19
by @mommuhseen
*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_
*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseen
wattpad name
Humaira3461
🅿️.......19
Koda na dawo daki cire kayan jikina nayi saboda daman kagare nake na cire akwai nauyi, wanka nayo nazo na shirya cikin kayan bacci na riga da dogon wando, inayi ina tunanin abunda ya faru yau saidai inyi murmushi kawai, duk yadda baso zuwa ba na samu kaina cikin jin dsd'i, amman dana tuna gobe zan koma gidan momy sai inji gaba daya hankalina ya tashi addua kurin nakeyi, inda so samune ace naje naga su innamu kafin na koma gidan momyn, tunda ba lallai ta barni ba idan na koma din.
Zama nayi najingina da gado na tankwashe kafafuna gift din yah usy na dauko na ke bud'ewa ba abunda ke tashi sai kamshin turarensa ke tashi, shima ba daga nan ba indai wajen bulbula turarene amman har yanzu banji irin na yallab'ai ba.
Bansan sadda bakina yace, "wow this is so beautiful bungles, yan hannu ne manya masu kauri guda biyu kalar golden, sai agogo mai dan karen kyau itama golden color, fuskata dauke da murmushin jin dad'i yah usy yana matukar hidimta mun, baya gajiya da siya mun abu.
Saida na gama gwadawa sannan na maidasu cikin dan akwatinsu na maida cikin jakkata da nagama had'ata don tafiya gobe, na dawo na kwanta yar wayata na lalubo in duba time idona ya sauka akan missed call da wata no mai + a mugun zabure na tashi zaune, jikina har rawa yake tabbas duk duniya babu mai kirana saishi tunda ya bani wayar shi kadai yakirani kuma tunda ya tafi ba wanda ya sake kirana, yau kuma da naga kira ya tabbatar mun da cewar yallab'ai ya kirani yadda jikina ke tsuma har mamaki nake, tabbas inada kud'i sosai akan layin hannuna na rawa na soma bin number da aka kira da ita, kiran shiga yake amman ba a dauka ba runtse idona nai na sake jarabawa amman har ta gama rurinta ba'a dauka ba, raina yaimin babu dad'i ainun saboda na saka ran jinsa sosai, kira uku nai ba'a dauka ba sai na hak'ura kawai.
Bazan iya cewa ga iya lokacin dana dauka kafin bacci yazo mun ba, nasan dai na dad'e sosai karshe ban saan sadda nayi baccin ba.
**********
*ASAAD*
Tun daga ranar daya sauka spain baida lokacin kanshi, kasancewar dogon hutun dayazo yayi agida yasanya yana isowa ba'a bashi wata damar zama ba balle tunaninta ya gallabesa, training suke ba kama hannun yaro ba zama in dare yayi yazo ya kwanta gajiya ce take masa yawa daya fara tunaninta baisanin bacci ya sace shi, bai samu kanshi ba saida suka gabatar da wasan da yan wata k'asa cikin ikon Allah kuma sune sukai nasara, alokacin sunan sa ya k'ara yin shura ba a Nigeria ba ba acan spain d'in ba saboda kwazonsa da hazak'arsa, ga tarin kud'i da yake samu kamar hauka a lokacin da suka buga wasan Abba har can yaje kuma ya kalli wasan d'an nashi yana sakeyin alfahari dashi, saida ya kwana uku sannan ya bar kasar bai sanar da kowa cewar yazo ba sai usy, a sadda ya samu kanshi yake lokacin hutawa sai tunanin ta ya zame masa tamkar abokin rayuwarsa, duk inda zashi duk inda zai shiga itace mak'ale acikin zuciyarsa daidai da rana guda bai tab'a jin zai kirata ba, saboda a wannan lokacin baya da wani