18
by @mommuhseen
*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_
*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseen
wattpad name
Humaira3461
🅿️.......18
Kafin lokacin da yace zaizo yayi gaba d'aya ja rasa sukunin zuciyata, na kasa samun matsaya akan inje ko kar inje, gashi dai na amsa masa cewar zanje d'in to amman inajin tsoron binsa, bana zargin sa cin amana amman kuma wannan rawar k'afar da yake akaina fa?
Sannan a matsayin wa zan bisa Kanwa? Ko kawarsa? Kome...........rufe idona nai na kwanta kan gadona ina ta tunanin abunda ke faruwa dani, yah usy ya kasance mai kyautata mun da abunda nake so da wanda ma ban nuna inaso ba yimun yake, da karfin sa da kuma aljihunsa duk da nasan yallab'ai yana tura masa dukkan wasu kudi da zai mun hidima dasu, amman nasan wani abun da nashi yakeyi, don ma sun kammala exams dinsu ta final kwanakin baya shiyasa yake samun lokacin kulawa dani, aganina kulawar kamar taso tayi yawa amman idan na tuna kalaman yallab'ai kafin tafiyarsa sai inga yana yin abunda ya dauki alkawarinsa ne,..............shigowar Anty munirat yasa nai saurin tashi zaune tace,
"Kina son zaman daki Jannah bakijin komi"
Murmushi nayi nace "hutawa dai nake Anty, naga ba abunyi shiyasa"
Zama tayi tana cewa "ramma ta gama komi ai karki damu, yau nake koma wa night duty na usy yace zakuje party birthday dinsa ko?"
Na sadda kaina cikin sanyin murya nace, "dazun yake gaya mun, ni dai bana son zuwa Anty gashi na riga na amsa mashi"
Murmushi tayi tace, "ba wani abu insha Allahu karki damu, na yadda da usy sosai kije d'in idan yazo gashi yace na baki yanzu ya shigo ya fita,"
Jikina a sanyaye na anshi ledar da take bani nace, "Anty yah usy duk ya canza mun wallahi"
Dariya tayi tace "mekika gani ke?"
"Anty da ba haka yake ba, abu kadan indai akaina ne yanzu karki so kiga yadda yake rawar jiki akansa, sannan yaita yin wasu abubuwan da ni bana ganewa ni bana son hakan"
Kamar zan kuka nake maganar saboda har zuciyata bana son ya canza wannan alak'ar,
Rik'o hannuna tayi cikin lallashi tace,
"Karki tada hankalinki, ke amanace hannunsa kisama ranki babu wani abu tsakaninki dashi face matsayin yayanki ke kuma kanwarsa, da ace baki ansa masa zakije ba zan hana ki zuwa ne amman kin ansa idan kika ce baki zuwa yanzu zaiji babu dadi, ki dai kame kanki kinjiko wannan gown ce da zaki sanya, yace in tambayeki size din takalminki"
A sanyaye na amsa mata da cewa "36 or 37 duk ina sawa"
Saida ta sake kwantar mun da hankali sannan tatafi, na bud'e kayan ina dubawa kyawunta ya dauki hankali ainun red and black GE gown din, tashi nai na kangata ga jikina tsaf kuwa naga tsawon yai daidai dani, nai mamakin yadda ya san size din tsawona haka saina tuna rannan dana rakosa zai tafi gida har na juya ya tsaidani, inda nake ya karaso ya daidaita tsawonsa dani alokacin naji tsoro sosai yadda kusancin namu yai yawa haka, duk tsayina iyakar kirjinsa nake banma karasa ba kadan, yai murmushi yana cewa "Ashe ma ke yar gajerace na zata kinfini tsayi ai"
Ashe daman don ya gane tsayin rigata, harda wani net ajikinta hannun ma net ne ajiki ana ganin fatar jikin, har da veil acikin ledar sai wani dan box na sark'a silver mai dauke da sarka da yan kunne harda zobe,kayan sun burgeni sosai da sosai ainun dagani kuma zasuyi kudi sosai, maido kallona nai ga zoben azurfa ta da yallab'ai ya bani alokacin da muke bankwana, lumshe idona nayi sannan cikin sassanyar murya nake cewa a fili, "yallab'ai ban san iyakar lokacin da zan dauka wajen tunanin ka da kewar ka ba, zuciyata kullin da sabon abu take tashi akanka, har yau na gaza tantancewa na kasa sanin inda zuciyata ta nufa akanka, sannan ga kuma wani sabon abun makamancin irin naka daga d'an uwanka, ina fatan zaka mun uziri banda wata hanyar tserewa lamurransa, amman alk'awari na ne bazan tab'a bujire maka ba"
