Chapter 8
by @mamanyusuf
♠️♠️ *HUSNA KO HUZNA* ♠️♠️
*MALLAKAR*
*Maryam Umar Abdullah (mmn Yusuf)*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*____________________________________*
*Littafin na kudi ne 200 maiso ta turo kudinta ta wannan account number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Account no 1647784887
Account name Access bank
Name Maryam Umar
Ko katin waya ta wannan number 👉🏻***
🅿️-8
Wai kai sai yaushe zakayi aure da a Garin nan kake da yanzu kanada yara biyu ko ukku ,
Wata irin dariya ce ta su'bucewa Yaya Mu'azzam yace kajimu da tsohuwa yanzu saboda Allah inna ta ina na isa aure kofa karatu ban gamaba gaba daya shekarata nawa ne inaji 26 ne ,
Tsaki Inna tayi tace shekara Ashirin da shida ne kawai to bari kaji mu a nan mai shekara ashirin da shida ai tuzurune , to bakayi aure yanzu ba sai yaushe zakayi ? Ko sai kagama tsofewa a gida ,
Tsadadden murmushin shi yayi yace "share kawai Inna bazaki gane bane , Mamah dake gefe tana zuba masu kalolin abincin da suka zo dashi tace Ai Inna Yanzu yana karatu ne amma yakusa gamawa yana gamawa doli zai fitar da Matar aure Don nagaji da zama da wannan mai murd'dad'd'en halin , leme baki Inna tayi tace ai duk ku kuke d'aure mashi gindi ,yanzu shi in zaiyi aduba mashi wad'an nan fa ? Tayi maganar tana nuna su Anty Harira taci gaba da cewa yanzu saboda Allah kamar wad'an nan uwayen matan za'a zauna dasu ba aure to wai ma ubanmi sukeyi a gidan in anzo ai sai akasa bambancewa tsakanin ku dasu , Mama ce ta tare zancan Don kar abun yayi tsawo Don ta lura Inna acike take da kowa a wannan karon sam duk wannan hak'urin nata da kawaici yanzu babu shi tace
" ai Inna har yanzu basu samu mijin bane amma ai in sun samu aurar dasu zamuyi fatan dai Allah ya kawo masu nagari ,
Tsaki Inna tayi tace ai kaji irinta dama taya wani zai kawo kanshi garesu suna irin wannan iskancin yanzu saboda Allah dubi irin shigar da yaran nan sukeyi saikace yaran arna kuma Hussaini yana kallonsu yakasa tsawatar masu saboda yazama mijin tace ko ? To mu wannan ba tarbiyar nan Gidan bace yazama doli su canza taku inba hakaba wallahi sai nasa anemo masu maza anan Garin abayar dasu sadak'a in yaso naga k'arshen iskanci tayi maganar tana zabga masu harara Don ba k'aramun haushi suka bata ba wai a matsayinta na uwar mahaifinsu sam batada darajar da zasu gayar da ita tundazu tana kula dasu sai wani toshe-toshen hanci sukeyi ko ubanwa ke wari oho
What😳lallai ma kakus ki dubemu Sama da k'asa kinga munyi maki kama da wad'an da zasu iya ko kwana ne a wannan k'auyen? bare har kice amana aure aciki ?Wata dariyar rainin hankali Saudat tayi tace wai tatsuniya
Anty Harira tayi tsaki tace dan Allah yimana shiru saudat cinkikamun kunne kema kika kulata har kikaji abunda take cewa ,
Salati inna ta sanya tace yanzu rashin kunyar taku har takai haka lallai yau nak'ara tabbatar da ba abunda kuka baro na uwarku ai in bakuyi hakaba sam Ba Ni'ima ta haifeku ba dangin marasa tarbiya ,
Duk abun nan da akeyi Umma na zaune tana taunar cingom sai k'as-k'as-k'as take irin na cikakkun 'yan bariki ranta in yayi Dubu to ya 'baci kuma tabbas sai inna tasan tacemata dangin marasa tarbiya , Don wallahi sai ta nuna mata wacece Ni'ima yanzu ma tana bin dokokin boka ne Don ya shaida mata karta kuskura tace zatayi jayayya da tsohuwar ta jira har su dawo zai sake sabon aiki akan Abee ,wannan yasa kawai take dag'ama tsohuwar k'afa da tuni ta shukkamata rashin mutunci wallahi😏
Ammi kuwa duk da tana cike da Inna amma bata nuna komai ba saima murmushi da tayi tace
"Sai hak'uri Inna kinsan halin yaran zamani muma acan hak'uri kawai mukeyi da rashin mutuncinsu kingansu nan ba wanda suka bari..............to munafuka algunguma uwayen kissa da kisisina ke har kinada bakin da zaki cewa su Saudat basuda mutunci ,duk irin fitsarar Safiya da Surayya to wallahi bari kiji bana son munafunci wallahi zan miki abunda bakiyi zato ba kindai San wacece Ni'ima tayi k'wafa taci gaba da dannar wayarta Don tana ganin in ta ce zata kula inna a yau komai zai iya lalacewa Don ayadda taga Abee na rawar k'afa akan tsohuwar nan to tasani komai zai iya faruwa ,
Ammi kuwa murmushi kawai tayi yayinda ta fakaici idon mutane tayiwa Umma signal da ido alamar zamu had'u , kamun tace Ayya Yaya Ni'ima ai ba fad'a na nemaba Allah yabaki hak'uri kawai dai abunda yaran keyine basa kyautawa amma bazan k'ara magana ba tunda abun yazama haka,
Wani ban zan kallon na tsantsar tsana Umma ta aikamata dashi aranta kuwa tunani takeyi yakamata fa ta takawa Aliya birki inba haka ba nan gaba zata iya zamemata d'an hakin da ka raina, Don ta kula Matar bala'in makirace ta bugawa a jarida amma Ba komai zatasan abunyi
Hmmm lallai Ashe haka Gidan naku yake har Hussaini yakeso ya jaj'i'beni na koma !! To badani ba dasake ba inda zan biku don ba shegen da zaisamun hawan jini ina zamana lafiya ,
Hehehe Haka mukeso kakus mu dama can bama buk'atar zamanku wallahi kawai Abee ne ya matsa ............
