Chapter 16
by @mamanyusuf
♠️♠️ *HUSNA KO HUZNA* ♠️♠️
*MALLAKAR*
*Maryam Umar Abdullah (mmn Yusuf)*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*____________________________________*
*Littafin na kudi ne 200 maiso ta turo kudinta ta wannan account number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Account no 1647784887
Account name Access bank
Name Maryam Umar
Ko katin waya ta wannan number 👉🏻***
🅿️ 16
Da hanzari Mamah ta nufi inda Huzna take tana fadin "subuhanallahi Husna Miya sameta , ? Talla'bota tayi tana duba cikinta ,
Ke ubanmi kikeyi hakane kinyi tsaye kina wani ihu a gaban yara salon kisa su rainaki , ........wallahi Umma anrik'emun k'afa gaba Daya nakasa tafiya da ita sai wani irin zafi da zugi takemun ta karasa maganar tana fashewa da kuka , jin hakan yasa Umma da Nasma suka nufi inda take ,
Wai mi yake faruwane cewar Abba da shima hayaniyarsu ce ta fiddashi ,da sauri Hussaina ta tace Abba anty Saudat ce ta Shure Huzna ga ciki sosai Kuma sannan muma tayi ta dukanmu tayi maganar tana hararar inda Saudat take , kallon Saudat Abba yayi yace toke mi kikewa kuka ne, ?
Cikin matsanancin kuka da tsoro tace Wallahi Abba nakasa daga k'afa ta sai wani zafi takemun kamar zata cire haka nakeji walahi,
Dafe Kai Abba yayi kamun ya dubi wajan da Husna take kallo Daya yamata yasan ba lafiya don tunda suke bai taba ganinta acikin irin Wannan yanayin ba , wannan yanayin yasha bam-bam da irin Wanda yasaba gani a wajansu , wasu yawu ya had'iye k'ut Yana tunanin ta inda zai fara , gashi bayason mutanen gidan su fahimci abunda yake damun rayuwar yaran nan , to wai ma mi ya hanasu kaisu wajan malamin nan da sukayi magana da Hussain gabadayansu ba Wanda yak'ara tada zancan , tsaki yayi a ranshi yace to ai ga irinta nan yanzu ai doli kowa zai San abunda ke faruwa don yasani Sarai bazata saki k'afar nan ta sauki ba ,
Sunyi iya yinsu Amma Saudat takasa daga k'afarta sai uban kuka take wasawasa suma abun yafara tsoratasu , haka suka kinkimeta suka nufi cikin gidan da ita tambayar duniya sun mata akan mi ya samu k'afar amsa Daya take basu shine Bata sani ba ,
Ganin sun shige cikin gidan ne Abba yaje kusa da Husna yafara lalla'bata akan tayi hakuri ta sakar mata k'afa tun mutanen gidan basu fahimci daga gareta bane , ganin ko kallonshi taki yi yasa yayi ajiyar zuciya sannan yamaida kallonshi ga Mamah da har yanzu take kan Huzna tana lalla'bata yace
" Maman yara akwai fa matsala wannan matsalar daga Husna ne irin abunda nake gaya maku kenan yanzu miye abunyi ? Nidai nayi iya yina Amma taki saurarata don Allah kijata part dinki ki lalla'bata kamun su Ankara , jinjina Kai Mamah tayi cike da mamakin wannan al'amari na su HUSNA , lallai doli iyayensu su shiga damuwa Abu sai kace aikin sihiri ,to allah ya kyauta gaskiya doline su tashi tsaye akan yaran nan ,
Duban Abba tayi tace to insha Allah yanzu zan lalla'bata , wai yau ina Hafsee najita shiru ,? Tayi tambayar tana kallon Abba ,
Yace "Yau mmn biyu ba lafiya inajin ma haihuwa ce ,don yanzu haka Inna na wajanta shiyasa baki ganta ba ,
Jin hakan yasa daga Husna har Huzna da Hussaina suka kalli Abba da sauri kamun fuskarsu ta washe ta bayyanar da tsantsar farinciki kamun kace mi gaba dayansu sun nufi part din aguje ciki kuwa harda marar lafiyar😂
Abba da kallon mamaki yani Huzna kamun ya gyada Kai yace Allah ya kyauta , yarinyar da ke zunduma ihu tun dazu Kamar ana zare ranta sai murkususu take tana rike ciki Amma wai itace daga jin zancan haihuwa cikin abunda baiwuce second ba ta wartsake harda gudu🤔