Zuwa nai na aje kayan saboda la'asar tayi naje nai alwallah nai sallar, su ashraf da sharifa suka dawo school ni nake shiryasu daman, muyita hira dasu muna dariya ba kamar sharifa tafi ashraf sakewa dani sosai, na gama masu suka ci abinci sannan muka zauna dasu study room dinsu na karatu, duk homework dinsu na taimaka masu sukayi Anty najin dadin wannan kulawar da nake masu, saboda wani lokacin bata zaune ma'aikaciyar asibitice in bata nan dagasu sai ramma mai aikinta, tunda nazo kuma sai ni nake hidima dasu kamar dai wata kanwarta hakan yana sata jin dad'i, har rannan tace ita wallahi daman nai zamana anan, saidai nai murmushi kawai bance komi ba, wannan zuwan ma da dalili da kila bazan tab'a zuwan ba.
Misalin karfe takwas na dare lokacin da yah usy yace zaizo ya daukeni, saida nayi sallar isha sannan nashirya shafa nayi daidai misali, ban tsawwala ba don daman ba gwanar kwalliyar bace ni powder da kwalli na saka a fuskar tawa sai dan jan baki red color, wannan kadai yasa naga nai wani irin kyau kamar zara acikin taurari, ni kaina wani lokacin inajin tsoron wannan kyan shiyasa kodayaushe nake cikin addua Allah yatsare ni daga dukkan masu sharri, ai banga nayi kyauba saida na sanya wannan doguwar gown din ko amarya sai haka sharifa ya aiko da takalman kala d'aya da veil din duk red ne, sai wani turare dan mitsili amman sakawa guda naji gaba d'aya ya baibayeni da mugun k'amshi, lumshe ido nai saboda ina masifar son turare karma ace na tuno kamshin turaren yallab'ai asaad, ina da burin mallakar wannan turaren koda zan karar da kudina inhar na samesa, Anty ce ta shigo nace "na daman inason zuwa ince miki bansan yazan daura wannan veil din ba"
Tana murmushi tace "masha Allah Jannah, kin ganki kuwa wannan ko ranar aurenki sai haka kinyi mugun kyau, don Allah kiyita addua kinjiko kodan bakin mutane"
Ina wasa da hannu na nace, "nagode Anty insha Allahu xan keyi"
Ita ta zauna ta gyara mun gashina dake kunce sannan ta daura mun veil din, tace "duk wanda ya ganki koda mace ce saitaji kinyi bala'in daukar hankalinta, to balle cikekken namiji kiyita karanta hazbunallahu wani imal wakil"
Tana sanya mun sarkar da yan kunnen ne mukaji yayi knocking yana cewa, "in shigo?"
Antyn ce tace"Aa ka koma falo gamu nan fitowa"
Har ban san yadda zan misalta kyan da nayi ba, zan iya cewa tsawon rayuwata ban tab'a ganin nayi kyau irin na yau ba in banda waccen ranar da yallab'ai ya kaini wajen gyaran jiki, wadannan lokutan bazan manta dasu ba.
Tunda muka fito idon yah usy bai dauke daga kallona ba, ko kyafta idonsa ma bayayi kamar ya manta da inda yake, kallona yake tun daga sama har k'asa, shigarsa irin tawa ce suit ne jikinsa bakake sai rigar sa sheet din ta ciki red color idan ka ganmu nidashi zaka dauka cewa wasu sabbin ma'aurata ne,gaba d'aya naji jikina yai sanyi Yah usy yana behaving ba daidai ba, wani miyau na had'iya kakkaura a sadda ya taso ya iso inda nake, idonsa akaina yake amman anty yake ma magana cewa,
"Anty kinyi mu sayar waccen jannah da wata ko? Na kasa yarda itace wannan"
Dariya take tace, "idonka ne kawai ya nuna maka haka, amman ita d'ince dai ba wata ba"
Kin kallonsa nayi saboda nasan wannan kallon da ya fara mun na yan kwanaki shi zan tarar yana yi mun, ni kuma bana son sa ko kadan.
