58-59
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
58_59
"Bayan kwana biyu, yau ta kasance Saturday, babu aiki kenan, "burin imaan naya zata kuntatawa omar take dan yanzu ba laifi suna dan taba hira da ya farooq Amman ba sosai ba, "omar kuwa har abada bazata manta abinda yyi mata ba, "bangaren omar kuwa Sam Allah be hada jinin sa Dana imaan ba, ko kadan bayason ganin ta, shu hakanan yake daukar ta a kazama. "Imaan CE gaban dining tana jera abinci, mummy ta karaso wajen ta tace je ki kira yayunki muci abinci. "Imaan tace toh. "Side din su ta nufa. "Wajen farooq ta fara zuwa kasancewar ta taba zuwa sau daya, a daki ta sameshi yana kwance be tashi ba. "Daga bakin kofa tahau Kiran sunan shi, ya farooq Amman shiru, dan haka imaan ta hau kan gadon sannan taja kunnen sa kamar yanda yake Jan kunnen ta muddin ya tarar ta tana bcci, kamar a mafarki yaji an fisgi kunnen sa, ai da sauri ya mike yana karkade kunnen sa, imaan ta kyalkyalce da dariya, bayan ta sauka kan gadon. "Farooq yaja tsaki yace wallahi na kamaki saikin gayawa 'yan garinku imaan ta murguda masa baki tace ehdin, saukowa yyi zai kamata ta kwashe a guje tana fadin Nima mummy CE ta aikoni wai kazo muyi break. "Farooq ya girgiza kai kawai sannan ya shige toilet.
"Sashen omar ta nufa anan ta tura kofar a hankali kamar wata munafuka, bayan tayi sallama taji shiru, har kusan sau uku ba'a amsa ba. "Har zata tafi wata zuciyar tace bude dakinsa mana, aikuwa hakan tayi. Bude dakin tayi Amman taga baya nan sai mamakin tsaftar dakin take tamkar na mace, haryafi na wata macen ma. "Jin alamun zubar ruwa hakan ya tabbatar mata a toilet yake, dan haka ta tabe baki a zuciyar ta tace idan yaso karma yaci abincin. "Haka ta juya abunta. "Daidai zata fita ta hango ayaba kan fridge da Alama anason sata ciki ne, imaan har zata wuce wani tunanin yazo mata. "Anan ta koma jikin fridge din, sannan ta balli kwaya daya, tass ta cinye, sannan ta dauko bawon ta dawo dakin omar, a hankali ta tura kofar, wata irin hamdala tayi ganin har yanxu be fito ba, dan haka ta la6a6a daidai bakin kofar ta jera bawon ayabar. "Tana gamawa ta fito a hankali tare d jawo kofar kamar yanda ta gani. "Sannan ta fice daga side din zuciyar ta fal cike d murmushi.
"Lkcn da ta koma bangaren mummy har farooq ya isa wajen. "Imaan tace laah harka fito? Farooq yyi banza da ita, sai alkcn ta tuna lefin da tayi, a take ta canja fuska itama tace kuma kuma ma ai Kaine ka faramin nima na rama... Bata karasa ba farooq yace kikace me? Imaan tayi shiru, ganin mummy tabar wajen tasan sarai zai iya murde mata baki, dan haka taja 'yan matan bakin ta tayi shiru... Gane hakan yasa farooq ya matso ya jawo kumatun ta yace maimaita abinda kikace? Imaan tsabar zafin rikon d yyi mata batasan lkcn data saki kukan shagwaba ba, mummy ta fito da sauri tana fadin lpy? Farooq yace rashin kunya tayi mummy, mummy tace mwtss Allah ya kyauta, sannan ta koma inda ta fito. "Farooq kuwa yyi murmushi yana me kallon imaan.
"Toh 6angaren oga omar fah 🤔...
Nuceey luv😘