Chapter 15
by @mamanyusuf
♠️♠️ *HUSNA KO HUZNA* ♠️♠️
*MALLAKAR*
*Maryam Umar Abdullah (mmn Yusuf)*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*____________________________________*
*Littafin na kudi ne 200 maiso ta turo kudinta ta wannan account number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Account no 1647784887
Account name Access bank
Name Maryam Umar
Ko katin waya ta wannan number 👉🏻***
🅿️ 15
*BAYAN SATI DAYA*
Acikin satin nan abubuwa da dama sun faru don gaba Daya Husna da Huzna dakuma yan uwansu Hassan da Hussaina sun buwaye kowa a gidan , rashin jinsu kullum Kara gaba yake Kuma wani abun mamaki daga Abba har Abee ba Wanda ya k'ara zancan Kai su HUSNAà wajan malami Kamar yadda suka tsara ,
Acikin kwanakin an gyarawa Su Abba part dinsu Wanda akwai tazara sosai tsakanin part din Dana su Abee , a yanzu kam basuda matsalar komai Kuma ba Wanda yake takurasu kasancewar sunyi nesa da mutanen gidan sai idan sunyi ra'ayin shiga wajansu , Inna ma a part dinsu ta dawo da yake akwai yalwan d'akuna a part din sama da k'asa ne , babban falo ne da d'akuna biyu acikin falon kowane da akwai toilet aciki sai wajan dinning dakuma kitchen duk acikin falon , sai Sama inda hima ya kunshi d'akuna biyu da falo , inda anan aka gyarawa su Abba yayinda Inna ta dauki dakin k'asa Daya su Huzna Daya , wanna yasa suke zamansu hankali kwance ga kayan abinci Abee ya cika masu sito dashi ba abunda Babu hakama fannin sutura Abee ya kashe masu kudi sosai ya dink masu Kaya masu yawa dasu da yaransu ,
a gaskiya ba abunda zasuce sai Alhamdulillah ,
Ba k'aramun farinciki Mu'azzam yayi ba ganin yadda Abee ya dawo hanya yanama Dan uwanshi da mahaifiyarshi hidima,
Husna da Huzna kuwa kiri kiri sukace su fa bazasu zauna a wannan part din da aka basu ba lallai lallai saidai su zauna acikin na su Umma acewarsu nan yafi kyau , Abee kam dariya kawai yayi yace to ai ba matsala sukoma can din , Abba da mama kam basu so ba don sunsan ba komai neyasa suka ce sai can suke so ba sai don su samu wandan da zasu dinga tsokana da neman fitina tunda nan ba Wanda zasu tsokana ,
A part din Mamah suka zauna inda sukayi masauki a dakin Hussaina don Hassan tuni aka ware mashi wajanshi daban kasancewarshi namiji akicikinsu , Amma a haka kullum yana manne dasu a dakinsu suna rashin ji ,
Sati biyu da dawowarsu aka koma school da yake dama su Hussaina suna hutu , nan fa Abee ya siyowa su Huzna form inda akayi yar cuwa-cuwa harka ta kudi aka sanyasu primary 2 da yake dama su Hassan a primary 2 suke , inda aka Nemo kwararren malami da zai dinga yi masu lesson a gida tunda basu San komai ba yanzu zasu fara ,haka suka fara karatunsu cike da farinciki , ba k'aramun kyau sukeyi a cikin uniform din makarantar ba Kamar ka sacesu ka gudu , rigace doguwa wadda da kadan ta wuce gwuiwarsu sai hula irinta yan makaranta a gaskiya sunyi kyau sosai acikin uniform din Kamar yaran turawa abunka ga farare tas Wanda suka saje da Hussaina suka koma triples saika rantse yan ukku ne
Abba kuwa ba k'aramun farinciki yayi ba sai addu'a yakewa Dan uwan nashi don tabbas a yanzu yaga amfanin ilimi Mama Hafsee da Inna ma sunyi murna sosai suna ganin yanzu yaran zasuyi hankali tunda sunfara boko (to Allah yasa😂😂😂)
Sati Daya da fara karatunsu sai gashi sunfara ganewa don lesson teacher dinsu ba Wasa cikin kankanin lokaci sai gasu sun San kalmomi da Dan abunda ba a rasa ba da yake yaran akwai kwakwalwa duk abunda za'a koya masu nan take zasu dauke wani abun mamaki Sam basa sa Wasa aduk lokacin da suke karatu sosai suke maida hankali daga makarantar har nan gida , Wanda hakan ba k'aramun faranta ran iyayen nasu yakeba ,
Wannan Abu ba k'aramun 'batawa Umma rai yayi ba tanajin ciyon yadda Abee ke kashe wa wadan nan matsiyatan kudi a cewarta , Hajiya Ni'ima ta tsani taga alhaji Hussain yayiwa wani alheri ko Yaya ne komai tafison daga ita sai yaranta tana da mugun son zuciya wannan yasa kullum take biye da malamai ,
_______________
Da kyar take taka k'afarta haka ta k'araso falon inda k'awarta Talatu ke jiranta , tun daga nesa Talatu ke kallonta tana tintsara mata dariya a cikin zuciyarta , har ta k'araso inda Talatu take zaune ,
Kasa rike dariyar Talatu tayi nan ta bude baki tarinka babbakamata dariya Saida tayi Mai isarta sannan ta tsagaita ,
Umma kuwa tunj ta shak'a don tasan da ita take.
