๐งโ๐ฆฝ๐ญSUN GUJE NI ๐ญ๐งโ๐ฆฝ
14
๐จ๐ปโ๐ญSUN GUJE NI๐ญ๐จ๐ปโ๐ฆฝ
(SANADIN CUTAR LAKKA)
IT BASED ON TRUE LIFE STORY.
LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
*AK saraki Facebook group wannan Shafin na ku ne,tabbas soyayyar ku ga wannan littafin Yana burge ni,Allah ya bar kauna*
SHAFI NA GOMA SHA UKU.
CUTA BA MUTUWA BA.
A cikin kwana na ukun Yusuf ya dawo cikin hankalin sa duk da ba doguwar Suma ya yi ba amman sam bai san in da ya ke ba bai Kuma san menene ya faru da shi ba tsabar zafin ciwo,
Yana dawowa cikin hayyacin sa ya ji duk jikin sa tamkar an daddaure musamman hannun sa da wuyar sa da ya ji Wani irin mugun ciwo tambayar da ya fara yi ma innar sa ya ce "ba ya Jin kafafuwan sa mai ya same su?aka ce mi shi hatsari ya yi,nan aka jero mi shi halin da ya ke ciki,cikin mugun firgici ya fara fad'in Kalmar"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un "Dan labarin da aka ba shi ya dawo mashi da abin da ya faru da shi tamkar walk'iya,
Cike da rad'adin ciwo ya ce"a d'ago mi shi kafafuwan shi ya gani Dan Sam ji ya ke yi tamkar ba sa jikin shi,sai da ya gan su sannan hankalin shi ya kwanta Dan haka aiki d'aya daga cikin masu jinyar shi da ya je ya kira likita,
Ya dawo shi dan Aiken da dadewa kafin shi isashshen ya karaso ya fara yi ma Yusuf tambayoyi Yana rubutawa ajikin takarda,da biro ya yi amfani tun daga Dan yatsar Yusuf Yana caccakawa tare da tambayar Yusuf shin Yana Jin alamun ya tab'a Abu a jikin sa sai ya ce "ba ya ji "sai da ya iso kan k'irjin sa kafin ya fara Jin alamu a takaice dai likitan ya rubuta mummunan record dangane da jinyar Yusuf d'in Dan gani ya ke Yusuf jikin shi ba zai k'ara Wani amfani a duniya ba,
Dan haka ya rubuta wuyar Yusuf ya karye tare da nuna rashin Imani tsantsa Dan gani ya ke ko kafin ya je ya dawo Kila majinyacin ya mutu(ana samun irin wadannan matsalolin sosai acikin manyan asibitocin gwamnati da ke fadin kasar nan Hakan ba ya rasa nasaba da yawan marasa lafiyan da Dakta 1 ke dubawa ba Amman duk da Hakan ina mai Jan hankali ga malaman kiwon lafiya da su dinga Sanya tausayi da Imani acikin wannan aikin na ku Dan aiki ne da zai iya Kai mutum aljanna zai Kuma iya Kai kq wuta Allah ya sa muda ce ya kawo mana kyakykyawan sauyi acikin hargitsatstsiyar kasar mu Amin).
Dan haka ya daura ma Yusuf ruwa ba tare da yin wasu gwaje-gwajen da ya kamata ayi mi shi ba,ta bangaren Yusuf kuwa Yana cikin mawuyacin hali dan ko kwakwkwaran motsi ba ya iya yi da hannun sa balle Kuma Akai kan kafar da Sam bayajin alamun ta a tattare da shi,ga masifaffen zafin da ya ke Jin Yana tsirga jikin sa duk da fanka da fifitar da yan'uwa da abokan arzikin da ke baibaye da shi su ke mi shi Amman abin ya faskara dan har sai an Nemo ruwa an yayyafa a jikin sa sannan ya ke Jin Dan salama,
Babu Wani mahaluk'in da zai ga Yusuf a wannan lokacin ba tare da ya tausaya mi shi ba Amman ban da Ra'isat wacce kasuwa ya bud'e ma ta na samun kud'i tana adanawa dan ita sai ta kwana ta hantse sannan ta ke bugo wanka na gani na fad'a tamkar wacce za ta bikin gasar kyau sannan ta ke zuwa asibitin da yamma lik'is dan ta san wannan lokacin an fi zuwa duba marasa lafiya,
Cingum ta ke sawa a baki tana k'as k'as ita ga tatacciyar y'ar iska ta zauna a reception tana k'arban duk Wanda yazo duba Yusuf dan ta mi shi rakiya,ana mik'o abin dubiya kuwa ta ke jefa shi a jaka ta koma mazaunin ta,
Al'umma sun cika da mamakin halin Ra'isat dan haka mafi yawancin mutanen da ke zuwa suna Allah wadai da halayyar matar Yusuf saboda yanda rashin tausayi da rashin imanin da ta nuna a Fili,abin ka ga Mai mutane wannan yazo wannan ya fita sai lamarin ya jawo cece-kuce,Amman da ya ke k'anwar shaidan ce ita ko a jikin ta hasalima surutun ba ya hana ta zama ta ci duk abin da ran ta ya so har ma ta d'aga kwalbar Coke ko Fanta,
