JANNAH

20

by @mommuhseen

*_💔JANNAH💔_*

_{A TRUE LIFE STORY}_


*E.W.F*


By

Mrs Bb

mom muhseen


wattpad name

Humaira3461



🅿️.......20



Usman tun kafin su tafi party wayarsa take silent bai bita kanta ba har aka kammala partyn ya dawo da jannah, gabaki d'aya yana cikin wani shauki kasancewarsu daren ranar jinsa yake daban, sannan kasan zuciyarsa yanajin tamkar yana yin abunda ba daidai ba amman kuma bai iya hana zuciyar tasa abunda take umurtarsa da yayin, wanka yayi yaci dan wani abu saboda yunwa ya kunna computer yayi abunda zaiyyi ya kashe yaje ya kwanta, ko kadan ransa bai bashi wayarsa silent take ba kuma bai dubata ba balle yaga tarin missed call din yayansa, ya dad'e bai bacci ba saboda tunanin sallamarsa jannah abun har kasan ransa yakejin sa, duk tarin yan matansa baijin wannan abun akansu anya yayima kanshi adalci kuwa???


Da wannan tunanikan barawo ya sace sa.



*****



Makara nayi sosai don ban tashi ba sai wurin karfe shidda da kwata, a firgice na diro na ruga toilet nai wanka had'e da alwallah sannan na fito na tada sallar, har nakan kance rabon dana makara sallar asuba gaskiya bazan iya tunawa ba, amman jiyan nan saboda rashin kwanciya da wuri dole gashi na makaran,lumshe idona nai nai jimmm zuwa can na bud'e su ina rarumo wayata na soma bincikar koya kira da daddare ban dauka ina bacci, amman babu alamun ma anyi kiran jikina yai sanyi sosai, banyi k'asa aguiwa ba na sake kiran wannan karon sai akace ma akashe take jinai kamar marar lafiya gaba d'aya gana cikin yana yin jin dad'i, ban fita ba duk da inajin motsin Ramma Anty sai bakwai take dawowa shirin makaranta na farayi don gaf ake da fara exams d'in third term, na mance ban sanar daku position dina ba na first term DA second, na first term nayo na goma ni banma zaci zanyi kokari haka ba duk daukana zan je gidan karshe ne, second term kuma nayo na biyar wannan karon na zage sosai ina burin ace ko banyo na daya ba to karna wuce na biyu, saida na gama shiryawa sannan na wuce dakin su shareefa na iske har an musu wanka, idasa shiryasu nayi ramma ta wuce don kammala breakfast don yayan shima fitar wuri yake.


Zuwa karfe bakwai da rabi Anty ta dawo drivern dake daukar su shareefa ya iso ya daukesu, inta duba time saboda makara in ka makara wankin toilet ake saka mutum, ni kuma bana so saboda kyankyami nake Antyn tace "lafiya usy baizo ba har yanzu"


Cikin damuwar hakan nace "wallahi kuwa Anty ko zaki kira mun shi pls...........ban ma idasa maganar ba sai gashi yai sallama kananun kaya ne jikinsa ash din sheet sai farin jeans yai kyau ainun, lumshe ido nai ina mik'ewa yace "Anty ina kwana kunjini shiru ko?"


"Da yanzu zan kiraka naji ko lafiya"


Kanshi yake shafawa yana murmushi yace, "makara nayi yau wlh, muje rankiyadad'e"


D'an zaro idona nayi kannemun ido yayi yana cewa "saimun dawo Anty zan dawo na karya banyi break ba"


Ta amsa masa cewar saiya dawo d'ina muka fice ina niye dashi nace, "yah usy babba dakai kana makara"


Wani kallo ya jefoni dashi yana cewa, "ki rantse kema yau baki makara ba"


Yar dariya nake bayan ya bud'e mun motar zan shiga nace, "aini in na makara ba laifi akan ka,"


"Saboda ni ba dan adam bane halan?"


Rufe baki nai ina dariya kadan nace, "Aa wallahi ba haka nake nufi ba, kawai dai shikenan abar zancen"


Fita mukai muka dauki hanyar makaranta kamar ba zamuyi magana ba zuwa can nace,

"Yah usy jiya...........Bros yakira ni jiya har five missed call ban Sani ba, sai yau da safen nan ma naga kiran, nasan duk inda hankalinsa yake yana nan na kirasa ban samu ba"


Lumshe idona nayi ina cewa, "abunda zan gaya maka kenan nima, na dawo na iske kiransa da wayar daya ban, na bi kiran alokacin ta shiga amman har sau uku ba adauka ba, da safen nan nasake kira ance kashe yah usy duk na damu wallahi"


Kauda kai yayi kadan kamar baiji me nace ba, tukinsa kurin yake daker ya amsa mun da cewa, "don't worry, nasan inhar ya samu kanshi zai sake nemana me zan gaya mashi?"


Ina murmushi nace, "kawai dai kace ina gaida shi........kuma kinyi kewarsa sosai hakane ko?"


Na zaro idona nace "Aa yah usy ba haka nake nufi ba, ba sosai ba kawai dai da baya nan d'in duk..........bakijin dad'i da baya nan?