buri daya wuce ace jann ta samu ingantaccen ilimi wanda zata tsaya da kafafunta, watan watarana zata dauki nauyin dawainiyar iyayenta da ita kanta, tun yanzu idan ya rikita mata zuciya da soyayyarsa ba zata samu damar maida hankali akan karatun ta ba, shiyasa duk irin halin da yakejin sa aciki game da ita yake jurewaa, inhar yaji tana lafiya bakin usman hakan kad'ai yana sama sa natsuwa, kuma duk bayan sati biyu yana kiran principal d'insu yaji ya yana yin kokarinta, yadda yake samun good information daga garesa ba kadan yakejin dadin hakan ba, hakan yasa yaji bazai iya neman ta ba ya rikita mata zuciya don tabbas inhar ya kirata sai taji ajikinta, ya sama ransa cewar ba zaije gida ba akalla sai sunyi weac, ko kadan baya hutawa wajen turama usy kud'in hidimarta baya jiran karshen wata yayi daya samu daya tura mashi, sun dad'e basuyi waya da usman ba shine kwana biyu duk abunda yake faruwa yana sanar dashi wanda zai bashi shawara ya bashi wanda kuma zai dauki mataki ne nan danan zai dauka, kwatsam abakin hindu yaji cewar jannah bata gidan momy ranar da sukai video call yake mata fad'an rashin maida hankali a makaranta, cikin son jin ya Janna take yace mata "ga jann nan tama fiki maida hankali, in baki wasa ba zata baki mamaki"
Ta turo baki cikin shagwab'a "yaya ita ba karatu suke da yaya usman ba, ni kuma ba yayi dani ko"
"Zan mishi fad'a kema ya ringayi dake, ina jann d'in take tana kokari islamiyya kuwa?"
"Sosai ma Yaya kasan yanzu mun zama abokai, tare ma muke karatu idan akai mana k'ari, kwana biyin nan ne da bata nan bamuyi ba"
Yamutsa fuska yayi yace "ina taje? Ko gidansu taje usman bai gaya mun ba"
Ta bashi labarin d'an abunda ya faru da tafiyar su usman da jannah,
"Amman ban san inda ya kaita ba, muna dai had'uwa islamiyya haka a school ma muna had'uwa"
Sallama sukai da ita ya kira Abba sukai magana yake cewa zai dauki mataki sosai karya damu, zaima usman magana ya dawo da ita yayi haka ne don ta samu hutu.
Daga ranar bai samu lokacin magana da usman ba suka fara shirin buga wani wasan a kasan england, saboda muhimmancin wasa yasanya duk wayoyin sa a kashe suke duk kiran da usman yake masa baya samun sa, Asaad bai samu kanshi ba saida suka buga wasan daker suka sha sannan ne ya dawo hayyacinsa, ranar kamar an tuna masa da wani abu mai muhimmanci yai saurin duba kwanan wata, a zabure ya dauki wayarda time d'in yana bakin ruwa shida abokinsa ya kira usman.
"Bro's kayi wuyar samu 2days"
"Baka kalli wasan mu ba da yan real Madrid a england mukayi sa ban samu lokaci ba wlh"
"Ayya bros wallahi na shafa'a kuma Abba bai sanar dani ba, fatan kun lashe su nasan inhar akwai Bros ba zasu kai labari ba"
Murmushi yayi yana ce masa, "ehy mana amman ai daker mukasha, yanzu dai ba wannan ba ya kake ina ajiyata?"
Yar dariya usman yayi ta yak'e yana shafa kanshi yace, "tana nan lafiya bros"
"Meyasa baka gaya mun abunda ya faru agida ba usman? Ban gaya maka duk abunda ya taso wanda yafi karfin ka ka sanar dani ba"
Ransa a dagule yace, "yah abun nasu ne fa yayi yawa bazan iya jurewa b..........runtse idonsa yayi jin yana shirin tafko katob'ara,
"Menene ba zaka iya jurewar ba?"
