JANNAH

13

by @mommuhseen

*_💔JANNAH💔_*

_{A TRUE LIFE STORY}_


*E.W.F*


By

Mrs Bb

mom muhseen


wattpad name

Humaira3461



🅿️.......13




Inayin sallama da shukra naci karo anty Aneesa tana ta balbala masifa ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, akan rashin zuwanta da wuri da batai ba gefe guda kuma naga bakuwar fuska da alama itama yar gidance don naga fuskar momy jikin tata, sunyi kama sosai kwabo da kwabo.


"Zaki tashi daga gabana ko sai nayi kwallo dake, kidahuma kawai"


Tana shashshekar kuka ta mik'e sauri-sauri tabar wurin, kasa shiga nayi saboda gaba d'aya na tsorata sai lab'e nake bakin k'ofa jikina na tsuma, su duka banga alamun sassauci daga garesu ba basuda tausayi da rangwame.............."momy idan kina son ki zauna lafiya mu zauna lafiya muma dole ki bamu had'inkai, agaban kowa fa kika ce yai miki warning akan yar aiki, yar talakawa wadda bata kai darajar takalminki ba, shi yaya khalid d'in yana wajen kuma baice komi ba"


Aneesa tace, "Anty fareeda don Allah kibar maganar nan, ya riga ya wuce gobe ma zai bar kasar ba shikenan ba, nifa duk abunda xai cutar dashi bana so............zaki rufen baki ko saina ci ubanki Aneesa? Shegiya da bata kishin uwarta,kodayake dan wani daman bai zama naka"


Cike da rashin kunya tace, "Niba shegiya bace Anty fareeda, kuma ni da kike gani nafiki kishin momy duk da bata haifan ba"


Fitowa nai daga karamin falon nayo waje, nama rasa ina hankalina yake kaina ya kulle ban fahimci duk abunda suke cewa ba, bazan iya bi ta gabansu ba tabbas in suka ganni akaina zasu huce, tunda nice silar komi.


Wajen maigadi na nufa na sake gaidasa cikin sanyin jiki nace, "baba mudi akwai wata hanya da zata kaini bangaren mu banda waccen"


Yace"zo muje na nuna maki, ai don kina bakuwa amman waccen kofar ai ba hanyar fitowarki bace"


Binsa nayi zarai zarai har muka zaga baya sai gamu kofar kitchen ta baya, kadan muka kara matsawa sai na samu shukra tana ta kuka ga wanke wanken tana tayi har taci rabinsa, baba mudi ya koma bakin get ni kuma nai tsaye bayanta naji duk ta bani tausayi,

Muryar baba uwani naji tana isowa wajen tana cewa,

"Ki hanzarta ki gama tunda ba shikadai zakiyi ba, duk ke kika jawoma kanki bakijin magana shukra ko kadan.........Aa aha ke kuma yaushe kika shigo?"


Sai lokacin shukra ta waiwayo nai ajiyar zuciya nace, "yanzu na dawo, sannu da gida babaah uwani"


"Yawwa kema sannu, kije kicire kayan kizo mu dora sanwa"


Na amsa mata da to ja wuce ta kofar na isa har dakina ba tare da na had'u da wani acikin su ba, kaya nake cirewa ina sake tariyo maganganun su da naji a falo, Anty Aneesa ba yar gidan bace kenan? To shi yallab'ai khalid d'in fa? Wannan dai Anty fareedar da alama itace kebin yallab'ai hisham duk da har yau bamu had'u dashi ba, wane hadin kai take son momyn ta basu? Duk bai wuce akan abunda ya faru dazun da safe ba,


"Ya Allah ga murjanatu! Ka taimakeni ka kawo mun dauki, ka kareni daga wadannan mutanen"


Har ga Allah tsoron su nake matuk'a,momy kanta abun tsoroce shirun da take baya nufin alkairi, haka dai naita zancen zuci har na wuce muka fara aikin nida babaah uwani, saukin mu akwai time table na abincin da akeyi duk rana, sannan ba kullin mukeyin na dare ba nida babaah akwai babah azumi itace keyi akin yamma har wanke wanke da gyaran kitchen da sanwa, daman sai bayan laasar take zuwa ita.