"Jannah da gaske kece?"
Kai kurin na daga mashi alamun bashi ansar shi, yaja ajiyar zuciya yace "Anty mun tafi,"
"Don Allah usyn mama a dawo da wuri nima fita zanyi asibiti zan tafi"
"Insha Allah zamu dawo da wuri"
Kasancewa takalman Hill's ne dole nake tafiya ahankali wanda inka gani zaka dauka yanga ce, rigar har jan k'asa take daga baya duk da tsinin takalman, sadda muka iso bakin motar sa harya bud'e mun gaban, shiga nayi ya rufe sannan ya zagayo ya tada motar muka fita, banda natsuwa ko kadan zuciyata bugawa take sosai gaba ki d'aya yah usy ya canza duk alak'ar da yafaro da fari, tun sadda ya daukoni zuwa nan gidan komi ya sake canza wa bansan meke ransa ba amman tabbas akwai abunda yake hidden, shiru motar tayi banda kamshi kala biyu dake tashi bakajin komi saifa sautin kid'a dake fita k'asa-k'asa, inata tunane tunane na naji sautin muryar sa cikin kunnuwa na cike da wani a muryar tashi.
"Ban Saba ganin fuskarki a haka ba don Allah ki saketa kozan samu natsuwar fuskantar mutanen dana tara"
Runtse idona nayi kalamansa basa mun dad'i ko kadan, na hadiye abu daker cikin raunanniyar murya kamar zan kuka nace "Yah usy..........shiiiiiit karki ce komi please"
Dole na had'iye maganata har muka karasa wajen daya kama aka shirya shi tamkar wata gagarumar liyafa, abokan sa ne na makaranta maza da mata gasu nan kowa cikin shiga mai kyau, yana tsayawa da motar akazo aka bud'e mana muka fito, abune aka shimfid'a har zuwa cikin wurin wasu bayan mu wasu gaban mu, hayaniyar mutanen har cikin kwalwata, abokan sa ihu kurin suke suna watsa flowers suna kunna abu mai kara yana tats tats ana shewa har muka iso mazauni ga cake nan yasha kwaliya, kowa yazo wurin mu maganarsa akaina nane yayin da naga kishi idanun yan matansa wadanda suketa rawar kai akanshi, yadda suka ga yana wani nan nan dani yasa ransu ya b'aci, saboda hotuna idona har gajiya yayi abokan sa maza kamar zasu fad'o kaina, yah usy yai kokari gaskiya don ko wane table rabin kaza ce ake ajewa da snacks sai lemu da ruwa, tsarin wurin ya had'u sosai ga kid'a dake tashi mai dad'i, saida akaci aka sha sannan aka fara kokarin yanka cake, nidai lemu kurin nasha zuba mun yai a cup d'in ya mik'o mun, sai sannan muka had'a ido dashi daidai kuma sadda mai daukar hoto ya dauke mu, bazan iya fassara kallon da yake mun ba ban ankare ba ya samu cup din ga bakina, dan lumshe idona nayi kafin naji shewar mutane dole na ringa sha har na sha rabin sa, sannan na girgiza kaina cikin sanyin murya nace "na k'oshi fa"
Ajewa yai sannan ya d'an mun rad'a shima a hakan saida camera man ya dauka, bai damu ba yace mun "kinga kin korar mun yan mata na"
Zaro idona nai ina kallonsa, ya wani kashe ido guda yana cewa "dan sassauta pls sunyi mun girma da yawa"
Ba shiri na maida kaina k'asa, sannan akafara kokarin yanka cake d'in abokan sa sukaita karad'i ana wakar happy birthday, hannuna ya dora bisa nashi wanda ya rik'e wuk'ar dashi muka yanka tare, tafi akai tayi mana mai hoto bai huta ba shi kuma.
sannan ya cire wanda muka yanka tare ya nufo bakina dashi, marairaicewa nayi amman bai hana shi samun ga bakin ba, dole na gutsira sannan yabi abokansa yana basu wata dana lura tacika ta batse kiris ya rage ta fashe daya nufota sai kawai ta fice tabar wajen, atakaice dai ba a tashi wannan partyn ba sai eleven.
