17
by @mommuhseen
*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_
*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseen
wattpad name
Humaira3461
🅿️.........17
Karfe tara muka iso wani gida mai kyau babban get ne aka bud'e mana muka shiga ciki, tashin ginin yai mana sallama duk yadda nake cikin rud'ani bai hana ni ganin tsananin kyan ginin ba, fuska duk hawaye sun bushe na kallesa, hararata yayi yana cewa "akoke kawai, ke komi na kuka ne wajenki"
Na sadda kaina kurin bance masa komi ba, bud'ewa yai yafito ya zagayo ya bud'e mun, kallon sa kufin nake da mamaki sometimes ina mamakin wasu abubuwan daga garesa........"malama fito don Allah karki cinyeni da kallo"
Fitowar nayi ya zaga ya dauki jikkata dake baya ssnnan na bisa baya ina ta yaba gidan daya dauki hankalina, fitilune ta ko ina kuma akwai bene can sama gidan gaskiya babu karya binsa nai tayi har muka ratsa cikin babban falon inda mukai sallama.
Wata farar mata ce da yara guda biyu mace da namiji, sai kuma maigidan shima yana nan kallo guda nai masa naga fuskar yallab'ai Asaad ajikin tashi, mamaki sosai ya kamani yayin da dan danan matar da yaran suka fara murnar ganin mu, ko ince ganin yaya usy saboda ni basu sanni ba,
"Usy dan mama kaine da daren nan? Sannun ku karaso nan yan mata ki zauna"
Matar ta fad'a cikin sand'a na isa na zauna gefenta ina gaida ta,
"Lafiya lau yan mata, usy ina ka samu kyakkyawa haka"
Yaran duk sun baibaye shi suna masa surutu babansu ne yai musu magana sannan suka natsu, cikin ladabi na gaida shi shima ya amsa mun cikin faram faram sunata jan yaya usy da tsokana.
"Anty bakuwa na kawo miki zatai miki kwana biyu sunan ta Jannah"
Tana ta dariya tace, "masha Allah suna mai dadi, ba komi usyn mama"
Tatashi ta wuce kitchen don kawo musu wani abun, ya dubin yayan nashi yace kasa-kasa "yaya itace ajiyar Bros fa"
Zaro ido yayi yace, "dagaske usy?"
Murmushi yayi yana cews "wallahi kuwa yaya, to ya kaganta?"
Duk a munafurce suke maganar, murmushi yayi yace "shegen nan ya iya gane gane har ya gano wannan tsaleliyar haka, amman miye labari nasan akwai dalilin kawota nan?"
"Muje ciki kaji komi yadda akai,nama sanar da Abba don kar ya koma ta tsara masa munafurci"
Tashi sukai yaya usy na cemin "bari na zo jannah"
Rausayar dakai kurin nayi suka barni nan ni kadai har ta dawo,
"Ayya jannah ke kadai ko"
Ina murmushi nace "babu komi Anty"
Lafiyayyen Irish ne soyayye da kwai ga yar sos a sama anyita da kifi, sai kuma dambun nama da ruwa da lemu, jinai yunwa tai mun sallama inhar ina nan bazan sake ba har naci na koshi, sai nace mata "Anty inaso nayi sallar isha sannan"
Tace"to ba damuwa muje ciki inkika gama saiki acan zaifi"
Dasu ta bini ni kuma na dauki jikkata nabita, gidan karshe ne wajen had'uwa gaskiya, daki guda ne yaji kayan gado masu kyau ga labulaye nan da fitilu masha Allah, tace "to ga toilet nan inkina bukatar abu don Allah kimun magana karkiji komi"
Nace"to Anty nagode sosai"
Zama nai naci nai hani'an saboda sosai nakejin yinwa tun kalacin safe banci komi ba, nai hamdala naje na wanke bakina na dauki kayan na fidda kitchen din na same ta ansa tayi tace, "aida kin barsu zanzo na dauka"
Nace"Aa haba ni miye amfanina"
Wanke wanke take na tayata munayi har muka gama muna fitowa suma suka fito yaya usy yace, "Anty munirat ni zan wuce dare na karayi zan dawo gobe na duba ajiyata"
Tace"to usyn mama saika dawo din, kanaji da wannan ajiyar taka dai karka damu zan kula maka da ita"
Had'a ido mukai dashi yace, "zaki rakani ko?"