Isa-isa ta ke koman ta saboda tana dauke dan Dan masu gida a jikin ta duk da yan'uwan shi mata al'amarin ta na masifar k'ona ma su rai Amman ba su isa su d'au mataki ba sai innar mu ta Hana ta hanyar ce mu su"halin da d'an'uwan ku kadai ya ke ciki ya ishi Mai hankali wa'azi Dan haka ku kyale ta da halin ta in nagari ne za ta gani a kwaryan tuwon ta,ni dai babban burina Allah ya tashi kafadar d'ana",
Wannan dalilin kadai ya sa su ka zuba ma ta na mujiya Amman da ya ke mutuniyar ta ku jaka ce ko a jikin ta hasalima Hakan ita dad'i ya yi ma ta Dan ta yi kane-kane akan dukkannin Wani alhairin da ake yi ma majinyaci tana sawa a lalitar ta dan malamai,abokai,ubangidan Yusuf da sauran mutanen arziki suna ta tururuwa domin zuwa duba shi tare da taimakawa da kudade masu tsoka dan ganin halin da ya ke ciki,
Aikuwa ta adana Dan Umman ta a rana ta biyu da tazo ta ga jikin Yusuf ta ma ta huduba da cewa"to yanzu dai mijin ki Bai da maraba da matacce Dan haka dukkannin arzikin shi na ki ne keda Dan da za ki Haifa masa a matsayin magaji Dan haka banason wargi,dangin nan na sa da ba son ki su ke ba na San za su yi kaka-gida akan komai da ya shafe shi dan su tattara komai su bar ki da tumunin takaba,Dan ki da Bai Tako doron kasa ba ya tashi a wahqle Dan na San zasu wawushe komai tunda uwar da uban na raye dole Suma suna da gadon shi,dan haka ya zamana ke ce akan komai kin ji ko,duk kud'in da zai shiga ya zama Yana hannun ki inna zo sai in karba Dan a fara siya mi ki k'addara"
(Allahu Akbar kabiran rayuwar duniya kenan mutum da ran shi tun Bai mutu ba Amman har an fara rabon gadonsa,wannan wace irin rayuwa ce Mai cike da dauda da k'azanta wallahi mata Muji tsoran Allah mu sa ni za mu mutu, y'ay'a matan da Allah ya ba mu ba hajoji ba ne na kasuwancin da zamu baza Muna cin kasuwar duniya da su, amana ne a garemu Kuma zai tambaye mu dangane da kiwon da ya ba mu,tabbas wannan littafin darasi ne ga rayuwar iyayen yanzu wadanda su ka fitinu da son abin duniya,babban burin su ganin y'ay'an su sun auri Mai kud'i tare da mallake abin da ya mallaka,wasu matan suna mancewa da kiyama za ta tsaya Kuma za su yi bayanin duk abin da su ka aikata a gaban makagin su yayin da gabban su za su magantu da dukkannin miyagun ababen da su ka aikata tare da Bada shaida,Allah ya datar damu hanya madaidaiciya Amin).
Da wannan hud'ubar tsiya Ra'isat ke aiki dan haka ta ke Jin za ta iya taka duk Wanda ya kawo mata wargi acikin lamarin ta.
Yusuf kuwa duk da yanayin da ya ke ciki Amman ya fuskanci wasu daga cikin makusantan shi SUN GUJE SHi musamman abokan da ya fi kusanci da su tare da sake jiki da su da yi musu hidima bakin rai bakin fama,
Bangaren yaran da su ke Neman abinci a karkashin sa ma mafiya yawa daga cikin su tun da su ka zo sau d'aya su ka ga halin da ya ke ciki ba su ko k'ara leko shi ba,tabbas wannan lamari ya bashi mamaki matuk'ar gaya Dan a wannan lokacin Yana bukatar tallafin su Yana Jin son ganin su a tattare da shi ko Dan su debe mi shi kewar abin da ya rasa na lafiya alhalin su ga shi ubangiji ya ba su lafiyar ba tare da ko sisin su ba Amman sai SU KA GUJE SHI acikin sati d'aya kacal da Allah ya jarabce shi,
Daman shi ba yasa Ra'isat a lissafi saboda ya lura da ita da irin mugun kallon da ta ke bin sa da shi na kyama tun da an Sanya mi shi abin fitsari,daman ba ta saba ba shi kulawa ba tun Yana da lafiya Ina Kuma ga yanzu da ta ke kallon shi a matsayin matacce,
Wadannan damuwowin su su ka k'ara ta'azzara ciwon na shi,Daman Kuma gashi ba Wani gaggarumar kulawa ya ke samu daga likitoci ba ganin ba bu Wani cigaban da ake samu sai ma ci baya ya sa y'an'uwa su ka fara fafutukar ganin an canza mi shi asibiti Dan haka aka bidi da oganniyar ta ku ta fito da kudaden da ke wajen ta.
Ummu-jiddah.๐จ๐ปโ๐ญSUN GUJE NI๐ญ๐จ๐ปโ๐ฆฝ

Ummu-jiddah.