Weekend ne muke yin girkin safe dana rana,sai idan za'ai ma Abba tuwo ni nakeyi masa, sauran gyare gyaren kuma working day's nake yinsu weekend kuma shukrace, ba laifi ina dan samu hutu matsalar mutanen gidan ne basuyi ba.


Muna cikin aikin ne naji an shigo kitchen din, juyawa nayi mukai ido biyu da bakuwar ta yau na risina ina gaidata,


"Ina wuni, anzo lafiya"


Wani kidahumin kallo take wurgamun kafin cikin izgili tace, "kece jannah?"


Gabana na fad'uwa nace, "eh nice"


Taja wani dogon tsaki ta bud'e frij ta dauki lemu tana cewa, "babaah me kuke girkawa yau"


Ba tare da babaah ta kalleta ba tace, "pride rice ce da nama, sai tuwon shinkafa da miyar agushi da naman kaza"


"Ohhh duk ciki banada abunci, kee!"


Na jiyo ina kallonta tace, "maza ki jik'a wake alale nakeso da kwai aciki, asanya mata alayyahu da sannan ai mata miyar kifin gwangwani"


Wani rugugin tashin hankali naji ya rufto mani, na had'iye miyau daker...........bakijina ina magama jakar banza"


Ina kerma nace, "to...to zanyi yanzu"


Tana jan tsaki tace "kidahuma"


Tana ficewa hawaye na zubo mun, na aje wukar hannuna ina sharewa babaah tace "kiyi hakuri murja, mutanen gidan nan abunda suka iya kenan yana daya daga cikin abunda yasa yan aiki basa zama da sun fata kwana kadan suke guduwa, ki kara hakuri abunda kawai zance maki kenan, sai kuma ince ki ringa addua kina rokon Allah ya tsareki daga dukkan mai sharri"


Naji dadin lallashinta saboda da ciwo aimaka cin mutunci bakada wanda zai lallasheka ya baka hakuri, waken na jika sannan na tuka tuwon na barsa ya silala sannan na hau kullashi, babaah ta dora mun naman kafin in gama kulla tuwon.


Atakaice dai nasha bakar wuya nice har wajen karfe uku da rabi a kitchen, ga yunwa ga gajiya ko sallar azahar banyi ba gashi duk bayan mintyna zata shigo ta zageni akan wai ban gamaa ba, don ma akwai blander sai nayi markaden agida.


Ina cikin shirya mata abincin naji kamshin nan da idan najisa nakejin natsuwa da sassauci acikin raina, lumshe idona nayi inajin wasu hawaye sabbi suna zubo mani, bazance ga dalili ba nai saurin sharewa ina juyawa muka had'a ido dashi,

Yana jingine jikin frig yai crossing legs dinsa ya saka hannunsa daya cikin aljihun jeans din dake jikinsa, kansa yasha gyara irin askin yan kwallon nan kuma yai masa kyau sosai,na sauke idona daga kallon da muke ma juna nace,


"Sannu da dawowa yallab'ai"


Cikin cool voice dinsa yace, "sannu da aiki Jann"


Yau kuma wani sabon suna na samu kenan, na fada araina nace "yawwa nagode"


"Mekike yi haka? Abinci kala nawa yau kukai kamar za'ai baki"


"Bakuwar da tazo akai ma wannan tace ba zataci wancen ba...........wai Fareeda kike nufi?"