Haba Abban Husna shine Kuma baku gaya manaba da saidai muji haihuwar kenan ,haba Mana shiyasa duk yau banji duriyar ta ba , to Ni zan Kira Alhaji na gayamai , Bari naje na ganta sai nazo nashirya inkaita hospital,
Dariya Abba yayi yace to ai kinji abunda bataso wannan ne yasa ta hana a gaya maku tace batason haihuwa a asibiti,
Ai bazai yiwu ba Abban Huzna tunda likita yace in haihuwar yazo akaita asibiti saboda yaron a zaune yake doli tana bukatar kulawar likita ,
Yadda ta fada haka akayi Abee na kasuwa ta kirashi ta shaida mashi nan take yabata umurnin ta kaita asibiti gashinan zuwa , haka ta Sanyata a mota suka asibiti tareda Ammi da Inna , su HUSNA da kukansu akan sai an tafi dasu da kyar Mamah ta lallabasu akan sujira yanzu zasu zo masu da new baby nan suka fara tsallen murna ,
Shin wai Taya akayi ma kikaji ciyon , cewar Umma ta tafara gajiya da ihun Saudat nan Saudat ta kwashe dik abunda ya faru ta gayama Uwar , aikuwa nan Umma tafara zage-zage tana cewa ai dama nasani wadan nan yaran mayu ne to wallahi kurwar 'ya'yana tafi karfinku kurwata kur wallahi, nan fa Umma takama masifa da zage-zage kamun ta dauki waya ta Kira k'anwarta Jummai ta gaya mata duk abunda yake faruwa , nan fa itama Jumma tafara zage-zage irin na yan Tasha da yake goggagiyar yar bariki ce nan ta fara kwantar ma da Umma hankali akan tabar komai a hannunta zataje gidan Uban mayu inma maitar ce saidai suci kansu ,
Basu Sha wahalaba aka kar'bi Mama Hafsee dayake tafara zuwa asibitin awo aka shiga da ita dakin haihuwa , daga Inna har Mamah sun tausaya mata ganin irin wahalar da takesha , suna haka saiga Abee da Abba sunzo , Abee ne yaje har gida ya dauko Abba , nan Abee ya nemi ganin babban likitan baisha wahala ba aka sadashi da shi nan Abba yamashi bayanin halin da matar Dan uwanshi take ciki , likitan da kanshi yaje ya duba mama Hafsee , yajima a dakin kamun ya fito ya nemi ganin Abee nan yake mashi bayanin anshawo kan matsalar yanzu yaron yakoma dai-dai kowane lokaci zata iya haihuwa , nan suka murna suna fatan Allah ya sauketa lafiya ,
Bayan kamar 30mnt sai ga wata ma'aikaciyar jinya tazo wajansu da saurinta tana tambayar yan uwan Hafsat Hassan , nan suka zabura da saurinsu suka nufeta suna tambayar Yaya ?? Albishir ta masu da samun Baby boy mama Hafsee ta sauka lafiya aikuwa nan suka hau murna kamar mi Abba ma bakin nan yaki rufuwa sai wani irin farinciki yakeji azuciyarshi Ammi kam na gefe sai ta'be baki takeyi da taga wani zai kalleta sai tayi sauri ta watse hakora a doli itama tana murna azuciyarta kuwa haushine sosai don tasan a yadda taga Abee na wani rawar k'afa a haihuwar nan sai kace shi akayiwa tasan sai aljihunshi yayi kuka ,
Wallahi in mama ta haihu Ni aka haifawa ke Huzna sai Takoma haihuwa ta baki , tayi maganar tana wani girgiza jiki irin na alo tsiya alo danja din nan😂😂
........"wai ma ai wallahi saidai ke ki jira har takara haihuwa Amma wannan nawa ne tayi maganar tana murguda ma Husna baki ,
"Wai ma ai wallahi saidai arabashi ukku abawa kowa Daya don Nima mama tace kanena ne don ku sani cewar Hussaina tana wani rik'e k'ugu ,
Kajita sai kace mamanki ce ta haihu aidai mamanmu ce Kuma bazamu baki yaronmu ba , ai wallahi sai anbani shi Nima ai dai mama tace Nima kaninane , Husna tace to arabashi ukku kawai kowa ya dauki d'aya , Hussaina tace eh na yarda arabashi ukkun haka dai suka lalace wajan gardamar yadda zasuyi da yaro kowacce tana cewa nata ne ,
Ba'a jimaba aka fito masu da yaron an shiryashi cikin kayan sanyi masu matukar kyau yaro k'ato dashi fari tass kamar Dan larabawa sak Abba , haka sukayita daukan yaron suna yabawa basu jimaba itama mama aka basu damar ganinta , Alhamdulillah tana cikin koshin lafiya saidai ta fada sosai don ta wahala , nan fa sukayi waya suka sanar a gida nan da nan sai gasu Yaya Aliyu da Jamil , basu jimaba saiga Yaya Mu'azzam yazo ya dauki yaron Yana kallo cike da farinciki ,don Yaya Mu'azzam akwai son yara sosai ,
