64-65
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
64_65
"Omar yana komawa side dinsa ya fara tunanin abinda suka faru shida imaan, tsaki yyi a fili yace komeyasa na dauke ta ma? Mtwss haka yyi tayi abunda.
"Bayan kwana biyu yau ta kasance monday, sosai tayi kyau cikin uniform dinta, a gurguje taci abinci, mummy tace farooq tashi maza ka kaita. "Farooq yace toh. "A mota sai hira suke abinsu, har ya kaita skul, kafin ta fita farooq yace kiyi kr2 d kyau kinji koh. Imaan ta gyada kai, murmushi yyi mata sannan ya daga mata hannu, har ta shige cikin class sannan ya tada mota yabar wajen. "Koda aka tashi farooq yana office Amman hankalin sa nakan agogo dan mummy tace ya dauko ta, hakan kuwa akayi tun karfe daya tayi masa a skul din. "Imaan ya tarad bakin gate, fitowa yyi a mota, imaan na ganin sa ta taho da gudu tayi hugging dinsa. "Farooq ya shafa kanta yace imaan ya skul? Imaan tadan ta6e baki tace lpy. "Farooq yace toh muje gida nasan mummy nacan na jiranki, imaan tayi murmushi sannan ta shige gaba. Shima zagayawa yyi ya kunna motar suka bar wajen. "Kullum farooq shike kaita ya dauko ta hakan yyi wa omar dadi dan tun Monday ya kirkiri cewar yanada emergency, dan kar mummy tace shi zai kai imaan skul. Yanxu kuwa ya lura mummy ko kadan batayi masa zancen imaan saima maida farooq d tayi driver'n karfi d yaji.
"Yau data kasance weekend ne, duk suna gida, yanxu haka suna falo har daddy hira suke sosai hankalin su kwance, daddy yyi gyaran murya hakan ya tabbatar musu da yanada magana kenan dan haka sukayi shiru suna sauraron sa. "Daddy ya kira sunan omar d farooq gaba1 suka amsa a tare, "daddy yace na lura Ku Sam babu zancem aure a gaban Ku, nayi muku magana kunyi biris d ita koh? Dukkansu suka sunkuyar d Kansu kasa, "daddy yace idan bazaku fitar d mata ba ni zan kawo muku matan aure, omar yyi saurin kallon dadday da kyar ya iya furta No daddy pls, daddy yace toh zaman me kuke da vazakuyi aure ba? Kalle Ku fah dukkan Ku zaku kai 29, da zarar kunje 30 kun fara tsufa. Shekarun ka yana jaa, "Omar kansa a kasa yace kayi hakuri daddy zamu kawo maka mata, Amman a bamu nan d wani lkci. "Daddy yace kamar yaushe kenan? Karfa Ku jaju6omin 'Yar talaka, sai alkcn mummy tayi saurin dago kanta ko kadan batason Kalmar da daddy yake furtawa yaransu, imaan dake wajen kuwa sunkuyar d kanta qasa ta sakeyi tana me jinjina lamari irin na daddy. "Daddy kuwa sarai yasan mummy batason Kalmar Amman y kauda kansa kawai yana meci gaba da mgn. "Sai alkcn farooq yace daddy duk yanda kace ai hakan zamuyi insha Allah. "Daddy ya gyada kai yace wannan shine karo na farko, karku bari na sake magana ta qarshe dan saidai Kuji an daura muku aure da wasu. "Gaba1 suka gyada kai.
"Da yamma imaan taci kwalliya ta kalli mummy dake kan gado tace na shirya mummy, mummy tace toh jeki ki kiramin Omar, imaan tace toh. "Side dinsa ta nufa. Tayi sallama saidai taji shiru, shiga tayi taga baya falo, dan haka ta karasa dakinsa. "Kwance ta ganshi yyi shiru d alama y tafi duniyar tunani dan haka ta buga kafansa da sauri ya mike yana Binta d kallo, duk Wanda ya kallesa yasan ransa a bace yake, tasowa yyi imaan ta matsa da sauri, matsowa ya sakeyi ta sake matsawa ganin yanda yake binga da kallo dukta tsorata da shi. "Omar kuwa bai bar matsawa gareta ba har saida ya hadata da jikin bango har numfashin su na haduwa.
Nuceey luv😘