Yadda yai maganar cikin fusata saida naji tsoro cikin sauri nace, "Aa yallab'ai karkai magana nice nace zan mata"


Hararata yayi ya juya yana cewa ki saman a can falon,

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un, yallab'ai zai sake janyo mun fitina na shiga ukuna"


Daukar kayan abincin nayi na dora ruwa da lemun da tace mun, na nufi can babban falon hankalina atashe, khalid,usman,hindu,Anty Aneesa da Anty fareedar sai momy da yallab'ai Asaad, ina rawar dari na risina na aje bisa table din dake gabanta nace, "gashi Angama"


Taja tsaki "wawuya kawai bar nan wajen.............ya zama last warning da zaki zageta! Kinci arziki an gama abincin wallahi da ba zatayi ba, kin son wannan din ki koma gidan mijinki mana kici, momy daga rana irin ta yau kar wanda ya sake had'a masu aiki mai yawa haka, suma fa mutane ne sun buk'atar hutu............idan hutu suke buk'ata meya kawosu aikatau, aida sai su zauna gidajen uban ninsu su huta dakyau nan kau dole suyi aiki matsayin bayi suke"


Khalid yai maganar cikin gadara da isa cikin kufula Asaad yace, "nidai na gaya maku idan hakan ya sab'a kowa bazaiji dad'i ba"


"Wai Yaya Assad aikin nata dole nan gidan? Ta tarkata ta tafi mana asamu wata, tunda baka son tasha wuy..........fareeda!!!"


Momy ta daka mata tsawar da duk saida kowa yaji ajikinsa jikina rawa yake kamar mazari saboda gigita, cikin fada sosai take cewa, "Asaad shiya kawo Jannah nan gidan tare da yardata, yana da ikon da zai tsawatar akan abunda yaga ansata dayafi karfinta, kowa yana jina anan kar wanda ya sake sanyata aikin da ya wuce wanda takeyi, na fada maku da babbar murya muddin mutum yana son zaman lafiya dani, ke kuma"


Ta watso mun idanunta wanda najisu har cikin yan hanjina ta cigaba da magana idonta akaina tana zarosu, "duk wanda ya saki abu muddin baya cikin aikin ki kuma kikayi nidake ne acikin gidan nan,"


Bakina na rawa nace, "zan kiyaye momy ki gafarceni"


Ta kauda kanta daga gareni harna tafi naji muryarsa data shak'e yace, "zoki dauki wannan"


Na dawo na dauki ledar babbace cike da fruits, "ki raba uku ki saka kashi daya frig ki kawo masu kashi guda nan, gudan ki yi min fruit salad ki kawo mun"


Nace to ina mazari nabar falon, duk yadda yace nayi haka nayi na kawo masu nasu, na koma na had'a masa fruitsalad din na zuba kankara aciki don nasan yanzu zaisha, ta taga na hango fitarsa da mota, saina sanya frig karya huce na wuce naje nai wanka nai sallar azahar da la'asar saboda itace ake kira yanzu.


********


"Yaya kanaganin abunda momy tayi ko? Wai momy tana cikin hankalinta kuwa? Nifa na gaji da wannan abun wallahi"


Khalid daya kafe waje guda da kallo baice mata komi ba, suna cikin dakinsa lokacin kallo daya zakai masa kasan cewar akwai wutar dake ci cikin ransa...........yaya kayi shiru bakace komi ba"


"Fareeda ki bani lokaci dole hakarmu zata cimma ruwa, nayi alk'awarin muddin ni d'an babana ne inhar na cika dan halak saina wulak'anta rayuwar Asaad, ke gabar taki yar mitsilace akansa kiyayyar da kike masa batakai ta kawo ba, inda zaki laluba raina kiga abu da ke ciki akansa,sai kin kasa bacci don haka kar hankalinki ya tashi kina dani koda sanin momy ko babu saninta saina saka Abba yai masa korar kare cikin gidan da yake tak'ama dashi, yake tutiyar gidan ubansa ne yana mana kallon mu y'ancin arziki"


Ajiyar zuciya tayi tace, "naji dadi, har hankalina ya kwanta zan saurareka amman komi ake ciki karka saka wannan jakar Aneesa, shegiya haukar son da take masa bazai barta ta goya mana baya ba"


Jinjina mata kai kurin yayi sannan ta fita daga dakin.








*muje zuwa yanzu aka fara bamu saka ko yatsa ba*





Mom muhseen✍🏻