Ya yanko masa tambayar cikin sauri yace, "abunda su momy keyi ba zanso ace ina gani suna cutar da janna ba bacin kace nayi bakin kokarina"
Lumshe idonsa yayi yana jin wani irin feeling kamar yai tsuntsuwa yaje yaga jann d'insa, cikin serious talk yake masa magana, "ina ka kaita yanzu?"
Usman cikin yana yi marar dad'i ya amsa da cewa, "tana gidan yah hisham"
"That's good, abunda zan gaya maka shine daga yau koma miye ya taso sanar dani kafin ka yanke hukunci, munyi magana da Abba komi zai kafa ka maidata gida insha Allah zan samu time ko yaya ne inshigo, na yaba da kokarinka sosai kuma ina bayanka akan ko sau d'aya karka barta tayi kuka, gobe shine ranar birthday d'inta kaima kuma goben ne naka, inaso ka shirya mata birthday zanso inaga tayi farinciki idan na dawo zanga pictures d'in, akwai kud'i dazan turo maka kayi amfani dasu please"
Ajiyar zuciya usman yayi yace "to yah insha Allahu za'ai duk abunda kace, yaushe zaka zo d'in?'"
Yana shafa kanshi cikin yar damuwa, "I don't know usy,amman dai zan zo insha Allahu"
"Ka kula mana da kanka we miss u so much, har jann ma tana kewarka jiya dai da takai bango har tambayata tayi"
Wani kayataccen murmushi ya sauke yana lumshe idonsa yana jin wani irin yana yi, yace "I'm Eiger to see her face, me kace mata to?"
Runtse ido usy yayi yace "shashantar da maganar nayi kurin, Allah ta damu please kadawo"
Wannan karon dariya yayi yace "dole ne ma, duk da ba haka naso ba inzo a time din da basu gama makaranta ba, amman bazan iya dakatar da zuciyata ba sai nazo usy"
Da haka sukai sallama yana kwanciya cikin yashin da bakin ruwan, abokin nashi yace "be a man mana Asaad"
Idonsa a rufe yake maganar, "inda ace kaga fuskar yarinyar koda sau d'ayane ba zaka ga laifina idan na shiga wani yanayi ba, ahakan ma ni nasan ina jarumta"
Dariya yai masa yace "miye amfanin wahalar da kanka da kake kuyi aure mana.........."Aa shareef wannan burin bana yanzu bane, inason na cika mata nata burin kafin nawa ya cika yar marasa karfi ce hasali ma wanzu wata garesu shine ya kawo sauyi kadan tattare dasu, na daukota daga gidansu zuwa namu saboda ina son na inganta rayuwarta fiye da tunanin ta, tabbas ranar farko na kamu amman na b'oye har sai naga ta cimma manufa a rayuwarta, don haka dole na zama namiji wajen jure feelings dina don samun cikar burinta"
Jinjina kai shareef yayi yana cewa, "Allah ya cika maku burinku, yadda kake fadar kyaunta akwai risk Allah dai ya kareta daga sharrin makiya"
Ranar birthday din wurin eight na dare dukai waya da usy yace masa gashi nan zaije ya dauketa, cikin damuwa yace "please usman karfe goma ka maidota gida, bana son dad'ewar nan kanaji na"
"To yah insha Allah da wuri zan dawo da ita gida"
A Daren bai bacci ba time to time ya na duba agogo, duk da akwai banbancin awanni tsakanin Nigeria da nan kasar na kusan 2 hours, sadda ya kira usy yaji sun dawo acan kasar karfe shabiyu,su kuma can goma na dare ne yaima usy kira yakai biyar bai dauki wayar ba,hankalinsa yai mugun tashi har yaji bazai iya hakuri ba ya soma kiran jannah itama bata dauka ba, hakan ya tabbatar masa basu dawo ba hankalinsa ya kasu kashi babu adad'i, wannan daren bai runtsa ba acikin daren kawai ya shirya jikkarsa ya tura sakon daukar permission asubar fari sai airport shareef ma bai sani ba.
Ayi hkr ba yawa👏🏻
Mom muhsen✍🏻