Ya na iya dole nabisa zuwa inda ya aje motar tashi tsaye yai ya rungume hannu yana kallona sai naga tamkar yallab'ai ne yake kallona, sadda kai nayi bance komi ba saida ya gaji naji yace,
"Baki tambaye ni nan ina ne ba"
Nace"ai nasan ba zaka tafi ba saika sanar dani"
Murmushi yayi yana cewa, "Jannah kenan, nan gidan yayana ne mai bin Bros sunan sa Hisham, zaki zauna dasu har sai wannan ramar dakikai ta koma inba haka ba bazaki koma wancen gidan ba Allah ko"
Zaro idanuna nayi yace"yes haka nake nufi, don haka ki saki jikinki nan ma gidane ba abunda zaki nema ki rasa kuma su sunada kirki ba kamar wadancen ba"
Na rausayar dakai bance komi ba,
"Watau bazakiyi magana ba kenan"
Murmushi nayi saboda nasan haushin wannan shirun da nake masa yake nace, "to yaya usy zan zauna din nagode sosai da kulawa"
Iska yaja sannan yace "zan ringa zuwa kullin ina ganinki"
Saurin kallonsa nai saboda yadda yai maganar so silent gently, sai na maida kaina kasa nace "to yaya usee Allah ya kaimu"
Lumshe idonsa yayi yana cewa, "duk uniforms dinki suna nan na sanyo miki, gobe zanzo mu wuce school"
Nan ma rausayar dakai nayi, kamar bazai tafi ba daker dai ya shiga motar yace "Good night jannah"
Daker na kakalo maganar nace, "ok by"
Saida ya fita nikuma na koma cikin gidan zuciyata cike da wasu abubuwa da na kasa ganesu.
********
Lamarin yaya usee ya fara daure mun kai abubuwa ne yake mun da kwalwata ta kasa daukar su, kaina yana kullewa ba wani abune na tashin hankali ba amman hakan yana rikita ni, misali yawan kallon da yake mun ina yana mun magana kamar yana lallashina, duk wani abu daya shafeni cikin hanzari yake yinsa idan muna zaune ko muna wani darasin yaita jan abun saboda kar agama da wuri, tun da nazo gidan yaya Hisham shine zai kaini makaranta ya kaini islamiyya, shine siyo mun wancen kawo mun wancen daidai da rana guda bai tab'a mun maganar yallab'ai Asaad ba, rannan da na cika sati biyu agidan na rakosa xai tafi da daddare na kasa hakurin danne abunda yake damuna tun tafiyar yallab'ai, kamar dai yadda ya saba yai shiru yana kallona sai nayi amfani da wannan damar nace,
"Yah usee yaushe yallab'ai Asaad zai dawo? Yaufa watansa biyu harda sati uku"
Sai kurin naga ya bud'e mota ya shiga ya ja yai tafiyarsa, idona waje nake bin motar da kallo har ya fice kamar an shukani a wajen saboda kad'uwa da abunda yayi, na dad'e nan kafin na koma cikin gida wayar daya bani na d'auko na tusata gaba ina kallo, iyakar sanina layin da yake kirana dashi kona kira bazai je ba, saboda bazai amfani dashi acan kasar ba shiyasa ban tab'a gwadawa ba, har zuciyata babu daren duniya da bazan dauki dogon lokaci ina tunanin sa ba, yau kam ban sani ba naji kwalla na d'igar mu saurin la kutota nayi ina kallonta kamar zararra, sai na goge fuskata na dauki qur'ani na ina tilawa.
Wannan bai hana shi zuwa washe gari ba don kaini islamiyya da yake weekend ne, nuna wa yayi kamar ma baisan meyafaru ajiyan ba muna hanya ne ba mai magana naji yace,
"Hindu ta isheni akan yaushe zaki dawo, don ban gaya mata inda kike ba tace kema baki gaya mata ba hakane"
Ina kallon waje ta taga nace"uhm"
Bai damuba ya cigaba da magana, "to yaushe zaki koma?"
Nan ma ban kallesa ba nace, "duk sadda ka shirya maidani,"
Burki naji ya taka da karfi ya jiyo cikin fushi, "ni kike ma wannan shariyar ehy? Kin sani sarai bana son wannan abun"
Kadan ya hana ban bushe da dariya ba amman saina sake shan mur na kauda kai naki masa magana, "dake nake magana kika jiyar dakanki ko"
Nan ma nai masa tsitt, ya dad'e mai sake cewa komi ba na dauka ma ya hakura da mun maganar sai naji yace cikin raunin murya kamar zai kuka,
"Ni nake miki magana kina banza dani? Shikenan.............Yah usee ni meka mun jiya fisabilillahi? Tambayarka nayi ko kallona bakai ba kurin ka shige mota kai tafiyarka ka kyaleni, don Allah ni bakai tunanin abun zai mun babu dadi ba"
Na katsesa da fad'ar haka saboda Allah ya sani naji babu dadi sosai, duk yadda nake bashi girma nake gudun abunda zan bata masa shi baya gani.
