JANNAH

21

by @mommuhseen

*_💔JANNAH💔_*

_{A TRUE LIFE STORY}_


*E.W.F*


By

Mrs Bb

mom muhseen


wattpad name

Humaira3461



🅿️.......21



Kafafuna naji sun mun nauyi na kasa daukar wannan sabon abun da yadawo dashi, menai masa haka da zafi? yadda nake d'okin dawowar sa kullin ban zaci inya dawo za abunda zai zo dashi kenan ba.


Ajiyar rai nayi sannan na kalli fuskata a mudubi bansan me bake kallo akai ba, abu guda na sani shine inajin wani nauyi a kirjina duk akansa tsawon lokacin da yatafi ban huta ba haka zuciyata bata huta da tunanin sa ba, shine ya dawo zai zo mun da haka?..........jin wayar na sake daukar ruri yasa nai firgigi daga dogon tunanin da nake, ashe fa cewa yai naje shaf na mance cikin sauri na dauki kiran bakina na rawa nace, "kayi hak..........ko ni zanzo in sameki?"


Na lumshe idona inajin kamar nai kukaa cikin karyayyar murya nace, "don Allah kayi hakuri yallab'ai gani nan"


Bai kulani ba ya kashe wayar sa, kwalla naji sun cika mun ido duk yadda bake karfafa zuciyata akan kar nayi basuyi shawara dani ba sadda suke layi akan fuskata, gogewa nake ina fita daga dakin amman hakan bai hana wasu sake zubowar ba, har naje bakin k'ofar dakin suna silalowa daker nai karfin halin rik'esu na share fuskar sannan na tura zan shiga naji muryar sa cikin tsananin b'acin rai yana cewa, "saboda ban yarda da kowa ba sai kai yasa na damk'a amanarta hannunka, meyasa zakai mun wasa da hankali usman?"


Cikin sanyin murya yace, "kayi hkr Bros bazan sake ba"


Sallama nayi na shiga saboda rashin shigar kuma zai sake janyo mun wata damuwar,


Da yah usy muka fara had'a ido yai saurin sadda kanshi k'asa, yallab'ai yana cikin kujera ya dage kanshi sama ya rufe idonsa na sakeyin sallamar, yah usy ya amsa mun na samu gefe guda daga k'asa na durk'usa na soke kaina k'asa kurin ina tsifar yatsuna.


Zuwa can daya mula ya mulmule yace, "kana iya tafiya,"


Tashi yai cikin b'acin rai ya fita daga falon yabarni dashi, shakar kamshin turarensa kad'ai da nake ni kadai nasan illar da yake mun acikin raina ganin kamar bai san nazo ba yasa cikin rawar murya da nasha kuka nace,


"Gani yallab'.........na ganki Jannah! na ganki!! Saida kika gama raina mun wayau sannan zakizo ko? Yar tafiyar danai har yasa kin waye haka ban sani ba, usman ya bud'e miki ido ko?"


Yadda yake zuba fad'a da masifa yai masifar tayar mun da hankali, dan danan na rikice ina shashshekar numfashi girgiza kai kurin nake, ina jan yatsuna idona kuwa tuni ya cika tab da ruwa bakina har rawa yake nace,


"Yallab'ai ka.....kayi hak.....hakuri wallahi ba haka ba....bane don girman Allah...........will u keep quiet?"


Runtse idona nayi yayin da ruwan hawayen dake ciki suka samu damar zuba, na sauke kaina kasa ina shashsheka ina jan numfashi jikina sai rawa yake, tunda na had'u dashi bai tab'a daga mun murya ba sai yau,sannan kuma gani mai tsananin tsoron shouting bana son fad'a gigicewa nake,


Shiru yayi yana jin kirjinsa yana wani irin zafi, a mugun tun zure yake da ita duk da yasan ba itace ummul aba'isin faruwar komi ba, amman ta bada goyon bayanta duk dokinsa da zalk'insa na son dawowa don ya ganta ashe abunda zai tadda kenan, ya dauka tsawon wannan lokacin zatai mugun kewarsa zai ga wani canji sosai tattare da ita,amman shine zai tadda kusancin ta da kanensa har yafi wanda take dashi, babu abunda yake tun zirashi irin pics d'in da yagani hauka ne kawai bai ba, wani irin zafi yakeji aransa, shashshekar kukanta dake shigar masa zuciya yakejin wani iri tsikar jikinsa ke wani irin tashi, had'iyar abu yai ga mak'oshin sa yana sassauta zafin daya d'auka muryasa ta shak'e yace,


"Kimun shiru"


Goge hawayen nake ina kerma shashshekar ce na kasa tsayar da ita, haka hawayen ma sun kasa tsayawa, wani abu nakeji ga kirjina ya kasa wucewa.........."meke tsakanin ki da usman?"