Dafe kai nayi ina cewa "Aa yah usy, bansan ma me zance ba kawai dai ka gaidasa sosai shikenan"


Fuskarsa dan danan ta nuna b'acin rai har muka iso makaranta bai ce mun komi ba, hakan dana lura yasa na kifita ina kallonsa,shi kuma yana kallon side din tagar da yake zaune nai gyaran murya don yajuyo nace,"kasan me yah usy?"


Bai waigo ba ya amsa da cewar, "Aa saikin fad'a"


Na b'ata fuska ina cewa, "saika jiyo kozan fad'a"


Jiyowar yayi yana kallona idonsa yai wani kala, nace "fushi kake ko?"


Lumshe idonsa yai yana amsa mun kamar baida lakka,"ehy fushi nake menene?"


Nai kicin kicin da fuska nace, "to menai maka? Daga yin magana shikenan sai fushi,nifa ba ina nufin banjin dadin kulawarka ba"


"Naji kije karki late"


"Korata ma kake yi ko? Shikenan nama fasa yin abotar, ina son nai maka albishir cewar na amunce da friendship din amman kake fushi"


Na bud'e na fice inajinsa yana kirana ko waigowa banyi ba, da yar class dinmu muka had'u sai muka wuce assembly kawai.


*******


Banjira ya zo daukata ba ina da kud'i a hannuna sai kawai na hau napep ina adduar Allah yasa na gane gidan, cikin ikon Allah na gane hanya na sallamesa na shige ciki tun a compound d'in gidan inda asuke parking mota naga alamun kamar anyi bak'i, sabuwar motace da ban saba gani ba nagani a cikin parking space d'in, sai na tsinci zuciyata da mugun bugawa ras ras har naji k'afafuna sun kasa daukata, adaddafe na k'arasa bakin k'ofar falon tun anan naji wannan mayataccen turaren wanda kullin nake burin mallakarsa duk da kasancewarsa na maza,wani irin dokawa kirjina yai na had'iye miyau muk'ut na saka kaina cikin falon tare da sassanyar sallamata abakina, ilai kuwa sai gashi idona yai mun kyakkyawan gani wani irin sanyi naji yana ratsa zuciyata da ruhina, yayinda na kasa dauke idona daga kallon da yake mun, fuskata cike da mamaki da kuma tsananin farin cikin ganinsa saidai abun da ya fadar da gabana yana yin kallon da yake mun shine yasa guiwata sacewa, cikin sand'a nake tafiya ina ta yak'e ga yah usy nan zaune shima wayarsa yake dannawa kamar baiji sallamata ba, Anty ce ta fito daga corridor maganarta ce ta tsinke mun halin da nake ciki


"Aaa jannah kin dawo, yanzu nakema usy maganar daukoki sai gaki"


Muryata kanta kerma take nace, "ehy ganin inada kudi yasa nace bari na huttasheshi, Anty ashe bak'o mukai"


Na fad'a ina satar kallonsa murmushi tayi mun tana cewa, "gashi kuwa kin gani,muma kawai saidai muka ganshi"


Tana wuce wa kitchen, inda yake na d'an matsa na durk'usa ina cewa, "yallab'ai ina wuni, barka da isowa"


Kamar dai yadda ya saba lumshe idonsa yayi yana amsa mun kasa kasa,

"Thank you ya school din,?"


"Alhamdulillahi yallab'ai komi lafiya..........jeki had'o kayanki mu wuce gida"


Naji maganar kamar daga sama, duk da nasaj cewar yaud'in zan koma amman miye na gaggawa haka? Acikin maganarsa akwai wani abu bansan menene ba, a iyakar tsawon lokacin daya dauka baya nan ban zaci idan ya dawo zan samu wannan tarbar ba, sai na mik'e kurin daker na iya amsa mashi da cewar, "to yallab'ai"


Ganin yah usy kamar bai ganni ba yasa nace masa, "yah usy ba magana"


Murmushi yai mun kurin baice komi ba, duk naji babu dad'i jikina yai mugun sanyi sai na wuce kurin na fara kokarin cire kayana, wanka na shiga anan naga mp dina yazo sai na fasa yin alwallar na fito kurin, gaba daya kasala ta sauko mun banji dadin tarbar dana samu daga wajensa ba, to meyafaru? Ni kam dai bansan ma da zuwansa ba balle nayi masa wani laifin, kila don ya kirani ne ban dauka ba to amman ni kira nawa nayi masa a time din dana gani,haka naita sake saken zuci har na gama shafar na saka auduga na gyare jikina nasaka turaren da yah usy ya siyo mun rannan, doguwar rigace jikina ta kanti pink and golden ce sai zanen flowers da stones ajikinta hijab na saka iyakar guiwata, na hada kayana daman sauran abunda yake nawa na idasa had'awa karnayi mantuwa, ina cikin tattarawa naji vibrate din wayata saurin dauka nayi hannuna har yana rawa nace, "Assalamu alaik...........had'a kayan ne yake da wannan jinkirin?"