Waya Ammi ta dauka ta Kira anty Safiya ta shaida mata maza ta hado abinci Mai kyau ta kawo asibitin itada Suhaila daga nan suga Baby ,
"Kai Ammi mi Kuma zanyi a asibiti yanzu don Allah ki k'yalesu in sun dawo Naga babyn Amma yanzu ina hutawana zaki wahalar Dani akan wadan nan yan kauyen , ......"ke banason shashanci kinji ko in bama haka ba taya kikeson su saki jiki damu har mu samu mu aiwatar da nufinmu , ai doli Saida siyasa ta bayan gida zamu dinga bullomasu ta yadda nan gaba duk abunda aka gani ba'aza zargemu ba sai dai a zargi wannan shashashar ,cewa da Umma ,
Tunzuro baki tayi gaba irin dai an takurata din nan sannan tace to zamuzo yanzu don akwai abincin da nayi sai nazo maku dashi ,..."yawwa yar albarka maza hanzarta ,
Haka akayi ba'awani jimaba sai ga safiya da Suhaila a asibitin da abinci niki-niki , aikuwa daga Inna har Abee da Abba sunji dadin abunda sukayi nan aka zubama maijego abunda zata iya ci ,sunjima sannan sukayi sallama suka koma gida da yake su Yaya Mu'azzam suma basu jimaba suka koma ,
Washe gari aka sallamosu tunda safe misalin karfe 8am nan fa gida yaka rudewa da murna su HUSNA kuwa kamar su taka kan jariri in wannan ta dauka wannan ta dauka sai rigima suke
Wayyo Umma wayyo kafata zata cire wayyo Umma nashiga ukku na lalace , 😨zaro ido nayi lokacin danayi ido biyu da k'afar , ta kumbura tayi suntum sai wani wankiya take yayinda Saudat ke rike da k'afar duk ta hada zufa sai aikin ihu da Kiran sunan Umma take ,
Itakuwa Umma tana zaune ta zuba uban tagumi gaba Daya abun duniya ya dameta tunjiya daga Talatu har Jummai sai yawon gidan bokaye da malamai suke Amma har yanzu ba wani bayani gashi jiya gaba Daya basuyu bacci ba sai ihu Saudat keyi har yanzu aikin kenan ga Alhaji tunjiya Bata sanyashi a ido ba gaba Daya tacika tayi fam , gefenta Harira da Nasma ne suma dai acikin damuwar suke , ana haka saiga Abee da Yaya Mu'azzam sun shigo falon nasu ,
Dukkansu ba k'aramun tsorata sukayi ba da sukaga yanda k'afar ta kumbura , cike da tashin hankali Abee ya dubesu yace ke yanzu Ni'ima haka k'afar nan tayi amma kika kasa kirana ko a waya ne kokuma ke kije ki kaita asibiti Amma kwa zauna da ciyo irin haka a gida ,
Tsabar haushi umma tama kasa tankashi har yayi yagama sannan ta dubeshi tace kagama , ? Nace kagama , tunda kan can wajan hidimar wani Taya zaka kula da naka yaran tunjiya aka sanar da Kai Amma shine sai yanzu zaka shigo kanacan asibiti sai kace Kai za'a haifawa Dan to.........ke banason maganar banza kinji ko kinsani Sarai a cike nake dake don haka wallahi ki iya bakinki , maza ku kamota ku fito da ita ina mota mutafi asibiti daga haka yasakai yayi tafiyarshi ,
Da k'yar suka talla'bota suka nofo inda ya faka motar , suna kokarin Sanyata a mota ne saiga Abba yana ganinsu ya k'araso da sauri Yana fadin subuhanallahi Saudat k'afar ce har yanzu ? Wallahi shaf na manta tunjiya da maganar k'afar nan ,
"Ai doli ka manta Mana tunda ba yarka bace shi ai tun jiya yanacan wajan hidimar taka haihuwar yabarta da wannan ciyon shine Kai har zaka manta da tashi 'yar to ai ko.........wata irin tsawa Abee ya daka mata yace wai kekam wace irin sakarya ce , ke Sam bakisan maganar da ya kamata kiyi ba to wallahi yanzu sai na sassa'ba maki shashasha kawai, to in ma ya tunatan mi zai mata wayasan Inda take ta jiwa kanta ciyo da zakizo kina gayama mutane magan .......