Ke banson iskanci kefa Sam bakida mutumci wallahi , cikin dariyar Talatu tace maida wuk'ar aminiya dariya kawai kika bani wallahi ke kinga yadda kk wata irin tafiya a duk'e gaskiya Aminiya yaran nan yakamata adauki wani mataki akansu, yanzu waja wata Daya kenan har yanzu kafar nan na wahalar dake wai Yama akayi kikayi irin Wannan faduwar ne tayi maganar tana kunshe dariyarta ,
K'wafa Umma tayi tace ai shine dalilin kiranki wallahi yadda yaran nan suka 'batamun komai nawa nayi alk'awarin sai na lalata rayuwarsu sai na d'aida'aita su sunbi duniya sai na raba tsakaninsu da iyayensu Dani suke zancan suma wadan nan munafukan duk Randa na juyo kansu wallahi sai sun gane basuda wayo yanzu batasu nakeba ta uban gayyar nake inaso duk yadda za'ayi ayi ko nawa zan kashe inason alhaji ya dawo hannuna kamar da wannan kadai zaisa burina ya cika akanshi don inba haka bazan taba samun aiwatar da kudirina ba ,
Kije wajan boka na kan tsauni inaga zamufi samun yadda mukeso ,
Dariyar mugunta Talatu tayi tace shiyasa nake kaunarki Aminiya Sam bakida wasa insha Allah gobe zanyi sammako inje don inaso na dawo da wuri zamu fita da Alhaji Sani , tsaki Umma tayi tace ai aikinki kenan nidai don Allah karki k'i zuwa kikama hanya kiyi tafiyarki ki barni da jira ,
"ah haba dai ai tunda nace zanje zanje ne kedai kawai kizuba Indo to shikenan daga haka suka shiga wata firar,
___________________
Yau Assabar ba makaranta ,zaune suke a dakin Inna suna wasan yar tsana sai gardama ake tafkawa in wannan yayi da wancan wannan yayi da wannan ,gaba Daya Inna tagaji da hayaniyarsu sanna tasan kota korasu bazasu tafi ba ,
Huzna zo muje wajen motoci muyi wasa cewar Hussaina ....ko rufe bakinta batayi ba Huzna ta Mike tace muje , Husna ma mikewa tayi suka nufi wajan aguje ,
Alhamdulillah Inna ta furta don Allah yagani sun dameta da hayaniya yanzu kuwa zata samu ta Dan kwanta kamun su dawo
Kusa da wata hadaddiyar. Mota bak'a suka zauna har sun fara Wasa kamar da gaske saikuka Husna tace gaskiya motar nan tayi datti ko muzo mu wanketa ne , nan take suka maida dubansu ga motar duk da halin yarinta sun San motar batada datti ko kadan saima wani kyalli da daukar ido da takeyi ,Amma tsabar Neman abun magana sai cewa sukayi eh wallahi duk tayi datti har wari take zo muje mu debo ruwa to ,
Da sauri Hussaina ta dakatar dasu tace Kai fa wannan ba motar gidan nan bace kila bak'i akayi sukazo da ita ,
Harararta Husna tayi tace to ai kota waye mu taimakamasa zamuyi kilama yabamu wani Abu in yaga munyi Masa aiki ko Huzna , daga Kai Huzna tayi tace eh wallahi kilama zai bamu irin alawar nan da Abee ke kawo Mana Mai shegen dadi tayi maganar tana watse baki adoli zasu samu kyauta ,jin hakan yasa Hussaina cewa to kozo muje mu dauko kayan aikin , nan fa suka bazam cikin gidan inda kowacce ta ciko Dan madaidaicin boket da ruwa sanna sukaje toilet suka kwasu susunan wanka da sabuku ,
Nan fa suka hada uban kumfa suka fara diban ruwan suna watsawa motar kota ina , Huzna ce ta dubesu tace Bari naje na dauko mofa in mun gama sai muyi moping ko , nan suka eh je ki dauko nan ta ruga da gudu cikin gida ta dauko mofa,