Abunda naji yace kenan ko sallamata ban idasa yi ba, na lumshe idona kamar nai ihu nace "kayi hkr yallab'ai gani nan........naji kitt ya kashe wayar numfashi najaa nai saurin had'a komi na dauki jikkar da school bag d'ina na fito, afalo na iske antyn inata mata yak'e nace "Anty zan tafi, nagode sosai da kulawa Allahu yasaka da alkairi, idan Abban su Shareefa ya dawo ace ina masa godiya sai watarana"


Rungumeni tayi cikin rashin jin dad'in tafiyata tace "ba yadda banyi da asaad yabarki nan ba yakiya, ki kula da kanki jannah kinjiko Ki dage da addua Allah ya kareki, Allah ya sadamu da alkairi"


Kwalla ne suka silalo mun na goge nace, "nagode sosai, mun tafi"


Na zame jikina daga nata nabisu wajen tunda daman tuni sun fice, ni kamar sunyi rigima ma nagani kowa fuska daure babu fara'a ko k'adan nidai shiga baya nayi yah usy ne yaja motar muka d'auki hanyar gida, tunda muka tafi babu abunda bake sai addua don ji nake hankalina yana tashi ainun tsoro yana kamani, mun dad'e a hanya kafin muka k'araso gidan jinai kamar na juya na koma saboda gabaki d'aya tsanar gidan da mutanen cikinsa nake, kwata kwata hankali baya kwance, dole na fito na dauki jakata ina biye dasu har cikin babban falo, kamar anyi shelar dawowata kaf d'insu suna falo don time d'in anyi sallar la'asar, idona cikin na momy duk nabi na tsure mai makon naga ta mako mun harara, sai naga tsananin murmushi akan fuskar ta daidai sadda Abba ya shigo shima, ashe duk basu san da dawowar yallab'ai ba yadda naga Abba na murnan ganinsa ya tabbatar mun irin yadda yake ji da Yallab'ai din, momy sai fara'a take tana nan nan dashi Aneesa kuwa kamar taje ta fad'a jikinsa, hindu da gundun ta fada jikinsa tana masa oyoyo sai yanzu naga murmushin sa da fara'ar sa, har gaban Abba naje na risina ina gaidashi yana cikin annashuwa yace,


"Barka da dawowa Jannah yaudai zanci tuwonki kenan"


Ina murmushi nace, "insha Allahu Abba, momy ina wuni barka da gida"


Gani nai kurin ta janyoni jikinta cikin kissa da makirci tace, "barka kadai Jannah kowa yai kewarki sosai, gidan babu dad'i bama kamar wajen girki munfi jin babu dadi"


Yak'e kurin nake nace, "Momy na dawo kenan komi zai daidai insha Allahu, Yah khalid ina wuni"


Tunda na shigo nakejin idonsa akaina mugun tsoronsa nakeji matuk'a, kamar babu abunda ya faru ya saki fuskarsa yana mun murmushi yace, "Jannah yar gudun hijira kin dawo ko, Allah yasa ba zaki sake gudunmu ba"


Na Sadda kaina daga kallon da Yallab'ai ke jifata dashi nace, "ba zan sake guduwa ba"


Na gaida Anty Anee wadda kamar ta cinye yallab'ai da kallo, fareeda ce kurin bata nan saida aka natsuwa sannan Abba ya fara magana cikin natsuwa da jawo hankali,


"Dukkan abunda ya faru naji labarinsa, bana son tado da abunda ya wuce saboda gudun b'acin rai, ina fatan komi ya wuce daga yanzu, Jannah dai aiki tazo yi don Allah ku barta tayi aikinta sannan bance ku maidata baiwa ba saboda itama mutum ce kamar kowa, sannan daga yau albashin ta ya dawo wuyana bana son na sakejin wata rigima ta sake bullowa don Allah, ke uwace Hafsat ki zama mai saka ido akan komi kiyima kowa adalci akan aabunda kikaga yayi wanda ya dace ki dauki mataki, ku kuma nan dukan ku y'ay'an mune dole ku kasance masu yimana biyayya kuma masu bin dukkan umurnin mu,don haka bana son sakejin wani abu ya taso kai usman kaba momyn ku hakuri akan abunda kayi mata yanzu nan"


Yah usy kamar zai bindiga yace, "kiyi hkri bazan sake ba"


Ta na murmushi ta amsa mashi da cewa, "haba my son karka damu ai na huce na yafe maka"


Abban yace, "magana ta k'are Jannah kici gaba dayin ayyukan da kika faro, daga yau ba wanda zai sake takura miki kinji ko, anshi nan wannan katina ne inhar kina da matsaka ki sameni ki gaya mun karkiji komi"


Na amsa cikin girmamawa ina masa godiya yace, "kuna iya tashi kutai na sallameku"


Zuruf na dauki jakata nai cikin gida bangarenmu, ina aje jikkar naji karar wayata yallab'ai nagani ina dauka muryarsa kamar dazun yace,


"Ki sameni bangarena yanzun"


Ya kashe batare da yajira mai zance masa ba.







Mom muhseen✍🏻