Wani mugun bugawa kirjina yayi sai wasu sabbin hawayen suka fara zuba, "yallab'ai Yah usy........idan na sake jin wannan sunan saina sab'a miki, ki kirasa da usman d'insa"


Ina shashsheka ga ruwan hawaye kamar an bud'e famfo nake cewa, "kamar yayanmu na daukesa bacin matsayinsa na kanen ka da yayana babu abunda ke tsakanin mu, dukkan kulawar da kace yaban ya bani bai tab'a cutar dani ba, wallahi yallab'ai Yah usman bai canza matsayina a wajensa ba"


"Wad'annan hotunan kuma fa???"


Ya jefo mun wayarsa batai masauki ko inaba saiga kirjina, azabar da naji ce tasa nace da dan karfi "wayyo Allahna!!!" Ina dafe kirjin..........saida kurin na jishi gabana "innalillahi ta dokeki ko? Sannu ban san zata dokeki ba I'm sorry please bana sane,"


Tattare kafafuna nayi na saka kaina cikin guiwata kurin na fara rera masa kuka mai cike da kunan rai, ba kadan wayar ta dokar mun na fulanina ba wani irin zogi naji sukeyi,jinai inba kukan nai ba zan iyarasa numfashina bacin zafin da nakeji turarensa yazo yaimun k'ak'agida ga zuciyata, ni kaina nasan kukan da nake ya isa ya rud'a duk mai saurarensa, tabbas ya rud'en ba abunda yake yace fad'a face,


"Jannah, Jannah please stop crying, Im very sorry I don't mean to hurt u, please kinji"


Tunda uwata innamu ta haifani ban tab'ajin abu irin wanda nakeji yanzu ba, shi kanshi kukan da nake naji ya canza sauti sake makale jikina nayi, saboda yadda nakejin wani yammmm, bai fasa maganar ba kamar ba shine yake mun ihu akai ba..........


"Jannah don Allah, please kiyi shiru I'm very sorry, nine na Saki kuka ko?"


Kaina na d'aga masa kurin ya lumshe idonsa yana jan numfashi, "to kiyakuri, stop crying kinji bazan sake ba"


Tausasan kalamansa dole suka saka kukan ya dauke wanda bansan ya dauke ba naji dai nayi shiru, sai ajiyar zuciya nake ahankali duk fuskana tayi zufa nak'i dagowa daga d'uk'en da bake, zaman dirshen yai gabana yana sauke ajiyar zuciya ahankali har inajin ta cikin kunnuwa,


"Jannah"


Naji muryarsa da babu kwari acikinta ya kirani, can kasa na amsa mashi yasake cewa "dago fuskarki"


Kunya nakeji bazan iya kallon sa ba, kukafa nasha sosai gabansa taya zan iya dago kaina in kallesa, "bazan iya hana kaina dago da fuskarki ba muddin baki dago ba"


Jin haka yasa ba shiri na d'ago amman ko kusa ban kallesa ba, ajiyar zuciya kurin nake sauke, baisa sadda ya furta, "ya subhanalallah!"


Zufar da tai yasaka duk gashin ya kwanta na goshinta lashes dinta sun manne sun kwanta, lips dinta sunyi jaaa gaba d'aya wani annuri take fiddawa, runtse idonsa yai kamar zai haukace ya danne yana cewa "bani wayar"


Ahankali na dauko na mik'a masa.


Ansa yayi yana ajeta gefe saboda baya son sake ganin wadannan hotunan, sune suka gigitashi haka bai san zai iya mata fad'a sosai ba amman tsananin zafin da yakeji idan ya tuna yadda akai hotunan kamar zai haukace, shiru mukai mu duka nidai sai ajiyar rai nake gashi nayi mugun takura so nake ya sallameni, don zan iya rasa kaina anan gashi kuma banga alamar zai ce na tafi ba, muryata nake gyarawa don ta shak'e can kasa-kasa nace masa,


"Zan je nayi aiki"


Na fad'a ba tare dana dubi inda yai daman dirshen ba, tazarar mu babu nisa daga inda yake naji ya mun magana cikin sanyin rai,


"Zaki tafi idan kin dago kin kalleni,"


Kamar ya sake tun zirani na maida kaina cikin guiwata kawai, don wallahi bazan kalli cikin idonsa ba bacin ya gama mun masifa yazo ya sani kuka shine zai tilasta mun kallonsa, me hakan zai amfane sa.


"Au shine kika maida kanki,? Idan usman ne ai bazaki k'i kallonsa ba tunda gashi nan a pics dinku kun yi kyau"


Dajin yadda yai maganar abun yana masa ciwo, ban san me zance na kare kanmu ba, nidai nasan har zuciyata babu abunda ke tsakanina da yah usy,


"Wallahi summa tallahi babu abunda ke tsakanin..........tashi ki tafiyarki please"


Ya katseni daga maganar da nake, ban hakura ba naci gaba da cewa "Yallab'ai ko Anty munirat zaka tambaya..........I said get up!!!"