Tunda suka fara maganan yana duk'e da kanshi yana aikin da yazame mashi kamar ibada wato dannar waya kai ka rantse da Allah baisan da wanzuwarsu ba a wajan tsabar yadda yayi ko in kula dasu ,duk kuwa da irin yadda zuciyarshi ke suya akan maganganun yaran, ranshine yaji ya 'baci sosai Don ya kula in bai takamasu birki ba zasu iya wargazamashi shirinshi na komawar inna Don yasani inhar inna bata yarda ta bisu ba tofa Abba bazai ta'ba yarda ya tafi ya barta ba ,
Bud'e baki Nasma tayi zata k'ara magana kenan sai jin saukar tagwayen maruuka biyu tayi a kan fuskarta. Lokaci daya jinta da ganinta suka d'auke zai k'ara mata wani ne Umma ta rik'e hannunshi , fisge hannunshi yayi da sauri ya nufi Saudat da Anty Harira bel ya cire yafara nad'a masu na jaki dama shi baya masu ta sauki cin ubansu yake kuma babu Wanda ya isa ya hanashi shiyasa duk suke matuk'ar shakkarshi , gaba dayansu ihu sukeyi kamar zasu tashi Gidan ,
Su Safiya da mahaifiyarsu kuwa banda dariya ba abunda sukeyu dama suna sane sukayi shiru Don sun San tunda Yaya Mugu na nan kamar yadda suke ce mashi tofa lallai bazasu sha da dadi ba shiyasa sukayi lifff yanzu kuwa sai dariyar k'eta sukeyi
Da sauri Umma ta rirrik'eshi tace kul kul wallahi Mu'azzam ina gargad'inka akan yarana kafita hanyarsu tunda ba bayin uwarka bane akan mi duk lokacin da haukanka ya tashi sai ka rinka saukewa akan yarana to wallahi ahir dinka wallahi duk randa na waiwayo kanka bakaji dadi ba tayi maganar cikin masifa duk kuwa da k'arfin haline kawai takeyi. Don ita kanta tana tsoron fushi irin na Mu'azzam haka yake komawa tamkar mai jinnu bayaji baya gani in yafara masifa wannan yasama take dan d'aga mashi k'afa Don tsaf zai iya karya wata daga cikin yaranta sam bashida hankali in ranshi ya 'baci kuma ba wanda ya isa ya sauko dashi.