But d'insa da bayan motar cike suke da kyaututtuka kala-kala yunwa nakeji saboda banci komi ba a wajen banda lemu da guntun cake din daya bani, to amman bazan iya ce masa yunwar nakeji ba na bari mu isa gida bazan rasa abunci ba, tunda muka taho ba mai magana nidashi yayin da yake tukin kamar baida lakka ajikinsa, har saida nayi magana akan hakan.
"Yah usy baka da lafiya ne?"
Kamar jira yake yace "sosai ma"
Saurin kallon sa nai cike da son karin bayani, don nidai naga lafiya lau muka taho haka har aka gama partyn banga wani alamun rashin lafiya tattare dashi ba, na kasa hakuri nace "kamar ya? Bacin dazun kalau dinka kake"
Kamar zai kuka yace, "to yanzu kuma ba kalau nake ba jannah"
Na rausayar dakai kurin ban sake magana ba, naga alamar shagwab'ace kurin yakeji kuma ni bana cikin wadanda zai yima ita ehe,
"Bazaki tambayi meke damuna ba"
Ban Kulasa ba nace, "Allah ya sawak'a yah usy"
Murmushi yayi sunan da take kiransa dashi ba kadan yakejin dadinsa ba, sai ya amsa da cewar "Ameen jann..........mugun fad'uwar gaba naji asadda ya ce wannan jann d'in, don yallab'ai kad'ai ke kirana dashi kuma zanfi son ace shikad'ai zai dawwama yana ambatarsa, uffam ban sake cewa ba har muka iso gida a waje ya tsaya don daga nan gida zai wuce har na aza hannuna zan fita naji kamar daga sama ya rik'e gudan, arikice na juyo ina duban sa idanun sa sun lumshe sosai ya kwanta cikin sit d'in, muryata har rawa take nace "yah usy..............Jannah"
Ya katseni da maganar da zan abu ya dauko abayan motar ya mik'o mun, "ba cinye hannun zan ba kike zare mun ido"
Bansan nai murmushi ba na anshi abunda yake mik'omun nace, "idan mutum yai birthday shi akeba kyauta ba shine yake bayarwa ba"
Murmushin ya sake saki yace, "bansan meke cikin kanki ba har yasa kika mance da ranar haihuwarki, *Happy birthday beautiful! I hope you have a wonderful day filled with joy and happiness.* Allah ya karo shekaru masu albarka"
Idona kamar zai fad'i saboda kallon sa danake surprise d'in yai mugun dukana, no wander a wajen taron mutane keta ban kyauta, na dauka duk nashine tunda shima ai yau d'in ranar zagayowar haihuwarsa ce, daker na iya cewa "yah usy wannan surprise haka? Wallahi na manta, thank you so much i really appreciate it ban San yazan na gode maka ba"
Yadda fuskarsa ta nuna kadai na gane yaji dadin kalamaina, gift din da ya bani nake jujjuyawa murmushi bai bar fuskata ba nace, "bansan me zan baka ba matsayin gift dinka kaima, abun yazo mun gagafa yah usy.........bana son komi daga gareki jannah, abu guda nake so shine yardarki ki amunta dani I WANT TO BE UR BEST FRIEND, ina son na zama abokin shawararki kusancinki nake buk'ata daga haka bana son komi daga gareki, dare nayi kije zamu sake magana zuwa gobe by take care"
Rausayar dakaina kawai nayi na shige gidan shi kuma yaja motar ya tafi.
*YAH USY SHINE MUTUMIN DAYA SONI YA KAUNA CENI ALOKACIN DA RAYUWATA TA SHIGA CIKIN GARARI,ALOKACIN DA NA RASA YARDAR KOWA NA RASA KAUNAR KOWA. MATSAYINSA A WAJENA BAZAI KWATAN TU BA.......KASHHHH KARNA KARAR MAKU DA LABARINA TUN ANAN KUCI GANA DA BIN MOM MUHSEEN* 😉
Mom muhseen✍🏻