Aguje na fita daga bangaren nashi har in bangazar Aneesa ban sani ba, ban tsaya bi ta kanta ba nai wuce wa ta dakina, gado na fad'a ina sake rushewa da kuka matsananci ban ankara ba naji ankira magruba, saurin tashi nayi naje na wanke fuskata na canza kaya xuwa na aiki sannan na fito zuws kitchen nasan Abba yasaka ran cin tuwona yau, hindu muka had'u a hanya ta biyoni har kitchen d'in tana mun magana.


"Yadai malamata, naga fuskarki tayi jaa kamar jan kosai"


Murmushi nayi ina kunna gas na dora ruwan tuwan na bud'e frig don duba abunda ke akwai,nake cewa "ko kuma jan fanke ba"


Darewa tayi bisa cabinet d'in kitchen din tana cewa, "nifa ban gane ba, yah usman nacan na k'unci ke kuma naga fuskarki alamun kinsha kuka mekuke b'oyewa?"


D'anyen kifi da kayan miya na fiddo inso nayi masa miyar kub'ewa danga da kifi, na fara gyara kifin ina wanke shi nace, "babu komi fa,kin cika bincike"


"Ba wani bincike gaskiya nakeson sani, wallahi jannah duk wanda yaga idonki saiyace kinyi kuka karki b'oye mun pls,ki daukan yar uwa kuma kawarki,wata kila zan iya baki shawara"


Maganarta yasa naji kwalla sun silalo mun, nai saurin gogewa saida na gama wanke jifin na tsaneshi, na hau gyaran kayan miya zanyi greeting dinsu ta ansa tana yi mun, na dauko kub'ewar ina gurzawa kamar bazance komi ba na daure nace, "Hindu yallab'ai Asaad ne, na kasa fahinttar abunda yake zarginmu dashi, tunda ya sauka yau yake ta d'acin rai yanzu ba dad'ewa daga wajensa nake fad'a ya rufeni dashi, wai yah usy ya bud'e mun ido meke tsakanin mu, wallahi hindu babu komi tsakanin mu, shifa ya damk'a amanata hannunsa meyasa zayyi wannan abun, dan uwansa ne fa shin zaiji dadi yaji irin zargin da yake mana?"


"Kibar kukan hakanan don Allah, Yah Asaad tsoro yakeji Jannah koda bashine ba ko waye dole zaiji tsoron faruwar wani abun, ke ba kamar kowacce mace bace na shaida hakan, Allah yai miki kyawun da ko mace yar uwarki zataji kin dauke hankalinta, inaga namiji ba kowane namiji ne zai iya kauda kanshi akanki ba, kuma kina da tabbacin cewar shi yah usman bai da wani feeling akanki? Kin shiga zuciyarsa? Karkiyi saurin daukar zafi da Yah Asaad don Allah shi yana ganin akan daidai yake, duk sadda mukai waya dashi baida wata magana sai cewar kuyi karatu hindu shine kadai gatan da zamu iya tsaya maku kanshi, karatun y'a mace yana da matukar muhimmanci shiyasa nakawo jannah nan gidan ba domin aiki kad'ai ba, bana son tun kuna kananun ku soyayya ta rude maku idoku kasa yin karatu in kukai hakuri komi yana da lokacinsa, acikin kalamun sa na fahimci Yah Asaad baida wani buri a kanki Jannah face yaga kinyi karatu tuk'uru baya son wani abu ya d'auke miki hankali daga wannan burin"


Bada hankalina kad'ai nake sauraren hindu ba harda zuciyata da dukkan kunnuwana, kuma maganganun sun ratsani ainun nace mata "Hindu wallahi ko kadan Yah usy bai tab'a nuna mun yana sona ba, balle har bakisa yakai ga furtawa, yana bakin kokarinsa wajen ganin na iya dukkan abunda ake koyar dani, da taimakon sa na samu har nakai matakin dauko position dinda ban tab'a tsammani ba, nidai har raina nasan Yah usy ba sona yake ba"


Murmushi tayi tana cewa, "shikenan tunda kince haka, lokaci shine xai nuna mana hakan amman don Allah karkiji haushin Yah Asaad shine yake kan daidai"


Kusan tare mukai akin dinner da hindu, bayan na gama tuwon Abba muka d'ofa jullof d'in jallar makaroni mai kwai da alayyahu tasha magi sai k'amshi take, a ranar banga wani canji na b'acin rai akan fuskar kowa ba hasali ma santin girkina kawai ake, karma ace Abba don har kyauta yayi mun yaban dubu biyar, kud'in da nake samu bana komi dasu illa tarawa inaji araina kamar akwai ranar da zasuyi mun amfani, har albashina bana tab'a komi sai d'an abunda ba'a rasa ba, wanka na sake na gyara jikina nai shirin kwanciya sai ga kiransa................





Mom muhseen✍🏻