51-55
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
51_55
"Mamaki ne ya isheta, tayi kusan 10mins a tsaye ta Tara abin yi, "driving yake harya wuce sai ya ganta, hakan yasa yyi riverse, 'imaan na tsaye kamar soja sai ganin mota tayi ta tsaya gaban ta, da sauri ta matsa tare d kawar d kanta dan batasan ko waye ba. "Farooq yana daga ciki ya fito, imaan na dago kanta ta fahimci farooq ne kasancewar kayansu ya banbata bayan haka har motar su iri dayace. "Farooq ya matso kusa da ita sanna. Yace imaan me kike anan wajen? "Imaan kamar zatayi kuka, tace ya omar ne ya ajeni a nan kuma mummy tace ya kaini skul ayi duk abinda ya dace, "farooq y jijjiga kai yasan bro dinsa ba'a taboshi ba yana wulakanci bare kuma aka tabo shi. "Nan yace shiga mota muje. "Imaan tace toh. "Har zata shiga baya yace dawo gaba, haka tabi abinda yace. "Ga mamakin ta nan suka sake gangarawa inda omar y sauke ta, basuyi tafiyar 5mins suka isa makeken gate din Queen Amina secondary school, a sai yanzu ta fahimci dalilin kudin da ya omar ya bata wato taje tayi komai da kanta kenan?, yo ita idan mutum ya sani ba taya zaisan akwai skul ta wajen? "Ahaka suka karasa bayan sun shiga cikin skul din. "Nan farooq yyi mata komai yanda ya kamata har akayi mata interview yana wajen yana mamakin yanda imaan ke ja, komai aka tabo ta sani. For d first tym yaji tadan birgeshi Kadan dan yanason yaro me hazaka. "Bayan an gama PC skul din tace zuwa Monday ta fara zuwa skul. Farooq yyi mata godiya sannan suka fito. "Bayan sun fito imaan tace am ya farooq, farooq ya kalle ta batare d yace komai ba. "Kudin hannun ta d omar ya watsa mata take mika masa tace gashi, farooq ya yatsina fuska yace mezan dasu? Imaan tace kudin skul din kenan ai. "Farooq yace mtwss shige muje. "Imaan taja bakinta tayi shiru batare d tace komai ba, sannan suka bar makarantar. "Imaan na jiran ya maida ta gida sai gani tayi yabi wata hanyar, "imaan bata ida tunanin ta ba, taga ya shiga da ita hospital dinsu. "Har yyi parking imaan ta kalleshi zatayi magana farooq yasa yatsan sa a baki alamar tayi shiru, haka taja 'yan matan bakinta tayi shiru. Sanan ya fito, itama fitowar tayi, wata hanyar yabi dasu, dan haka itama ta fara binshi kamar jela, duk Wanda suka hadu saisun gaishe shi, ammn yi yake kamar besan d zaman su ba. "Ahaka su shiga can su fita can har suka kai office dinsa, imaan dai mamakin girma da lungu2 hospital din takeyi. "Bayan sun shiga ya nuna mata waje ta zauna. "Shikuma yasa rigar likitoci yafara gudanar d aikin sa. Imaan kam ta sunkuyar da kanta tana cike da kunya yanda mata ke fadar matsalolin su ga ya farooq, a yanda ta lura shi ko a kwalar rigar shi dan ko aikinsa yake batare d wata matsala ba. "Kusan azahar imaan na zaune harta fara gajiya, "ga yunwa data addabe ta, tana wannan zaman aka kawo mata abinci lkcn farooq ya fice dan yin salla. "Imaan tace waye ya turo ka? Yace oga. Sannan Wanda aka turo din ya fice. "Imaan kuwa yunwa takeji sosai dan haka ta fara aikawa cikinta abinci, har ta gama farooq be dawo ba, dan haka ta mike tayo alwala tayi salla. "A wajen yin addu'a ta bingire tana bacci. "Lkcn da farooq ya dawo tabe baki kurum yyi.
"Mummy na gida taga har azahar ba imaan babu labarin ta, dan haka tahau kiran omar Amman taji wayar a kashe, hankali tashe ta kira farooq tace dubamin omar ko lpy ya kashe wayar sa? Farooq yyi murmushi yasan imaan zata tambaya dan haka yace eh dazu munyi salla dashi a masallaci, saidai yacemin akwai emergency a gaban sa, maybe dan hakan ya kashe wayar sa. "Mummy ta sauke ajiyar hrt, har zata tambayr shi imaan sai kuma ta fasa. Nan suka katse wayar.
"Omar kuwa yana office hankali kwance yana gudanar da aikin sa, tun jiya wata number take damunsa, kuma duk layinsa dsme number ake kira, ana turo masa messages na kauna. Dalilin hakan yasa ya rufe gaba1 wayoyin sa dan bayason takura.
"Da yamma masu tafiya nayi, masu aikin dare na zuwa, omar ne ya fito a office bayan ya kammala abinda zaiyi, ya wuce inda motar sa take, anan ya shige yyi hanyar gida hankali kwance.
"Farooq kuwa sai magrib sannan yace imaan ta taso su tafi dan sosai hankalin imaan ya tashi duk taji zaman hospital din ya dameta, "lkcn da suka bar hospital din wata hanyar taga yabi da ita, da sauri ta kalleshi, "wannan karon ma hannu yasa mata alamar tayi shiru. "Wayar shice tayi kara bayan ya kara a kunne yace hello, oh yeah gani nan hanyar zuwa club din, ohk bye. "Imaan hankali tashe ta zaro manyan idanun ta batasan lkcn da ta furta club????? Da karfi ba, Wanda taso tsorata farooq, tsaki yaja yace yes, imaan tace dan Allah ka maidani wajen mummy, farooq yace cinyeki akace za'ayi? Imaan tayi shiru, farooq yace so karna sakejin bakin ki.. A zuciyar sa kuwa yasan dalilin sa nakin maida imaan gida da wuri, take yyi saurin kashe wayoyin sa ma gaba1.
"Omar kuwa bayan yyi parking a gida. Tsaye ya tarad d mummy a falo, yanayin sallama, mummy batare d ta amsa sa ba tace INA *imaan*??? darararammm take qirijin omar ya fara dukan Tara Tara danshi gaba1 ya manta da zancen wata imaan, shi sai yanxu ya tuna inda ya barta,a zuciyar sa yace so bata dawo gida ba kenan?, eh lalle yau mummy zatayi farfesun sa.... Bai ida zancen ba mummy ta katse shi da fadin bakaji me nace bane?
Nuceey luv😘