OMAR KO FAROOQ?

31-35

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓

31_35

"Bayan 5hrs yarinyar ta fara motsi da hannun ta,

can ta fara motsi da kafar ta, "daidai lkcin

mummy ta shigo dakin, ganin tana motsi tayi

saurin isa gaban ta sai hamdala take, fuskar ta

tashafa tace sannu koh, a hankali yarinyar ta

bude idanun ta, tass ta sauke su kan mummy, a

razane tayi kokarin tashi, mummy ta tayata

mikewa, yarinyar tsayawa tayi tana kallon dakin

daya yi mugun haduwa, tunda take arayuwa bata

taba shigar daki irin wannnan ba, shin kodai

gidan yankan kai ne? Take zuciyar ta ta bada

dammm, kallon ta tadawo kan mummy da itama

kallon ta take, "muryar ta na rawa tace baiwar

Allah dan Allah a INA nake? "Mummy tayi

murmushi tace kwantar da hankalin ki, yanxu dai

sakko daga gadon nan kiyi wanka tun jiya kike

bacci, "zaro ido tayi balo-balo tace bcci tun jiya?

Kallon Agogon dake manne a dakin tayi Wanda

yyi mugun haduwa 4:05 ta gani, a rikece tace

meya kawoni nan dan Allah... Bata karasa ba taji

cikin ta ya murda kanta ya Sara ahhhh tace,

mummy ta riko ta tace tashi ga bayi shiga kiyi

wanka daga baya saimu yi mgn, ba musu ta

mike, sannan ta fada toilet bayan mummy ta

taimaka Mata.

"Sanda ta shiga toilet din kallon kauyanci takeyi,

tayi kusan 5mins tana tsaye ta rasa inda zata

taba, fitowa tayi, mummy da mamaki tace harkin

gam...., bakin tane ya katse ganin ko alamar

wankan batayi ba, "yarinyar tace a hankali

bansan ya zanyi ba. Mummy ta mike ohk, follow

me, nan tabi bayan ta, cike da nutsuwa mummy

ta nuna mata komai sannan ta fito. Nan itama

tayi komai kamar yanda mummy tace.

"Fitowar ta, ta iske mummy bata dakin, nan tayi

gaban mirror, anan ta shafa mai me kamshi

kansancwar ta 'Yar son kamshi hakan be mata

wahalar gane wasu abun ba. "Bayan ta gama ta

juyo dan maimaita kayan ta. "Harta cira zata

saka mummy ta shigo rike da tray na abinci, "da

sauri mummy tace aa ga kaya nan na fiddo miki

dasu dauki ki saka, wata doguwar riga CE me

kyau gaban kirjin anyi mata kwalliyar duwatsu

masu hasken kyau. "A kunyace ta dauki rigar ta

saka tana mamakin wannan Matar daga haduwa

bata santa ba tahau yi mata hidima.

"Bayan ta gama mummy ta miko mata tea me

kauri, girgiza kai tayi tace ta koshi. "Mummy tace

ki saki jikin ki bazan cutar dake ba, jin haka ta

karbi tea din, daman cikin ta sai murdawa yake

ga kanta sai zafi yake mata tamkar zai tsage.

"Bayan ta kammala mummy ta miko mata plate

na dankali da kwai, nan ma saida taci kusan

rabin plate sannan ta aje, bayan gama mummy ta

bata magani tasha.

"Saida ta huta na 5mins, sannan mummy tace ya

sunan ki? Yarinyar tace *FATIMA* Amman amfi

kirana da _IMAAN_, mummy tace wow wat a nice

name, ta fada tana murmushi, Imaan itama

murmushi tayi dukda ta qagu taji dalilin ta na

zuwa gidan nan, "gane hakan yasa mummy ta

fara bata lbrin abinda ya sameta da yanda aka

kawota gidan, sai alkcin imaan ta tuna ashefa

wa'annan samarin da suka bita da gudu shi yyi

sanadin ta na tsallaka titi har abun yazo da

tsautsayi. "Mummy tace so ki fadamin inane

gidanku sannan meye dalilin ki na fitowa daga

gida A wannan tsohon Daren???