Da sauri mama tazo ta janyeshi ganin yadda jikinshi ke wani irin rawa tsabar yadda ranshi ya 'baci ,
Inna tace Alhamdulillah Allah dai yama albarka Ibrahimu wallahi kayimun dai-dai ka nunamun kai ka gaji mutunci kasan girman na gaba da kai , marasa mutuncin banza ai Baku yar a k'asa ba gado kukayi Don nan wani zuwa da uwarku tayi Garin nan agaban mutanen unguwa ba irin cin mutncin da batamun ba har kuka saida tasani kuma a gaba Hussaini amma da yake ta shanyeshi ba abunda ya iyayi to kusani wallahi ada banyi niyar komawa inda kukeba sam Don nafi buk'atar zamana ana akan can inda kuke tutiya dashi amma yanzu nafasa kudirina zan biku na zauna daku wallahi jikokina kadai sun isa su gyara maku zama duk sai kungane k'aryar rashin mutunci kukeyi , .............Don Allah inna kiyi hakuri cewa Mamah kamar zatayi kuka ganin yadda ran Inna ya 'baci dama tasan za'a Rina tunda aka had'u waje d'aya doli irin wannan zai faru Don acan Gidan ma kullum cikin tashin hankali ake in wannan yayi da wannan wannan zaiyi da wancan gida yakoma kamar sansanin yak'i
Yawan hayaniyarsu ce ta tayar da Huzna daga Baccin da ya dauketa a saman bishiya ,saukowa tayi tayi mik'a sannan tabaro wajan tana turo bakinta gaba alamar sun dameta da hayaniya amma bari tashiga taga abunda akema hayaniya haka,
_________________
😳Kazar wa za'a yanka Abba ? Amma dai ta Huzna zaku yanka ko ? Don wallahi ni bamai cin kazar nan Abba wallahi duk wanda ya yankarmun kaza da wanda. Ya cita hmmmm , hararata Mama tayi tace suk abunda zakiyi kiyi amma yau sai na yanka kajin nan Don nagaji da ganinsu ,na huta suma su huta da azabar da kuke gana masu tayau daban ta gobe daban ,koda jin haka sai Husna ta zunduma wani irin ihu wanda har mak'ota saida sukaji nanfa tafad'i k'asa tafara birgima ak'asa kamar macijiya
Tsabar haushi yasa Abba dauko wata yar k'aramar wayar caja yafara tsula mata aikuwa ihu take ba k'ak'k'autawa mak'ota kuwa sai dadi sukeji , don bak'aramr wahalar yaran suke sha ba dasu da yaransu ba wanda ya tsira kuma in kace zakayi magana yanzu sai kaga wani mummunan Abu yafaru da kai doli haka kowa yake hak'ura da iskancinsu yara kamar yaran shaid'anu
Gaba daya sau biyu. Kawai Abba ya daketa amma ihu take kamar wadda ake yankawa kamar kibiya haka tayi wuf ta isa inda kazarta take ta d'auketa ta rongume kamun Abba ya Ankara har tayi wuf ta fice daga Gidan , ganin haka yasa Abba bin bayanta taku biyu zuwa ukku ya damk'ota ya dawo da ita cikin Gidan haka Husna tanaji tana gani Abba ya yanka kajin nan ya mik'awa mama ,itakuma mama cike da murna yau tarabu da k'aya ta kar'bi kajin ta sanya a roba kamun ta hura wuta ta d'ora ruwan zafi ta koma gefe tana jiran ruwan yayi tazubama kajin ta figesu koba komai dai yau zasu canza yawu
Tunda aka yanka kajin Husna takoma gefe ta zauna banda ajiyar zuciya ba abunda takeyi yayinda ta tsurawa tukunyar da aka d'ora ruwan ido ,......yayinda Abba ya fita Neman cefane , da yake Abee yajima da barin Gidan yaje ganin wani tsohon abokinshi dan Gidan Maigari shiyasa duk abunda ake baisani ba ,
_________________
Kamar an jehota haka ta fad'o Gidan wanda shigo
warta yayi dai-dai da dawowar Yaya Aliyu da Jamil daga fitan da sukayi don zaga gari ,
Cikin tsiwa ta kallesu tace kai wai lafiya kukazo Gidan mutane kuna hanasu bacci ? Gaba daya 'yan matan zabga mata harara sukayi don dukkansu sosai sukejin tsanar yarinyar ,
UMMA kuwa tsura mata ido tayi tana karantar ta hade da mamakinta ,
Bud'e baki tayi zatayi magana kenan sai kuma ta zaro ido waje tare da cewa nashiga ukku wallahi wani Abu yafaru da kazata ta d'ora hannunta akai , 🙆🏻♀️ da sauri ta juya zata bar Gidan saiji tayi an damk'i hannuta da sauri ta juyo don ganin wane mai tsautsayin ne azatonta ko acikin 'yan matan ne
Ido hudu sukayi da Yaya mu'azzam fuskar nan sam ba fara'a cikin kaushin murya yace " ke ki natsu wallahi kona sassa'ba maki kamanni don naga alamar kanki na rawa to wallahi zan gyara maki zama , uban waye sa'anki anan wajan da zakizo kinama mutane magana a haka yar tatsitsiya dake sai aukin rashin mutunci ,
Kallon Mamah yayi yace Mamah bani Abincin da zankai Inda Mama ,don in ban bar Gidan nan ba zan iya karya kafafun yaran nan wallahi , harara ya watsa masu kamun yace dagaku har wad'an nan yantatsitsin sai na gyara maku zama wallahi,
Hahahaha to d'an gayu Allah yasa bamune zamu gyara maka zama ba , yanzu dai sauri nake zanje na duba kazata kabari zamu had'u anjima tayi maganar tana kokarin janye hannunta , don harga Allah hankalinta yayi gida inda kazarta shiyasa sam bata lura sa yanayin Yaya mu'azzam ba ,
Tunda tafara magana kallonta yake cikin tsananin 'bacin rai hannu ya d'aga zai daketa kamar daga sama yaji inna na fadin kai-kai Ibarahimu karka kuskura ta ta'bata.............✍🏼