Cikin sanyin murya yace, "I'm sorry"
Daga haka har ya saukeni bai sake cewa komi ba, ranar duk wanda muke gaisawa yasan bana cikin walwala, hindu ce tazo sit din mu.
"Haba mana yar uwa don Allah kidawo gida hakanan"
Murmushi nayi nace, "waye yace dake bazan dawo ba, zan dawo mana"
"Gidan duk babu dad'i baki nan, ni nake gyaran dakina kullin agajiye zan tafi sch, abinci saidai kashiga ka girka da kanka don baba uwani ma tayi tafiya, wannan yar iskar kuma ko tayi ba dad'i yake ba pls sister ki dawo gida"
Na rik'o hannunta cikin kulawa, "zan dawo insha Allahu, zan matsa ma yaya usee ya maidoni kinjiko yar gidan momy"
B'ata rai tayi tana cewa, "wace momyn kuma? Kedai kawai ki manta gidan nan ya sake rikicewa nida momy yanzu ai saidai gaisuwa"
Ban fahimci maganarta ba sai ban isheta da tambaya ba muka fara wata firar ta daban, har ta sanyo maganar yallab'ai da kanta.
"Jiya ai munyi video call da brother ga computer, sai fad'a yake mun wai principal ya sanar dashi bana maida hankali"
Jinai ta sosa mun inda yake mun k'ai-k'ai na lumshe idona saboda hirar sa kadai tasa naji wani iri araina, nace "Ashe kuna waya dashi?"
Tace"inafa, jiyane kawai shima don yai mun fad'a duk dokin ganinsa danake naji ya fita raina"
Ta fad'a tana b'ata rai, nai dariya nace "Ayya yana son ki maida hankali sosai shiyasa, yanzu yaushe zai dawo?"
Tace"tabdijam! Ai inajin har sai kun kusa weac sannan, daman inya tai Spain yana dadewa bai dawo ba, yaya ne kina kewarsa ne?"
Ta fad'a cikin zolaya tana kanne mun ido, murmushi nayi ina kauda kaina nace, "Allah ya shiryaki daga tambaya?"
Dariya take tace"ehy mana nagama ganoki ai, karki damu inhar kika dawo gida zan kira miki shi"
Daidai malam ya shigo mai yi mana sira da ishmawyi, dole ta koma sit dinsu sannan aka fara karatu, amman gaba daya hankalina akan maganar da mukai yake, sai naji na d'okantu da son komawa gidan kodan ta kira min shi d'in awaya.
Koda aka tashi na dad'e ina jiran sa yazo saida akai azahar sannan sai gashi yazo, yadda yake shigar sa da gayunsa kamar dai na yallab'ai Asaad sai naga yayi kyau sosai, cikin zolaya don in kauda fushin da yake bayan mun fata tafiya nace "yah usee zance zakaje ne haka?"
Wani kallo ya juyo yana mun kafin ya saki murmushi kamar bazai magana ba yace, "nayi kyaune?"
Nace"sosai ma kai baka gani ba"
Girgiza kai kurin yayi yace, "Aa ban gani ba yanzu dai nagani"
Ya mutsa fuska nai alamun rashin fahimta nace, "A ina kagani d'in to?"
"Share kawai, zaki koma gida gobe ne?"
Cikine sauri nace "ehy mana zan koma daman hindu sai complain takeyi"
"Uhm gobe kishirya sai kikoma Abba ma yanata magana wai yai missg tuwanki"
Dariya nayi silent da har saida ya juyo yana kallona nace, "Allah sarki Abba kace masa gobe dana dawo ya shirya cin tuwona"
Zuwa can yace "Jannah"
Juyowa nai ina kallonsa nace, "Naam"
Daidai mun iso gidan maigadi ya bud'e mana get mun shiga, saida yayi parking sannan ya juyo yana kallona saida gabana ya fad'i naga kamar yallab'ai ne gabana, cikin taushin murya yace "yau nakeyin birthday"
Cikin nuna farin cikina nace, "wow masha Allah, happy birthday ya usee"
Murmushi yayi yace, "thank you, na shirya wata yar liyafa ko zaki zo?"
Shiru nayi na dan lokaci saida ya sake cewa, "please...........kallon sa nai na maida kaina kasa sannan nace "shikenan zanje, amman ban san wajen ba"
Cikin jin dadi yace "Ai ni zanzo saina tafi dake, karfe takwas zanzo nama sanar da Anty munirat"
Yadda yake murna abun yaban mamaki fitowa nai muka shiga gidan tare, daki na wuce ina cire kaya amman zuciyata cike da tunani kala-kala.................
Mom muhseen✍🏻