56-57
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
56_57
"Murya na rawa yace am.. Daman.. Na turo ta gida bayan an gama komai na skul, "mummy ranta a bace tace abinda zakamin kenan omar? Ni nasan ko kamshin gsky babu a zancen nan naka, "omar y dafe kai, yace sorry mummy wlhy.. Common rufemin baki, abinda nakeso dakai shine duk inda kasan ka jefar min da yarinya kaje ka nemo min ita na baka 2hrs matukar baka dawo da imaan gidan nan ba sai ranka yyi matukar baci. "Omar yyi shiru ya juya zuciyar sa sai tafasa take, yanzu a duniya ba wacce ya tsana kamar imaan tunda har tayi sanadin da mummy take masa fada mwtsss yaja tsaki daidai lkcn daya bar gidan, yana fitowa kuwa rasa abun yi yyi, dole ya koma wajen daya ajiye imaan dazu.
"Farooq kuwa a mota yace imaan ta jirashi, sannan ya fice abinsa. "Yana wajen club har wajen 11:30 sai alkcn ya tuna da yabar imaan a mota, da saurin sa yabar wajen, sannan ya koma mota. Tana kwance har tayi kuka ta gode Allah bcci yyi awun gaba d ita. "Kiran sunan ta yyi, yaji bata amsa ba, dan haka ya dan buga hannun ta, a firgice ta tashi tana kallon sa sannan ta fashe da kuka tace dan Allah ka tausayamin ka kaini wajen mummy, farooq yace shiii, sannan ya furta kinason na maidaki wajen mummy? Imaan ta gyada kai, ohk toh idan mun koma kada kice na zo dake wajen club kinji abinda nace? Imaan ta girgiza kai alamar eh. "Farooq yace gud. Sannan yq tada motar sa suka bar wajen. "Sunyi tafiya me tsawo kafin suka iso unguwar tasu. "Farooq ya hango motar omar a kofar gida, hakan yasa shi yin murmushin mugunta, guddd ya furta a fili yasan wannan kadan daga cikin aikin mummy kenan, "omar kuwa yana mota ya kifa kansa tunanin duniya ya ishe shi, ya kira farooq yafi a kirga Amman shiru kkeji, dolen sa y tsaya zubawa sarautar Allah ido, ya kasa shiga gidan dan besan me zai cewa mummy ba gashi saura 5mins ya cika a lkcn data diba masa. Mwtsss yaja tsaki tare da furzar da wata iska me zafi.
"Lkcn da farooq ya shige gida, a tsaye suka tarad d mummy sai safa da marwa take, "mummy na ganin imaan tazo da sauri ta riketa tana tmbyr ta meya faru da ita? "Imaan ta kalli kofa daidai lkcn farooq shima ya shigo, mummy tace wai tare kuke? Farooq yace eh mummy, mummy tace garin yaya kukayi dare haka? "Farooq ya shafa kai sannan yace aiki ne ya rikeni mummy daga nan na biya ta wajen frnds dina can muka Dade, mummy tayi tsaki shirmen banza shirmen wofi wannan ai shashanci ne farooq, taya zaka dauketa maimakon ka dawo da ita gida sai ka wuce d ita gantalin ka? Faroiq Kansa a kasa yace sorry mummy, mummy taja tsaki tace wannan ya zama na karshe. Farooq yace toh sannan yabar wajen., shi badan komai yai hakan ba saidan omar yanda ranar yazo yana masa masifa akan deban jinin sa d yyi, shi yasa y rama ta wannan hanyar, da haka ya wuce dining table dan yunwa yakeji, mummy tace oya bishi kema kici abincin imaan tace toh.
"Tym na cika omar ya shigo gidan duk jikinsa a sabule, saidai yyi mamakin ganin motar farooq shi Sam bai lura da zuwan su ba. "Sallama yyi mummy ta amsa masa bayan ta jefe shi da harara, karasowa yyi ya sunkuta gaban mummy yace wallahi mummy bada gangan ta 6ace a hannu na ba, saida na gama mata komai na skul sannan na sata a napep kasancewar an kirani emergency, "mummy tace wai imaan hakane? Take gaban omar ya bada rasss cike da tsoron kada imaan ta tona masa asiri na wulakancin d yyi mata, hade d mamakin ganin ta d yyi. "Imaan har zatace aa sai farooq yyi mata alamar tace eh dan ya fara tausayawa twins dinsa, "imaan tace duk abinda ya fada hakane, take omar ya saki ajiyar zucuyar d be shirya ba. "Mummy ta tabe baki tace next tym karka karayin haka, omar ya CE toh, sannan ya tashi, yunwa yakeji Amman ya gwammace ya wuce side dinsu, daidai zai wuce ya wurgowa imaan wata muguwar harara, imaan ta saki baki tana ganin ikon Allah, a zuciyar ta tace zakasan ka harareni wallahi.
Nuceey luv😘