarda ba Abba sai dai kuce kunfi sona akan Husna wallahi inba haka ba......... Sai kuma tayi shiru , Hankalin Abba ya tashi don yasan Huzna ciki da bai tun tana zanen goyo take da muguwar mugunta ,Wanda har tsoro abun ke bashi, nan fa yashiga lalla'bata amma Sam ta kafe , yace "to shikenan tunda so kike Maman taku ta mutu , nan da nan ta zaro ido. Waje cikin tsoro tace mutuwa zatayi Abb...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.