Cikin fusata itama ta amshe zancan da cewa aikuwa shi yake da abunda zai mata tunda adalilin yar shi tashiga wannan matsalar duk abunda yafaru Yana da masaniya yarshi ce sanadi Kuma wallahi bazan yarda ba wallahi duk abunda yasamu 'ya ta sai inda karfina ya k'are ,
A hasale Abee ya bude baki zaiyi magana tuni Abba ya dakatar dashi ya ce kyaleta Hussain tanada gaskiya duk wannan abun laifin Husna ne kamar dai yadda nake gayamaka matsalarsu ,yanzu ma wannan haihuwarce ta mantar Dani inaga lokaci yayi da zamusan abunda yake faruwa da yaran nan abun yayi yawa gaskiya
Shiru Abee yayi jin bayanin Abba tuni yacika da mamaki to miye matsalar yaran nan ne ya tambayi zuciyarshi gyada Kai yayi ya dubi Anty Harira yace ku kamata ku koma zan San abunyi , haka suna kunkuni suka kamata suka juya Umma kuwa sai sababi takeyi ,
Abba ne da Abee sai Kuma Inna zaune a falon Abee inda suka yi Kiran su Huzna don su lallabasu su sakarma Saudat k'afa ,
Zaune suke a k'asa sun sadda Kai kamar na Allah 😂
Kallonsu Abee yayi yayi gyaran murya yace Husna da Huzna kubani hankalinku nan , acikinku wacece ta rikewa Saudat k'afa ??? Yayi maganar in serious don karma suga damarshi ,
Kamar hadin baki kowace sai ta nuna yar uwarta Husna ta nuna Huzna , Huzna ta nuna Husna , kallonsu Abba yayi ya girgiza Kai yace ku gayamana gaskiya kunji duk abunda kukeso zan baku matukar kuka rabu da Saudat ,
Wallahi Abee Huzna ce bani bace , "Allah k'arya take Abee itace nan fa suka kama gardama iyayen sai kallonsu suke ganin zasu maidasu mahaukata ne yasa Abba dakamasu tsawa wadda Saida suka shiga nutsuwarsu sannan ya dubi Husna yace ke Husna nasan Sarai kece na biku ta lalamane ko abun zaizo da sauki to wallahi in baki sakar ma yar uwarki k'afa ba sai na ballaki anan gun tunda ku lalama Bata maku ,
Kaga ba haka za'ai ba zonan Husna , cewar Abee ,kusa dashi ta koma ta zauna cikin
Tunzuro baki ,kinga 'yata kiyi hakuri ki sakar ma yar uwarki k'afa kinji komai kikeso zan saya maki kinji , daga kanta tayi alamar amsawa nan take duk sukaji sanyi a ransu ganin ta yarda , kallon Abee tayi tace to Abee zan sakar mata k'afar Amma wallahi sai an siyamun akuya Mai ido d'aya,
Dukkansu a razane suka kalleta cikin masifa Inna tace yau Naga ja'irar yarinya.............mikewa Husna tayi tayi tafiyarta Huzna ma mikewa tayi tabi bayanta............✍🏼