Abunda basu sani ba motar saurayin Saudat ce duk lokacin da yazo haka yake Kai motar can lungu inda da wuya a fahimci da mutum acikin , anan suke zance Wanda har yanzu ba Wanda yasan abunda suke aikatawa kasancewar gidan ba wani hadin Kai kowace tana part dinta sannan bamai shiga shirgin wani sai in ta kama duk a zatonsu acikin part din mahaifiyarta yakezuwa fira da yake duk gidan an San shi yana zuwa wajanta shiyasa in an ga motarshi ba Wanda yake damuwa abunda basu saniba shine duk lokacin da yazo acikin motar suke fira ba abunda suke sai lalube juna ba Wanda ya sani kasancewar motar Mai bakin Glass ce baka ganin Wanda yake ciki ,
Yanzu Ma hakance take faruwa gab Daya sunyi nisa basajin Kira sai kissing junasu suke Kamar wasu mayunwata Salim shine sunan saurayin nata Wanda gaba Daya ya fita hayyacinshi har ya Kai ya cire mata riga sai Wasa yake da k'irjinta ita kuwa sai Nishi take tana k'ara bank'aromashi su wannan yasa duk abunda su Huzna keyi basu kula ba don sosai sukayi nisa daga wanna duniyar ,
Kamar daga sama sukaga yaran zagaye da motar sai aikin wanketa suke Kamar Allah ya aikosu , nan fa suka zabura suka fara kokarin kimtsa kansu da sauri Saudat ta janyo rigarta ta Sanya yayinda shikuma yake faman gyara wandon shi gaba Daya baya cikin nutsuwa sosai yaso a yau Saudat ta mallaka mashi kanta Wanda yajima yana Neman hakan gashi yau har ta yarda dashi Amma wadan nan tsinannun sun ruguza mashi tsarinshi sai da suka gyara kansu sannan suka bude motar suka fito ,
Fitowar Salim yayi daidai da watso ruwan da Huzna tayi aikuwa caaaa sai a fuskarshi gashi sunkada sabulun da yawa aikuwa nan take kumfan yashige mashi ido , wani irin yaji yaji a idonshi nan take yafara murza idonshi yana fadin Kai Amma Allah ya tsine maku albarka ke saudat samomin ruwa na wanke idona ,
Ita kuwa Saudat tsabar jin haushi yasa batasan sanda ta daga k'afarta ba tayiwa Huzna wani mugun shuri a ciki Wanda Saida ta hantsila kamun ta fasa wani irin ihu , nan tafara mulmula a wajan tana rike cikinta tana kuka don ba k'aramun shuri ta mata ba ,
Ganin hakan yasa Hussaina arcewa da gudu zuwa cikin gida tana Kiran Mamah,
Husna kuwa kallonta take Bata ko kyaftawa lokaci 'Daya idonta yak'ara wani irin girma , ganin kallon da take mata ne yasa Saudat Kara harzuka cike da zuciya tayi nufin daga k'afarta ta nufi inda Husna take ta lallasata itama amm mi sai kuwa kafa tace bansan wannan ba ,
Nan fa tayi-tayi ta d'aga k'afar Amma takasa , Abu kamar Wasa saiga Saudat najan k'afarta da k'arfi Amma k'afa ko gezau Sam takasa daguwa ,
Wai Saudat mi kikeyi ne har yanzu bazaki bani ruwa na wanke idona ba , Saudat Saudat yakirata da k'arfi , cikin hasala tace "wai ubanmi zan maka ne kana ganin ga kafata nan Sam nakasa daga ta , to wallahi kayi maza kaja motarka kabar gidan nan kamun mutane su fito ,
Kefa wani lokacin yar rainin hankalice wallahi Taya zanyi tukin bayan na gaya maki bana gani sosai sai wani yaji idona keyi wallahi inaga harda barkono a cikin ruwan nan ,
Tsaki kawai Saudat tayi taci gaba da Jan k'afarta Amma wasa-wasa takasa sai wani irin ciyo da zugi da k'afar tafara mata kamar ana mata shocking , aikuwa Babu shiri tafara zunduma ihu , jin ihunta yasa Salim fahimtar da gaske take nan take ya lallaba yakoma mota yaja yabar gidan yana tafe yana tsayawa yana murza idonshi , fitarshi tayi daidai da fitowar mutanen gidan a gigice jin ihun Saudat da Huzna wadda har yanzu tana rike da cikinta sai ihu take ................✍🏼
Inkunga typing error kuyi hkr pls ba editing